Showing 1 words to 3000 words out of 85058 words

Chapter 1 - KANWAR MAZA 1 BY AYSHER COOL BY AISHACOLL .pdf

07 Dec 2025

2112

[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA:        ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES





https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a
baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.


*Ina fatan yadda na fara lafiya, Allah ya sanya na gama lafiya. Ƙirƙirarren labari ne, idan akwai
abin da ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne*


Page1

Bismillahirahmanirrahim



Daji Ajiyar Allah! La'asar sakaliya, a lokacin da hasken rana ya fara disashewa, ta doshi yamma
za ta faɗi, duhun magariba na ƙoƙarin shigowa ya maye ragowar hasken da ranar ta bari kan ta
ƙarasa faɗuwa.
Gamayyar bishiyoyi ne, dogaye da da madaidaita, haɗe da ciyayi da ga mabanbantan tushe,
suka haɗu suka yiwa dajin ƙawanya. Zai iya kasancewa abin sha'awa ga wanda ya zo yawon
buɗe ido, idan har bai san mai dajin ya ƙunsa ba.
Ga wanda ya san abin da ya ƙunsa kuwa, zai kasance wuri mafi razani, firgici da kuma tashin
hankali.
Gudu take yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, tana rungume da wani zani a ƙirjinta, babu yadda
za ayi daga nesa ka gane me ta rungumo haka take wannan uban gudun.
Ƙafafuwanta babu takalmi, jikinta babu mayafi, duk da yanayin garin babu zafi, amma laɓɓanta
sun bushe tamkar dutsen da ya shekara ruwa bai zuba a kansa ba, babu alamar tana gane in
da take jefa ƙafarta. Duk da wannan mawuyacin hali da take ciki, ta bawa abin da take rungume

da shi muhimmanci sosai da sosai.
Cikin rashin sani, tayi karo da wani abu da ita kanta ba ta kai ga tantance ko meye ba, sai dai
ƙarfi da nauyin abun ya sanya ta faɗi ƙasa, take ta saki wani marayan kuka, a lokacin da jini ya
fara zuba daga ƙeyarta.
Sai a lokacin abin da take rungume da shi ya tsala kuka, saboda firgitar da ya yi shima.
Jariri ne ɗanyen goyo, cibinsa ko faɗuwa bai yi ba, jikinsa duk busashshen ƙazantar haihuwa da
alama yaron ya kwan biyu, amma ko ruwa bai taɓa gani ba balle a wanke wannan ƙazantar!.

**************



Cikin garin Kano, unguwar ɗorayi tinga, misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar Alhamis, wani
matsakaicin gida ne, cikin rukunin gidajen dake ɗan ƙaramin layin,  kallo ɗaya zaka yi wa
gidajen, ka san na masu ƙaramin ƙarfi ne, duba da yanayin kwatoci da kuma kasancewar
gidajen awon igiya, ba magudanan ruwa, babu layuka masu kyau, kowa da in da fuskar gidansa
ta kalla, haka zalika kowa in da ya ga dama yake sako kwatar gidansa, wasu da gyara wasu
babu, ga gidajen 'yan ƙanana tamkar wani zai hau kan wani.

"Wai ba zaki fito ki je mini aiken ba, har sai gawayin ya ƙare tukuna?" Cewar wata matashiyar
dattijuwa, da take zaune a gaban kurfoti, hannunta riƙe da mafici tana firfitawa, gefe ga farantin
silba ɗauke da garin tuwon masara a kai.

Wata  yarinya ce ta fito daga wani ɗakin da yake bayan matar, hannunta ɗaya riƙe da hijjabinta,
ɗaya kuma sai matsar hawaye take yi.

Matar ta kalleta ta ce "Kukan me  ki ke yi?"

Aikuwa kamar mai jiran ƙiris, cikin sangarta yarinyar ta ce "Ba Huzaifa bane ba ya....

"Ni yi mini shiru, haka dai kuka iya faɗa kamar kuna ganin hanjin junanku, idan na hana ki zuwa
in da yake ai ba zaki hanu ba, maza ki ɗau kuɗin nan ki je mini gidan Laure, ta baki kuka ta
sittin, daddawa ta arba'in sai manja na naira ɗari ki kawo mini canjin, na yi maza in kaɗa miyar
nan kan magariba".
Kwaɓe fuska yarinyar ta yi ta ce "Wai yau ma miyar kuka za ayi Innalillahi wa innalillahi raji'un"

Baki buɗe ta bi Yarinyar da kallo, cikin hasala ta ce "Idan na kaɗa kukar kar ki sha, zaki ɗau
kuɗin ki fita ko sai na yi fatali da kanki a wurin?"

Ta durƙusa ta ɗau kuɗin, ta zura hijjabinta ta nufi hanyar fita, a ranta tana jin gara ace yau babu
abin da zasu ci, da wannan tuwon kamar na ibada.

Cike da kashedi matar ta ce "Idan kin ga dama kuma ki je ki zauna, kar ki yi sauri kiga yadda
zan yi da ke, ko ki biyewa yara ki tsaya shashanci a hanya"

Ba to ko waiwayo ba, ta yi gaba abinta tana kalle-kalle.

Gidansu ƙawarta Habiba ta fara biyawa, ta tarar da maman Habiba a tsakar gida ana yi mata
kitso, ta durƙusa ta gaida Maman Habiba, sannan ta ce mata wurin Habiba ta zo.
Habiba ta fito daga ɗakinsu tana kallonta tana murmushi, ta ƙaraso in da take tsaye ta ce
"Ruma ina zuwa ne?"

Cikin muryar Raɗa Ruma ta ce "Dan Allah Habiba aron tayar Sani zaki bani, Mama ce ta aikeni
so nake nayi sauri na je na dawo".

Habiba ta ce "Kaii, Ruma kin san Sani yafi kashi ɗoyi, kar na baki ki je ki salwantar da ita, daga
ni har ke mu shiga uku".

Ruma cikin ƙwarin gwiwa ta ce "Wallahi ba zata salwanta ba, ke dai ki aramini, so nake na yi
gudu na ne na dawo".

Habiba ta ja Ruma soron gidansu, ta duba saman kejin kajin da ke cikin ɗan tsukakken zauren
gidan, ta ɗaukowa Ruma tayar Sani ta bata ta ce "Dan Allah Ruma ki kula, kar wani abu ya
samu tayar nan, ki yi maza mi garata ki je ki dawo"

Ruma tayi murmushi ta ce "Kar ki damu, yanzu zan fyalla naje na dawo, ina son tayar nan ta
sani dama ya bar mini, 'yar dandaɓasa da ita, yanzu zaki ga naje na dawo".

Habiba tayi murmushi ta ce "To shikenan, yi sauri kafin ya dawo".

Ruma ta dafe kan taya, ta garata ta dinga zura gudu ta lunguna kamar wata namiji ba mace, ba
ta tsaya da gara tayar ba har sai da ta isa gidan Laure.
Ta yo sayayyarta ta gama, ta fito ta kuma garo taya zata tafi gida, can ta hango wasu 'yan
makarantar allonsu, a ƙofar gidan Hanne mai markaɗe suna 'yanta, ba tare da ta tuna da
kashedin Mama ba, ta ajiye kayan aiken da canjin haɗi da tayar da ta aro, ta shiga aka hau
'yanta da ita.
Kasancewar ƙwararriya ce a harkar shagala da iya rinto, nan da nan wasa ya ɗau zafi, ganin
tana ta cinyesu a 'yantar ta hanyar rinto, sai wasa ya koma faɗa, daga nan aka hau dambe, a
wurin Ruma ta kifar wa da wata markaɗenta ga ta da ƙarfi kamar doki. Da ƙyar wani mutum ya
raba faɗan, Ruma ta haɗa yaran mutane ta zane musu jiki, sai da mutumin yayi mata barazanar
zai gayawa yayanta, sannan ta haƙura da damben.

Yarinyar da suka yi damben, ganin an musu asarar markaɗe, an kifar ga duka, ya sanya ita da
ƙannenta suka fasawa Ruma Manjan da ta sayo wa Mama, suka kwashe canjin aiken, suka

farke ledar aiken suka gudu, daddawar ma sai da ƙyar ta tsinto wasu, an fasa ledar kuka duk ta
watse.

Ta kwashi sauran kayan, ta tafi gida, tana tafe tana tunanin wace ƙaryar za ta jirgawa Mama,
dan ta kaucewa faɗanta, dan a duniya ba ta son faɗan Mama, gefe guda kuma tana tunanin irin
dukan da zata naɗawa Safiya idan suka haɗu a makaranta allo, saboda abin da suka yi mta.
Lokacin da Ruma ta isa gida tuni an fara kiraye-kirayen sallar magariba, domin wasu masallatan
har sun tayar, sai a lokacin ta sake shan jinin jikinta, tsoro ya ziyarce ta.

A soro ta rakuɓe tana leƙa cikin gidan, ta hango Mama a gindin rariya tana alwala, Mama ta
ɗaga ido tayi mata kallo ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da alwalarta.

Cikin sanɗa Ruma ta shiga tana satar kallon Mama, ta ji mai Maman za tace mata, amma ta ji
ba tace mata komai ba.
Ta lallaɓa ta ajiye abin da yayi saura na aiken, ita ma ta faɗa banɗaki tayi alwala.
Ta lallaɓo falo, ta tsaya a bayan Mama ta tayar da sallar ita ma.
Mama ta idar, ta tashi ta fita tsakar gida, ta duba abin da Ruma ta kawo mata na aiken, taga irin
aika aikar da Ruman ta yo.
Ta dawo falon tana jiran Ruma ta idar da salla ta dirar amata, amma Ruma ta ƙi idarwa, ta hau
nafifilin babu gaira babu dalili, matar da wataran sallar ma sai Mama ta haɗa .mata da duka
take yi, amma yau sai gashi har da nafila.

Can da Mama taga abin nata bana ƙare bane ba, sallar taƙi ƙarewa, ta damƙo wuyanta ta baya
ta zaunar da ita, ta kalleta cikin haɗe fuska ta ce "Gidan uban wa ki ka je dana aike ki?"

Cikin tsoro Ruma ta girgiza kai ta ce "Ba ko ina Mama"

"Ƙarya kike yi, zaki gaya mini ko sai na murɗe miki wuya, tun la'asar na aike ki amma sai
magariba kika shigo mini, gidan uban wa kika je?"

Cikin zazzare ido Ruma take jujjya kai tana rantse-rantsen rashin gaskiya, "Wallahi Mama ban
je ko ina ba"

Cikin tsananin Fushi, Mama ta ce "Ba zaki gaya mini ba!"

"Mama wallahi dagaske nake"

"Assalamu alaikum" aka yi sallama a tsakar gida.

Mama ta amsa sallamar tana huci, wani matashin saurayi ne ya shigo ɗakin, yana faɗin Mama
na dawo".

Mama ta ce "Sannu da zuwa"

Ya amsa da yauwa, ya dubi Mama dake tsaye a kan Ruma, Ruma sai wulƙita ido take, kamar ta
zagi sarki.

"Mama meyafaru ne?" Yayi Maganar yana son jin ba'asi.

Cikin ɗacin rai Mama ta ce "Saboda tsabar iskanci na yarinyar nan, nan da gidan Laure, ta je ta
sayo mini kayan miya, tun bayan la'asar sai yanzu ta shigo mini gida, babu aiken babu dalilinsa,
kuma babu canjina, nayi-nayi ta gaya mini in da ta tsaya amma taƙi faɗa sai rantse-rantse take
yi".
Ya kalli Ruma ya ce "Ba zaki faɗi inda kika tsaya ba, kuma ina canjin? Ko zuwa ki ka yi ki ka
kashe mata kuɗi tunda kin saba"

Cikin tsiwa da rashin kunya, Ruma ta ce "Ban sani ba, kai kuma waye ya saka da kai, zaƙin
zaƙafere mai gida feraye kabewa, ai ba da kai ake yi.....
Kan ta ƙarasa Mama ta rufe bakin nata da duka, da sai da tayi zaton bakinta ya fashe.

Ja da baya tayi da sauri, ta dafe bakinta tana yarfe hannu, saboda ta ji zafin dukan nan sosai da
sosai.

Ya jinjina kai ya ce "Mama ƙyaleta, ba dai bata da kunya ba, kar ki wahalar da kanki, ki bari mai
sunan Baba ko Haidar su shigo, sai su tuhumar miki ita".

Jin abin da ya faɗa ya sanya Ruma ta yi wata irin zabura, ta ce "wallahi Mama gaskiya na gaya
miki, dan girman Allah kar ki gaya musu, canjin ne suka zube a hanya, na faɗi ƙasa man jan ya
fashe dan Allah kar ki gaya musu".

"Wallahi Mama ƙarya take yi, kin san dai ƙaryarta ba ta salla, ki tuhumeta bari mai sunan Baban
ya dawo zaki ci ubanki".

Cike da gamsuwa Mama ta ce "Ai hakan za ayi tun da ba ta da mutunci"

Ya fakaici idon Mama ya yiwa Ruma gwalo.

"Mama kin ganshi ko yana mini dariya, dan Allah kiyi haƙuri"

Banza Mama tayi da ita, ta bawa Huzaifa kuɗi ya kuma yi mata wani cefanen.

Rumaisa ta koma gefe tayi tagumi, zuciyarta na ta zullumin halin da zata iya shiga, idan har aka
sanarwa da Mai sunan Baba ko Haidar abin da ta yi, gashi ko giyar wake ta sha ta san ba zata
iya gayawa Mama haƙiƙanin abin da ya faru ba.
Salati kawai take yi, tana roƙon Allah ya rufa mata asiri, kar Mama ta gaya musu, ƙasan

zuciyarta kuma tana yi wa Huzaifa Allah ya isa da ya bawa Mama shawarar ta haɗata da su
Haidar.

Ta na tsaka da tunanin, ta jiyo Mama da Huzaifa suna hirarsu a tsakar gida, kamar ba ita ta
gama faɗa ba.
Suna yi mama tana ƙarasa aikin miyarta.
Sallama aka yi a tsakar gida, Ruma ta rikice, dan kusan muryoyinsu duk kusan iri ɗaya ne, ta
ɗan nutsu ne da ta tuna mai sallamar muryarsa ba ta kai ta su Haidar fashewa ba, kuma shi
dama sanyin hali ne da shi.

Jiyo Mama tayi tana faɗin "Fodiyo, an dawo"
"Eh Mama, ya gidan?"

"Alhamdilillah, sannu ka je ka watsa ruwa kafin nan na gama miya"

Usman da Mama ke kira da Fodiyo ya ce "To Mama, ga wannan" yayi maganar yana ajiye mata
leda.

Miƙewa Ruma tayi tana leƙa window, tana son gane me ye a cikin ledar da Fodiyo ya kawo.
A ranta ta ce "Allah ya sa kifi ya kawo, idan kifi ne a bani kasona, dan idan aka saka a wannan
baƙar miyar ban sha.

Ba ta kai ga gano meye a ledar ba, idanunta suka sauka a cikin na dodonta, da ya shigo gidan
ko sallama bai yi ba, gani tayi tamkar yayi mata wani irin mugun kallo, ko dan dai a tsorace take
ne oho.
Mai sunan Baban Mama kenan, Umar faruk.
Cikin takunsa na ƙasaita ya ƙaraso tsakiyar tsakar gidan, sannan ya yi sallama.

Hannu Ruma ta ɗora a ka, muryarta ƙasa_ƙasa ta ce "Na shiga uku, yau kashina ya bushe
ƙayau idan ya san me nayi".

Tun daga sallamar da ya yi, bai cewa kowa komai ba, shi ma ya ajiyewa Mama ledar da ke
nasa hannunsa, ya wuce ɗakinsu.
Bai jima ba ya fito tsakar gida, ya ɗau buta zai yi alwala.
Ruma ce ta fito kamar munafuka, ta ɗan risuna ta ce "Yaya Faruk sannu da zuwa"

Ɗaga ido ya yi ya kalleta, bai amsa ba ya mayar da kansa ya cigaba da alwala.

Cikinta ya ɗuri ruwa, ta ɗau tsintsiya ta tafi falon Mama ta hau shara a daren, kai da gani ka san
sharar ba ta domin Allah bace ba.
Huzaifa ya faki Idon Mama ya bi Rumaisa falon, ya dinga leƙata yana tuntsura mata dariya.

Ba dan tana cikin yanayi na tashin hankali ba, babu abin da zai hana su kafsa faɗa da Huzaifa a

daren nan, amma ta san biyewa Huzaifa su yi faɗa alhalin Faruk yana gidan nan, wata babbar
matsalar ce, mai zaman kanta, dan ƙarshe sai tayi kuka.

"Ba zaki fito ki ɗebi Abinci ki ci ba?" Mama tayi maganar cikin ɗaga murya, yadda za ta jiyota.

Daga ɗaki Ruma ta ce 'Mama na ƙoshi"

A ƙufule Mama ta ce "To uban me ki ka ajiye da zaki ci, ba zaki fito ki ci Abinci ba?"

Ruma ta ɗan tura baki tayi shiru.

Usman ya ce "Ai kin san kin yi maƙiyin nata tuwo, mussaman miyar kuka da ma wata miyar ce
ba wannan ba, ƙila ta ci"

Mama ta ce "Abin da nake da shi ba shi zan dafa na bata ba, zan fasa girki ne dan ba ta cin
tuwon?".

Cikin kakkausar muryarsa Umar ya ce "Ki ƙyaleta, tun da a cikinta zata zuba, ta kwana da
yunwa mana".

Mama ta gyaɗa kai ta ce "Ai shikenan"

Muryarsa kawai da ta jiyo, sai da ta sake shiga cikin tashin hankali, tsananta addurta ta yi, a kan
Allah ya rufa mata asiri kar Mama ta gaya masa ta yi mata laifi.

'yan mazan nan suka kewaye Mama, suna ta hira kowa da abin da yake ce mata, banda mai
sunan Baba, da  yake duba wayarsa, ba tare da ya tanka musu ba.

Jin suna ta hira, Mama ba ta gaya masa tayi laifi ba, ya sanya take ta murna, tayi maza ta yi
sallar isha'i ta shimfiɗa katifar ta ta kwanta.
Ta cigaba da Addu'a a cikin zuciyarta.

"Assalamu alaikum" aka yi sallama a tsakar gidan.

Suka amsa baki ɗaya, Suka zubawa yaran da suka shigo ido mace da namiji.
Duk da akwai wutar lantarki da fari Mama ba ta gane yaran ba sai daga baya.

Suka gaida Mama da su Umar, Mama ta kallesu ta ce "Habiba ya aka yi me?"

Habiba ta ce "Ruma tana nan?"

Umar yayi caraf ya ce "Yaya aka yi?"

Kasancewar sa mutum mai tsanain kwarjini, sai da Habiba ta ɗan ruɗe sannan ta ce "Dama
ɗazu ne da aka aiketa ta zo ta ce na bata aron taya, zata jewa Mama aike, to tayar ta Sani ce,
ta ce zata dawo da ita kuma haryanzu shiru".

Mama cikin mamaki ta ce "Taya kuma?"
Habiba ta jinjina mata kai.

Gaba ɗaya Ruma ta manta da ta je ta aro taya, sai yanzu da ta ji maganar Habiba, dan tun da
aka kwashi damben nan a nan ta yasar da tayar ta yo gida.
Ɗora hannu tayi a ka ta ce "Na shiga uku, Habiba shikenan kin kasheni".

Mama ta ce "Kina ina zo nan, mara kan gado, babu yadda ban yi dake ba a kan ki gaya mini in
da kika tsaya, amma kika ce ke baki tsaya ko ina ba, ashe yawon aron taya kika tafi ko, ko ina
sai kin nuna hali ƘANWAR MAZA, ina ke ina taya ban da hauka, zaki fito ki basu abarsu ko
kuwa?"
Jikinta na tsuma ta fito ta tsaya daga bakin ƙofar falon Mama, tana satar kallon Umar, amma
taga kamar ma bai san me ake yi ba.

"Ma.m.maama.. wallahi dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0