Showing 57001 words to 60000 words out of 81438 words
Chapter 20 - BURI DAYA Complete Hausa Novels By Mamuhgee .pdf
idan Kuma kinason kwada qarfin ikon danake dashi ne akanki
da rayuwarki ki gwada zakisha mamakina sbd inanan bawai canzawa nayiba.....
Fixgewa tayi itama cikin Hana kukanta zuwa tace"
Bana magana akan rayuwar kowa da canzawar kowa anan Ina magana akan rayuwatane da
abinda Naga damar Yi da Wanda Naga damar bari,
Idan kana maganar baka canza ba to Ni na canza ba Nadiya bace wannan ND NOAH ce...and
stay the hell out of my life.....
And bana buqatar ganin qarfin iko ko dukiyan dakake dashi sbd dama Abu ne nasa kaina sbd
tunanin anrabani da abinda nakeso fiyeda tawa rayuwar Ashe bansaniba shine ya rabu Dani
Dan haka Ni kaina daga yau na fita daga fadanda Babu ruwana zanje na fuskanci Wainda suka
cancanci qaunata da lokacina.
Tana Gama fadar hakan ta fice da gudu sbd wani irin kuka Mai tsananin nauyi da qarfi dakeson
zuwan Mata tana dannesa numfashinta har sarkewa yakeyi jikinta Babu inda baya rawa.
Kasa motsi yayi sbd duk jijiyoyin jikinsa sun daure da mamakinta da fargabar tashin hankalin
maganganunta dake bayyanarda tsantsar radadin baqin cikin barinta datake ganin yayi.
Securities Basu wani hanata fitaba tana fita ta tari wata taxi data kawo ta fada kawai sai
alokacin tasake wani irin kuka Mai tsananin cin Rai da damuwa tareda ciwon abin datake ji cikin
ranta.
Har Sukayi nisa Bata saniba Saida yasake tambayar inda zai kaita ta bude baki daqyar tareda
fada masa tana share hawayenta tareda qoqarin barin kukan duk da tasan bazata iya barinba.
Yana Isa qofar mansion din ta fito ahankali tareda ce masa ya jirata tafito.
Ciki tayi tana qoqarin maida kukan dayake sake taso Mata sbd fammah data hango tsaye jikin
qofa tana knocking qofar side din am tana kuka sosai kamar zata shide.
Kasa riqe nata itama tayi tasakesa tareda wucewa ciki da gudu tanajin inama duk shekarun nan
a gaban babanta ta zauna tayisu da tabbas bazata cutatu yanda takejin ta cutatu yanzu ba.
Sama ta haye tahau hada duk wasu kayanta tafara jawo luggage dinta tana share hawayenta
dasuka qi tsayawa a Palo taci Karo da am da fammah tsaye dukkaninsu Babu Wanda baibata
tausayiba take zuciyarta tasake karyewa ta silalo hawaye masu radadi ta rintse idanuwanta ta
bude saitaji takasa kallon fammah ga am da zuba Mata idanuwansa dasuka shanye sukai jajir a
dare guda ya lalace yakoma tamkar asalin Dan giyar dayayi shekaru ashirin Yana sha,
Hawaye ne cike da idanuwansa Saidai Basu saukoba sbd muguwar karayarda zuciyarsa da
gangar jikinsa suke ciki,
bude baki tayi daqyar ta furta"
I'm leaving......
Ba zato qafafuwansa Suka sare ya zube gabanta tareda riqo qafafuwanta cikin wani irin yanayi
na kuka da tausayi yace"
Baby Dan allah karki barni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,
I can't live or survive without you,
Karki tafi kibarni a wannan halin I will die if you leave me.... please baby idan na Miki wani laifi
ne forgive me Dan Allah please baby don't leave.....
Kuka tasake sbd akaro na farko daya fara Bata tausayi musamman yanda fammah ke jansa
tanason tayar dashi cikin tsananin kuka Yana kwacewa Yana surutai da kuka sosai..
Cikin tsananin kuka itama ta janye qafafuwanta ta ja Baya yayi saurin rarrafowa Yana wata irin
magiya gabaki daya baya cikin hayyacinsa.
Cikin tsananin kuka fammah itama ta zube gefen Dan uwanta ta dago ta kalli nadey din tana
kuka tace"
Dan Allah Ina roqonki daki rausayawa rayuwata ki tallafi Dan uwana dashine kadai ya ragemin
a yanxu,
Bansan wane sirrine yake boye a tattareda saninki da familynaba Amma Dan Allah kiji tausayin
maraicina ki tallafi Wanda zai tallafi tawa rayuwar.....
Girgiza Mata Kai nadey tayi hawayenta na sake gudu ahankali ta furta"
I'm really sorry fammah...
Tana fadar haka ta fice da sauri tana sakin siririn kuka tana jiyo ihun fammah na Kiran sunansa
Amma Bata tsayaba sbd zuciyarta data fara karyewa alhalin itama tallafin take buqata a tata
kuncin Wanda zuwanta gaban mahaifintane kawai zai yaye matashi.
Taxi din tashiga sukabar gurin.
Direct gidansu Annah yakaita canma Basu gane kantaba tana Shiga ta tattara sauran kayanta
suna tayata hada kayanta data kasa hakuri anan ne tasaki kukanta Mai qarfi datake riqewa
mum din Annah da Annah na gefenta Suka Bata damar tayi kukan duk dake cikin ranta kozataji
sauqin zuciyarta.
Sosai tayi kukanta saidataji sauqin nauyin datakeji a qirjinta kafin ta shiga toilet tayo wanka tana
fitowa takira JJ da wayan annah ta shirya cikin skinny jeans fari da farar loose chiffon top ta
Dora black full-length jacket da black scarf ta fito da kayanta daidai isowar JJ kallo daya
yamata yaji nauyin zuciyarsa ya qaru sbd idanuwanta dasuke a kumbure musamman data
gansa sai idanuwanta suka sake cikowa da hawaye tun kafin yayi magana ahankali da rawar
murya ta furta"
Dady j I can't handle this anymore,,,inason ganin babana Dan haka it's time for me to go
home....
Da sauri ya qaraso gabanta cikeda kulawa Yana cewa"
Baby please karki dagamin hankali tell me yafaru?
Meya sameki?
Waye ya daukeki?
Ina ya kaiki?
Meya Miki?
And....and..fuskar Wanda ya daukeki Dana gani was it re.....
Yes dady j shine,Yana nan da ransa Bai mutu ba Muna wahalarda rayuwarmune akan Wanda
baisan munayi ba....
Da manyan idanuwansa yake kallonta ko qyaftawa yakasa Yi shima duk jarumtarsa zuciyarsa
bugawa takeyi sosai sbd kukuwar yarda da zancen,
Girgiza kansa yakeyi tareda juyawa da qarfi ya daki iska Yana sake girgiza Kai sbd wannan
zancen ya girmi tunaninsa Kai tsaye Rana tsaka ace Wai sarki Bai mutu ba,
To meyesa ya boye musu kansa???
Idanma Bai nemi kowaba shi Bai kamata yakasa nemansaba qarin abin tashin hankalin shine
suna taredashi Bai sanarmusuba Kai this is so confusing.
Wani murmushin takaici tasaki tace"
Shall we???
Dago jajayen idanuwansa yayi ya kalleta yaga yanda fuskarta tayi jajir ta kumbura take yaji
ransa yaqara baci Saidai shikam yau zasuyi face to face da sarki yau zasuyi magana as man to
man.
Direct airport yakaita Babu me magana acikinsu harsuka karbi tickets ta juyo ta kallesa zatayi
magana shima daqyar yarigata da cewa"
Karki damu yau zuwa gobe zamu Gama claiming komai a gobe zaa buga sunayen Noah's a
kamfaninsu da mansion dinsu da angama zandawo jibi insha Allah.
Jinjina masa Kai tayi tareda juyawa ta shige shikuma ya koma.
Bata fi mintuna ashirin ba aka Kira flight dinsu ta tashi ta shige.
Yamma sosai ta Isa starling city dad da kansa yazo daukarta sbd yayi wata da JJ yafada masa
komai dake faruwa gameda haydar.
Ji yayi duk duniya farin cikinsa yadawo Sam kasa boye farin cikinsa yakeyi tuni labarin yafara
yaduwa a cikin abokanan mu'amalarsu ta business har zancen yafara fita.
Duk murnarsa raguwa tayi dayaga halinda nadey ke ciki yafara qoqarin danne murnarsa da
farin cikinsa Yana duba yanayinta itama sbd tabbas wannan abin abun dubawa ne ga miji yabar
matarsa tsawon shekaru Babu waiwaye.
Da gudu baby z tazo ta rungumeta itama cikin tsananin kewa da soyayyar 'yarta ta rungumeta
tareda rintse ido hawaye na silalo Mata.
Nanny Nancy ma rungumeta tayi cikin kewarta dasukayi suka shige har dakinta har lokacin
baby z na maqale a jikinta itama Sam takasa sakin 'yarta.
Wanka tayi tayi sallah tana qoqarin danne komai tasake dasu Suka hau labarai dad ma sakewa
tayi taqara masa bayanin halinda ake ciki gameda mansion dinsu Dilla data siye harda na
Nigeria and dad Insha Allah I will be going back to Nigeria next week zanji da maganar claiming
takardunsu na can da muka karba.
Kallonta yayi cikin farin cikin ganin Bata wani dauki abin da zafi ba yace"
Ok allah yakaimu Saidai idan kinje ku zauna gidan Dr sayyid tunda nasan za'ayi renovating
gidan Yaya dattiya ne sbd nasan no matter what Yaya bazai iya barin anguwar nan ba.
Murmushi tasaki ahankali sbd tuno irin burikan babanta musamman na zama sarkin maroqa.
Da daddare da 'yarta ta kwana bayan tayi waya da JJ.
JJ kuwa daga airport gida ya wuce ya shiryo cikin wasu irin suits yasa aka Kira media akan
yaune zaa karbi sunan dazaiyi replacing dillas Wanda yakeson acan ne zai fuskanci sarki
Sarki ya fuskancesa.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan
numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863*
*_Mamuhgee37_*
Cikin gaggawa fammah tafara ihun Kiran sunayen masu aikin gidan Suka fito amatuqar rikice a
gigice take cewa su kirawo Mata Dr kar am ya mutu ya barta.
Aikuwa amatuqar gigicen Suka fara neman wayar Kiran Dr din daqyar Suka samu tashiga Yana
dauka Suka sanar dashi yace gashinan zuwa.
Da kanta ta kamashi tareda taimakon su Jenna Suka kaisa bedroom din mum dinsu dake
kusadana dad.
Kasa zama tayi takasa tsayuwa tana kaida kawo cikin tsananin tsoro da tashin hankali.
Kafin zuwan Dr hankalinta yakai qololuwa gurin tashi sbd dad dinsu daya farfado adaidai
wannan lokacin shima Saidai basusan ya zasuyi masa su rabasa da oxygen dinda ke maqale a
fuskarsaba.
Gaban dad din ta zauna tareda riqo hannunsa cikin tsananin farin cikin farfadowarsa tana Kuma
hawayen kwantawar Dan uwanta.
Isowar Dr ce tasa tayi saurin miqewa ta basa guri yafara zare oxygen din dad Yana yabawa da
yanda ya farfado lokaci daya kafin ya juya gurin am dake buqatar taimako yahau dubasa.
Sosai ya dubasa tareda dubarunsu na likitoci saigashi ya bude idanuwansa dasukai jajir Yana
qoqarin tashi fammah da Dr na dafesa cikin kulawa Dr yace masa Yana buqatar hutu a yanxu.
Wani irin wahalallen kuka ya sake tareda qanqame hannun fammah dake kuka tuni yace"
Fammah meye laifina????
Meye laifina danake Mata mugun so irin wannan??
Fammah kinsan radadi da ciwon danake ji a zuciyata sbd ta tafi ta barni??
Ciwo nakeji anan sosai"""yafada Yana dafe qirjinsa dake masa tsananin ciwo musamman sbd
alcohol dinda dayasha sbd Sam baya Sha baima taba shaba.
Ahankali fammah ta rungumesa tareda lumshe ido hawayenta na sake gudu sbd batamasan
mezata iya cewa ba.
Bayan tafiyar Dr gurin dad dinsu Suka tafi acan Suka zauna tasa aka kawo Mata abinci Mara
nauyi ita tayi feeding dinsu su biyun tabawa kowannensu magani anan Suka koma bacci tare ta
miqe ta kashe musu aircon ta fita.
Dakinta taje ta tube tayi wanka daqyar tayo alwala tazo tayi Sallah Wanda zamanta da nadey
ne tasan tayi sallah akan lokaci Kuma duk lokaci idan yayi sbd itadai bazata iya tuna lokacinda
iyayenta Suka taba cewa tayi sallah ba kokuma idan tayi shiyasa so da dama idan tayi to wani
lokacin Kuma idan lokaci ya wuce shikenan saikuma gobe Amma zama da nadey tun tana
basarwa harta fara Jin kunyar nadey na sallah itama musulma kamarta Bata cikayiba sai hakan
yasa tafara dagewa tanayi cikin lokacin Kuma ko yaushe,
Tun abin na gasane hartazo tasaba ko nadey na gida ko batanan idan lokacin sallah yayi yin
sallarta takeyi.
Tana Gama sallar ta duba agogo taga dare yayi sosai saitayi kwanciyarta agurin tana tunanin
yanda rayuwa ta juya musu baya lokaci qanqani.
Washe gari tunda safe abinda yafara yaduwa a gidajen tv da jaridu shine makeken sunan
NOAH'S PUBLICATIONS daya bayyana baro baro a saman makeken kamfanin dillas dakuma
qaton mansion dinsu suna ciki basusan ancire sunansuba ansa Noah's.
A tv Suka fara gani da safen Dilla yayi zuru ya qurawa tv ido sbd balain dayake ciki yafi qarfin
magana sbd mamakinsa akan kenan nadey Noah duk sune su JJ tazo ta yaudaresu sun karbe
musu komai.
Am kuwa wasu irin hawaye ne ke gangarowa daga idanuwansa jikinsa na wani irin rawa
ahankali fammah tasake qanqame hannuwansu su duka biyun sbd tana zaune ne a tsakiyansu.
Babban tashin hankalinsu shine inda zasu zauna sbd yau Dole zasu bar gidan gashi kayan
jikinka kawai kake fita dashi.
Cikin wani irin yanayi na sanyi da tsananin damuwa Dilla ya kalli fammah zaiyi mgn ta miqe da
gudu tabar gurin tana kuka.
Dakinta taje ta hada kayanta cikin akwati guda da duk abinda yakeda amfani da mahimmanci
agareta.
Daga nan dakin dad taje shima ta hada masa komai a akwati daya hakama mum tayi Mata
akwati daya ta jawosu ta fiddo dasu ta nufi dakin am shima ta ha'do masa nasa takawo palon
tana kallon yanda am ke kuka sosai cikin baqin ciki da radadin da zuciyarsa ke ciki.
Dad ma daka kallesa kasan kowane irin lokaci zuciyarsa na gap da bugawa.
Passports dinsu ta fitar ta dauki wayarta ta fita harabar gidan takira tayi musu booking tickets
din Daren yau dazai tashi zuwa Nigeria.
Dawowa tayi ta zauna tsakiyarsu tareda sakin murmushi Mai ciwo ahankali tace"
Wannan wata jarabawace daga ubangiji mu karbeta da hannu bibbiyu insha Allah it will pass.
Suna nan zaune jigum jigum akazo Basu tunin lokacin fitarsu gidan yayi fammah ta riqo dad da
har lokacin baida wani kuzari suka fito am kuwa idanuwansa sunyi jajir ko dagowa ya kalli tarin
media dake gurin baiyiba Suka fito mansion din sai daukarsu hoto akeyi.
Black anaconda fc din haydar ce ta Sha gabansu tareda motar police biyu a bayansa.
Cikin wasu black Armani wears yafito motar fuskarsa sanyeda Benz dark shades ya qaraso
gabansu ya tsaya daga gefen JJ dashima yake tsaye gabansu cikin Gucci's.
Kallo daya Dilla yamusu numfashinsa ya sarke yafara Jan numfashi daqyar Yana dafe qirjinsa.
ganin Yana kokuwa da numfashinsa yasa fammah saurin riqosa am kuwa motar police dinda
aka bude aka fitoda mum dinsu data sauya kamanni gabaki daya gefenta kuwa mayor ambryam
ce cikin shigar kayan sanyi.
Da gudu yayi kan mum din ya qanqameta Yana Kiran sunanta
Itama kukan takeyi sosai....
Jin fammah na Kiran sunan dad din yasa Suka juyo da sauri Suka yo kansa cin tashin hankali
am ke shafa bayansa Yana kirana sunansa tareda nuna masa yaja numfashinsa da qarfi.
Cikin wata irin murya me Kama da rugugin damuna haydar yakoma zakinsa yace"
Ku daina wahalar ceton Wanda tasa tariga tazo qarshe rufe sauran babinsa zamuyi kamar
yanda yasan yasaba rufe babikan wasu....
Dikko ka miqe tsaye da kyau ka fuskanceni sbd yaune zanbaka bugun zuciyarka na qarshe.
Ka godewa Allah haryanzu sa'a na tareda Kai sbd JJ and....kasa fadar sunanta yayi ya lumshe
ido yacigaba da cewa"
Sun lalata rayuwarka batareda Ni na qaddamar da abinda na shiryowa rayuwarka ba Wanda
zaisa ka dauki makami da kanka ka dauke rayuwarka da kankaba,
Kaji dadi sun baka hukunci Mai sauqi sbd Dilla da nine kasamu hukunci daga gareni toda ko
kare bazaici namankaba sbd nayi niyar mayarda rayuwarka mafi qanqancin rayuwa wadda
dabba saiyafi daraja a idanuwan duniya Amma saigashi kasamu hukunci Mai sauqi daga
familyna Wanda ko hakan ya isa ya tabbatar maka da cewa Zaki ko baya raye zuriata sunfi
qarfinka..and one last thing shine dukkanin cases na kashe kashenda kayi tun kafin haihuwata
na budesu you're not going anywhere dilla..
Files din hannun lawyernsa ya karba tareda budewa ya saki wani mugun murmushi tareda daga
masa files din yace"
17 murders cases,
One murderer,
Kafara da kashe uncle dinka da matarsa da yayansu biyu a Dilla Ethiopia ka gudo da dukiyarsu
Nigeria inda ka kashe wani dattijo a wani qauyen jalingo ka gade gidansa,
Ka kashe yayan matarka zeel kuka gade tasa dukiyar kuka Kori yayansa,
Ka kashe ma'aikatan dasuke maka aiki da dama kafin kazo ka kashe Amininka ALIYU HAIDAR
NOAH... Owner NOAH'S PUBLICATIONS, Noah's empire....
Dukkaninsu atare Suka dago Suka kallesa cikin mummunan firgicinda tunda aka fara wainnan
balain Basu shugesaba....
Dagowa Dilla yayi da kyar ya kalli Zaki da idanuwansa dasukai jajir sbd tsananin azabar ciwon
dayake ciki zaiyi mgn Amma yakasa bude baki police suka marmatso cikin bindigoginsu da
cuffs zasu kamasa ya kalli zeel,am da fammah ya bude baki daqyar zaiyi magana zuciyarsa ta
buga ya zaro ido Yana dafe qirjinsa take yafara tari Mai qarfi Wanda sukaga jini na biyo tarin Koda su am Suka riqosa cikin tashin hankali tuni jinin yafara biyowa ta hancinsa da bakinsa
Koda Suka tarosa jikinsa yasaki suna ihu suna kuka suna kallonsa ya rasu agurin..
Rintse idanuwa JJ yayi sbd irin kukan dasukeyi da ihunsa irinsane yayi alokacinda aka kashe
masa nasa iyayen Yana tuno abin har lokacin yanajin radadin abin...
Zaki kuwa juya baya yayi sbd kukan fammah dayake taba zuciyarsa da dukkanin tausayinta
akaro na farko..
Ambulance na zuwa aka daukesa har lokacin kuka sukeyi sosai cikin tsananin tashin hankali da
baqin cikin dasuke ganin zai samesu idan sun rasa dad.
Ambulance na barin gurin da Dilla wasu karnuka dake gefen Mansion dindake kusadana dillas
din suka qaraso suna shinshina jinin suna haushi.
Karnukan am ya kalla ya dago ya kalli Zaki Suka hada ido hawaye suka gangaro masa ya riqo
mum dinsa da fammah dasuke kuka suna shidewa ya sakasu a taxi sukabi bayan ambulance
din.
Watsewa gurin yayi kowa ya wuce har Yan media tuni Suka watse ana yada labarin rasuwar
Dilla.
Juyowa yayi zaiyi magana yaga yanda JJ ya tsaresa da manyan idanuwansa
Ya saki wani sirrin numfashi tareda zare shades dinsa yayi tareda kallon JJ zaiyi magana
saikuma yakasa ya rungumesa da qarfi Suka rungume juna kowannensu najin tsaftatacciyar
qaunar Dan uwansa wadda sunsan Allah ne yasaka musu qaunar junansu fiyeda komai.
Sunkoma ahaka kafin Suka saki juna JJ yasake kallonsa cikin mutuwar jiki yace"
Nasan reason dinka baifi karka dawo garemu a cutatar damu sbd Kai Amma meyasa bakayi
tunanin idan Muna tare zamu iya Kare junanmu tareba musamman bab.....
Kasa karasawa