Showing 24001 words to 27000 words out of 81438 words
Chapter 9 - BURI DAYA Complete Hausa Novels By Mamuhgee .pdf
zaune
hartana buge qafarsa dayake bai tsaya daidaiba saiya fado kanta gabaki daya.
Wani irin zaburowa tayi hakan yasa qirjinta ya hadu sosai da nasa Wanda yasa numfashinsa
tsayawa na wucin gadi yayi jarumtar miqewa da sauri Yana qoqarin tamke fuskarsa cikin duhun
ya kunna wutar dakin sbd har asubar akwai nepa.
Haske na gauraye dakin tafara gyara rigarta da sauri tana saka hijabinta.
Fuska a tamke ya fice batareda ko sake kallonta ba.
Yauma Ras ya tararda kawun a tsakar gida riqeda buta yama kasa alwalar.
Ta gabansa yashige bayin sbd qara manna masa hauka tundaga cikin bayin yayo alwala danma
kawun ya dauka wanka yayo.
Yana fitowa yawuce baice masa qalaba.
Itama fitowa tayi tayi alwala lokacin kawu yafice masallaci shima.
Kodata idarda sallah kwantawa tayi agurin tana karatun alqur'ani cikin ranta ahaka bacci yasake
dauketa.
Shima Yana dawowa komawa yayi ya kwanta sbd Yana buqatar hutu yau.
Sosai sukayi bacci harsaida goma ta gota ita tafara farkawa tayi saurin miqewa sbd buga daki
da akayi.
Gyara hijab dinta tayi ta nufi qofar zata bude kamar daga sama cikin muryarsa data qara girma
sbd bacci taji yace"
Idan kika bude qofar nan saina karya hannuwanki.
Juyowa tayi da sauri sbd atunaninta bacci yakeyi.
Still idanunwansa a rufe suke tayi baya ahankali tadawo Saidai Bata zaunaba.
Tashi yayi ya sauko ya nufi qofar ya bude.
Nanu ne ya gaidasa cikeda basa girma ya miqa masa Dan madaidaicin flask na ruwan zafi
Yana cewa"
Sarki yau Dan Tani zubawa ruwan shayinsa suka kafin a amso ammasa afuwa sbd mantawa
yayi shine fa Saida aka Kira ya dafa maka wannan Mara sugan.
Karba yayi tareda bude baki yace"
Ka Debi yara kuje ku tarbi motocin alee dikko dazasu shigo ta dajin bayan gari karku Bari jami'ai
su San dashigowar motocin yau Ina hutu kafadawa Wainda za'a Bari banason hayaniya Kuma
akwai wani Dan kasuwa dake barraj shago na shida jiya daya sakarwa su kawu kare daga
sunje gurinsa kafin ku wuce kuje kuyiwa arzikinsa kariyarda gyaranta sai Allah.
Kawu daya kawo yaji abinda yafada ko kallonsu baiyiba ya wuce ciki Yana cewa"
Shi wannan duk qarfinsa bai ishesaba sai yahada Dana Rashin Shan suga Dan kawai ya
kashemin 'ya nayi mgana yace zaiyi magani na,
Shikuma alhajin kwatano yau zaisan ya tabo dangin Zaki indai zakine hasararda zai goga masa
saiya gwammace baizo cirani Nigeria ba Dan dama tun Yana yaro ba'a taba 'yan gidan shikadai
yafiso yayita cin uwarsu basuda maceci sai allah.
Koda yashigo aje flask din yayi yafice yayi brush yadawo yadauki kayan wankansa ya fice.
Ita taje takai masa ruwan wanka tadawo tafara gyaran dakin.
Fes tagyara koina ta gyare shimfidarsa tayi shara.
Yana shigowa ta fita taje tahau gyaran tsakar gidan tadawo ta tararda yasha tea harya koma ya
kwanta.
Sauran Wanda yabari Tasha ta tattare gurin tafito Dan taya zainab wankin dataga ta fitar tanayi.
Sai azahar Suka gama tayo wanka a dakin zainab ta shirya zainab harda shafa Mata jambaki
daqyar ta iya zuwa tadauki kayan sawa tadawo cikin dakin zainab ta shirya Takoma can tayi
sallah lokacin yafita sallah azahar masallaci.
Da abincin Rana yashigo Mata wannan karon sakwara ce da Miya anan ta zauna taci sbd sanin
bayason dogon iyayi shiyasa taketa taka tsantsan kartayi laifi ya kakkaryata kamar yanda yake
fada.
Da daddare ma yau indomi sukaci Suka kwanta Amma saidata Dade gurin zainba ta rage dare
kafin tashigo ta kwanta.
Ahankali lokacin yafara ja yanzu kusan satinta cikin na uku da tarewa dakin tuni harta Saba da
rayuwar shirun dasukeyi sai Kuma hakan yasa fargabarta ta ragu sosai Saidai tsoronsa dayake
daram cikin ranta.
Cinta da shanta ya canza gabaki daya sbd cimar datake ci yanzu safe Rana dare harya zamto
yanzuma itace ke kawo musu abinci cikin gidan Dan kuwa sosai su iya talatu ke Jan gararsu
Babanma dayaga dai cutar yawa zatai masa idan ankawo wani lokacin shike karbewa ya cinye
ya hanasu Yana cewa ai kullum suke ci yaudai rabonsa ne shikadai.
Lurada Bata iyaci Bata bawa babanta ba yasa kawai yayo siyayyar abinci jibgi guda yasiyo da
gaton risho yasa su Nanu Suka kawo.
Buhun shinkafa 'daya da katon din macaroni da spaghetti sai galan na mangyada da manja
saisu tarkacen magi dasu ashana harma dadu omo da sabulai.
Sosai iya talatu ta bude baki da hanci tana kallon kayan abincin lokacinda ake shiga dasu
dakinsa ta sake numfashi Mai shegen qarfi tana kallon dattiya dake shigowa gidan Yana
waiwayen soron gidan da ake shigoda kayan saura kadan yafada cikin durum din ruwa Saida
talatu ta riqo rigarsa tana cewa"
Yi ahankali karka karye mu cinye kayan kana kwance.
Fixge rigarsa yayi Yana Mata mugun kallo yace"
Ke Kuma shine baqin cikinki kar aci kayan Dani,
To inagadai ai badan niba da bazaki ciba kema tunda dabanyi masa aurenba zaisiyone yakawo
harkici din ke me bakin cin.
Au yanxu Kuma alfaharin auren kakeyi sbd ganin buhun 'yar gote.,
To mudai Kam ai dama munsan arziki yanxu zamu fara cinsa duk uwar dukuyarda dikko ke loda
masa yanxu Kam ci zamuyi musamman Ni.....
Ke banason zaqewa talatu wlh ki kiyaye ni.
Kallonsu zainab tayi cikin takaici tace"
Dan Allah baba karku fara fada tun yanxu akan arzikinda ko samunsa baayiba tukuna.
#MAMUH*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan
numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863
*_Mamuhgee18_*
Fusgar iska yayi ya sake ficewa Yana hura hanci duk da cikin ransa yaji Dan dama dama na
ganin gararda zai fara kwasa a kwanakin musamman ma da idanuwansa Suka qyallo masa
kiret din kwai da doya da dankalin turawa jiyayi wata Yar dariya na neman subuce masa ya
dauke Kai tareda tamke fuska ya fice Yana cewa"
Wannan Yar baqin cikin batason naci wannan kayan ai wlh Saidai kowa ya rasa muguwar
tsohuwa.
Cikin dakin Suka shigarda abincin suka jera inda yace a ajiye Suka fice.
Harta rufo dakin zata shiga cikin gida Nanu yadawo riqeda wata ledar ya miqa Mata yace"
Sarki yace kiyi abinci.
Karba tayi tayo cikin gida zainab tayi saurin karbar ledar tareda budewa ta zaro ido ganin
Naman kajine masu qanqara da kayan Miya.
Wata gudar jin dadi iya talatu tasaki tareda miqewa ta sauke tukunyar tuwon gari datayi niyar
dafawa tana cewa"
Yau dau allah yayi wahalata taqare zanfaraci daga Zaki Kuma daga 'yaya.
Itadai Nadiya Babu wani dogon farin ciki ko murna atareda ita sbd tsoron karta dafa tayi masa
ba daidaiba dukda dai ta iya girki sosai tunda itakeyi na gidan tun batai hakaba.
Jiki sanyaye tafara wanke kayan miyar da Naman
zainab kuma ta hada rishon tazuba kalanzir da aka kawo dashi cikeda galan.
Iya talatu daki tashiga ta dauko Mata tukunyoyinta guda biyu sabbi data siya Mata na aurenta
da Bello dabaayiba ta miqa Mata tareda kula Mai guda uku da plate biyu sai Kofi uku da cokali
biyar duka sabbi Saidai bawai masu tsada bane kawai dai Babu laifi.
Zainab ba wata gwanar aiki bace Saidai fira datake taya nadiyar dashi harta gama abincin,
Tuwo tayi na shinkafa da miyar busashen ku6ewa dataji Naman kajin gidan har wani qamshi
yakeyi har maqota
Dattiya daya fesawa idi Suka kasa Suka tsare a majalisarsu ta dattijan anguwa suna jiran dare
yayi suje suci banza Dan kuwa shima idi cewa yayi wlh daga yau tareda dattiyan zasu riqa ci
tunda ai tare sukeshan wuyarsa idan yatashi Rashin mutuncinsa akansu.
A sabuwar kula zainab ta dibarwa zakin komai aka goge aka Kai masa daki tareda plates din da
sabbin cups dinta.
Iya talatu harna dumame ta Diba a qaton kwanonta tashigewarta daki.
Babansu ma cika masa wata tsohuwar kula sukayi kafin Suka zauna sukaci nasu zainab tabar
gurin
Itakuma ta dauki rushon tashigar tsohon dakinta tareda galan din keron ta fito ta tattara gurin ta
share gidan tas Takoma ta sharo dakinsu tazo tadibi ruwa tashiga wanka.
Tana fitowa tayi alwala ta nufi daki.
Komai Bata shafaba bayan spray dinda ya siyo Mata Wanda shima yakusa qarewa ta saka bra
saita maida zaninta iya qugu tafara neman rigarda zata saka sai kawai taji shigowarsa gashi
akwai nepa.
A rikice ta miqe tsaye jikinta na rawa sbd tsananin kunya da fargabar yanda take din.
Aka bra dinta data 'dan yi Mata kadan qirjinta sun fito ta gaban idanuwansa Suka sauka atake
ya dauke Kai Yana daure fuska musamman dayaji maqoshinsa yawu na neman qin wucewa.
Hijab ta fizga da sauri tasaka tareda durqusawa ta dauki rigar dake Daman kayanta kawai
tafara qoqarin zurawa.
Zama yayi bakin katifata tareda kunna wayarsa Yana latsawa sai kawai yaga yama rasa Mai
zaiyi ya miqe tareda sakin tsaki yayi wurgi da wayar Yana cewa"
Ke bani abinci.
Aje hijabinta tayi bayan tagama saka doguwar rigar bacci har qasa Mai kauri ta nufi kulolin
takawo gabansa tareda plate da spoon.
Koda yaga tuwo ne bai wani damuba Dan dama shi bazai iya tuna yaushe rabanda yaci tuwaba
arayuwarsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Sanin baya mugun ci yasa tazuma masa daidai yanda tasaba ta miqa masa.
Ba laifi yaji dadin abincin Saidai Sam bayason yaji ko kadan can qasan maqoshi yace"
Karki Kara saka yaji abinci wuwuyar yarinya kawai.
Ruwa daya ta dauko takawo masa ta tayarda sallar magriba da akayi tun dazu.
Tana Gama sallah ta tattara gurin ta fita da kayan takai tsohon dakinta inda ta ajiye risho.
Kodata dawo Yana kwance ya rufe idanuwansa kamar mai bacci sai kawai ta zauna itama tana
shafawa qafafuwanta Mai sbd akwai sanyi sosai.
Su dattiya kuwa koda Suka zauna cin abinci Babu Wanda Wai washe dukkanin haqoran da
Allah yayi masaba shida mal idi sbd farin ciki mal idi yace"
Yaushe rabo""""
Cinyar kaza dattiya yakai baki Yana cewa"
Eh ai wahalarmu ce zamu rage anan tunda Allah ne kawai yasan iya hasarar daya goga Mana.
Mal idi da kunnuwansa sukai wata rawar da'din miyar da Naman yace"
Wlh mudai wannan Abu gwara da akayi,
Wata gararma sai Abu yayi nisa qilamafa ayi maka sarkin maroqa kaga ni Kuma mataimakinka
ko.
Wani murmushin Jin dadi dattiyan yayi Yana cewa"
Hmm ranarda akamin wannan sarautar ai kaima kasan Banda wani mataimaki bayai Kai.
Iya talatu dake jinsu a tsakar gidan tace"
Allah dai ya shirya wainnan masu mutuwar zuciyar.
Washe gari tunda wuri ta tashi tahau aikin gidan tadora ruwan zafi ta cika masa flask tadawo
tahau aikin yimasa breakfast lokacin Yana ciki Yana motsa jikin daya Saba.
Doya ta soya masa da kwai Wanda zainab ce take qara nuna Mata yanda akeyi harsuka Gama
ta adibar masa nasa takai masa lokacin Yana gurin wanka tana cikin gyaran dakin yashigo tana
gamawa ta fice Dan zuwa wanke wanke.
Yana gama cin abinci ya fita.
Sai bayan azahar tsamu ayyuka suka rage Mata tayi wanka tayi sallah ko hutawa batayiba iya
talatu takirata suka hau wani aikin.
Da daddare kodata kwanta jikinta har wani ciwo yakeyi sbd wahala Dan aiki Kam yayi Mata
yawa fiyeda da can.
Duniya sabuwa aka bude a cikin gidan sbd cima Kam yanzu ansamu safe Rana dare Kuma
lafiyayyan abinci sukeci wani lokacin saiyanajin takaicin yanda tun farko baya Basu abinci tunda
yanada halin hakan wata qilama hakan da tuni yasa kawun ya daina yawon ta zubar dinsa.
Dattiya kuwa yanzu da aka bude Jin dadi sabo duk inda yake lokacin cin abinci nayi to Yana
gida Dan kuwa yanxu wani lokacin idan yaci yaji yayi nas har wata kasalar futa yawon maula
yakeji saiyayi zamansa Yana Shan iska Yana sakatar haqori cikin wata irin Isa Yana hura hanci.
Zainab ma ba laifi ta 'dan rage yawo sbd ganin kusan abinda takewa yawon yanzu suna samu a
gidansu Dan dama yunwa ce kesata yawon batanan batacan.
Nadiya kuwa yanxu Kam tafara zama abin tausayi sbd duk wata wahala tana cikinta Dan kaf
gidan aikinsu suci su qoshi ne kawai duk wata wahala ta gidan ita keyi,
Ko cokali Babu Mai iya dagawa sai itace keyi gashi sanyi yashigo sosai sai abin yafara tabata
Dan kuwa kumburi tafarayi sbd sanyi dayayi Mata mummunan kamu yatsar qafafuwanta har
wani yankewa sukayi sbd aikin ruwa da sanyi.
Gashi bikin Yaya dahiru yazo sosai ake hidimar biki a gidan sai abun ya ninkar Mata ko zama
batayi idan gari ya waye sai dare idan ta kwanta tayita juye juye sbd ciwon jiki da qirji.
Yana lureda ita duk baqar wahalarda takesha idan tazo da dare tanata murqususu sai abin ya
ringa qular dashi Amma dai ya qyale yaqi Mata magana.
Abinda yabawa kowa mamaki shine kayanda ya dinka Mata a dinkensu masu 'yar tsada har
kala biyar Wainda aka dinko daidai jikinta har zainab na tsokanarta da cewa"
Lallai Yaya Zaki har hannuwansa sun haddace girman komai na jikinki..
Rintse ido tayi da sauri tareda barin gurin zainba din tana saka kayan cikin kayanta Suka fito
tana cigaba da tsokanarta.
Ranarda akayi biki aranar da daddare kasa bacci tayi tafara juye juye dafe da qirjinta tana
hawaye cikin tsananin azaba ga tarinda takeyi mai tsananin zafi a maqoshinta Wanda shiyasa
tafara Yi kamar zata fice hayyacinta.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan
numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863
_*Mamuhgee 19*_
Jin nishinta da motsin data daina yasashi daukar wayarsa ya kunna fitila ya haskata,
A miqe take jikinta gabaki daya ya saki ta daina motsi sai bakinta dake budewa alamar tanason
Jan numfashi Amma takasa.
Aje wayar yayi lokaci guda ya isa gurinta tareda cirota da sauri ya Dora kan katifa Yana Kiran
sunanta tareda 'dan jijjiga fuskarta Yana kallonta cikin tashin hankali Saidai Yana qoqarin
dannewa.
Sakewa jikinta yaqarasayi numfashinta ya tsaya cak.
Wannan karon da qarfi ya girgizata Amma Sam tariga ta some batasan yanayiba.
Bai tsaya komaiba ya dauketa tareda wayarsa da key din mota da atm ya fito Yana kallon
fuskarta yanaji kamar zuciyarsa zata buga.
Qafa yasa yayi kyauren fita gida shuri 'daya take qofar tabude ya fice baiko tsaya nemansu
nanuba ya nufi motarsu dake pake gurin masallaci ya bude da hannu daya yasakata.
Yana qoqarin shigane Nanu yafito riqeda fitila da wata sharbebiyar Adda tana kyalli cikin duhun
sbd motsinda yajiyo.
Ganin mutum na qoqarin shiga motarsu yasa ya Dalla fitila ga mamakinsa yaga Zaki da sauri ta
qaraso Yana cewa"
Sarki matsala ce????
Batareda ya kallesaba yafara qoqarin shiga motar
Nanu yayi saurin cewa"
Sarki kawo naja kamar zaifi saika kulada ita a bayan.
Miqa masa key yayi sbd bayason doguwar hayaniyarda zata tayarda mutane suka bar gurin
suna Hawa titi Nanu yabata wata irin wuta na mugun gudu.
Dattiya dayaji anyiwa qofar gidan mugun bugu cikin bacci yayi mugun zabura tareda lalubar
fitilarsa Yana qoqarin kunnawa Amma taqi kunnuwa.
Ahankali ya miqe tsaye tareda nufar qofa Yana tafiya ahankali.
Bude qofar dakin yayi yafito yanabin bango atake qirjinsa yayi mugun bugawa lokacinda ya
hango qofar gidan a wangale
Wani mugun zufane ya karyo masa yadawo daki da sauri qafafuwansa na mugun rawa yasawa
qofar dakin sakata yafara lalubar inda talatu take.
Da Dan qarfi ya buga qafarta ta zabura tana cewa"
Wayyo Allah innalillahi.
Wani sabon zufane ya gangaro masa ya bude baki qasa qasa yace"
Talatu yau ranar rabuwarmu tazo wlh barayine Suka shigo Kuma tunda kikaji tsit wlh sungama
kashesu Zaki Ni wlh bantara komaiba ahaka nazo duniya ahaka zankoma yau mutuwar
wulaqanci zamuyi Dan wlh kashemu zasuyi tunda bamuda abun Basu....
Yana kaiwa nan sai kawai muryarsa ta fara rawar kuka yanason dannewa.
Iya talatu kuwa kuka take sosai harda shesheka tana tuna irin rayuwarda sukayi a baya tanajin
tausayin zasu mutu yau wace irin rayuwa zasu tarar.
Har akayi Kiran asuba suna zaune suna jiran tsammani zuwa lokacin tuni idanuwan iya talatu
sukayi luhu luhu sbd kuka dattiya ma yayi sharben hawaye harya gaji.
Saidaya tabbatarda anfito masallaci har gari yafara Dan washewa kafin ya bude daki ya leqo
Yana qwalawa zainab Kira.
Cikin maganin bacci ta fito tana amsawa.
Yana ganin haka saiya qarasa fitowa Yana goge zufa ya daure fuska yace"
Waike Sam bakya tashi sallah kan lokaci ko??kullum Saidai baccin lalaci maza wuce kije kiyi
sallah kafin na fasa bakinki a gurin.
Wucewa tayi tana murza ido tana Dan tura baki.
Shima a dubarance yayi alwalar dan karta gane shima baiyiba yakoma daki ya tayarda sallah
iya talatu ma said lokacin ta fito tayi alwala Takoma yin sallah.
Suna isa asibiti a gaggauce aka karbeta sbd yanda jikinta yayi sanyi sosai kamar zata sandare
Dan tuni ta miqe kamar bazata iya lanqwasuwaba.
Likitocin dake on call (NIGHT DUTY) suna ganinta Suka gano abinda ke damunta Dan kuwa
data Jima ahaka to shikenan za'a iya rasabata dankuwa zata iya mutuwa abinda yaji likitocin na
fada kenan kafin ace yafito.
Zama yayi kan waiting kujerar dake bakin gurin tareda Dan rintse idanuwansa ya fitarda
numfashi Mai qarshi idanuwansa na kadawa zuwa ja sbd bacin Rai da tension.
Nanu dayaga yanayinsha Saida yasha jinin jikinsa Yana zazzare ido a qofar Yana fatar kar
abinda yasamu nadiyar sbd sarkinsu.
Saida gari yayi haske sosai har lokaci yaja guraren qarfe takwas wata