Showing 12001 words to 15000 words out of 81438 words

Chapter 5 - BURI DAYA Complete Hausa Novels By Mamuhgee .pdf

Mamughe   

23 Nov 2025

2042

dama sai tawul rataye a wuyansa fuskarnan tamke kamar ko
yaushe.

Zainab ce tafara hangosa ta miqe tareda daukar wayarta dake gefenta tareda takalmanta data
gama wankewa ta nufi dakinsu tana cewa"

To Bello sai anjima nizan shiga na Dan yi waya.

Cikeda jin dadi bellon yace"

Yauwa zainab to nagode.

Cikin 'daga murya iya talatu tace"

Ke Nadiya bazakiyi sauri kifito bane kinbarsu sun gaji da tsugunawar qafafuwansu harsun fara
rawa.

Batareda dattiya yasan da zuwansa ba yace"

Shashanci me kika tsayayi haka za'ayi auren kije kina masa sanyin jiki?

Baice musu qala sai ita daya kalla lokacinda tafito sanyeda sabon hijabi zainab ta sanyo mata
Hoda harda janbaki maroon dayayi mata kyau sosai kasancewar Bata taba saka janbaki mai
kalaba iyakacinta Vaseline abaki.

Wani mugun kallo ya watsa mata atake ta rikice tana neman juyawa cikin muryarsa mai saka
shiga taitayinta yace"

Bani ruwan wanka.

Da sauri nuhu abokin Bello ya miqe Yana cewa"

Sarki Bari na debo maka da kaina ma...

Wani kallo sarkin yayi masa dayashi saurin sakin bokitin...

Gyaran murya dattiya yayi tareda hararar gefen zakin yasaki yaqen Dole yace"

Nuhu Aida kabarshi ta Diba tabashi saiku koma daga soron gidan zaima fi muku nutsuwa can
din.

Aikuwa kamar jira suke Suka miqe Suka koma soron gidan Dan dama dukkaninsu a tsarge
suke da ganin Zaki na gida sun dauka bayanan.

Aikuwa tana Kai masa ruwan tadawo ta nufi soron gidan tanajin ba dadi cikin ranta sbd ganin
wani kallo dayayi mata lokacinda ta aje masa ruwan.

Suna ganinta Bello yahau washe baki sai alokacin Suka saki jiki Suka fara gaisawa itadai tana
rakube a gefe.

Nuhu ne ya zaqe yanata jawo musu fira sbd yafi bellon rawar Kai da iyayi shikuwa bellon sai
kallonta yake Yana murmushi Dan kuwa shi harya farajin sati biyar dinda Suka rage sun masa
nisa.

Qamshin sabulun wankansa na imperial L da ita kadai tasani yasata sake rabewa tareda
sunkuyar dakanta

Bello kuwa harda qara Ware idanuwansa da kyau Yana sake mata kallon qurulla
Ga nuhu sai kawo musu zancen soyayya da yanda Bello kesonta yakeyi Yana qarawa.

Tsaf fararen idonsa Suka shiga cikin nata atake jikinta yadau rawa taji hawaye na ciko
idanuwanta.

Yana shigowa soron JJ yataso daga qofar gida yashigo
Kallo daya yayiwa Zaki yaga ba fuskar masa magana harya shige dakinsa shikuma yajuyo
gurinsu Bello fuska a hade yace"

Kai ku Ware daga nan bamason hayaniya,

Wuqa ya fitar mai shegen kaifi da qyalli ya Dora saitin wandon Bello da jikinsa yafara mazari
yace"

Duk Randa nasake ganinka gidan nan saina maka zanen gobirawa anan""yaqarasa fada Yana
zungurin wandon da wuqar.

Nuhu tuni yayi muryar sanyi yace"

Zamu kikyaye oga JJ.

Qofa ya nuna musu tuni Suka wuce da sauri wani na tunkudar wani musamman sauran yaran
neyon dake cikeda qofar gida duk sun mimmiqe.

Kamar Bello zai fashe da kuka haka ya isa gida ya tube yasaka riga da wandonsa na aiki ya
nufi shago Yana fushi Dan kuwa wlh JJ yacucesa daya korosu Dan kuwa so yayi yau ya dasa
soyayyarsa a zuciyar nadiyarsa.


JJ kuwa bayan fitarsu mayarda wuqarsa yayi ya juyo gurinta fuskarsa a sake sosai Dan dama
dashi kadaine take dadewa Yana Mana fira.

Fira yadinga mata wani lokacin har murmushi takeyi tana rufe fuska sbd rabi duk tsokanarta ne
yakeyi da maganar soyayya.

Ahaka har kusan magriba kafin yabarta tashiga gida tana murmushi shikuma yayi waje Dan
kuwa yasan sarki baison kusancin kowa ayanxu.

Dattiya dake jiran shigowarta ya qurawa hannunta dake cikin hijabi ido
Cikin sanyi take qarasowa tana murmushinda itama Bata saniba

Ahasale dattiya yace"

Wai meyene haka kike tafiya kamar Mara ruwan jiki???bazaki cire hannunki daga hijabin bane
saikace matar alaramma.

Fitarda hannuwanta tayi yaga Babu komai a hannun ya tsuke fuska yace"

Ruwan alwala kikazo dibar musu???

Girgiza Kai tayi tareda masa alamar sun wuce.

Cikin yayi da qananun idanuwansa tareda miqewa ya dauki buta baisake cewa kowa qala ba
yashige bayi tun acan ma yayo alwalarsa Yana fitowa butar kawai ya aje ya fice.

A masallaci ma koda yaje kusada Zaki da JJ yasamu sahu nan yasake tsuke fuska musamman
dayaga JJ namasa wani ladabi yasan cutarsa zasuyi Saidai ganin fuskar JJ a tamke tam Babu
Wasa yasa yasake tsuke tasa shima Dan ko gaisuwa baiso.

Ana gama sallah yafito JJ yabiyo bayansa suna fitowa yaja ya tsaya yace"

Lafiya zaka bini?

Murmushi JJ yayi Yana Sosa Kai cikin 'dan ladabi zaiyi magana kawun ya katsesa da cewa"

Wannan ladabun mai amsheka ba sam,
Kafitomin a zallar yanda kake kamun magana idan ma itace kakeda ita.

To kawu dama inson Nadiya ne shine nakeson sanarda Kai Kuma Nima aurenta nakeson yi......

Wani kallon takaici kawun yamasa kafin cikin bacin Rai yace"

'yar tawa zanbawa magajin dake jiran gado a dabanci,ta'addanci,da Sara Suka?
Wato gani dattiyan mahaukata tunda kaga Ina sake muku fus....

Ido hudu yayida Zaki dake bayansu saiya qarasa maganarsa da cewa"

Kaga jabiru kabarni da wannan maganar nariga nabawasu Bello saura sati biyar bikin ma.

Juyawa JJ yayi sbd jin yanda kawun yayi magana cikin lalama sabanin farko daya fara masa
Rashin arziki
saiyaga Zaki yasaki murmushi kenan ganinsa yasa kawun sassauta harshensa.


Ahankali yaqaraso yau kyawunsa duk yasake bayyana sbd jallabiyace yasako ash data fito da
farin fatarsa ta asalin Igbo.

Kallon kawu yayi yace"

Muje gida kawu.

niba gida zani ba inada abinyi.

Juyawa sukayi Suka barsa
Sanin akwai abinda ke Shirin faruwa yasa yabiyo bayansu Yana zuba masifarsa suna jinsa
sukai banxa dashi.

Har tsakar gida Suka shiga Zaki ya kalli kawun yace"

JJ nason auren waccan yarinyar
Meyasa baza'a bashiba?????

Kallon JJ kawu yayi yace'

Sbd Ni ubanta namata miji.

Kallonsa Zaki yayi yace"

Shikenan????

Eh"kawun yada Kai tsaye sbd shima yau Rashin arzikin yakeji.

Juyawa yayi ya wuce JJ yabi bayansa suka fita.
#MAMUH.*_BURI DAYA Yana cikin Zafafa2020 na siyarwane ba free ba idan baki biyaba ki
nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin amincin allah._*

07067124863
08030811300


*_Mamuhgee11_*
Qarfe goma Sha 'daya su JJ da Suka fito kowane 'dan daba ranar dai manyan Kaya sukaita
sawa wani suyi masa kyau wani kamar irin mutanen 9s dinnan sbd tarin sumar kansu gashi
ranar Zaki yabada umarnin kowa ya aje makaminsa Babu ta'addanci yau tunda ranar auren
magajinsa ce,
JJ kuwa wata farar shadda ce ajikinsa wadda Zaki ya dinka masa ba laifi tanada 'yar tsada Dan
kuwa dubu ashirin yasiye ta yadi goma goma guda biyu shi tasa sky-blue ta jj din fara.

Tuni qofar gidan da layin yafara cika da mutanensu Amma sai 'yan anguwa dasuka fara
halartowa
shidai dattiya kallon kowa yakeyi zuciyarsa ba dadi ga cikin gida ma Nadiya jikinta sai rawa
yakeyi sbd tashin hankalin data samu kanta aciki ga zazzabi tanaji ga Rashin sukunin da

zuciyarta ke ciki.

Lokacinda yafito cikin sky-blue din shaddarsa 'yar ciki da babbar riga ga hularsa Yana daura
agogo yafito daki daidai fitowarta daga daki zataje Kiran iya talatu cak ta tsaya tareda juyowa
ahankali daidai ya kallo gefen Suka hada ido.

Wasu irin hawaye ne Suka ciko idanuwanta sanin daga yau idan ta auri Bello bazata sake
rayuwa a inda yakeba.

Dauke Kai yayi Yana sake hade fuska ya fito waje.

Wani irin annuri da haiba ke fita a fuskarsa sbd tsananin kyawun da yayi tamkar shine angon
musamman izzarsa dake qara masa burgewa da kyau.

Nufosa JJ yayi cikin tsananin farin ciki ya miqa masa hannu sukai musabaha batareda ya saki
hannunsa ba yace"

ALEEYU HAIDAR Ina cikin farin cikin ganin kana taredani a yau ranar aurena Rana mafi farin
ciki agareni Saidai Ina roqon wani Abu daga gareka.

Wani irin murmushi yayi Yana basarwa yakalli JJ din ganin yanda yayi wani iri sai habarsa ta
dakesa atake yaji tsananin qaunar JJ din nasake shigarsa Dan kuwa shikadai yasan irin son
dayakewa JJ Wanda yasa yake danne ciwon dayakeji a qirjinsa ganin JJ na farin ciki da auren.

Cikin kulawa yace"

Kafadamin abinda kakeso agurina zan baka kodan tarihin wannan Rana agareni.

Murmushi JJ yayi yace"

_*NADIA*_ nakeson tasamu dukkanin farin ciki da walwala tareda kulawa da qauna data rasa
tun rasuwar umma,

Kallonsa yayi tareda dauke Kai Yana zame hannunsa daga nasa fuska a daure yace"

Wannan duk zaka Bata bayan aur.....

Bai qarasaba ya juya zai wuce
JJ yace"

Nayi Mata alqawarin nema Mata lafiyarta matuqar Ina raye da lafiyata,
Saidai bansaniba kozan iya,
Roqona anan shine Ina roqonka da a duk lokacinda na gaza cika wannan alqawarin to

cikaminshi koda inanan ko banan.....

Juyowa zakin yayi Saidai kafin yayi magana ya hango kb tafe cikin mutane ya rufe fuskarsa
Yana boye wani Abu cikin riga.

Janye JJ yayi da sauri zai tare kb din Saidai jj na juyowa yaga sharbebiyar wuqarda ke hannun
kb wadda asalinta bakin lace ne da Ida kamar tafiyar maciji idan aka sokeka da ita yanada wuya
ta fito Bata yanko hanjinkaba shiyasa ba'a tsallaketa.

Kb na daga wuqar JJ ya tare atake ta shige cikinsa gaba dayanta kafin kb ya fizgota da qarfi
yanda zatafi yimasa illa.

Wani irin numfashin wahala JJ yasaki tareda zubewa qasa kb na ganin hakan ya gudu
musamman da Babu Wanda ya Ankara da abinda ke faruwa

Zaki zabura yayi ya damqo hannun kb JJ yayi saurin riqe nasa a wahalce yace"

Ina buqatar kusa Dan Allah.

Cikin karaji yacewasu nano subi kb su kamosa karsu Bari ya gudu.

Atake guri ya kaure da hayaniya sbd ganin abinda ya faru jini gabaki daya ya Bata farar
shaddar jikin JJ har qasa.

Wani irin runguma Zaki yamasa Yana cewa"

JJ Dan Allah karka rufe idonka zamuje asibiti zaka warke yanxu muxo a daura maka aure,
Karka manta Kaine kuzarina da ganina,
Kaine magajina,
Karka rufe idonka Dan Allah JJ......

Cikin tsananin karaji yace akawo masa mota.

Hankali tashe da ganin jininda ke zuba Suka sakashi mota a gigice Zaki ke tuqin hannunsa
daya na damqe dana JJ da tuni idanuwansa Suka rufe.

Duk yanda su dattiya ke cikin 6acin Rai hankalinsu yatashi matuqa da abinda yafarun Dan kuwa
tabbas kowa yasan JJ shine abunda Zaki yafi so,shine komai na Zaki.

Zancen na shiga kunnen Nadiya ta sulale qasa tana tsiyayo hawaye da idanuwanta dasuka
gama kumbura dayin jajir.

Suma sauran mutan gidan sun firgita sosai da jin zancen musamman da aketa cewa JJ yariga

ai yarasu.


A asibiti kuwa suna zuwa 'yan sandan da ale dikko yaturo musu suna isa nan aka karbesa a
gagauce akai cikin theatre dashi.

Kasa zama Zaki yayi tareda yamutsa sumarsa yanajin zuciyarsa kaman tana qonewa sbd
tsananin tashin hankali da baqin cikin dayake ciki.

Su nano tuni Suka iso asibitin sbd dai kb ya gudu Amma dai aisunsan bazai guje musu ba idan
hankali ya kwanta.

Sosai suke cikin tsananin tashin hankali da fargabar abinda zai faru,

Asibiti kuwa atake kowa yasan yau su sarki na asibitin Dan kuwa tuni kowa ya dauko makansa.

Minti goma Sha hudu da shiga dashiga dashi likitoci biyu Suka fito fuskarsu ba dadi Kai tsaye
'dayan yace"

Sai hakuri Allah yamasa rasuwa..

Akaro na farko arayuwarsa da hawaye Suka sauko idanuwansa yayi baya tareda zubewa a
kujera Yana dafe kansa dazai tsage sbd wani irin sarawa da jijiyoyin kan sukeyi.

Su Nanu kuwa tuni duk Suka saki makamansu kowanne na sunkuyar dakai cikeda baqin cikin
rasa 'dan uwansu,aminsu mai qaunar dukkaninsu.

Sosai Dr aminu da Dr faruk Suka tausayawa halinda Zaki yashiga musamman dasuka lura
kansa yake ruqewa sunsan illar dake cikin hakan sukai saurin sa nurses maza su kamosa
ashigo ciki dashi Yana buqatar kwanta suyi masa allurar minti goma.

Miqewa yayi da kansa yashiga kodan yaga gawar JJ 'dinsa Saidai suna shiga yaga gawar JJ
din rufe har Kai da qafa
Atake yaji zuciyarsa na neman tarwatsewa itama ya isa bakin gadon yayi shiru Yana tuno
maganganunsu na qarshe.

Ya dade Yana kallon gawar kafin ya juyo baiko tsaya sauraron Kiran da Dr kemasa amasa
allura ba yafito atake yaransa Suka Mara masa baya musamman dasukaga fuskarnan ba
rahama ko daya.

Cikin motarsu Suka figeta sai qofar gida lokacin Sha biyu saura minti ashirin gashi mutane na
nesa basusan da abinda ke faruwaba tuni aka sake cike gurin taf da 'yan zuwa daurin aure.

Dan kuwa tuni akayi shimfidu anata gaishe gaishen barka da zuwa.

Suna sauka Kai tsaye gurin kawun ya nufa shima yana ganinsa yayiwa idi ido nan aka fara
shelar za'a daura auren.

Take kowa ya zazzauna aka fara.

Yana isowa ganin mutane da yawa yasa yazo har kusada kawun ya zauna Kai tsaye yace"

Zanyi magana dakai kar a daura sbd JJ ya....

Cikin nutsuwa kawu yace"

Kabari agama daura auren muyi magana yanxudai ka nutsu auren 'yatane bana son matsala.

Miqewa yayi yabar gurin ya hargitse kansa yake.

Cikin nutsuwa dattiya ya fitarda dubu goma a miqawa liman yace"

Ga sadakin 'dana nan.

Karba akayi aka miqawa mal idi dashine yayi waliyin Nadiya.

Yakai mota zai shiga subar gurin yaji ana cewa"


*_AN DAURA AUREN ALIYU HAIDAR DA NADIYA DATTIYA AKAN SADAKI NAIRA DUBU
GOMA LAQADAN BA AJALAN BA ALLAH YASA WANNAN AURE SAI MUTUWA_*

Aminnnnnn jama'a Suka karba anata miqawa dattiya hannu ana tayasa murna nan guri ya
kaure da hayaniyar Taya murna.
#MAMUH*_BURI DAYA Yana cikin Zafafa2020 na siyarwane ba free ba idan baki biyaba ki
nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin amincin allah._*

07067124863
08030811300


*_Mamuhgee12_*
Kasa shiga motar yayi hakama yakasa juyowa
Zuciyarsa nason qin gasgata abinda kunnuwansa Suka jiyo masa musamman yanda numfashi
ke sauri gurin fita.

Dukkanin yaransa kuwa wuta Suka dauke Basu nuna farin cikinsuba daya wanxu cikin
zukatansu sbd jimami da radadi dasuke ciki na Rashin dayan jigonsu JJ.

Ahankali ya juyo bayan ya rintse idanuwansa ya bude atake Suka qara kadawa Suka rikide.

Kallon kawun yayi daketa miqawa mutane hannu Yana yaqen dole Dan kuwa shima ayau din
zuciyarsa dif take da damuwar wannan aure Saidai baida yanda zaiyi Dan kuwa wani bangaren
auren Zaki ga nadiyarsa shine mafita Dan kuwa idan tana matsayin matarsa Babu shegen da
zaiyi Gigi ko gangancin ko yiwa inda take mugun kallo, Saidai ta bangaren rayuwar aure yasan Zaki bazai taba kulada Nadia ba musamman ganin
yanda yafi hukuntata akan kowa.

Hada ido sukayi sukayiwa juna kallon cikin ido kowanne zuciyarsa cikeda damuwa da tsananin
bacin Rai Saidai hakanan ya juya yafada mota sukabar gurin Dan zuwa dauko gawar JJ azo ayi
Mata sallah.

Suna barin gurin aka fara watsewa sbd wasu da dama basusan da rasuwar JJ ba.

Acikin gida kuwa lokacinda dahiru yashigo bayan daurin aure shine yafara shigowa ya nufi
dakin iya talatu dake 'dan cikeda mutane anata hayaniyar biki ya miqa Mata goro da dabinon
daurin auren yana cewa"

Ga goron nan ki ajiye har baban yashigo andaura aure da yardar Allah Saidai abin mamakin
baba baya qarewa mu munxo da sanin Bello ne mijin saigashi mukaji baba agurin yacewa liman
da Zaki za'a daura auren.

Saurin kamo goron daya kusa zubewa iya talatu tayi tana kallon dahiru tace"

Zaki fa kace????

Eh, Allah yabasu haquri da juna shine fatar kawai tunda andaura.

Numfashi iya talatu tasaki tana sake zare 'yan fici ficin idanuwanta cikeda mamakin dattiya da
Rashin sanin abin fada kawai tace"

To Allah ya sanyaya zuciyar Zaki mudai da wannan danyen hukuncin na babanku.

Kallon zainab dake tsaye gefenta tana waya da wasu qawayenta datakewa kwatancen gidan
tace"

Auren nan kinji da Zaki aka daura.

Wani zaro ido tayi cikeda mamaki da son qin gasgata zancen tace"

Yaya Zaki yanxu shine mijin Nadiya????

Kwarai kuwa cewar dattiya daya shigo gidan.

Aikuwa nan aka dauki guda ana Allah ya sanya albarka.

Zainab kuwa daki tayi da sauri Dan fesawa Nadiya zancen.

Qare Mata kallo tayi daga bakin qofar tana kwatanta irin dacewarda zasuyi da ace zasuyi
zaman aure kamar na kowane maaurata Saidai tasan Yaya Zaki Kam ko kallo Nadia bazata
ishesaba duk da wasu lokutan tanayi musu kallon masoya duk da irin tazarar halaye da
banbanci dake bayyane a tsakaninsu.
Qarasowa tayi cikin dakin ta zauna kan katifar dake dakin tareda aje wayarta tana daukar Hoda
tafara shafawa fuskarta da Bata rabo da kwalliya koyaushe hankali kwance race"

Andaura aure dai yau kukan auren Bello yaqare Saidai na Yaya Zaki....

'dago jajayen idanuwanta tayi takalli zainab din ahankali batareda hawayen cikin idonta sun
gangaroba sbd kokawar da zuciyarta keyi gurin auna zancen kafin ta yarda dashi a zuciyarta.

Aje hodar zainab tayi tareda kallonta tace"

Baki yarda bane ko me?kike min kallon qurulla...

Sallamar dattiya tasasu kallon qofar dakin atare,
Zainab ta miqe tareda daukar wayarta da gyalenta ta fice Dan tarbo baqinta.

Cikin sanyin jiki data fara ganin mahaifin nata dashi akaro na farko rayuwarta taga yashigo ya
tsaya akanta zuciyarsa ba wani dadi yakalleta tayi qasa da Kai hawayenta na sake saukowa
sbd yanayinsa kawai ya tabbatar matada zancen da zainab tafada gskia ne da Yaya Zaki aka
daura Mata aure.
Cikin sanyin murya yafara cewa"

Nadiya Allah yayi yau nasauke nauyinki dayake kaina amatsayin mahaifinki Dan kuwa na 'daura
Miki aure ayau din da Zaki Wanda shi na zabar Miki amatsayina na mahaifinki Dan haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0