Showing 81001 words to 84000 words out of 85058 words
Chapter 28 - KANWAR MAZA 1 BY AYSHER COOL BY AISHACOLL .pdf
sai na kuma rubutawa, zaka gane ba ka da wayo,
ai talauci ba hauka bane, mai kyan banza" haka ta tsaya a gaban mudubi, ta cigaba da kuka.
Kamar zararriya ta ɗauko jakarta, ta ɗauko wayar ta kuma komawa kan account ɗin da Jabir ya
saka hoton takawa, ta sake rubuta "Wallahi Allah ban yafe ba, sai na kai ƙararka wurin 'yan
sanda, zaka san da ni kake yi" ta ajiye wayar tana fatan Allah ya sa kar idan mama ta dawo ta
fuskanci wani abu.
****
Baba uwani ce ta shiga kitchen ta tarar da iman tana faten dankali.
"A'a mutuniyar ba kya gajiya da aiki, Ammin ake yiwa girki ne?"
Iman ta yi murmushi ta ce "A'a baba uwani, nice zan ci"
"Au yau ba za a ci abincin namu ba ne?"
Iman ta yi murmushi ta ce "Ba haka bane, kawai da wannan ɗin nake sha'awa bana son takura
muku ne"
"A'a ai da kin faɗa ma babu wani abu, sai ayi miki, ni kuwa na ce takawa lafiya ƙalau kuwa
yake?"
Cikin rashin fahimta iman ta ce "Me ki ka gani?"
"Ganinsa na yi duk wani iri"
"A'a lafiyarsa ƙalau, ina ga hakan ya na da alaƙa da yanayin aikinsa, kin san abubuwa su kan yi
masa yawa"
Baba uwani ta ce "haka ne wallahi, ina tausayawa takawa yadda al'amura suke shan kansa
Allah ya yi masa jagora"
Iman ta ce "Amin" a dai-dai lokacin ta juye dankalin a plate ta ɗauka ta fice.
Baba uwani ta yi tsaki ta ce "Kai wannan yarinyar kininabbiya ce ba wani abu da zaka samu
daga wurinta".
Takawa fa abubuwa suka sake rikice masa, tun bayan haɗuwarsa da ruma, da ya ji muryarta da
take masa yawo a kunne, yana ta tuntuntuni, mutum ce ko akasin haka, dan iya ƙwarin gwiwar
ta, da rashin kunya da ayar tambaya a kanta.
Yau gaba ɗaya bai koma gida ba, ya wuce gidansa ya tura wa Ammi message a kan ba zai
shigo gida ba, a gidansa zai kwana.
Bayan ya turawa Ammi saƙon, ya kuma komawa Instagram, ya duba comment ɗin da ruma ta yi
a kansa, kawai ya ci karo da sabon saƙonta, ya tabatta kenan ita ɗin ce dai ta yi comment ɗin
farko.
Kiran Ammi ne ya shigo wayarsa, ya saita nutsuwarsa ya ɗaga tare da yin sallama.
Ammi ta amsa sanna ta ce "Yanzu na ga saƙonka, ka sam yadda yanayin jikinka yake, amma
ka ce zaka kwana a gidanka kai kaɗai, kar wani abu ya sameka fa"
"Ammi kar ki damu, babu abin da zai sameni in sha Allah, ina son gabatar da wani aiki ne"
"To shikenan, amma dai da ka ji wani abu ka kirani a waya".
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, in sha Allah sai da safe" suka yi sallama ya katse kiran.
Ya rintse ido, yana jin muryar ruma na sake amsa kuwwa a kunnuwansa, ya tuna yadda ta
danganta shi da sata, take ya ji ya tsani yarinyar, kuma daga uniform ɗin jikinta zaka gane 'yar
talakwa ce, amma sai ƙarfin hali da rashin mutunci, to yayi faɗa da wannan 'yar ma ya ce ya yi
da wa? Wani uban tsaki ya ja, ya koma ya kwanta yana ƙwafa. Ya kuma komawa ya na duba
comment ɗin ruma, amma ya tarar Jabir ya goge posting ɗin gaba ɗaya.
***
Ko da mama ta dawo, ta tarar gaba ɗaya ruma ba ta da walwala, duk tayi wani iri, mama ta
tambayeta ko ba ta da lafiya, ta ce ita lafiyarta ƙalau kan ta me yake ciwo, mama kuwa ta
ƙayleta, amma ta cigaba da monitoring ɗin ta.
Yau ko wannan uban surutun da take kamar an jefeta a ka, babu ta yi shiru sai tunane-tunane
take a ranta, a kan me za ta yi wa wannan ɗan tahalikin ta huce, gashi ita ba ta san a ina ma za
ta sake ganinsa ba, balle ta gaggaya masa magana ta huce da abin da yayi mata.
Mama suna ta hira suna tsara yadda bikin saukar su Yasir zata kasance, ruma ta koma kusa sa
Abdallah ta ɗan yi ƙasa da muryarta ta ce "Yaya Abdallah, dan Allah waye galadiman Kano?"
Ya dubeta ya ce "Basarake ne a Kano, ba shi ne aka ce yana Germany ba bashi da lafiya,
meyasa ki ke tambaya?"
"Babu komai kawai tamabaya na yi, amma ba ya mutu ba?"
"Anya, gaskiya ban sani ba, na ji dai an ce yana Germany babu lafiya"
Ɗan shiru ta yi ta na tunani, a wurin Hauwwaliya kawai za ta samu abin da take so, dan haka ta
sake gyara zama ta ce "Yaya dan Allah ranar juma'a mu je cikin gari"
"Ba zani ba, ina da abin yi ranar"
"Dan Allah, na ji mama tana waya da mamansu, an ce Hauwwaliya babu lafiya dan Allah ka
kaini na ganta"
"Ke na ce miki ina da abin yi ranar"
"Ai Allah na ce, ka taimaka" ta yi maganar cikin magiya.
Abdallah ya ɗan yi tsaki ya ce "Zan yi tunani"
Ta ce "Dan Allah ka kaini"
Bai sake kulata ba, saboda baya son magiya, ruma kuwa ta ƙware a kanta.
***
Kamar wasa Samha ta kira Khalifa a waya, kamar dama jiran kiranta yaje, tana kira ya ɗaga.
"Adon gari ya kike?"
"Ba dogon surutu ba, ina son sanin deal ɗin da kake son mu yi, na gani idan zan iya"
Murmushi ya yi, tare da kashe sigarin hannunsa ya ce "Kin yi tunani kin ga ni ke da mafita dai
kenan? Sai dai kin so ki makara dan na samu wanda ya kawo tayin shiga deal ɗin, ban sani ba
ko ta wurnki aka samu bayani, amma duk da haka kema akwai role ɗin da zaki taka, a ina zamu
haɗu?"
Cikin mamaki Samha ta ce "Amma waye haka, da har ka ke tunani ta hanyata ya ji labarin deal
ɗin nan?".
"Kar ki damu da sanin waye, mu haɗu a hotel ɗin da muka haɗu last"
Ta girgiza kai ta ce "No, kar ka manta ni 'yar babban gida ce, ba zai yiwu ma din ga yawon hotel
ba, ka sama mana wani wurin kawai".
"To Shikenan, zan turo miki wani address ɗin, ki huta lafiya" ta sauke wayar daga kunnenta,
tana tunanin anya ba ta yi garaje ba wurin amincewa da Khalifa ba tare da ta san aikin sa za ta
yi masa ba?.
***
Ranar juma'a ana tashi daga makaranta ruma ta taho gida, saboda ta tirke Abdallah ya cika
mata alƙawarin kai ta cikin gari, dan tuni ta tambayi mama, mama ta barta Abdallah ya kaita,
musamman da ta ji ta ce Hauwwaliya zata duba.
Ƙasan zuciyarta kuwa, so take ta sake haɗuwa da takawa, ta yi rashin kunya ko ta huce abin da
ya yi mata.
Duk wani hoton Adam yake kan account ɗin Jabir, sai da Jabir ya sauke shi, ƙarshe ma yayi
blocking ɗin ruma, bayan yayi reporting account ɗin ta an rufe mata shi.
Abdallah ya ce "Sai dai ruma ta yi haƙuri, dan wani wurin za shi, amma mama ta ce ya daure ya
kaita, dan ruma a zahiri damuwa ta nuna da rashin lafiyar Hauwwaliya.
Ba dan ya so ba ya tasa ruma a gaba zuwa mandawari, Hauwwaliyarma ta samu sauƙi, bayan
sun gaisa da mutanen gidan, Abdallah ya ce da yamma zai zo ya ɗau ruma.
Hauwwaliya ta yi ta murna da ganin ruma, dan rabon da su haɗu tun wancan zuwan.
Bayan ruma ta ɗan jima, ta fara ƙoƙarin aiwatar da abin da ya kawota.
"Hauwwaliya, ina ne gidan Galadima ne?"
Hauwwaliya ta ce "Wai makaranta?"
Ruma ta yi tsaki ta ce "Galadiman kano"
"Wanne?"
"Au biyu ne?"
Hauwwaliya ta ce "Ai akwai Galadima na yanzu, wanda ba shi da lafiya yana Germany, sannan
akwai gidan Galadiman kano wanda ya rasu"
Ruma ta ce "Wanda ya mutun"
Hauwwaliya ta yi dariya ta ce "Ke ai wan baban su Janna ne, jikar turakin nan da muka je gidan
su biki ta bamu kaya, kuma yayan Galadiman kano na yanzu ne duk fa 'yan uwa ne, sarautar ba
a rabawa a bawa bare dole sai su"
Ruma ta yi tsaki ta ce "Ni fa ba nasaba na tambayeki ba, ina ne gidan na sa"
Hauwwaliya ta ce "Shi wa?"
"Ke wai ya ina magana kina raina mini hankali, maganar wa muke ne?"
"To ke meye alaƙarki da su da ki ke tambayata?"
Ruma ta ce "Assignment aka bamu a makaranta"
"Aka ce me?" Ruma ta ɓata fuska ta ce "Hauwwaliya, ni zaki wulaƙanta?".
Hauwwaliya ta kwashe da dariya ta ce "Yi haƙuri, Galadiman da ya rasu gidansa a bayan gidan
sarki yake, wani ƙaton gida gari guda, baki ga katangar gidan ba, doguwa sosai a nan dai gidan
yake"
"To kin san 'ya'yan gidan?"
"To meye alaƙata sa su da zan san 'ya'yan gidan, suma 'ya'yan gidan duk a cikin assignment
ɗin suke?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "A'a dan Allah in anjima mu je, ina son in ga dokuna"
Haka ruma ta din ga lallaɓa Hauwwaliya, suka tafi yakasai, har family house ɗin su Takawa.
Ruma ta yi mamakin girman gidan, ya fi na Turaki da suka je rannan, suka gama yawonsu suka
koma gida.
Yau ma sai magariba sannan Abdallah ya ɗauketa, suka koma gida, sai dai tun da suka koma
gida, ruma take tunanin ta ina za ta ga Takawa, dan ta ƙudirce a ranta ba zata haƙura ba.
Sai dai gate ɗin gidan na su kawai girmansa abin mamaki ne, babu wata 'yar kafa da za ta bi ta
shiga, ga masu gadi a zaune a ƙofar gidan, da alama shiga gidan ba zai zama abu mai sauƙi
ba.
***
Tun da Samha ta koma gida, take tunani a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi, dan ba abu
ne mai sauƙi ba. Amma duk tunanin da ya kamata ta yi ta yi, shikaɗai me mafitar da ya rage
mata, dan takawa hankalinsa sam ba ya kanta, idan har ba kawar da alaƙar nan ta yi ba, to ita
da Adam sai dai kallo daga nesa, haka zalika sai ta yi ƙoƙari wurin takawa su Hajiya Jamila
burki a wasu ɓangarorin dan idan suka nakasta shi, to ita suka yi wa.
***
Mama ta zauna ta tattauna da yaranta, a ƙarshe suka amince da a sayar gonar mahaifinsu ta
can katsina a garin Ƙanƙara, domin yin hidimomin da suke gabansu, masu registration ayi
musu, masu exam a biya musu, masu buƙatar jari duk ayi musu. Sannan still akwai filinsu da
aikin gwamnati ya bi ta kai, za a basu diyya. Sai dai mama ta ce ita tsoron garin nan take ji, kawai ayi waya su sayar ɗan abin da ya samu
da na diyyar a aiko musu, can dangin babansu suka hau mitar cewa mama ta mallake yaran ba
ga son su je in da suje, ƙarshe aka yanke Aliyu zai je.
Yaya Abubakar ya ce "Dan Allah mama idan zai je, ya kai musu ruma, tun da dama exam za su
yi, su yi hutu, ko a samu su daina surutun nan da suke yi na rashin zumunci, rabon da aje da ita
garin fa tun yaye, rannan da na je baki ga mita da faɗan da suka din ga yi ba, wai kin fiye son
'ya'ya, wayar da muka yi da baba Habu shekaranjiya a kan biyan diyyar nan shi ma ba ki ji
faɗan da ya yi ba".
Mama ta ce "Ba ƙi nake ba, ka san halin rashin jin yarinyar nan shi nake tsoro, ga yanayin garin
babu lafiya".
"Mama ai a cikin ido ake tsawurya, in Allah ya yadda babu abin da zai faru sai alkhairi"
Mama ta ce "To, Allah ya sa"
Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe ɗaya ta fi son sai ta tafkawa
takawa ɓarna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.
***
Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare, ƙamshi duk ya
gauraye ɗakin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.
"Mutum kwalliya sai ka ce aljana" dariya ta yi har sai da dimples ɗin ta suka lotsa, ta ce "To idan
ban kwalliya ba me zan yi?"
Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce "Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai"
ɓata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana faɗin "My
Chubby girl".
***
Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan
tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da
yake garin.
Gaba ɗaya Instagram sun yi banning account ɗin ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram
ɗin sam.
Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta
yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.
Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.
Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi
niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.
A ƙofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga? Cikin dakiya ta tunkari ƙofar
gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.
Gadan-gadan ta nufi shiga, wani ɗan sanda yayi mata tsawa ya ce "Ke wurin wa ki ka zo?"
Ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Wurin wani"
"Waye wanin?".
"Sunanshi Adamu"
Wado ido suka yi gaba ɗaya suna kallon ruma "Ke! Baki da hankali?" Saroro ta yi tana tunanin
me ta yi kuma?
"Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki faɗi wannan sunan haka? Zaki bar wurin nan ko
sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki"
"Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga"
"Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga".
"To a wurin wa zan nemi iznin?"
Ɗaya daga cikin su ya ce "Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar 'ya da
baki fil-fil kamar robot"
Ta kalleshi ta ce "Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina" tayi maganar idonta ƙyar a cikin
nasa.
Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya jiƙawa yarinyar nan jikinta.
Ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana kallon hanya. Suka kunna sigari suna sha, ruma ta
kallesu ta taɓe baki a hankali ta ce "An yi asara"
"Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?"
"Ni dai ba a kanku nake ba, ku ƙyaleni mana" ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta
ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu naɗi.
Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara'arsu suka fara mata magana "Baba
Sabuwa, kin dawo?"
"Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?"
Suka amsa mata da Alhamdilillah.
Ruma ce ta taso da sauri tana faɗin "Baba" baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce "Yarinya ya
aka yi?"
"Dan Allah gidan nan zaki shiga?"
Ta ce "Eh, a gidan nake aiki"
"Kin san wani Adamu a cikin gidan?" Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da
fatan Allah ya sa wani bai ji ba.
"Ke 'ya ta ai ba a faɗar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san
shi"
Ruma ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an
hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata"
Baba uwani ta ce "To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?"
"Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi "
Baba sabuwa ta ce "to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda".
"Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku"
"Zo mu baki sigari " ɗayan ya faɗa cikin iya shege.
"Sai dai uwar sigari" ta faɗa a hankali.
Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani
mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.
Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a ɓangaren Mummy,
kuma tana ɗaya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan.
Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar ɗakinta takardar su fara dubawa
ko kuwa? Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a ɗan tofinta, ta cigaba da
ayyukanta.
Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana
komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da faɗa, dan babu wanda ya san ta
fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin saƙonta zai je in da take so, sai Addu'a take Allah
ya sa baba Sabuwa ta bayar da saƙonta. Aliyu ya tasa ta a gaba zuwa gida, suna tafe yana
ƙare