Showing 6001 words to 9000 words out of 81438 words
Chapter 3 - BURI DAYA Complete Hausa Novels By Mamuhgee .pdf
zasuyi miki dasun kamaki????
Share hawayenta tayi sbd tasan tabbas rayuwar Lagos dinnan idan har bakada mai kulawa
dakai to sunan rayuwarka lalatacciya,
Tabbas zata amincewa neyo suyi aure dataje tafada halaka.
Bayan sungama yanke shawara acikin Daren yakaita har qofar gida tashiga kafin yadawo da
niyar gobe zasuje adaura musu aure.
Haka kuwa akayi washe gari sukaje wani masallacin yorbawa aka daura musu aure bada sanin
azumi ba dagacan suka tattara Suka bar Lagos sukai abekuta.
A abekuta yayi amfani da kudinsa Suka kama hayar daki daya da toilet inda yasiyo musu komai
na amfani da daidan gwargwadon abinda suke buqata Suka fara shimfida rayuwarsu inda
yasamu aiki awani garage dake kusa.
Bayan aurensu da wata biyar ciki da cutar sanyi ta bayyana ajikin ruqayya nan hankalin neyo
yatashi gashi yanxu abincima gagararsu yakeyi saiyayi daqyar yake samowa.
#MAMUH*_Buri daya_*
*_Mamuhgee5_*
Cikinta na wata bakwai Abu yayi tsanani Dan kuwa kumburi ne tayi tako Ina Wanda ya sauya
kamanninta tsaf Dan kuwa ko qafafuwanta daqyar take dagawa.
Lokacinda abin yayi tsamari yahada kudi daqyar yakaita asibitin kudi atake Suka Bata gado sbd
ganin mummunan halinda take ciki Suka tabbatar masa lallai dole za'ayi mata aiki acire abinda
ke cikinta Dan kuwa za'a iya rasasu su biyun sbd sanyi yakama qashi da bargon jikinta sosai ta
yanda yazamo ha'dari ga rayuwarta data abindake cikin,
Kudi naira dubu saba'in Suka masa total tareda basa telar biyan kudin.
Kallon telar yasakeyi tareda rintse idanuwansa dasukai mugun jajir suna neman zubo ruwan
tausayin ruqayyarsa.
Fitowa yayi asibitin Yana tafiya da qafa kan hanya Yana tunanin shida ko dubu 'daya baida ina
zai samo dubu saba'in?.
Zama yayi bakin wani babban shagon siyarda kayan masarufi ya rafka tagumi baiko damu da
ranar dake dukansaba.
Yafi awa biyu zaune agurin har wasu na basa sadaka idan sun fito atunaninsu bara yakeyi.
NEYO"""yaji ankira sunansa ya dago ahankali cikeda sanyin jiki.
Yayi saurin miqewa Yana qoqarin tattaro kuzari yake kallon Wanda yakira sunansa Yana cewa"
Dikko Kaine nake gani haka????
Rungume juna sukayi dikko na sakin wata dariyar jin dadi ya janye Yana kallon neyo daga qasa
zuwa sama yadan yamutsa fuska Yana cewa"
Neey what's happening?
You look terrible??
Numfashi neyo yasaki tareda gyara zaman rigarsa data gama yimasa yawa yace"
Dikko matata na asibiti aiki za'ayi mata sbd ceto ranta da abinda ke cikinta Kuma ana neman
kudi nera dubu saba'in Wanda wlh banidasu banida inda zan samesu.
Jansa dikko yayi sukaje mota yashiga tareda bude masa shima yashigo ya tayarda motar Suka
fara tafiya
Batareda ya juyo daga kallon hanyaba yace"
Neyo kasan ni,
Kasan yanda nake Kuma bazan taba canxawaba,
Bana aikinda nasan banada riba Dan haka bazan iya baka dubu saba'in ba kyauta Saidai
zanbaka wani aiki dazakai kasamu dubu 'dari biyar Wanda zaka biya kudin aikin matarka harma
kayi lalurar komai na bayan haihuwar.
Kallonsa NEYO yayi batareda mamakiba sbd yasan waye dikko
Yasan akan kudi baida yarda ko ragi ko akan waye,
Duk aikinda zaiwa dikko yabashi dubu dari biyar yasan ba qananan maqudan kudi shi dikkon
zaisamuba Saidai yasan aikin dikko Babu Wanda ba gur6atacce neba
Dole wani mugun abun ne zai masa.
Sauke numfashi yayi yakallesa yace"
Wani irin aikine??
Wani sample na maganin chloeziadenes zaka samomin a matatar magunan qasa dake cikin
Lagos
Na dauko 6oyayyun ma'aikatan daga qasar China zasumin irinsa a sirrintaccen kamfanin buga
maganin bugina zamu sakarwa mutaneshi duk da Sha kawai zasu riqayi basusan bugineba
Babu maganin cutar dazai ringa musu.
Kallonsa NEYO yayi tsawon mintuna hudu Yana jinjina Rashin Imani da mugun son abin duniya
na dikko sbd kowace gurbatacciyar sana'a ya iya bayako jin shakku da fargabar yanda mutane
ke rasa rayukansu akan abubuwan dayakeyi.
Girgiza Kai yayi kawai sbd shi yanxu bayako sha'awar rayuwa da dikkon,
Kai tsaye yace"
Fadamin inda zanje nakaima idan nasamo,
Kuma ka tabbatarda kudina nanan ajiye hannunka ayau zan kawo maka sample din da yardar
Allah.
Dariyar jin dadi dikko yayi sbd shiyasa yake mutuwar son mu'amala da neyo ya iya aiki ba tsoro
ba shakka ga sa'a dayakeda ita.
Bakin wani qaton factory dikko ya tsaya da motarsa yacewa neyo"
Idan kadauko kasameni bayan gari gidan mai mai suna Dilla filling station,
Best of luck.
Maimakon yaga neyo ya fita saiyaga ya fada wajen motar Yana mulmulawa kamar baida Rai
take kansa dake bubbuguwa da dutse yafara fashewa bai damuba sbd ganin masu tsaron gurin
suntaso suna qoqarin taimakosa sbd sunga lokacin aka jefosa daga cikin motar data gudu.
Dikko bai tsaya komaiba ya fige motarsa da mugun speed Yana wani shuumin murmushi sbd
yasan aikine neyo yafara.
Daqyar Suka taresa suna qoqarin dagosa sbd tuni fuskarsa ta baci da jini kamar Wanda aka
Dade ana ganawa azaba,
Sam basuga numfashi atareda shiba nan Suka daukosa sukayo ciki dashi sbd basuda fargaba
ko tunanin komai akan factory dinsu tunda sumsan tsaftataccen aiki sukeyi ba gurbatacceba
bare suji shakkar shigoda wani.
'yan lokitocin dake cikin factory din Suka dubasa sukai masa dressing shidai yanajinsu yaqi
motsawa Saidai numfashinsa dake fita ahankali alamar dawowar numfashin.
Bayan futar dukkaninsu daga 'dan dakinda Suka taimaka masa ya miqe da sauri tareda fara
bincike cikin dakin cikin sa'a yasamu uniform din ma'aikatan gurin yadauki daya yasa da sauri
tareda Jan hular uniform din yarufe fuskarsa yafito Yana sunkuyar dakai sbd kar aganesa atake
ya saje da 'dinbin ma'aikatan dake gurin.
Kai tsaye computer room dinsu ya nema ya sidada yabude qofa ya leqa yaga numbern room
dinda samples suke yafito ta nufi room 17 inda yaci babbar sa'ar security din qofar abude yake
wani doctor Yana ciki da sauri yafada dakin
Doctorn na juyowa yakai masa wani mugun duka a hanci atake likitan ya yanke jiki ya some
Nan yafara dudduba sample dinda dikko yace
Yanayi Yana kallon qofa.
Takun tahowa yaji daidai lokacinda yagansa yayi saurin dauka daga cikin wani box mai kamar
fridge yasaka cikin wandonsa yayi saurin ficewa.
Daqyar ya mayarda kansa dakinda aka barsa yayi saurin cire uniform din ya mayarda kayansa
yakoma Yana kwantawa aka bude qofar.
Yanaji an buga alarm na danger ya miqe ya fito da satar jiki ya iso gate sukuwa security Suka
bude masa ya fice.
Gudu yakeyi sosai sbd wajen garine sosai
Kusan kilometers tara ne tsakaninsu da cikin gari.
Daqyar ya kawo titi Yana hango mota tafe yayi sauri daga hannu Saidai bai gama aje hannunba
motar tayi sama dashi yafado gefen titi jini na fita jikinsa sosai.
Atake mai motar ya gudu yabarsa nan
Rai hannun Allah.
Jini yake fitarwa sosai gashi ko motsi baya iyayi atake yasan mutuwa zaiyi Saidai yayi baqin
cikin mutuwa cikin wannan yanayin gashi ruqayya da cikinta baisan wane hali zasu shigaba..
Dishi dishi yake gani idanuwansa na neman rufewa yaga dikko yazo kansa ya tsaya tareda
wasu yaransu biyu.
Cikin Rashin tausayi dikko ya girgiza Kai yace"
I'm really sorry best friend Amma Kona daukeka yanxu lalura zaka zamarmin gskia sbd dai
mutuwa zakayi Dan haka bazanyi hasarar kudina gurin kaika asibiti muyita wahalar banxaba
koba komai kaga Allah nasona da yawa shiyasa hakan tafara sbd kar kudina dazan baka
suzama west...
Kai ku cajesa kuciromin sample Dina.
Yanaji Yana gani Suka ciro sample din daga jikinsa Suka wuce Suka barsa hawaye na
gangarowa daga idanuwansa harsuka rufe.
Asibiti sunyi jiran dawowarsa har kwana biyu ba labarinsa tuni Suka sallameta nan hankalinta
yayi mummunan tashi tafara nemansa lungu da saqo cikin abeokuta
Ga ciwo ga nauyin ciki Amma haka take yawon nemansa Takoma kamar mahaukaciya tun ana
Bata sadaka tana qin karba harta fara karba.
Bayan wata daya wani abokin aikinsa daya gaji da zaryar datakeyi gashi yace Takoma gida taqi
ita saitaga neyo
Kawai sai yazo yasanar mata anga gawarsa hanyan Lagos sunje sunmasa sallah sun rufesa
Ban yabata kudin mota yace Takoma gida arewa.
Tanajin haka tayi tawakkali Bata tsaya Bata lokaciba bayan kwana biyar tadawo arewa.
Ranar data isa agalabaice ta isa sbd kwana biyu ahanya suna tafiya kodata iso tafara ficewa
hayyacinta.
Talatu na zaune tsakiyar gida da tsohon cikinta tana Shan radio taganta tashigo tana daddafa
bango.
Gyara zama tayi tareda kallonta dakyau ta tabbatarda ita dince ruqayya.
Batayi mamakiba ta kalli qofar dakinta tace"
Dattiya saika fito kaga baqin magribar dasuka sauka
Dama nafada komai Daren dadewa saita dawo
Gashinan harda 'dan kawu aka samo maka.
Fitowa yayi Yana saka hula akai Yana ganin ruqayya ya zaro qananun idanuwansa akan cikinta
hankali tashe yace"
Ruqayya mezan gani ajikinki?
Nida nasaki jiki duk Randa Zaki dawo da 'dibbin dukiya Zaki dawomin shine kika kwaso min
wannan iskancin Lagos 'din???to wlh ko zama bazakiyiba dashi acikin gidannan maza wuce tun
kafin nayiwa shegen jikinki duka...
Wato tunda na hanaki auren tubabbe shine kika 'daukomin abinda yafi auren tubabben kunya
da takaici.
Wata dariya talatu tasaki tana cewa"
Dan Allah da gaske dattiya kasan kunya dahar kake gudun abin kunya?
Rufe ido yayi yafara zazzaga mata Rashin mutunci sbd shi cikin bai wani damesaba kamar
yanda tadawo hannu rabbana kamarma wata mabaraciya...
Cikin tsananin azaba ta durkushe gurin sbd naqudar data dirar mata lokaci 'daya.
Beda yanda zaiyi Dole yaje yakirawo shafa'atu matar idi da innaje sukazo dole akai cikin dakinta
tun na budurcinta Suka fara qoqarin karbar haihuwarta.
Cikin ikon Allah ana Kiran magriba ta haifi yaronta Wanda yake fari tas jinin Igbo tamkar
mahaifinsa.
Cikin qanqanin lokaci aka shiryata
Dattiya da fada dakomai yasiyo kala biyu da sabulun jarirai guda daya da man jarirai yakawo
aka sawa yaron.
Dattiya kuwa Duk yanda yake fada da kukan baida dole yake yimata wasu abubuwan itada
jaririnda da kanta tayiwa yaronta huduba da sunan mahaifinsa wato *_ALEEYU HAYDAR
NEYO_*.
Yanaji yana gani ya yanka mata 'dan ragonsa Yana sake jaddada mata aro yabata zata biyasa
kudinsa tace taji idan ta warke zata biyasa.
Ahaka suka fara Gina wata sabuwar rayuwar mai cikeda qalubale gashi bayan haihuwarta da
wata biyu talatu ta haifi namiji itama aka saka masa suna dahiru.
Dole ta mayarda hankali tafara sana'a sbd lalurarta data Zaki Dan kuwa tun Yana yaro take
kiransa Zaki tunda sunan babansa yaci,
Babu Wanda yataba tambayarta ya akayi tasamu cikin Zaki sai itama Bata bi takan zancenba
tafara sanointa Dan tallafawa rayuwar 'danta daya girma harta sakashi makarantar primary.
Zaki ya taso a cikakken marajin yaro sbd ganin irin rayuwarda akeyi acikin gidansu ta Rashin
taimako da tausayi kowa tasa ta fishesa akeyi a gidan,
Idan kanada kaci idan bakada ka kwana da yunwa,
Ga shegen son kudi da abun duniya tsakanin talatu da dattiya baasan Wanda yafi waniba.
#MAMUH*_Buri daya_*
*_Mamuhgee6_*
Sanin Babu Wanda ke ragarwa mahaifiyarsa a gidan yasa Babu Wanda yake ganin girmansa
acikinsu saima dai idan Yana gida Babu mai iya yanka mata Rashin arziki sbd tsoron Rashin
mutuncinsa Dan kuwa Duk da yake bamai shekaru sosaiba yanada matuqar kwarjini dakuma
farin jini saidaifa baida sauqi ko kadan idan katabasa.
Sosai dahiru yamayarda hankali kan karatu Amma Zaki Sam yaqi mayarda hankali ga manyanci
yafara kama umman tasa yanzu Bata iya cewa kullum saitaje makaranta taga idan yaje,
Yau zuwa gobe Rashin zuwa ahaka dai yagama primary yashiga js 1
A wannan lokacin ne dattiya ya auro amaryarsa daga wani qauye dasukaje maula gurin wani
mai kudin qauyen,
Amaryar tasa yarinyace 'yar kimanin shekara goma Sha Tara shiyasa abin yafi baqantawa iya
talatu yarasa wadda zai aura sai yarinyar daya kusa haihuwa.
Tun zahra'u najin wuyar rayuwar gidan harta Saba da taimakon ruqayya Dan kuwa tun satin
farko dattiya ya daina siyo mata abinci yace tashiga Sanaa Dan kuwa gidan kowa sanaa yakeyi
yaciyar dakansa dukda idan yayo samu yakan siyo mata tsire da nono sushige dakinta su cinye
yace ta goge bakinta.
Ahaka shekaru Suka ja harta samu ciki
Lokacin ruqayya ke kulada ita sosai sbd cikin yazo mata da matsaloli gashi na farin tuni ta
kumbure tako ina
Sosai ruqayya kejin tausayinta.
Dattiya ma tuni hankalinsa yatashi sbd har cikin ransa yanason zahra'u sbd biyayyarta da yanda
ta iya zama acikinsu ta koyi hakuri da duk halayensu.
Zaki madai duk gidan itace abokiyar shirinsa anty zahra'unsa abinda take fada mata ko
ummansa baya fada mata sbd karta masa fada ita kuwa anty zahra'u Saidai tayi masa nasiha.
talatu tahaifi mace da sati biyu
Zahra'u ta haihu Saidai tana haihuwa atake Allah yakarbi ranta yabar 'yar jaririyar data Haifa
wadda taci suna *_NADIA_* 'yar talatu kuwa aka saka mata suna ZAINAB.
umman Zaki itace taci gaba da rainon Nadiya wadda ta taso cikin maraicin uwa da uba Dan
kuwa dattiya tunda zahra'u ta rasu kamar Wanda aka zarewa notin Kai 'daya ya qara zaburewa
Sam baya ragawa uban kowa yanzu ga shegen son kudinsa daya qaru
Danma wani lokacin Zaki na shige masa gaba sbd ta'addancin daya fara qarfafa acikinsa.
Nadiya tunda tafara girma umma ruqayya tagano Bata iya magana suka fara yawon asibiti
Saidai koyaushe kudine ake tsago musu Wainda Batasan Ina zata samosuba shiyasa suka
dangana,
Zaki da Nadiya Sam Babu wata jituwa sbd Sam bayason iskanci da raini bare wata banzar
shagwaba wadda umman ke shagwabata duk da haka alqawrine ya dauka da yardar Allah
shine zai nemowa nadiyar lafiya kowace irin qasace tunda ummansa naso.
Ahankali shekaru suka shude Nadiya nada shekara goma Sha biyu ummansu ta rasu tabarta
cikin maraici Dan kuwa tuni rayuwar gidan tafara mata tsanani duk da ba duka ba zagi Saidai fa
rayuwar gidan wata juyayyar rayuwace ta kowa da kalar halinsa da dabiarsa,
Makaranta ma tunda tagama js 3 sai karatun ya tsaya kasancewar Bata mgn gashi batada
Wanda ke janta a jiki da kulawa bare tasamu qwarin gwiwar yin karatun.
*_SARKI ZAKI NEYO_* yazama riqaqqen sarkin yan daba da Babu kamarsa a yankin Dan
kuwa kowa na tsoronsa da shakkarsa,
Babu ubanda yake tsoro sbd girman mulkin dayake bazawa a dabanci gashi manya sun daure
masa gindi ko hukuma Bata tabasa,
Daqyar ya hada diploma wadda itama rabi zuwa rabi Rashin zuwa,
Shahararren mai kudi DIKKO DILLA dake zaune a qasar south Africa da matarsa 'daya da
'yayansa biyu mace da namiji, yadawo qasar Nigeria sbd wani boyayyan burinsa dayakeson
cikawa akan wasu takardu dayafi shekaru goma Sha takwas Yana so Saidai bazai samesuba
Saida jajirtaccen mara tsoro wato Zaki Wanda ya dade Yana bibiyarsa sbd labarinsa da aka
kawo masa akan izzarsa da tarin mulkin dayake bazawa a troway yakuma tabbarda shine kadai
zai iya samo masasu shiyasa yajaza ajiki tun dawowarsa Nigeria yazamto shine babban
yaronsa Wanda duniya ta shaidar Dan kuwa yafi yarda dashi akan 'dansa dayake kusan sa'anni
da zakin kokuma ma ya girmi zakin.
Zaki shine yasan dukkanin wani sirri na dikko na dukkanin gurbatacciyar sana'arsa da
dukiyarsa,
Duk wani aiki dikko baya shawara da kowa sai amintaccensa Zaki Dan kuwa ba laifi Yana
matuqar qaunar Zaki duk da shima wani lokacin Zaki baya ragar masa Kuma shima ba'a taba
Wanda yaji Yana shakka da fargababa kamar Zaki Dan kuwa Zaki shine yaronsa Amma shine
yake shakkar Zaki ba zakine yake shakkarsaba.
Hakan yasa *_AMAAN DILLA_* da mahaifiyarsa *_MRS DILLA_* tsananin kishi da tsanar zaki
wanda sukaci alwashin nakasta rayuwarsa ta yanda har abada za'a manta da sunan zaki
atarihi.
Zaki tun bayan rasuwar ummansa Babu Wanda yake qauna samada Nadiya saidai Bata
gabansa har mantawa yakeyi da ita musamman dayaga irin rayuwar kadaici da maraicin
datakeyi a cikin gidan idan bai dauke idanuwansa akansu ba zai raba dukkanin yan gidan da
wasu sassa na jikinsu ne kawai shiyasa ya tattarasu ya watsar,
JABIR shine mutum na biyu da Zaki yake tsananin qauna aryuwarsa sbd tsintosa dayayi
adaidai lokacinda dikko Dilla yasa aka kashe masa iyaye shima aka biyosa akashesa shine ya
kubutar dashi duk da shima baisan dikkone yasa aka kashe iayayen jabir ba,
Abin yaso taba qwaqwalwar jabir sosai Dan har tabin hankali yayi tsawon lokaci Zaki na kula
dashi agidan
Kosu baba dattiya da iya talatu sunci wuyar ciwonsa sbd yanda yake hauka tuburan
Haka Zaki yayita wahala dashi harya warke yazama babban yaronsa shima duk da ba wata
tazarar shekarune a tsakaninsu ba,
Zakine ya gabatarwada dukkanin yaransa na kusa Dana nesa jabir amatsayin JJ baban
yaronsa wato magajinsa.
JJ ayanzu duniya baida kamar Zaki Wanda yakejinsa tamkar jininsa Dan zai iya bada
rayuwarsa akan zaki.,
Lurada abinda Zaki yafiso duk duniya yasa baida abin qauna kamar Nadiya,
koyaushe shine mai tattali da bawa Nadiya kulawa duk da Zaki ko ajikinsa Saidai Yana fada
masa bayason kowa nashiga shaanin cikin gidan.
Dattiya da talatu kuwa tuni Zaki yazamar musu uban Dole Dan kuwa cin uban kowa yakeyi a
gidan shiyasa ba'a masa ganganci,
Shikuwa dattiya Rashin danganarsa kesa Yana shiga huruminsa
Shikuwa yasa adaidata masa shi.
Zainab Sam Bata jin magana akwaita dason rayuwar qyale qyale Wanda yasa kullum take cikin
kwashe kwashen qawaye da samari Wanda koda Gigi basa zuwa qofar gidan fira sbd hurumin
zakine Saidai su hadu wani wajen,
Zakine kawai ko sunansa taji take shiga taitayinta sbd tsoronsa sanin baya wasa yanzu ne zai
sauya mata kamanni hardai idan yaji tanayin Rashin kunya cikin gida.
Dahiru dai malamin makarantar secondary ta kwana ta maza a wata local government shiyasa
Sam baya zama acan yake zaune staff quarters.
**********
Babban gurin taron na stadium yacika maqil da manyan qusoshin qasa shiyasa securities sukai
yawa agurin ga yan jaridu da masu tv stations sai dauka sukeyi ana cikin haka shugaban taro
dikko Dilla ya iso da babban yaronsa