Showing 51001 words to 54000 words out of 85058 words

Chapter 18 - KANWAR MAZA 1 BY AYSHER COOL BY AISHACOLL .pdf

07 Dec 2025

2106

zaci kin ci
bulus, ai faɗa ni da ke daga yau har ranar busa ƙaho, ba dai uwata ce tsohuwar banza ba sai ka
ce babata sa'arki ce ba? Ai ki yi mini komai ban da taɓa uwata, ban taɓa zagin uwar wani ba,
kema babarki  jibgegiyar bayerabiya masu kashi a leda"

Gigicewa Asiya ta yi, tana kuka tana son kaiwa ruma duka, amma ta kasa sarrafa hannunta ga
ciwon da jikinta yake yi mata.
Ruma ta durƙusa ta dinga dumbuzar ƙasa hannu bibbiyu tana watsawa Asiya a fuska. Ban da
kuka babu abin da Asiya take yi.

Ranar ma sai da aka tashi sannan aka sallame su, aka ce gobe da safe za su cigaba da

punishment.

Rumaisa ta riga Asiya tafiya, ta je ta samu hanya, ta tattara duwatsu, ta tara su a cikin jakarta.
Ta kuma datsar Asiya a hanya, ta dinga kabbara tana jifanta. "Sheɗaniya gara na jefeki na huta,
na ga haka ake yi idan an je makka a jefi sheiɗan, gobe ko cewa aka yi ki kalleni, ba zaki sake
ba balle ki dakeni"
Sai da ruma ta gama abin da Allah ya nufeta da yi, sannan ta wuce gida. Yau kam bakinta har
kunne, jin ta take wasai ba ta da wata damuwa ko banza ta rama abin da aka yi mata har da
riba, malamai kuwa ko zasu kwaɗata su cinye bai dameta ba.

Abdallah ne yake ta shiri, ruma sai tambayarsa take ina zashi?.

"Ke wai kin aikeni ne?"

"A'a, amma dan Allah ka gaya mini"

"Cikin gari zani ziyara"

Ta haɗa hannayenta biyu ta ce "Dan annabin rahama ka tafi da ni" hararta ya yi ya cigaba da
shirinsa.
Ta dinga bin sa tana lallaɓa shi, har ya amince zai tafi da ita.
Mama ta ce "Hmm in dai ruma ce zata baka kunya, Allah ya sa kar ta ɗauko maka magana"

"Ta ɗauko ma, dakuwa zata yi wallahi"

Ruma ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta a cikin gari cikin 'yan uwa, akwai 'yan uwan mama sosai
a cikin gari, sai dai mama ba ta zuwa da ita, saboda ta din ga neman magana da dukan 'ya'yan
mutane kenan.

Akwai wata 'yar cousin ɗin mama, da rashin jin su ya kusa zuwa ɗaya da na ruma, duk da ruma
ta fita. Ta ce "Ruma, zo mu je yakasai, akwai ƙawata a gidan Turakin Kano, jikarsa ce biki ake a
gidan, kuma za ayi kilisa, kan Abdallah ya dawo mun je mun dawo, mu je mu ciyo banza"

Ruma ta ce "yauwwa hauwwaliya, yi sauri ki shirya mu tafi kan ya dawo ya hana ni zuwa"

"Ke har da babbar leda zan ɗauko, idan mun ci mu ƙullo sauran"

Haka suka shirya, suka yi sallama a kan zasu je biki su dawo.

Suna tafe a hanya suka sai masara, suna tafe suna ci suna hira.

Tabbas idan ka ji wane ba ƙarya ba, gidan ya tsaru yayi kyau sosai da sosai, gini ne na sarauta

da aka ƙawata da kayan alatu, ruma sai rarraba ido take yi.

Ƙawar hawwaliya ta din ga murna da ta gansu, ta kai su wani falo suka zauna.

Ruma kuwa hankalinta na kan wata mata, da ta sha ado sai kai wa take tana komowa tana wani
hura hanci, tana dakawa mutane tsawa.

Ruma ta ce "Taɓ, wai wacece waccan?"

Yarinyar ta kalli wadda Ruma ta nuna ta ce "Laa Anty Samha ce, ƙanwar mama ce, ba mata
bace ba ta da aure".

Ruma ta ce "too na ganta wata gwabjejiya, sai masifa take yiwa mutane, ni na zaci matar sarki
ce ma, yakamata a samu mai kwaɗeta ya zata din ga hantarar mutane?"

Hauwwaliya ta daki cinyar ruma ta ce "Ke, ƙanwar mamanta cefa"

Yarinyar ta yi murmushin yaƙe ta ce "Bari a kawo muku Abinci, sai mu je wurin kiɗan ƙwarya da
kilisa"

Ruma ta miƙe ta ce "Hauwwaliya, ni dai zan je wurin da na ga an ɗaure dokuna na kallesu, idan
an kawo Abincin ki ƙulle mini nawa a ledar da ki ka zo da ita" buɗe baki Hauwwaliya ta yi, da jin
hansfreen da ruma ta yi musu.

Kai tsaye ruma ta fito tana cigaba da kallon gidan, da yadda manyan mata ke shiga suna fita,
da shiga kala-kala.

"Ke ba kya gani ne, meye haka?" Ruma ta ɗaga kai ta kalli wadda ta daka mata tsawar. Matar
da take ta hantarar mutane ce.

"Eh bana gani, sandata na fito nema, ke da ki ke gani meya hana ki kauce?" Ruma ta yi
maganar tana tsare Samha da ido.

Wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Samha, da ta yi tozali da idanun ruma, ga ta ƙarama
amma wani abu mai kaifi ne a idanun ruma.
Ruma ta raɓata ta wuce abinta. Da sauri Samha ta bi bayan ruma, amma ta nemeta ta rasa.

Kai tsaye burgar dawakin da suka wuce ta je ta tsaya. Ta tarar da wani dogari yana basu Abinci.
"Sannu da aiki"
Ya kalli ruma ya ce "Yauwwa sannunki"
"Dan Allah ina dokin sarki a nan?" Yayi murmushi ya ce "Nan babu dokin sarki, na 'ya'yan sarki
da manyan Hakiman fada ne"
"Dan Allah ka cewa sarki ya bani doki ɗaya"

Yayi dariya ya ce "Ke idan aka baki doki ya zaki yi da shi?"
"Hawa zan din ga yi mana" ruma ta din ga yiwa dogarin nan surutu, sai da ya gaji sannan ya ce
"To ai Shikenan, yanzu dai fita za ayi da su, za ayi kilisar angwaye"
Ta jinjina masa kai, ta koma gefe ta tsaya, tana kallo aka shirya dawakan, aka yi musu kwalliya
sannan aka fita da su.
Hauwwaliya ce ta fito ita da ƙawar ta ta tana faɗin "Ke ruma, tun ɗazu jira nake ki dawo, amma
ki ka ƙi komawa"
"Ke ƙyaleni, kallon dokuna nake"
Ƙawar hawwaliya wadda suke da Turaki, ta ce "Mu je to, sai mu kalli kilisar"
Suka fita daga cikin gidan gaba ɗayansu, kan barandar wani gida suka je suka tsaya, suna
tsumayin a fara kilisar.
Abin yana burge ruma sosai da sosai, duk wanda ya zo wucewa sai ta ɗaga masa hannu tana
tsalle.Tun da suke wucewa babu wanda ta kira sarki, sai da ya zo wucewa tare da ango.
"Sarki mai koriyar alkyabba, a dawo lafiya, dan Allah ka bani kyautar doki, ko kuma ka ɗanani a
kan dokinka!!!"
(Wannan 'ya ni kaina tana bani ciwon kai 😒 in kun ji ni shiru ku dinga yi mini addu'a, Allah ya
ƙara mini lafiya í ½í¹�)

Mai nema daga farko, ya duba watpad Please �
Ayshercool
08081012143
[21/07, 10:53 am] JAKADIYAR AREWA:                 ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN
NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU
RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI
SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE
DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA
SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*

*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani
supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi
gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta
tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko
sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*




https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai
amana kuwa😒*

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.



*Ina yiwa 'yan uwa musulmi barka da shigowar, sabuwar shekara musulunci, Ubangiji Allah ya
sada mu da alkhairan da yake cikinta, akasin haka kuma Allah ya iya mana*

P 15




Gaba ɗaya aka juyo ana kallon ruma, mutanen wurin suka hau dariya.
Shi kansa Jamil da yake ango, da sauri ya ƙara rufe fuksarsa da rawani yana murmushi, dan
saura ƙiris dariya ta ƙwace masa.
Adam kuwa sake tsare gida yayi, kasancewar dama can ba mai yawan fara'a bane ba, jin
muryar ruman yake a wani abu daban, anya mutum ce?. Kamar zai juya domin ganin fuskarta,
sai kuma ya fasa ya sake rufe fuskarsa da rawaninsa, yayi gaba.

Ƙawar Hauwwaliya kuwa ɗan zaro ido ta yi ta ce "Ke kin san waye wannan kuwa?"

Ruma ta ce "Ba shine sarki ba?"

"Ba sarki bane ba ai, ɗan gidan marigayi Galadima ne da ya rasu, sunan sarki ne da shi,
Takawa ake ce masa, wallahi ki ka bari ya kamo ki, sai kin gayawa mutanen garinku, ba ki san
yadda muke jin tsoronsa ko a family ba, hmmm su Ummanmu sun girme shi amma tsoronsa
suke ji, ba ya wasa da mutane"
Bayan gama jin jawabin da aka yi mat, ta taɓe baki ta ce "Taɓ, na gama yaya umar, ni gani nake
kamar na taɓa ganinsa ma, ko a ina oho mini dai na manta, so nake na ga fuskar sa"

Dariya yarinyar ta yi ta ce "Ki zo wataran mu je gidansa, ko gidansu sai ki ga fuskar sa amma
daga baya zan laɓe ke ki shiga" ruma ta kwashe da dariya ta ce "Ke da wasa nake miki, amma
dai zan zo wataran a ɗanani a doki"

Yarinyar ta dubi Hauwwaliya ta ce "To yaushe zaku kuma zuwa?"

"Ke, ita fa ruma ba a nan unguwar take ba, zuwa ta yi yau zata koma gida, a ɗorayi take fa"

"Haba, idan mun zo hawan salla wataran, sai na zo gidanku"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo ki, amma baki gaya mini sunanki ba"

"Sunana Jannah, ke kuma ruma ko?" Ruma ta jinjina mata kai alamar eh.

Ta miƙowa ruma ledar viba ta ce "Ga saƙonki" ruma ta karɓi ledar ta yiwa Jannah godiya, suka
tafi gida.

Allah ya taimaketa, Abdallah bai dawo ba sai bayan salla magariba, sannan ya ɗauketa suka
tafi gida.

Tun a hanya yake tambayarta meye a ledar hannunta, amma tayi mursisi ta rungume ledarta
taƙi nuna masa, har suka je gida.

Mama sai da tayi mita "Abdallah ka ɗaukar mini 'ya ka tafi da ita, tun ɗazu nake zuba ido in ga
ta ina zaku dawo, ka san da wuri take bacci, kun je kun yi dare".

Abdallah ya ce "Mama wai dama kina son yarinyar nan?"

Mama ta buɗe baki, tare da yin murmushi ta ce "Dan ƙaniyarka in haifi 'yar a cikina ka ce dama
ina son ta, ni duk cikinku waye bana so, ai banda hali irin na ruma son da nake yi mata daban
ne, kasancewar ta mace ɗaya tilo a cikinku, amma sanin halinta ya sa wasu lokutan nake kamar
bana son ta, idan ba haka taɓarar da zata yi sai Allah"
Ruma ta ce "Kai ban taɓa jin kin ce kina sona ba, ashe idan na mutu zaki yi kuka"

Mama ta ce "Ke rabani da shiririta, tashi ki yi sallar isha'i ki zo ki ci Abincin dare ki kwanta, gobe
in Allah ya kaimu akwai makaranta".

Ruma ta tashi ta ce "Ai ni yau ba abincinki zan ci ba, na gidan sarauta zan ci" mama ba ta ɗau
maganarta da muhimmanci ba, sai da ta idar da salla, ta janyo viva, tana firfito da Abinci.
Mama ta matsata da tambaya, ta bawa mama labarin abin da ya faru.

Abdallah ya ce "Wallahi mama ban ma san ta je ba, na ƙarasa na gaisa da abokaina na
tsohuwar unguwarmu, shi ne ta samu ta tafi, yanzu da doki ya takaki ki ce me?"

"Doki bai takani ba, sai abin arziki da na samo, kun ga gidan sarautar nan, wai gidan Turaki,
gaskiya suna da kuɗi, mama kalli kaza guda ta sako mini, kalli kayan gara, ya ma sunan
wannan dunƙulellen abun mai kamar kashi?" Ta yi maganar tana nunowa mama Alkaki, gaba
ɗaya ko a jikinta, dan ita ba ta ji a jikinta ta yi laifi ba.
Mama zurru kawai ta yi da ido ta na kallon ruma, mama ta gaji da faɗa a kan halin ruma, dan
haka ta yi shiru ta na faɗin Allah ya shirya.

******

Yanayinsa ne ya nuna wa Ammi cewar ya na cikin damuwa.

"Takawar ka lafiya babban mutum, basarake kuma jinin sarakai, me yake faruwa ne?"

Adam ya yi murmushi ya ce "Bakomai Ammi, gajiyar bikin nan ce ta Jamil, kuma kwana biyu
ban hau doki ba yau na hau doki, duk jikina ciwo yake"

Ammi ta yi murmushi, a dole wai sai ya ɓoye mata akwai abin da yake damunsa, dan haka ta yi
murmushi ta ce "Shikenan, ka je ka ɗan watsa ruwa ka kwanta ka samu ka huta" ya jinjina mata
kai, yana shirin tashi ta ce "Yauwwa Takawa, ni ko tun da ka dawo, ka je ka gaida babarka?"

Take ɗan ragowar annurin fuskarsa ya ɗauke, ya ɗan ɓata fuska tare da girgiza kai alamar a'a.

"To ka san dai yakamata ka yi hakan, bana son ƙananan maganganu, tun da yanzu a gajiye ka
ke, kuma kana gidan nan yakamata in an jima ko da safe dai, ka je ku gaisa ka ce mata ka
dawo"

"To" ya amsa a taƙaice.

*****
Mama sai fama take da ruma a kan shirin makaranta, sai laƙai-laƙai take yi, sai ta fara shiri, sai
ta tafi banɗaki yawon kashi, saboda ciye-ciye da ta yi, ya ɓata mata ciki. Mama ta kai matuƙar
ƙuluwa sai faɗa take yi, ruma kuwa ko a jikinta.

Har ta ɗau jaka, sai ga kira a wayar mama.
Mama ta ɗaga tare da yin sallama.
"Da ga makarantar su Rumaisa ne, dan Allah idan za ta taho, a haɗota da wani babba daga
gida"

A ɗan ruɗe mama ta ce "Lafiya, wani abun ta yi?"

"A'a, a dai haɗota da wani babba, ko babanta ko wakili"

"To shikenan, babu laifi, za ta taho in sha Allah" mama ta ajiye wayar ta kalli ruma. "Ruma, me
ki ka yi a makaranta?"

"Ni kuma? Ni babu abin da na yi"

"Ki gaya mini tun kan raina da na ki su ɓaci"

"Wallahi mama ni babu abin da na yi"

"Amma aka ce ki je ke da wani babba, anya ruma ke fa ba gaskiya ki ka cika ba"

Ruma ta ce "Ni dai wallahi na san babu abin da na yi"
Mama ya gyaɗa kai ta ce "Ai shikenan, zamu gani".

Ta ƙarasa ƙofar ɗakin 'yan mazan, ta ce "Waye ba zai fita ba yau a cikin ku? Wani ya zo ya je
mini makarantar su yarinyar nan, an kira ni an ce ta je ita da wani"

Yaya Aliyu ya ce "Mai sunan Baba dai ya tafi makaranta, ni ma ina da lectures ƙarfe goma sha
biyu, amma bari na zo mu je na ji menene"

Ita kanta ruma tunani take Meyasa ake neman wani a gidansu a makaranta?

Suna tafe a hanya da Aliyu yana mita "Ke, kawai kin sa an katse mini bacci na, Allah ya sa na ji
wani rashin jin ki ka yi, na samu abin duka na zane ki"

Ta tura baki ta ce "Ni dai na san ban yi komai ba, wataƙila ma wani abun arzikin na yi ake
nemanku, amma kowa ba ya kyautata mini zato"

"Ruma ai ke abin arziki  bai karɓe ki ba, sanin halinki ne ya sanya ake tsoron lamarinki"

Suna tafe a hanya, yara da manya mata da maza kusan kowa ya san ruma, suna tafe ana
kiranta ta na ɗaga wa mutane hannu, har suka isa makarantar.
Ofishin Headmaster suka je, ruma sai rarraba ido take tana 'yan ciye-ciyen ta.
Aliyu suka gaisa da Headmaster, ruma ma ta gaida Headmaster ta koma gefen Aliyu ta tsaya.

Headmaster ya kalli ruma ya ce "Waye ya sallameki jiya ki ka tafi?"

Ruma ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba.

Headmaster ya dubi Aliyu ya ce "To, a gaskiya ƙanwarka ce ko 'yar ka ba ta jin magana, sun
samu saɓani da abokiyar karatunta, an yi musu sulhu amma ba ta ji ba, sun kuma faɗa jiya, ta
karyata a hannu, kuma ta bita hanya ta din ga jifanta da dutse wai jifan shaiɗaniya. To uwar
yarinyar nan ta ce ba zata yadda ba, yanzu haka tana division ta kai ƙara, suna jiran mu, ka san
ƙabilu wasu lokutan basu da tawakalli ba su san ƙaddara ba".

Aliyu ya ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke dan ubanki a garin yaya ki ka karya 'yar mutane,
kuma baki faɗa ba?"

Ruma ta zare ido ta ce "Kaii Innalillahi, wannan ɗan dukan da na yi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0