Showing 33001 words to 36000 words out of 85058 words
Chapter 12 - KANWAR MAZA 1 BY AYSHER COOL BY AISHACOLL .pdf
gaya mini"
Usman ya ce "Wallahi nima na yi mamaki duk ɓarnar nan da ta yi masa ya ƙyaleta"
Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.
Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ƙi
zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu ɗan mai makarantar ta liƙewa,
duk ajin da za shi ya yi ƙari sai ta bishi, gashi ta maƙalewa Auwal, yaya sama yaya ƙasa haka
take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.
Yanzu ma 'yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai ga shi
ya shigo shi da ruma.
Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata
zuwa ajinsu, amma sai gata.
Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu
kamar gaske aka yi ƙarin nan aka idar.
Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi 'Inyee ashe ka na ja,
hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na faɗa a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba"
Dariya 'yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.
Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce "Malam nima zan karanta"
Ya ce "To bisimillah"
Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai
shafi guda, ba ƙaramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.
Ɗari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja
ba.
Da ya kammala ƙarin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya haɗe rai ta ce "Malam
ni ka bar ni a nan ajin"
Malam Habibu ya ce "To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba
ruwan kowa da ita kar a takura mata"
Suka ce to.
Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata taɓa zama shiru ba.
Ruma ta shige cikin 'yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ƙasarta, amma duk tana
jin me suke faɗa.
Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.
Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ƙofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta
bata farar ƙasa kyauta.
Duk shegen son kuɗi irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ƙasarar nan, saboda shegen surutun
ta da nacin tsiya.
Ta karɓi farar ƙasarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ƙawaye, a cewarta ɗaliban
ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su ɗaliban sa'aninta kowanne ya mayar da hankali a kan
karatunsa ne, ita kuwa ruma 'yar abi yarima a sha kiɗa ce.
Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, "Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa
ya hallara zan faɗi me aka yi mini" jin kowa ya shareta ya ƙi kulata ya sanya ta ce "Mama yanzu
dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?"
"Da aka yi miki me?"
"Mama a gabanki 'ya'yanki suke ce mini ƙwaila, amma baki taɓa hana su ba"
Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce "To ba ƙwailar bace ba?"
Ruma ta buɗe baki ta ce "Au mama har da ke?"
Aliyu ya ce "To meye dan an ce miki ƙwaila, ai ƙwailar ce"
Ruma ta ce "Kutt, ƙwaila fa wadda ba ta da nono kenan?"
Aliyu ya ce "Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa"
Mama ta ce "ke waye ya gaya miki haka?"
"'yan ajin su Yasir ne suke faɗa, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin
su"
Mama ta ce "To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ƙwaila ba?"
"Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon,
na zo na ƙulla a leda na dinga sakawa" cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa
me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ƙyaƙyata dariya yake ƙasa-ƙasa lamarin ƙanwar
nan ta su sai Addu'a kawai.
Aliyu ya ce"Ke da ki ke ƙanwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai
kin fi kyau"
Ta ce "Kuma fa haka ne" ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa
"Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji
tana ɗan warin nan da ƙamashin turare "
"Fitar mini daga ɗaki dan ubanki, shashasha mara alƙibla fita ki bar mini ɗaki".
AYSHERCOOL
08081012143
[08/07, 4:58 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
*A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO
IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI í ½í¸’*
10
Ɗan tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce "Mama wai me na yi to?"
"Ban sani ba fitar mini daga ɗaki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an
canza mini 'ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan
gado irin naki?"
Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta.
"Ba zaki fita ki bar mini ɗaki ba, sai na taso kan ki?"
Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.
Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce "Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?"
Ta murguɗa baki ta ce "Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo"
"To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?"
Huzaifa ya yi caraf ya ce "Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo ɗin ta gani"
Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.
Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga ɗakin mama ya ɗau jakarta.
Ruma ta ɗaga murya ta ce "Mama, ga Huzaifa nan ya ɗaukar miki jaka"
Ya ce "To munafuka"
"Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki kuɗi"
Huzaifa ya ce "Mama aron naira ɗari zan ɗauka"
Mama ta ce "Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka ɗaukar mini kuɗi ba bani ka ke ba"
"Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi"
Daga kitchen mama ta ce "Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo ɗakin nan?"
"Mama wallahi bai ajiye miki ba"
A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka
ya fice.
Ruma ta ce "Dana sani na bar shi ya ɗauka, nawa nake bin mama ba biyana take ba"
***
Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma.
Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B.
Malamin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi".
Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi
magana.
Ƙarshe dai ruma ce ta taimaki 'yan ajinsu, gaba ɗaya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace
ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da ɗaliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi,
tsabar naci ne ya sanya a ka bata.
Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki
a saboda harkar karatu.
Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.
Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya niƙi-niƙi.
"Ke wannan kayan na menene?"
Ruma ta zubewa mama kayan ta ce "Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani"
"Meyasa aka baki?"
"Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ƙi koya mini, na je na yi ta yi da kaina,
shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar"
Mama ta ce "Hmm, ai shikenan"
"Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?"
"Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa"
Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Mama wace gurguwar kuma?"
Cikin gajiya da halin ruma mama ta ce "Ki tashi ki cire uniform ki yi wanka"
Ruma ta tashi ta cire kayanta, ta ɗebi ruwa ta shiga wanka. Ta na tsaka da wankan, ta jiyo
muryar Usman ya shigo, daga banɗakin ta buɗe murya ta ce "Yaya Usyy Albishirin ka"
"Ruma ban hanaki surutu a banɗaki ba?"
Ta ce 'yi haƙuri mama"
Ba dan ta gama wankan ba, cikin zumuɗi ta fito daga wankan 'Yaya usman, bari na nuna maka
wani abun mamaki"
Ba ta san a ya ta fito daga banɗakin ba, sai da mama ta daka mata tsawa, daga ita sai pant ta
fito. Ta koma ta ɗauko zani, sannan ta kwaso kyaututtukanta ta nunawa Usman.
Ya kalli ruma sannan ya kalli kayan ya ce "Ruma ban yarda da ke ba"
Ta ce "Saboda me?"
"Ina ki ka ga kwanyar da zaki yi wani abun arziki ke?" Tsuke fuska ta yi tana kallonsa ta ce "To
me ka ke nufi?"
"Ɗauko takardar da aka baki, na yi miki tambayoyi" ta miƙe ta je ta ɗauko masa takardar ta miƙa
masa.
Ga mamakinsa duk abin da ya tambayi ruma, sai ta bashi amsa daidai ko gyaranta ba ya ci.
Ya ajiye takardar, ya kalli ruma ya ce "Ni fa haryanzu mamaki nake, matar da take zuwa ta kusa
da ta ƙarshen aji, ita ta yi wannan ƙoƙarin"
Ruma ta yi murmushi sannan ta ce "Ikon Allah kenan, baku san haushin da nake ji idan aka ce
mini daƙiƙiya ba, shi ya sa na dage na je na iya"
"Congratulations, ina ma zaki cigaba da dagewa da kin ga cigaba a rayuwarki"
Ta taɓe baki ta ce "A'a da wahala gaskiya, ka san baƙar wahalar da na sha kan na iya wannan
abun, dan a dai na ce mini daƙiƙiya daga wannan ba zan kuma ɗaukar dala ba gammo ba"
Usman ya yi murmushi ya dafa kafaɗarta ya ce "Haba ƘANWAR MAZA, rayuwa ce fa, kuma
idan da rai da lafiya yanzu aka fara, kar ki sake ɗarsawa ranki cewa akwai wani abu da zai
gagareki komai wahalar sa, rayuwa sai da gwagwarmaya da faɗi tashi, musamman ga ɗan
talaka. Kar wani abu ya ƙara razana ki, ko ki yadda ke daƙiƙiya ce zaki iya komai kema" Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Dan Allah da gaske Yaya Ussy?"
Ya jinjina mata kai ya ce "Sosai makuwa, ki dubi rayuwarmu a cikin gidan nan, tun baki da
wayo, har zuwa yanzu a cikin gwagwarmaya muke, farincikinmu kawai ki ke gani, amma kowa
akwai kalar ƙalubalen da yake fuskanta, ki kalli mama ba ta yi karatu mai zurfi ba, amma ta
cancanci a kirata jarumar uwa, ba lallai ki fuskanci me nake nufi ba a yanzu, amma ki saka
maganganun nan a ranki akwai ranar da za su yi miki amfani. Amma ki tsaya a kan
ƙafafuwanki, ki fuskanci abin da yake baki tsoro, ke fa jaruma ce, bai kamata sunan daƙiƙiya ya
biki ba"
Ruma ta ɗan yi shiru sannan ta kalli Usman ta ce "Yaya Usy, in sha Allah zan dinga mayar da
hankali na yi karatu sosai na daina wasa"
"Yauwwa ko ke fa, ai hakan ya fi deluwa"
"Kuma zan cigaba da ƙoƙari, in zama mai ƙarfi sosai, duk wanda ya tsokane ni, in yi masa
dukan tsiya in farfasa masa baki da hanci, in kakkarya mutum"
Mama da take jin su ta ce "Ke kuma ba kya fatan ki girma ki yi hankali, sai rashin hankali ke ba
kya fatan Allah ya shiryeki ki daina faɗace-faɗacen banzan man a matsayinki na mace, faɗa ba
na 'ya mace bane"
Ruma ta ce "A'a mama, gara ki bar ni na koyi ƙarfi sosai"
"Sai kuma ki yi ai".
Usman ya kuma murmusawa ya ce "Ba irin wannan ƙarfin ake magana ba, ƙarfin zuciya da
kaifin basira wurin sarrafa duk wata Matsala da za ta tinkaro ki, kar ki bari matsalolin ki su
razana ki, ko sau ɗaya kar ki bada wannan damar, ki turje ki dake ƙalubale duk girmansa, ki yi
gaba da gaba da shi"
Ruma ta ce "Mhmm, gashi dai hausa ka ke yi, amma bana gane me ka ke faɗa, sai na ji kamar
ma wani yaren ka ke daban, ban wani gane me ka ke nufi ba"
"Ni ma na san ba zaki gane a yanzu ba shekarunki da hankalinki babu lallai ya kai, saboda ke a
yanzu ba ki sa wata damuwa ko matsala. Tashi ki zubo mana Abinci mu ci" Ruma ta miƙe ta tafi
kitchen.
Mama ta ce "Kai ma banda abinka, wannan zaka zaunar ka na wani gayawa wannan bayanan,
me zata gane a ciki? Ita ban da wautarta da tambayoyin ta na rashin kan gado me ta sani?"
Usman ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Haka kurum mama ina jin tausayin yarinyar nan, jikina na
bani za ta yi gwagwarmaya a rayuwa, gwagwarmaya a bugiren da ba zamu iya tsaya mata ba,
ko yi mata wani taimako ba, gwagwarmayar da take buƙatar ta tsaya da ƙafarta ta cimma
nasara" Mama ta ce "Tooo ikon Allah, to koma dai menene, ni dai addu'a kullum cikin yi muku ita nake,
ba ku kaɗai ba, dukkan 'ya'yan muslmai baki daya, Ubangiji Allah ya shiga lamarinku, ya tsare
gabanku da bayanku, ya kula da rayuwar ku"
"Amin mama, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana uwa ma bada mama"
"Amin ya rabb"
A ranar duk wanda ya shigo, sai ruma ta nuna masa kyaututtukan da aka bata, har a waya sai
da aka kira mata yaya Abubakar ta gaya masa, tun ana tayata murna da Allah ya sanya albarka
har ta fara ƙular da mutanen gidan. Dan hatta maƙwabta sai da ta shiga ta gaya musu ai tayi
ƙoƙari a makaranta an bata kyauta. Da ta je Islamiyya kuwa, har ofishin shugaban makaranta ta je, shi ma ta gaya masa, ya tayata
murna tare da sanya mata albarka, ta ƙarasa staff room bayan sun gaisa da malaman suma ta
gaya musu ai a makarantar boko tayi ƙoƙari an bata kyaututtuka. Nan suka yi ta mata fatan
alkhairi, ji take a duniya yau ta ƙure daɗi tayi abin da ba ta taɓa ba. "Malam to idan an idar da salla dan Allah a sanar"
Wani malami ya kalleta ya ce "A sanar da me?"
"Na yi ƙoƙari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ɗari biyu da hamsin fa
na haddace yadda ake spelling ɗin su"
"To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a
sanar wa ɗalibai"
Ruma ta ce "A'a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini daƙiƙiya su san ƙwaƙwalwata na
aiki, wataran zan bayar da mamaki".
Malam Habibu ya yi caraf ya ce "Ƙwarai kuwa, dole a sanar da ɗalibai wannan namijin ƙoƙari da
ki ka yi, nima ba rannan na yi ƙari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu" cikin jin daɗi ruma ta
ce "Yauwwa malam na gode"
Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce "Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah kaɗai ya san
wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka faɗa ɗin, za ta ji daɗi da ƙara samun ƙwarin gwiwa".
Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ƙofar masallacin
maza, ta leƙa ta ce "Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a faɗa ba".
Malam Habibu ya ce "To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka"
Haka malam Habibu ya tashi ya ce "'yan uwa ɗalibai da malamai, a taya 'yar uwa murna, wato
'ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta
samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu'a, Allah ya ƙaro nasarori"
Daɗi kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.
Huzaifa da suka yi salla sahu ɗaya da Yasir ya ce "Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi
ko?"
"Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ƙona banzayen
litattafan da aka bata, kowa ma ya huta".
Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka
sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo
hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida.