Showing 60001 words to 63000 words out of 81438 words

Chapter 21 - BURI DAYA Complete Hausa Novels By Mamuhgee .pdf

Mamughe   

23 Nov 2025

2030

yayi sbd jin nauyin sunan akaro na farko.

Kallonsa haydar yayi yaji wani iri shikansa sai ya basar da cewa"

Let's go.


Zama sukai a palon haydar na qurya
Haydar ya miqa masa glass of raspberries juice ya zauna suna facing juna ahankali yafara
cewa"

Dr sayyid yazo headquarter da Kash masu dibbin yawa akan bailing Dina gurin CM Kuma cikin
saa ya amince yace zai sakeni anjima da dare Amma ana Sakina nabar qasar,
Akan haka Suka gama magana Dr sayyid na tafiya cm yakirani har office yayi min bayani tareda
nunamin kudi da passports da Visa tareda ticket dinda Dr sayyid ya bayar akan abani Ina fitowa
cikin Daren naje airport akwai jirginda zanbi zuwa US.

Cikin Daren nan am yazo da kansa tareda yaransa hudu tareda dukiya Mai yawa akan sunason
abarsu su kunnawa cell Dina wuta.

Cm baya headquarter acikin Daren Ina kwance inaji Suka kunnawa side dinda muke wuta sosai
atake gobara ta tashi.

Shiru ya danyi cikin tuno irin azabar dayasha alokacin kafin yacigaba da cewa"

Daqyar da yardar Allah nasamu na buge window na fada baya bayan kusan gefen jikina yafara
kamawa da wuta Amma I couldn't give up sbd my family needs me.

Naso dawowa gida alokacin Saidai hakan zaikawo fitintinu da dama Wainda nasan Dilla zai iya
kashe kowa a familyna without anyi hesitation,
Daga nan ne naje office din cm na balle nashiga na dauki visa da ticket dinda akayimin da

check din kudin nafice.

Aranar na wuce sbd qonuwata is getting worst.

I suffer,
I suffer JJ,nayi rayuwar kadaici,baqin ciki,azaba,wahala da gwagwarmaya..tun a cikin jirgi
bansake sanin inda nakeba sbd qonuwata is very deep and serious.

Daga airport hospital aka wuce Dani and I spend morethan 2month a kwance asibiti.

Bayan na warke sun sake sakoni jirgi Suka dawo Dani Nigeria acikin Daren direct gida nadawo
and unfortunately Ina xuwane cikin tsakiyar Daren na tararda abinda yafaru Wanda adaren suka
kashe zainab...

Naganku lokacinda kuka fito,
Nabiku tun adaren nake bibiyar rayuwarku har lokacinda tayi zama a asibitin Zurich,

Sbd ita nakoma Zurich I started my business from there,

Every morning kafin fita aiki sainaje gurinta hakama da yamma before going home.

Ahaka Ina taredaku a asibiti ta haihun Saidai bazan iya zuwa na karbi 'yataba nayi Mata addua
duk sbd dillas.,

Bayan haihuwarta tadawo lafiya klau nakoma nashiga school a nan Zurich,

I spend 1 year Ina karatu Ina business din shipping cikin 5yrs nayi achieving duk wani Abu
danakeso ciki har soyayyan fammah akaina Wanda da itane dama zanshigo dillas...

Bantaba mantawa daku ba sbd koma meyene nayi nayi ne sbd ku...
Nayine sbd safey dinku,
Nayine sbd girman soyayyar....

Kasa qarasawa yayi sbd ja da idanuwansa Sukayi sbd tuno yanayinda suka rabu da ita jiyan
Wanda haryanzu abin ke cin ransa.

Rungumesa JJ yayi tareda buga kafadarsa ahankali ya iya furta karka damu zata saukane just
give her time.

Acikin Daren jirginsu ya sauka a starling city inda dad da kansa yaje daukarsu airport

Kallon juna Sukayi shida haydar kafin ya jawosa jikinsa ya rungumesa da qarfi cikin farin ciki
Mara iyaka yaugashi ga dansa.

Sunjima ahaka kafin Suka dunguma zuwa gida inda zuciyarsa ke harbawa da qarfi sbd yaune
Karo na uku dazai rungumi 'yarsa cikin jikinsa.

Ya rungumeta a Karo na farko a school dinta dayaje ganinta a boye itama Bata sanshiba
kawaidai ya daga Mata hannu Kuma taje da gudu.

Sai na biyu Kuma a garden din wasan yara dasukaje da nanny Nancy..

Mamanta ya tuno take yaji gabansa ya buga Amma a fuskarsa Babu Mai iya gane halinda
zuciyarsa ke ciki.

Suna Isa gidan dukkaninsu Suka fito zuwa ciki shikuwa duk takunsa daya qara bugawar
zuciyarsa yakeyi.


Dad ne agaba baby z tazo da gudu ta fada jikinsa tana ganin JJ tasake tayi gurin JJ tana cewa"

Yehhhhh nanny Nancy my daddy is back.

Dagata sama yayi cikeda farin cikin ganinta ya ajiyeta qasa Yana cewa"

I miss you my angel.

I miss you too Daddy.

Dan matsawa yayi tareda nuna Mata haydar dake tsaye Yana kallonta cikin wani irin tsananin
so da qaunar 'yarsa tsotsonsa da kawunsa yake gudun a haifar masa namiji
Take yasaki murmushi tareda ware Mata hannu aikuwa da gudu tayi gurinsa tana cewa"

Uncle you hia??

Daukarta yayi sama shima ya rungumeta tsam tsam yanajin soyayyar mamanta fiyeda kowane
lokaci.

Tsakiyar palon Suka dawo dukkaninsu har lokacin tana jikinsa sai farin ciki sukeyi shikuwa
idanuwansa nakan stairs akai akai.

A gajiye tadawo office sanye cikin traditional Milano gown lilac.

Kai tsaye tashigo palon riqeda keys da jakarta musamman datake jiyo hayaniyar baby z.

Tana shigowa a cikin idanuwansa nata idanuwan suka fara sauka qafafuwanta suka harde

atake saura kadan ta kife taku daya ya riqota Yana zuba Mata idanuwansa dasuka qarasa
rikitata tayi saurin kwacewa tareda Dan kallon gefensa ta wuce tana qoqarin sakin fuska tanawa
JJ oyoyo.

Bata wani tsayaba ta haye sama ta zauna tana jero ajiyar zuciya jikinta na Dan rawa.

Saidata nutsu kafin ta tashi tafada toilet tayo wanka tazo tayi Sallah tashirya saitakasa fitowa
takira nanny aka kawo Mata abincinta a daki.

Haka taqi saukowa har washe gari,

Cikin sauri tayi Shirin office zata fice gidan ta sauko ko gurin dad batajeba ta sulale ta fice.

Ko zama batayi a office ba aka bude qofar aka shigo ta dago zatai magana suka hada ido ta
daure fuska zatayi magana ya jawota jikinsa ya matseta tareda zuba Mata idanuwansa masu
mugun rikitata batareda yace qalaba.

Muryanta na rawa tabude baki daqyar ta iya cewa"

Let go of me please.

Please"takuma cewa muryanta na rawa.

Wani irin murmushi yasakar Mata take ta zaro ido tana neman some masa take abin yasake
sashi murmushi ba zato taji saukar kiss dinsa akan idanuwanta zata qarasa somewa ya cirata
sama gabaki daya ya fito office din da ita baidamu da kallon da ake musu ba yakaita mota yasa
Saida yadawo yashiga motar ahankali ya furta"
Nigeria zamu je a cikin Daren nan jirginmu zai tashi.

Da sauri ta kallesa gabanta na bugawa da sauri.

Gida Suka Isa ya bude Mata qofa ya wuce yabarta sake da baki tanabin bayansa da kallo.

Bata yarda da Nigeria zasu jeba Saida taga kowa na shiri haka tahau Shirin kayanta Dana baby
z.

A gurin cin abincin Rana tunda tazauna a dining din idanuwansa ke kanta Saidai abinda yafi
hautsinata shine yanda yakoma zakinsa tsaf kallonsa ma faduwar gaba yake sata.

Ganin takasa cin komai sai mutsu mutsu takeyi yasa ta miqe tabar dining din Takoma Palo.

Suna Gama cin abinci suka fice ko mintuna goma basuyi da fitaba akai knocking tana budewa

taga order ce akayi ta honey pancakes da sunanta.

Murmushi ne ya subuce Mata sbd tasan waye yayi wanan order din.

Karba tayi tadawo ta zauna tana kallo tanason ci Amma ta Hana kanta ci ta ajiye a inda zaigani
yasan bataciba.


Qarfe biyar na yamma dukkaninsu suna airport zuwa lokacin kowa baida wani dogon kuzari sbd
sanyi da jikinsu yayi yanda zasu samu su kawun dakuma yanda zaa karbesu su hudu da ake
sakaran sun mutu tun shekaru.

Har cikin jirgi Babu me wata magana acikinsu sai tunani har Suka isa gabanin asuba.

Dr sayyid ne yazo yadaukesu da wata baqar jeeb dinsa.

Ahankali Zaki yace"

Gida zaka kaimu.

Kallonsa dad yayi zaiyi mgn nadey ta rigasa da cewa"

Please dad muje can din first Dan Allah.

Daga Kai yayi suka Kama hanyar gidan kawu lokacin duk masallatai sunfito sallar asuba har
gari yafara haske.

A qofar gidan Suka tsaya Allah yasa babu wasu mutane suka shige gidan dukkaninsu suna Jin
kewar gidan nadawo musu sabuwa.


Da babbar malum malum dinsa yafito daga dakin iya talatu Yana hamma sbd yau baisamu
sallar asuba ba sbd kwana yayi da lalataccen ciki na wani romon Kai dasukaje Suka Sha shida
mal idi a gurin wani bikin daurin aurenda ko gayyatarsu baayiba.

Buta ya dauka zai shiga bandaki yaji sallama ahankali ya juyo yayi ido biyu da wadda ko
mutuwa yayi yadawo fuskarta Bata bace masa,,,

Zaro qananun idanuwansa yayi zai saki ihu saiyaga Zaki yashigo shima cikin sallamar
Take ya saki butar hannunsa jikinsa na daukar mazari saikga JJ yashigo tareda neyo.....

Hannu ya Dora akai tareda zubewa cikin tsananin tsoro da tashin hankali yafara qwala Kiran
sunan talatu Yana cewa"

Talatu zoki bani shahada lokacin tafiyar yazo matacci nake gani wlh,
Gashi nidai wlh ban dandadi dadin arkin danake roqoba Koda na awa dayane na roqi Allah
yamin arziki Kona wucin gadin ne Amma Banda rabo.....

A rikice iya talatu tafito dakin tana daura dankwali zatayi magana ganin Wainda ke tsaye saita
murza ido tasake murzawa...

A hasale cikin muryar kuka dattiyan yace"

Ke banason diban albarka zakiban shahadane kokuwa saina mutu Banda rabonta...
#MAMUH._*Mamuhgee38*_
Hannu iya talatu ta Dora akai Saidai kafin tasamu ikon yin magana jikinta yasaki tafadi a some.

Dattiya na ganin hakan baisan sanda ya fashe da kuka ba jikinsa na makyar kyarar tashin
hankali baki yakeson budewa yakira ceto Amma ya kasa gashi dukkaninsu sun jera masa tsaf a
gabansa murmushin Zaki daya Saba masa idan zai masa gayya shiyakeyi ko yanxun sbd
shiyace karkowa yayi mgn.
Ahankali ya sanya hannu aljihu yayi kamar zai Ciro Abu dattiyan na ganin hakan yasan addar
cire ransa ce zaa fitar sai kawai yasaki jiki yayi baya jikinsa na rawa cikin ransa yace gwara nayi
sumar qarya koma menene ayi idona rufe.

Da gudu nadey dake hawayen tsananin farin cikin ganin babanta na nan da hallayarsa ta tarosa
jikinta tareda fashewa da kuka tana cewa"

Baba karka Suma wlh Babu wasu matacci dakake gani mune gabanka bamu mutuba,
Kabude idanuwanka kagani mudin daine muka dawo gareka.

Dattiya najin hakan jikinsa yasake daukar mazari yasake sake jikinsa yaqi motsawa danyaqara
nuna a some yake,
cikin zuciyarsa kuwa kuka yakeyi sosai Yana tsinewa qarfin aljanunsa dasuka hanashi Suma
adaidai yanxun sbd hankalinsa ya mummunan sake tashi ganin matacci gabansa su hudu Ras
har Wanda rabonda yagansa shekaru fiyeda talatin.

Murmushi Zaki yasaki tareda matsowa gabansa ya tsaya cikin murmushi yacewa JJ ya shafawa
iya talatu ruwa.

Gyaran murya yayi Yana kallon kawun ya dago ya kalli nadey dake kuka cikin sakin fuska yace"

Lemme handle this.

Wayarsa ya fitar daga aljihunsa wandonsa ya kunna fitilar wayar ya kashewa kawun ido da ita

saiga idanuwan kawun sun fara marmadi alamar idanuwansa biyu.

Cikin sanyin murya Mai taushi Yana kallon nadey yace"

Ayyya sai hakuri fa yariga ya tafi JJ daukesa muje mu rufesa kawai dama yace idan yatafi kar
'dan dabar dayayi zaman gaisuwarsa.....

Jin kawai Sukayi ya fashe da kuka Yana cewa"

Talatu kinci amanar zaman tare dakika Suma kika barni...

Wata irin dariya Suka sake kusan atare Banda nadey da batasan lokacinda takai masa duka a
hannuba tana harararsa da hawayenta

Dad ma matsowa yayi yana cewa"

Ku matsa karku bugarwa da Yaya zuciya.

Kamasa yayi ya miqe daidai iya talatu itama ta farfado Suka zaunar dasu a tabarma dad Yana
sake kwantar musu da hankalin Babu wata fatalwa dayake gani ko matattu sudin daine.

dattiya da hankalinsa Bai Gama kwanciyaba murya na Yar makyarkyata yace"

Eh nidai kubari nakira Dan uwana mal idi zanfi Jin hankalina ya kwanta.

Zai tashi iya talatu tarigasa tashi sbd tasan bazai dawoba dagacan zasu iya guduwa shida mal
idi din tace"

Bari nakira makashi ta katanga.

Wata irin muguwar harara yabita dashi Yana ayyana irin Rashin qaunar dake tsakaninsa da
talatu datake masa irin wainnan abubuwan.

Zaki dayafi kowa sanin waye kawun yasaki murmushin dayasa nadey harararsa ahankali
Ya dauke gira daya cikeda mamakinta wato ta manta waye Zaki Dan bazaice Mata haydar ba
sbd shi kansa yafi qaunar Zaki akan haydar.


Mal idi da qarfinsa yashigo Yana asuwakinsa babbar rigarsa tun ta jiyace a jikinsa da ita ya
kwana da ita yatashi..

Yana ganin baqi masu Kama da turawa yasaki asuwakinsa tareda washe dukkanin haqoransa
Yana cewa"

Shikenan mafarkin dattiya yazama gskia da kuzarinsa ya iso shimfidar tareda zagayowa gurin
amininsa zaiyi mgn idanuwansa suka sauka akan fuskokinsu yafara binsu daya bayan daya da
kallo Yana Dora ido akan Zaki sukaga yayi baya Yana neman kakkafewa.

Dattiya ne ya tarosa Yana basa salati Yana cewa"

Daure danne mal idi wannan duk sharrin talatu ne Kuma zataga matakin dazan dauka.

Cikin yanayi na son fashewa da kuka mal idi ya kalli talatu Yana cewa"

Meya shiga tsakanina dake talatu da kikemin wannan bita da qullin.??

Cikin gyaran murya dad yace"

Wlh anan gurin babu fatalwa dukkaninmu Muna Raye Kuma bamu taba mutuwaba,

Haba Yaya Ina katabajin anmutu andawo ko acikin kafirai bare musulmai,

Tabbas akwai tsoro da bugawar Kai da zuciya kasan mutum ya rasu tsawon Koda wata biyu ne
kagansa bare shekaru tabbas wlh akwai furgitarwa..

Daqyar dattiya yabude baki yace"

Wlh Ni ko yanxu mutum ya mutu muka rufosa muka dawo nagansa to akwaifa qura bare
shekaru...

Mal idi shidai baisamu na tofawa ba zufan dake masa tsiyaya cikin riga ya sharce sbd wannan
shi ake Kira baqar safiya,
Gasu dai an rutsasu cikin gida Babu hanyar gudu to wlh Bari agama dattiya yashiga tsakaninsa
da talatu Banda manta alheri dabai tsaya Mata agurin dattiyan ba Aida ba ita zai auraba wata
hanne ce.

Sallah Suka farayi dukkaninsu a tabarmar tsakar gidan
Sudai su dattiya na rabe gefe mal idi jira yake yaji abinda bai masa ba yayi ihun kawo ceto.
Dattiya kuwa Banda tagumi daya rafka Yana Kiran Jin idan su dinne yafara zubo nasa zancen.


Aikuwa suna gamawa aka sake gaggaisawa nadey na kusada iya talatu da itakam tuni tafara
murna musamman la'akari datayi da cewa nadey dama basuda tabbacin ta rasu tunda Bata
tayi.

Ahankali dad yafaro bawa dattiya bayani tun daga ranarda yahadu da ruqayya a Lagos har

mutuwarsa da dawowarsa inda yake bibiyan nan gidan haryasan Zaki dansa ne,

Shima yayi gwagwarmaya ta sana'ar Mai kusan shekaru shida kafin yadawo yafada ta masu
aikin ginar zinari nanma kusan shekaru goma kafin Allah yayi anan arzikinsa yake gurin aiki
yasamu dunqulen zinarenda shine silar arzikinsa.

Ahankali ya koro musu duk labarin nadey Dana haduwarsu da Zaki tareda qarshen dillas...

Cikin tsananin farin ciki iya talatu ta janyo baby z dake jikin JJ ta rungumeta tana hawayen farin
cikin tasamu wata zainab din.

Mal idi kuwa gyara zama yayi yana sakin dukkanin fara'ar fuskarsa da bakinsa yafara hamdala
Yana kallon dattiya dake kallon nadey baya ko qyaftawa sbd tsananin farin ciki Yana sakin
hawayensa dasuka kasa boyuwa.

Zaki yakoma kallo Yana washe baki kafin yasake kallon baby z wadda allah yayi ba agansa
zatazo duniyaba duk irin qone qone da azabar dayaci akanta.

Jawota yayi jikinsa akaro na farko da tsananin son qananun yara yakamashi baisan lokacinda
ya washe baki ba Yana cewa"

Nadiya wannan 'yarki ce???
Oh ni dattiya Allah nagode maka Ashe dai arzikin ta jikoki zaizo.

Dariya yabasu mal idi yace"

Ai wlh alhaji dattiya kuka da baqin cikin Rashin Zaki da Nadiya ya qare Bari ma naje aikin shelar
a dare daya Allah yayi bature.

Washe baki dattiya yayi yace"

Eh daganan ka taramin layin almajirai zanyi sadaka yau dai daya.

Kallon iya talatu yayi haqoransa basa rafuwa yace"

Maza doramin wainar dubu 'daya zanbaki gobe.

Miqewa dukkaninsu Sukayi dad yace zaitafi gida tukuna.
Nadey kuwa nokewa tayi tace anan zata zauna tukuna.

Zakima dakinsu yashiga yaga ya lalace Sam ko shiga baa iya yi Dole ya hakuri yabi dad shida
JJ sbd su huta suyi wanka su sake gyarawa.

Bayan fitarsu gyara zama dattiya yayi Yana sake magana Sosai da 'yarsa idan ya kalli ko
qafafuwanta wani farin ciki yakeji Wai wannan baqar baturiyar yarsace
Wai har qasashen jirgi tayita Hawa.


Zabura dattiya yayi da kansa baby z na riqe a hannunsa Suka fito Yana cewa abi layi yau shine
zai bayar ba basa zaayi ba.

Ganin wainar zataja lokaci yasa ya fiddo duk tsiminsa na kudi yafara raba nera hamsin hamsin
Dasuka qare kuwa yace idi yabasa aro da sauri idi yakwaso duka kudinsa yabasa Yana cewa"

Dama alhaji dattiya wlh munada zuciyar bayarwa Allah ne baiyarda mubayar dinba shiyasa
muke a haka.

Wani iska yaji Yana kada babbar rigarsa duk idi yakirasa da alhajin nan
Jiyake kamarma yafi dikko kudi yanxu.


Nadey wanka tayi tashige dakin iya tayi kwanciyarta sbd Yaya dahiru da matarsa suntashi gidan
sun canxa gida sbd masifar iyayen nasu dabasu Saba da itaba.

Wani manya manyan dankalin hausa da ake soyawa da doya da fresh yo mal idi yasiyowa baby
z dake kallon mutane a tsorace sbd Bata Saba ganin mutane hakaba.

Fresh yo din kawai ta karba shima batashaba riqewa kawai tayi saita yo cikin gida tana qwala
Kiran mummynta.

Nadey najinta tayi shiru harsaida iya talatu ta nuna Mata dakin da hannu tashiga ta fada jikinta
tana cewa gurin daddynta zataje.
#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan
numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee39_*
Manya manyan dankalin dake hannun mal idi ya kalla cikin nishadi yace"

Mal idi waccan me Kama da wankakken karas din kasan bazata iyacin wannan shaquri danne
dinba maza hadashi gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0