Showing 3001 words to 6000 words out of 85058 words
Chapter 2 - KANWAR MAZA 1 BY AYSHER COOL BY AISHACOLL .pdf
nayi sauri ne, ya sanya na aro tayar, kuma wallahi na manta na
barota a wajen gidan Hanne mai markaɗe".
Mama ta riƙe haɓa kawai, tama rasa me zata ce gaba ɗaya.
Huzaifa ya ce "Wannan yarinyar idan kina da rabon yin hankali Allah ya shiryeki, ina ke ina taya
kina mace?"
Mama ta kalli in da Habiba take tsaye ita da ƙaninta ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, tun da ta fita
nima nake zaman jiranta, ban aiketa ta je ta karɓi kayan kowa ba, da safe in Allah ya yarda zan
turata ta je ta dubo muku" Mama tayi ta basu haƙuri, suka juya suka tafi.
Mama ta zauna ta dasa mita, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, su Usman na tayata, ita
kuwa Ruma da ta san ba ta da gaskiya, sai ta ƙule a kan katifarta, zuciyarta sai bugawa take
tana jiran jin me Yaya Umar zai ce, amma shiru bai ce komai ba.
Har suka watse daga tsakar gida, Mama ta shigo ɗakin, ta sameta ta rufe ido tana baccin ƙarya,
still Mama ta cigaba da mita, sai da Ruma ta ji kamar ta tashi ta barwa Mama ɗakin ta huta,
saboda Mama mitarta ba ta ƙarewa sam, gefe guda tana yiwa Allah godiya da Dodonta bai yi
magana ba.
Wani irin bacci ne mai daɗin gaske yayi awon gaba da ita. A cikin baccin nata babu zato babu
tsammani sai ji tayi an yi sama da ita da hannu ɗaya.
"Wayyo Allana, Innalillahi wa innalillahi raji'un, warin hannuna na hagu zai karye Mama!" Sai da
ya dungurar da ita a tsakar gida, suka yi ido huɗu, ta ga wanda yayi mata wannan aikin.
Jikinta ne ya hau kyarma, dan idonsa kawai idan ransa a ɓace yake abin tsoro ne.
A ƙasan zuciyarta ta ce 'Shikenan tawa ta ƙare, Allah ya sa na cika da kyau da imani!.
Ayshercool
08081012243
[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724
P2
Kasa ɗauke idanunta tayi daga kallonsa, saboda azabar firgici da razanar da ta yi.
Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya ɗan ƙura mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce
"Gidan uban wa kika tafi da ta aikeki, tun la'asar ba ki dawo ba sai magariba?" Yayi Maganar
yana tsareta da ido.
Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon fuskarsa da idonsa.
"Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da ido?" Ya daka mata tsawa.
Zabura tayi ta yinƙura za ta yi magana,amma ya sake cewa "Kuma wallahi kika yi mini ƙarya sai
na ci ubanki a daren nan"
Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan fitarta.
Huzaifa tun da yaga Yaya Umar ya shiga ɗakin Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin
jikinsa, dan ya san yau sai yadda Allah ya yi.
Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take faɗar gaskiya saɓanin ɗazu da ta yi
mata ƙarya.
Umar ya ce "Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?" Ta sunkuyar da kai tayi shiru.
"Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce ke?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya ɗora da cewa "Wato ke duk wani abu da za'a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na
dama, ya fita ta hagu ko?"
Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.
"Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi hankali ba".
Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata wani mugun kallo, ba shiri ta
miƙe ta durƙusa ta hau kamun kunne.
Gaba ɗaya Huzaifa ji yayi bai ji daɗi ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka
bari ta fara bacci, za a sakata kamun kunne, ya tsaya ta ƙofa yana leƙen tsakar gidan ya san
yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da yayi niyya sai
Hassan ɗin sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya nan.
Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tangaɗi take tana neman ta faɗi,
amma yayi banza da ita, dan ta san idan ta faɗi ko ta tashi ba zata iya ɗaukar wani hukuncin ba.
Tun tana kuka ƙasa-ƙasa har ta fara yi da ƙarfi, saboda azabar gajiyar da ta yi.
"Tashi" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Ta ɗago duk ta haɗa uban gumi, ga hawaye da majina
duk a fuskarta.
"Kukan uban me kike yi?"
Cikin kuka ta ce 'Yaya na gaji ne, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba, na tuba"
"Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur tun da kin gaji da kamun kunne"
Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har Sai da Mama ta ji babu daɗi a
ranta, amma tuna cewar yarinyar ba 'yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da
laziminta.
Aliyu ne ya fito daga ɗakinsu, cikin damuwa ya ce "Dan Allah Yaya kayi haƙuri ka ƙyaleta haka
ta je ta kwanta dare yayi, wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta".
A fusace Umar ya kalleshi ya ce "Ka ɓace mini daga gabana ko sai na haɗa da kai?" Ran Aliyu
ba ƙaramin ɓaci yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga banɗaki.
Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta huta, shi kuma ya tashi ya fita.
Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta take kamar babu nama a cikinsu sai
rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ƙashin bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da
yake yi mata.
Yaya Umar na fita, Huzaifa ya ƙaraso in da take yana mata sannu cikin tausayawa kamar ba shi
ne ya gama bawa Mama shawarar ta haɗata da Yaya Umar ba.
Ya je ya ɗebo ruwa ya bata, ta karɓa ta kafa kai tana sha tana kuka. Ta gama sha, ya karɓi kofin
ya ajiye yana goge mata hawayen fuskarta.
"Uban me kake a nan wurin?" Basu ji dawowar Yaya Umar ba, sai maganarsa kawai suka ji,
suka yi tsuru-tsuru.
"Zaka tashi ko sai na haɗa da kai?" Jiki na rawa Huzaifa ya tashi, ya koma ɗakinsu.
Ya kalli Ruma da ke ta ajiyar zuciya, ya tabbatar ta galabaita, ya san yanzu haka jikinta na ciwo,
ya jefa mata leda a jikinta ya ce "Maza ɗauki ki shanye"
Jiki na rawa ta ɗau ledar, doguwar jarka ce cike da youghurt mai sanyi a ciki, ta ɗaga kai ta sha
rabi, yana tsaye yana kallonta, ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Na ƙoshi".
Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta ɗago ta kalleshi, ganin yana mata wani irin kallo ne, ya
sanya ta cigaba da sha tana yamutsa fuska, da ƙyar ta shanye, ta ajiye robar tana jiran umarni
na gaba.
"wuce ki je ki kwanta"
Da ƙyar da yinƙura ta tashi, ƙafafuwanta na ta rawa saboda ciwo, ta shiga ɗaki.
Tana shiga ta tarar da Mama na salla, ta faɗa kan katifa tana kuka.
Mama har ta idar da sallar ba tace mata komai ba, ta cigaba da kukanta har bacci ya ɗauke ta.
Cikin bacci ta ji Mama na ɗala mata duka a cinyarta "Tashi" duk da yadda ta ji zafin dukan,
amma ta buɗe idonta a hankali ta kalli Mama, ba tare da ta ce komai ba.
"Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari a kwance, ke ba jaririya ba ba 'yar yaye ba"
jin abin da Mama ta faɗa ne ya sanya ta miƙe zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.
Waro ido ta yi ta ce "Na shiga uku, wallahi na zata a mafarki ne, dan Allah kiyi haƙuri"
Mama cikin ɓacin rai ta girgiza kai ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, zaki tashi ki fita kije ki
gyara jikinki ko kuwa?"
Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda jikinta ko ina yake yi mata ciwo,
saboda punishment ɗin da Yaya Umar ya sanya ta.
Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ƙarasa banɗaki, ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta
jingine katifar tayi kwanciyarta a ƙasa.
Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji gandar tashi, saboda bacci take ji
sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a banɗaki ta
zaci a gaskene ta saki fitsarinta.
Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani nannauyan baccin ne ma yayi
awon gaba da ita.
Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta tashi ta yi salla, dan sai da ta yi
iƙirarin haɗata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi sallar.
Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta, amma ta tura baki ta ce "Ai kina
gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata
kamar an mini ɗorin karaya haka nake ji na"
Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya fara shigowa ɗakin Mama ya
gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za'a ɗora na karin kumallo?.
Mama ta ce "Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai
a soya"
Huzaifa ya jinjina kai ya miƙe, har zai fita idonsa ya sauka a kan katifar Rumaisa, ya ɗan yi turus
ya dubi Mama ya ce "Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?"
"Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu'a kawai".
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, su Balama an yi asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da
ita daga ɗaki ba, sai ɗakin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana jariri ba, tashi
shashasha" ya ƙarasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka a ƙafa.
A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta daketa, amma taga Huzaifa a kanta.
"Me nayi maka zaka dakeni?" Tayi maganar a ƙule.
"An dake ki ɗin, tashi ki fitar mata da wannan katifar daga ɗaki, mai abin kunya ƙatuwa da ke
kina fitsarin kwance"
"Ba zan fita da ita ɗin ba, uban shishshigi ko ina ruwanka, tun da ba a kan ka nayi ba, kuma
ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba".
"Au Mama ƙarya take yi miki kenan, ba zaki tashi ba?"
Cikin tsiwa ta ce "Ba zan tashi ba"
miƙa hannu yayi, ya janyota ya ɗagata, ya ce "Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan
da kika yi tsiyar a kan su". Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na faɗace-faɗace,
gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma faɗa kamar suna ganin hanjin
junansu.
Mama ta sharesu ta ƙi ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga turjewa tana kwarara ihu.
Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar ɗakin, take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.
Cikin kaushin murya ya ce "Meye haka karnuka ne ku?"
Suka girgiza kai a tare.
"Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya kun daina ba?".
"Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da kayan"
Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce "Fitsarin kwance kuma? Kina me kika yi fitsari?"
Cikin rauni ta ce "Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa tashi nayi"
"Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ƙazamar banza kawai".
Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.
Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.
Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai
yayi farat ya gaya musu ai fitsarin kwance ta yi.
Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba ta saba yin fitsarin kwance ba,
ya je ya karɓi kayan ya tayata.
Kowa da abin da yake faɗa a kan Ruma, wasu na mata Addu'a shiriya wasu kuma na yi mata
faɗa har da zagi.
Tamkar gidan 'yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama aikin gida, wasu na
wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ƙarasa haske, hatta ruwan da Rumaisa
zata yi wanka, an dafa ta haɗa ta yi wanka.
Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa, Rumaisa kuwa sai shan kunun take
da ƙyar tana yamutsa fuska.
Can ta kalli Mama ta ce "Mama Kununa bai ji suga ba, yayi tsami da yawa".
Haushi ya kama Mama ta ce "Amma a gabanki aka zazzage sugan kowa ya ɗiba ko? Kuma kin
san ya ƙare"
Ta ture kofin kunun ta ce "Nifa dama kunun nan gudawa yake sani, gashi bai ji suga ba, ni
cikina ma har ya fara ciwo"
Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata taɓa zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi
abin da za a yi mata magana ba.
Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya ɗauko ɗari biyu ya bata ya ce "Jeki wurin
Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan zafi sai ki haɗa shayi ki sha"
Washe baki tayi, ta ce "Allah dai ya biya da aljanna, gadanga na Mama" ta ɗau kofin kununta ta
turawa Mama kunun ta ce "Mama ki shanye kunun na bar miki" tayi waje.
***
Da ƙyar ta ƙarasa makaranta yau, saboda ciwon cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya
Umar ya bata a daren jiya.
"Ruma hatsari kika yi ne?" Cewar wata matashiyar yarinya sa'ar Ruman, gannin yadda take
tafiya da ƙyar.
Ta haɗe rai ta ce "Me kika gani?"
"Gani nayi kina tafiya da ƙyar, kamar wadda ta warke daga karaya"
Cikin gatse Ruma ta ce "Eh, tirela ce tabi ta kaina, da ta wuce na taso na taho"
"A'a Allah ya baki haƙuri"
Duk da yadda jikinta babu daɗi, hakan bai hanata faɗace-faɗace da neman rigima ba, dan idan
ba tayi hakan ba ace lafiyarta ƙalau ba.
Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da katifarta a tsakar gida
kamar yadda ta barta.
"Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai anyi baƙi sun tambayi ba'asi ace fitsarin
kwance nayi?"
"Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?"
Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama ta ce "Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona
da fitsarin kwance tun ina jairiya, tun ban fi wata huɗu ba na daina fitsarin kwance" wani irin
kallo Mama tayi mata, jin uwar ƙaryar da ta saki.
Mama ta ce "Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ƙazamar
banza da yake ban yi magana ba, baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya
kai gobe in Allah ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki".
Hannu ta saka ta shafa kanta, ƙanann kitso ne a kanta, a ƙalla guda arba'in da ɗoriya, Mama ta
bata kuɗi ta je ayi mata kitson hannu guda biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta karɓi kuɗi a
wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ƙanana.
Ta san yau ko Mama zata kwaɗanta ta ta cinye ba zata iya gama wannan tsifar ba, haka nan ta
tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta leƙa
Window ta ga Usman da sallaya a hannu zai tafi masallacin juma'a, ta ɗau hijjabinta ta bi
bayansa. Sai da ta fito ƙofar gida sannan ya kalleta ya ce "Ina zaki?"
"Masallaci mana" ta bashi amsa.
"Kin tambayi Mama?"
Ta gyaɗa masa kai alamar eh.
Ya ce "Shikenan muje" ya sanyata a gaba suka tafi masallaci.
Mama ta daɗe tana yiwa Rumaisa Addu'a bayan ta idar da salla, kullum cikin Addu'a take yi
mata, amma tana girma tamkar ana sake turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.
Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce mata uffan ba, Rumaisa sai
raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata magana amma taga ta shareta.
Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da Yaya Aliyu, ya siyo kifi ɗauri biyu, ya bawa
Mama ɗaya ya ce gashi nan duka gidan, ɗauri ɗaya kuma suka ci shi da Rumaisa.
Bayan sallar la'asar, ta ɗau allonta ta tafi makarantar allo.
Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata cewar Sani ya ce sai ya yi mata
dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.
Tsaki Rumaisa tayi ta ce "To, ya kasheni ya huta mana, tayar banza da ta wofi, shi bai san
tsautsayi ba"
A ƙufule Habiba ta ce "Au hakama zaki ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki
ɓatar ko a jikinki?"
"To tayar da kuɗi ya saya? Idan da kuɗi ya saya ya faɗi kuɗinta, yayyena su biya shi"
Habiba da ta gama fusata ta ce "Dalla can, uwar meye a gidan naku, banda gayyar