Showing 18001 words to 21000 words out of 81438 words
Chapter 7 - BURI DAYA Complete Hausa Novels By Mamuhgee .pdf
Hijabinta ta jawo tasaka jikinta na sanyi ga tsoro da fargaba fal cikin ranta
Ta juya ta kalli gefen da iya talatu ke zaune taga ko dagowa ta kalleta taqiyi ta wuce tabi
bayansa qafafunta na 'dan daukar rawa sbd fargaba da tsoro gashi baba baya nan Dan kullum
cikin Mata kashedin zuwa dakin zakin yake ko kebewa dashi.
Saidata wuce iya talatu ta dago tabi bayanta da kallo Dan tana kalle dasu tayi kamar batasan
meke faruwa ba,
Dire robar hannunta tayi da Dan qarfi tana cewa"
Allah ma yasa yayi Mata ciki ko zamu samu masifarsa ta rage idan yaga Yana Shirin zama
uba,idan Kuma rabon wahala ne ke jiranmu kamar yanda dattiya yafada Allah ya nesanta dashi
Amma wlh masifa wlh Nima ta isheni duk wani tattalin arzikina kullum a karyewa yake sbd
masifar Zaki da badan Allah yayini da farin jinin sana'ar samuba da tuni na kakkarye Babu
sauran jarin da kuma tuni nabi bayan dattiya a yawon ta zubar dinsa.
Ita wlh ma ringa cusa masa Nadiya zata riqa Yi daga yau tunda dama ance duk iskancin mutum
idan yayi aure Yana raguwa idan Kuma aka haifar masama dainawa yakeyi
Sudai sunason Zaki ya daina ta'addanci ko zasu samu su shaqi iskan duniya hankali kwance
duk da wani lokacin baqaramin dadi takejiba idan tafita duk anguwar dataje indai akwai yayan
banza saisun taso sun gaidata ana cewa gwaggon sarki Zaki ce Saidai Kuma wlh tanason itada
'yan dabbobinta su sakata su Wala a gidan duk da dai tasan ba inda zasu a gidan zasu tare
Amma dai zai daina Basu gwale gwale komadai yayane.
Nadiya kuwa tana isa baqin qofar dakin dake soron gidan ta tsaya tsoronta na qaruwa takasa
shiga sai fargabar kar babanta yazo yaganta anan din takeyi gashi ana hango ta waje tunda
soro ne,
Kamar daga sama dattiya dake zaune taredasu mal idi dasu mal zailani a bakin masallaci yaga
kamar idanuwansa na hango masa hijabi hijabi a soron gidan ya hadiye wani yawu qut da qarfi
tareda miqewa Yana gyara zaman hularsa dake kife a kansa kamar ya zura kwano sbd batada
wata karyewa ko Dan wani qarfin starch da hula kedashi.
Hankalinsa na soron gidansa yace"
Ina zuwa Bari na dubo wani Abu cikin gidan yanxu....
Ko gama Kai qarshen zancen baiyiba ya wuce Yana Dan sauri Dan kuwa idan har Nadiya ce
zata shiga dakin Zaki dantaga bayanan dukan tashi Kisha gishiri zai Mata Dan wlh bazai yarda
ya qare a 'yayan troway ba,
Ruqayya ta Haifa masa acema yanxu yarsa ta Haifa masa.
Aikuwa itace'"yafada Yana qaro sauri zai shigo tun daga wajen yake cewa"
Ke Nadiya karki Bari na iso na sameki gurin nan wlh dukan akuya zanmiki idan nasameki agurin
wuce ciki maza maza.....
A tsorace ta juyo jin maganar babanta jikinta yasake daukar rawa ta juya da sauri zatayi cikin
gida taji anriqe hannunta da wani irin hannu dayasa dukkanin jikinta zazzabi ya sauka Dan
kuwa take rawar jikinta ta qaru.
Idanuwa cikeda hawaye ta juyo sukai ido biyu da Zaki daya riqeda hannunta jikinsa ba riga
dagashi sai wani sabon three quarter Mai zanen sojoji ajikinsa daga gani baigama shiryawa.
Hawayen idonta ne Suka tsinke suna gangarowa sbd babanta.
Dattiya nashigowa soron afusace zaiyi mgn Zaki ya fizgota cikin dakin dama labulen dakin
koyaushe a sake yake.
Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci dattiya baisan lokacinda ya banke labulen dakin ba zai
shiga a masife.
Jawota cikin jikinsa Zaki yayi Wanda yasa kusan numfashinsu daukewa atare musamman sbd
Babu riga ajikinsa gashi itama hijab din ta robace duk ta kwanta jikinta.
Kasa dagowa tayi sai qoqarin zamewa datakeyi jikinta na rawar tsoron abinda ke faruwa.
Shikuwa Zaki ko ajikinsa ya matseta cikin jikinsa tareda kallon dattiya dayayi mutuwar tsaye
cikin Izza yabude baki yace"
Wlh taku 'daya idan ka qaro cikin dakin nan saina Mata abinda bakaso ayau din nan...
Wani irin zafi zuciyar dattiya taqara dauka cikin tsananin baqin ciki da fushi yace"
Naji to saketa tayi cikin gida.
Bai saketaba ya juya da ita jikinsa har bakin katifarsa ya saketa fuskar nan tamke ko kallonta
bayayi yace"
Ke kwanta anan.
Juyowa yayi Yana fuskantar dattiya da idanuwansa sukai kamar ruwa sun ciko aciki ya nuna
masa qofa da ido Yana Kai hannu kan zib din wandonsa kamar zai cire.....
Da sauri dattiya yafito dakin yayo cikin gida ko gani sosai bayayi yana kaiwa kusada talatu ya
zube yayi zaman Yan bori tareda dafe Kai ransa na suya yace"
Wannan wace irin masiface ruqayya tasani aciki ta barni????
Uban waye baban Zaki Dan kuwa tabbas daga tsotson marasa kunya da mutunci yafito,
Wane kalar balaine nake ciki agabana wannan Dan yawon ta zubar din ke tabamin 'ya haryana
cewa zaiyi....
sai yakasa fada ya juya zancen cikin fargabar abinda ke can Yana faruwa a dakin zakin yanxu,
Jiyake kamar yaje ya siyo maganin suma yasawa Zaki yayi suman wata biyu bai tashiba.
Itadai iya ko kallonsa batayiba taci gaba da aikinta tana cewa"
Allah yabamu jikoki masu qashin arziki da tagomashinsa tunda dai gashinan 'yayanmu Babu
maishi saimu roqa daga jikoki.
Wani mugun kallon takaicinta yasako Mata tareda miqewa a fusace yayi ball da bokitin sauran
tsiminta yawuce Yana zuba sabon masifa da kowa agidan.
Shimfida tabarma yayi a qofar dakin zainab ya zauna Yana mita Babu inda zashi saiyaga fitowar
Nadiya Dan kuwa yau saiya karyata a gidan nan.
Bai juyoba ya dauki rigarsa Mara hannu Mai hula yasaka tareda ficewa bataredama ya nuna
tunawa da ita a dakinba,
Ahankali tasamu kuzarin sauke wani wahalallen numfashi bayan fitarsa,
Zamewa tayi qasa ta zauna tareda qanqame jikinta dake rawa har lokacin,
Tsananin kunyar babanta takeji kamar zata kasheta
Batasan ta Yayama zata iya kallonsaba yanxu.
Tunowa tayi da Yaya zakin saitaji kunyarta da tashin hankalinta ya ninku hartana sakin wani irin
kukan Rashin sanin abinyi.
Shikuwa Yana fitowa sanin tana ciki yabada umarnin kar Wanda ya shiga dakinsa duk da
damacan idan bashine ya aikesu basa shiga dakinsa.
Zama yayi cikinsu Suka hau ayyukansu harsaida alee dikko ya biyo ya daukesa tareda
securities dinsa Suka fita shima yaransa Suka Mara musu baya cikin tasu motar.
Har aka fara Kiran magriba Bata fitoba nan hankalin dattiya yasake tashi Dan bai lurada fitar
Zaki ba duk tunaninsa suna ciki.
Zuwa lokacin dukkanin jikinsa yagama yin sanyi Dan har wani mutuwa jikinsa yayi Dan kuwa
yasan yanzu komai dayake gudu yariga yafaru Saidai Nadiya tayiwa kanta Dan batasan gatan
dayake son mataba ta Shirin rabata da wannan auren qaddara dayakeyi.
Miqewa yayi daqyar jiki amace ya dauki buta ya nufi bayi Dan gabatarda alwalar magriba da
aka gama Kira.
Yana fitowa bayi itama tana shigowa tsakar gidan a rarrabe da bango kanta a qasa takasa
dagowa takalli ko dayansu sai hawaye dake gangaro Mata.
Da sauri talatu ta ajiye aikin daurin datakeyi tana yiwa nadiyar kallon tsaf kamar yanda dattiya
yayi Mata kafin ya dauke Kai cikin ransa Yana tsinewa Lagos ma gabaki dayanta da Wainda ke
ciki tunda acan uban Zaki yake,
Shi kenan Zaki yakaisa ya barosa.
Iya kuwa wata irin guda ta rangada tareda miqewa da sauri ta nufi nadiyar zata kamota tayo ciki
da ita dattiya ya fizgo nadiyar cikin baqin ciki ya turata yace"
Ni mahaifinki naki dokar Rashin zuwa dakin wannan dangin Lagos din kika take maganata kika
tafi sbd kin rainani Ni ban isaba ko???
To tunda haka kika zaba wlh kingama zama cikin gidannan ki koma can gurinsa na barmasa
tunda ya koya Miki kalar rashin kunyarsa da Rashin mutuncinsa....
Saurin zubewa tayi qasa tana kuka tana girgiza Kai da qarfi.
Wani wawan Marin takaicinta ya sakar Mata yanajin radadin abin aransa Dan kuwa baiso
rayuwarta ta wagarce a hakaba yaso taje gidan aurenta tayi rayuwar aure kamar kowa Amma
wannan rayuwar da Zaki Babu wani rayuwar aure aciki tunda anan suke zaune agabansu za'a
riqa Haifa musu jikoki Sam bai hango ta yanda zasuyi rayuwar aure anan ba.
Wannan abin ke cimasa Rai shiyasa yayita gudun faruwar hakan sbd za'ayita nunasa ana cewa
acikin gidansa ake cikin jikokinsa aciki ake haihuwarsu aciki suke girma,ba wannan rayuwar
yaso Mata...
Janta yayi da qarfi ransa na qara quna ya jehota soron gidan da qarfi daidai shigowarsa
shikuma ba zato ta fado kirjinsa.
Kuka takeyi sosai sbd tsoron ganin fushin baban dabata taba ganiba tayi saurin barin jikinsa
tareda durqushewa gefe tana kuka sosai.
Cikin bacin rai kawun ya kallesa ganin yanda yake qoqarin shigewa dakinsa ko kulasu yaqiyi
kamar baiga meke faruwaba yace"
Ka Gama daure dauren fuskarka da izzarka ta banxa Wanda Babu ta inda ka gaji sarauta anan
Saidai can a qasar dangin oduduwa
Wlh bazan zama wulaqantaccen mutumba dazai taraku agida ku ringa zubamin Rashin kunya
ba.,
Gatanan dagayau tadawo dakinka gwara nasan ta tare zaman aure takeyi da in ajeta Ina
zagayen banxa Kuna nuna Rashin kunyarku gwara ku qaratacan Kuma wlh kace bazata zauna
a dakinkaba to ku tattara kubarmin gidana kuje can kusan nayi.....
Fara neman daburcewa yakeyi sbd fararen idanuwan da zakin ya kafesa dasu,
Fara rawar murya yayi ga fargaba ga bacin Rai yace"
Eh kadaiji abinda nafada bazaku maidani dattiyan banxaba.
Wani malalacin murmushi Zaki yayi tareda Dan kallon gefen nadiyar cikin ko in kula yace"
Ke tashi ki shiga ciki.
Kasa tashi tayi sai kukanta dake qaruwa.
Cikin tsawa yace"
Zan karya Miki qafa fa.
Miqewa tayi da sauri ta nufi cikin gidan dattiya ya daka Mata tsawa yace"
Wuce dakinsa ai daga yau kin tare zaman aure zakiyi tunda kin nuna kinshirya.
Kallonsa takeyi tana tsananta hawaye ta juyo ta nufi dakin zakin ta rakube bakin qofa.
Dogon tsaki yaja tareda nufar qofa Yana cewa"
Wlh andai cuceni Ni dattiya.
Shikuwa shiru yayi agurin tareda rintse idanu ya bude ya juya ya watsar Mata wani mugun kallo
Yana cewa"
Zaki min shiru agurin kosaina karya wuyanki agurin.
Tsit tayi tareda qarasa shigewa bayan qofar.
Fasa shiga yayi ya fice shima Dan sallah.
Yana ficewa tayo cikin gidan Dan yin alwala itama tana share hawayenta dasukaqi tsayawa
tana kallon iya talatu dataki saka baki a alamarin.
#mamuh*_BURI DAYA na kudine idan baka biyaba ka nemi wannan numbers din ka biya ka
karanta cikin aminci_*
07067124863
08031181300
*_Mamuhgee15_*
Butarda baban yabari bayan alwalarsa ta qarasa ahankali ta dauka har lokacin hawaye take
zubarwa
Ruwa ta qarasa jikin durum ta Diba tazo tashige bayi har lokacin idon iya talatu na kanta tana
Mata kallon qurulla zuciyarta fal farin ciki Dan kuwa ganin take tafi kowa matsuwa da nadiyar
tasamu ciki ko zakin zai shiryu su samu yanci itada tattalin arzikinta.
Itadai alwalarta takeyi cikin tsananin damuwa da tsoron yanda zatayi rayuwa a daki daya dashi.
Tana gamawa ta nufi dakinsu itada zainab tashiga tana qoqarin tayarda sallah baban yashigo
gidan Yana qwala Kiran sunanta.
Saurin tayarda sallar tayi cikeda tsoron karyazo ya daketa duk da duka ba dabiarsa bace
iyakacinsa cika baki Saidai ganin yanda yau yaketa fada yasa takejin tsoron karya daketan.
Ta Jima tana sallar kodata sallame qin fitowa tayi tana qoqarin gyara zama zainab tashigo dakin
rataye da jaka ta ajiye tana kallonta tace"
Kije baba nakira yau fada yakeji Dan Nima yanzu yagama zubamin akan zuwa gidan anty
nafisa.
Hawayentane ke qoqarin dawowa ta kalli bakin qofar tana sako hawayen kafin ta miqe jiki ba
qwari ta fito tana share hawayenta.
Tun kafin ta iso gabansa yace"
Koma ki dauko jakar kayanki kixo ki fice gobe zansa asa muku hanjin gado da katifar Dana siya
Miki ta aure.
Qoqarin durqusawa take gabansa alamar roqonsa ya daka Mata tsawa Yana cewa"
Maza wuce tun kafin na karya Miki qafafu Mara kunya,
Kinsan bakyason zama dakin nasa kika biye masa kuka gama nunamin iyakata dazu,
Dama nasan ni shikenan Banda sa'a tunda duniya babu Wanda yagama rainani sai mijin 'yata
gashi yanzu kema rainanin zakiyi saura dabancin yarage yakoya Miki saiki hau gyarawa talatu
zama kema Kinga zuwa gaba gidan zamu bar muku Dan kungama riqa a harkar ta'addancin,,,
Zaki miqe ki wuce ko saina mangare ki agurin.
Miqewa tayi jiki sanyaye ta juya ta nufi dakinsu,
Zainab da sai yanzu taji abinda ke faruwa tayi saurin jawota cikin dakin tareda 'dan mintsineta a
gefen ciki tana 'yar dariya tace"
Iyye Nadiya Ashe yau tarewa za'ayi shine ko kifadamin nabada gudun mawar gyarawa Yaya
Zaki amaryarsa.
Gudu hawayenta Suka qara tana qoqarin sunkuyar dakai zainab din tayi saurin tallafota tana
cewa"
Ke meyene Kuma abin kuka anan?
Bari kiji wlh damace kika samu kiyi rayuwar dakikeso ta jin dadi
Yanzufa kowa shakkarki zai riqaji amarya guda a gurin sarki Zaki....
Kallonta nadiyar tayi tareda harara tana 'dan turo baki zata juya ta dauko jakarta.
Sake riqota zainab tayi tana cewa"
Ke tsaya Mana kiji kokuwa duk matsuwar tarewarce bazaki tsaya kiji darasin riqe miji ba tunda
iya talatu takasa baki Ni basaina bakiba..
Kinga Dan allah karkije kina masa wannan kwana da hijabin wlh shegen duka zai Miki ya
qarasa kunnuwanki dakeji Dan kuwa lokacin JJ yace Sam Babu abinda Zaki ya tsana kamar
dunkun dunkun mace..
Kallonta nadiyar tayi da sauri zuciyarta na harbawa..
Dariyar qeta zainab tayi ganin nadiyar tafara yarda da zancenta duk da qarya takeyi sai kawai
tasake gyara tsayuwa tacigaba da cewa"
Yes Kuma Yaya Zaki ya tsani taurin Kai wannan ai kema kinsani basai na fada mikiba Dan kuwa
kinfi kowa sanin ya sautin Marin Yaya Zaki yake...
Boye dariyarta tayi ganin tsoro qarara na bayyana tattareda nadiyar taci gaba da cewa"
Sai one last thing shine Yaya Zaki ya tsani qazanta duk da dai nasan ba laifi ke ba qazama
bace Amma Dole Zaki ninka tsaftarki akan tada tunda kina gani wanka biyu ko uku Yaya Zaki
keyi a yini Dan haka kina qazanta kinsan Babu Mai cetonki tunda kowa tsoronsa yakeyi har
baba kina gani.,
Dan haka nidai Ina sonki 'yar uwata banason rasaki Dan allah ki kiyaye abinda nafada Miki wlh
idan kika mutu rayuwarmu lalacewa zatayi...
Cikin sabon tsoro Nadiya ta fashe da wani sabon kukan tausayin kanta akan abubuwan da
zainab tafada Mata wlh itama batason ta mutu yanxu.
A boye zainab tasaki dariyarta ganin ta Dora nadiyar sosai saita daga hannuwanta tana share
Mata hawaye tace"
Daina kuka kinji nadiyata idan kin kiyaye Babu abinda zai faru Barima nabaki turare har biyu
Wanda Zaki ringa sawa idan kikayi wanka hakan zai qara tabbatarda tsaftarki gurinsa.
Jakarta ta bude ta dauko spray din smart collection na Lacoste tabata da madarar turaren
lamsa Mai Dan yawa kadan.
Karba tayi hannuwanta na rawa kafin ta jawo jakar kayanta tasaka
Zainab din ta daukar Mata jakar Suka fito sum sum kamar munafuka tabi bayan zainab din har
qofar dakinsa Suka shiga sbd sanin baya nan.
Wata muguwar harara dattiya yabi bayansu da ita har Suka shige yanajin kamar yace yafasa
tadawo tunda ai ba lallaine kebewarsu so daya ace tasamu cikiba.
Ciki mamakinsa da 'dan takaici iya talatu data sallame sallah tace"
Todai karkace tadawo Naga kanata kallon qofar soron kamar kaga kudi agurin
Kariga kace ta tafi to wlh idan kace tadawo shiyasa Sam bakada qima a idon zakin baida
marainin wayo kamarka.
Tsoki yaja cikin quluwa yace"
Wai ke talatu kullum bakya iya zama baki gasamin baqar magana ba,
Yanzu 'dan kanwar tawa kike cewa Banda qima a idonsa saikace wasu 'yan bariki.
Au dama kanada qima a idonsa shiyasa yake sakar maka karensa ko yaransa suna neman
zauta rayuwarka.
Eh naji koma meyamin Ina ruwanki inace kece kika qarasa zugani na Hana auren ruqayya da
neyo hartaje garin dangin oduduwa tasamo Mana wannan din.
Zatai magana ya miqe ya fice Yana baza babbar rigarsa ransa duk jagule.
Sukuwa suna shiga dakin zainab da Bata taba shigowaba tahau kallon dakin tsaf dashi kamar
baa cikin gidansuba,
Qatuwar katifa ce Mai tudu sosai adakin sai 'yar wardrobe qarama ta kayan sawarsa Dana JJ
sai takalmansa a jere gefe sai wata cupboard dake cike jereda makamai su adda,wuqaqe da
gariyo masu matuqar ha'dari da kaifi.
Tsakiyar dakin kuwa dama carpet ce ash shimfide.
Komai na dakin fes yake kamar dai JJ nanan.
Jikin wardrobe zainab ta ajiye jakar kayan nadiyar tana kallon dakin tanajin Ina itace zata dawo
nan wlh dataji dadi gashi harda standing rechargable fan a dakin.
Bakin katifar taje ta zauna tana latsawa tace"
Wayyo Nadiya wlh karki Bari kiyi laifinda Yaya sarki zai koreki daga dakin nan.
Dauke Kai Nadiya tayi idanuwanta na sake cikowa da hawaye
Zainab tayi saurin tasowa tana cewa"
Karkima fara wannan hawayen sbd baba yagama Miki gata yarinya.
Yanzu dai muje muci abincin dare saikiyo wanka kidawo ki kwanta cikin wannan qatuwar
lafiyayyar katifar wayyo allah inama nice gefe daya ga Yaya Zaki da wannan lafiyayyan jikin
nasa daga gani zaiyi laushi......
Saurin matsawa Nadiya tayi daga gefenta tana girgiza Kai cikin tsananin kunya da tsoron
zancen na zainab.
Itakuwa dariya tayi Kuma har cikin ranta take wannan zancen tasan wlh Yaya Zaki ba qaramin
iya soyayya zaiyiba sbd wannan Jan ajin nasa da kwarjinsa.
Bude jakar sukayi suka cire kayan dau'da sukayi cikin gida dasu da niyar gobe tayi wankinsu.
Indomin da zainab tashigo da ita guda biyu super pack ita zainab din ta dafa sukaci sbd Babu
wani abincin dare da akayi ko na ranama ba ayiba sauran biredin da zainab tarage da safe
dama