Showing 84001 words to 85058 words out of 85058 words

Chapter 29 - KANWAR MAZA 1 BY AYSHER COOL BY AISHACOLL .pdf

07 Dec 2025

2108

mata zagi.

Wajen ƙarfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa
gidan ba sai yanzu.
A gate jami'an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka
hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.

Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta
yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya ce "Kira mini Baba sabuwa" ta miƙe tana tunanin me yasa yake neman Baba
sabuwa a yammacin nan?.

Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya miƙa mata hannu ya ce "Bani saƙona" babu musu ta
fito da takarda ta miƙa masa. Ya juya ya fice.

Fauziyya ta ce "Sabuwa, takardar mecece?"

"Wallahi wata yarinya ce ta tsareni a ƙofa, ta ce a bashi ban san yarinyar ba ma"

"To meye a ciki?"

"Ai kin san ba iya karatu na yi ba"

"Kuma da baki iya karatun ba, mai ya hana ki kawo mini, tashi dalla usless" Sabuwa ta tashi
cike da haushin tsawar da Fauziyya ta yi mata, duk da ba yau ta fara ba.

Bai tsaya duba takardar ba, ya jefata a cikin jakarsa ya tafi wurin Ammi.

Gaba daya ya manta da takarda, sai washegari da daddare yana neman wasu takardu, takardar
ta faɗo.
Ya buɗe takardar wasu 'yan ƙananan rubutu ne, marasa kan gado a cikin takardar, bai yi zaton
rubutun zai karantu ba sai da ya fara karantawa, duk an gwamutsa Capital da small latter's.

*Da farko dai zan fara da yi maka Allah ya isa, dan da alama baka da ƙanne mata shi ya sa ka
yi mini abin da ka yi mini. Kamar yadda ka saka aka nemo ni, nima sai da na gano gidanku. Ka
saka aka ɗauko ni, ka zageni kuma ka ci mini zarafi, to wallahi ban yafe maka ba taɓa mini
nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka shaƙoni hannunka
yana taɓa wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya taɓa shi ciki yake yi,
to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun
zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na faɗa an saci kuɗin talakawa
an je karatu ƙasar waje. Mu zuba mu gani daga maƙiyiyarka  RUMAISA MAHMUD ƘANƘARA
ƊORAYI TUNGA ƘANWAR MAZA Kazo ka kasheni*

Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya
maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ƙirjinta
ranar da aka kai masa ita.

Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta
da ƙuruciya.

"Zan ƙure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen" ya maimaita
wasiƙar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ƙular da shi irin wai ya taɓa mata nono, duk da
bai riƙe cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.


Mama ta haɗawa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau
kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ƙarshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da
ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta taɓa nisa da ita na kwanaki ba, ga
kuma rashin ji irin na ruman.
Uniform ɗin ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya ɗoɗar Abdallah ne ya goge mata su, sai
ƙamshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye.
Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta,
ƙazantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta buɗe idonta, dan ta ga wani mara

mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?

A hankali ya sauke glass ɗin motar, suka yi ido huɗu da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma
kasa magana gaba ɗaya.

Buɗe motar ya yi ya fito yana ƙare mata kallo.

"Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na
ga saƙonki, abin da ki ka ce na taɓa ɗin ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba
in gani ko akwai".

"Wai kai ɗan iska ne?" Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar
Takawa, saboda ya kaita bango.
Maganar ta dake shi, amma ya ce "Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke taƙama da su, sai na
kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya".

Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.

"Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi
mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka
durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka" tayi maganar
har da dukan ƙirjinta.
Girgiza kai ya yi, ya buɗe motarsa ya shiga, ta durƙusa ta ɗebi taɓon wurin ta fara watsa wa
motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da taɓon wurin ya tafi.


(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA
TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALAƘARSA DA MAITA DA
HAJIYA JAMILA TA FAƊA? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA
SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ƊAN UWANSA.
ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU
KO KUWA? KAR AYI BABU KU, MAI BUƘATAR BOOK2 YA TUNTUƁENI TA LAMBAR
WAYATA 08081012143 YA YI PAYMENT*


Ayshercool
Whats app only, ban da kira Please � 08081012143

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0