Showing 27001 words to 30000 words out of 35296 words

Chapter 10 - Hira Da Matattu Complete Book By Jamila Umar Tanko.txt

Samira da sauri ta toshe ma ta baki ta yi magana cikin rada ta ce "yi a hankali Sharifah ce fa, tana cikin bandaki kada ta ji ki ba zata ji dadi ba. Allah Ya shirye su, su kuma. Babu wata fatalwa qawata ce kuma aminiyata."
Samira ta yi tsaki ta na magana a hankali ta ce "daman Aunty Sharifah ce? su har yanzu ba zasu bar maganar fatalwar nan ba ne? Bayan an fayyace komai zance ya wuce. Wallahi sun hana ni karatu sai waya suke, Anti Nana har da kuka take yi min a waya."
Samha ta ce "in ba ki gama Assignment dinki ba ki je ki gama kawai ki manta da su."
Samira ta gyada kai ta ce "ba mu gama ba na Taso wallahi. Allah Ya sa ma da motarki na je da na sha wahalar neman abin hawa. Bari in koma da sauri."
Ta fice da saurin, yayin da Samha ta jawo wayarta, missed calls dinsu ta gani ya fi ashirin da sakonni da na su da na Samira.
Sakon Nana ne ta rubuta wai Samha ta fada musu gaskiya idan itama ta zama fatalwar ne su rabu da ita, dan sun ga alamu har akwai munafunci tunda in an yi shawarar rabuwa da Sharifah sai ta sake jajubo musu ita.
Dariya ta kama ta ba mamaki ba, har sai da ta toshe baki, ta sha dariya ta gode Allah. Sannan ta ajiye wayar daidai lokacin Sharifah ta fito daga bandaki. Itama ta shiga don yin alwallah.
Bayan sun idar da sallah ne Sharifah ta tambaya wacece ta shigo? Dan ta ji tana magana da wata?
Samha ta yi murmushi ta ce "Samira ce ta zo ta dauki wani abu ta koma Makaranta."
Ita fa Samha har yanzu a labarin Sharifah ba ta ji an sauka a in da take so a sauka ba. Alaqar Sharifah da baqin kare da ciwo da mutuwa, sannan kuma da labarin Fanna yadda ta mu.
Samha dai sai tsokano labari take Sharifah tana zuqewa.
Sharifah da Hamidah ne suka yi waya, Hamidah tana bata labarin cewa Mahaifinta ya kira ta a waya yana bata hakuri akan rashin kula ta da baya yi, ya san yayi kuskure zai gyara. Sannan kuma yana so ta tubure ta cewa mamarta ta dawo gidansa.
Sharifah ta tabe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "Hmmm! Rabu da shi, idan ma mafarki yake yi to ya farka."
Bayan sun kashe waya Samha ta gyara zama ta ce "watakila ya canja halinsa, ki yi hakuri mana ku koma."
Wannan karon wata katuwar harara Samha ta amsa daga wajen Sharifah.
Ta ce "kin san kuwa bayan rabuwata da shi aure sa nawa? Ya kai aure takwas yi, wata ma watanni uku kacal ta yi ta fita, wasu matan ma basu kai watanni ukun ba. Dan bashi da hali ko kadan. Ya zagi iyayenki,ya zage ki, ga cin mutunci, babu abinci, babu Biyan kudin haya, babu kula da yaranki, ke hatta kudin wutar lantarki in baki biya ba sai dai a yanke ba zai biya ba.
Ga Hamidah nan zan iya rubuto abinda ya taba kashe ma ta tun daga ragon suna zuwa yanzu, ba ta ci dubu darinsa ba. Haba Samha ni kuma wacce irin asararriya ce da zan zauna da mai karancin addini?
Wasu abubuwan ma ba zasu fadu ba saboda alfarmar aure da haihuwa. Danginsa su na kirana a ways su na roqo wai in dawo dan Auwal ba zai iya zama da kowa ba sai ni. Saboda ni kadai ce na iya yin zaman shekaru masu yawa da shi. Sun kuwa san wahalar da na sha da shi?"
Samha ta bude baki ta dafa haba ta ce " wai! wai!! wai!! har abin na sa ya kai haka daman. Gaskiya wannan ba mijin zama ba ne. A haka kyakykywa da shi kamar wani gentle man."
Sharifah ta ce "kyawun dan miciji ne, shiyasa nake so 'yan mata su gane su rabu da kyawun sura, su zabi hali, duk namijin da bashi da hali mai kyau kuma addini bai ratsa shi ba toh kada su sake su aure shi, koda yana zubar da naira dan za suyi nadama duniya da lahira.'
Samha ta ce " gaskiya ne Allah Ya zaba miki wanda ya fi alkhairi kawata. Yanzu yaya kuke ciki da Adamu da maganar yara? Sanda mu ka zo na ga Hamidah tana kuka rannan, ta ce min an sace yaran ne. Ke kuma mu ka jiyo kina magana da Shariqah a daki. Me ya faru ne?."
Sharifah ta kwashe da dariya ta ce "shine ku ka fice da gudu ko? Ai na san kun ji shine har yanzu su Nana suke ta guduna? Ba su da hankali."
Samha ta ce " toh meye ya faru?"
Sharifah ta ce "da aka fara zaman sulhu sai aka ce in bashi yaran ya gani saboda sun shekara bai gansu ba. Kin ga ai ba zan hana ba tunda an ce sulhu, ga lauyana ga lauyansa ga barista Aisatu ba zan kawo komai a raina ba ai ko? Kuma an yi Hutun makaranta a lokacin.
Na rantse da Allah mutumin nan dan bashi da ta ido sai ya riqe yaran ya hana su, har sati biyar, ke har ya saka su ma a wata makarantar. Kamar mu na garin mahaukata inda babu doka. Ya manta a tsakiyar lauyoyi aka yi magana kuma an rubuta komai.
Ya tafi ya sami lauyansa wai ya zo su je wajen Bar. Aisatu a canja magana, saboda shi ya dauka kowa ne a Nigeria ya yake karbar cin hanci. Ai kuwa ta yi masa fata-fata kuma ta tabbatar masa ya karya doka. Daman kuma lauyansa ya fada masa gaskiya babu in da zai je a goyi da bayansa, akan abin nan da ya yi.
Su Shariqah ne suka shiga damuwa dan ta na zo min akai-akai, ranta a bace dan bata cika yin magana ba ma idan ta zo amma ina gane yanayinsa. Hamidah ce ma take ta kuka, shine a lokacin ku ka ji ina fadawa Shariqah gaskiya, cewa ta je ta kwanta wannan yakin na masu rai ne."
Tsoro ya kama Samha gami da daurewar kai ta ce "Sharifah na kasa gane abinda kike fada idan kika ce Shariqah ta zo."
Sharifah ta yi murmushi ta ce "ai na fada muku a baya, ni na gani da idanuwana mamaci yana sanin abinda yake faruwa a duniya."
Samha ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce " kuma ya mutu mutuwar gaske, amma ake ganinsa?"
Sharifah ta ce "ki dai mu je zuwa za ki ji komai. Ina zamana na ga an dawo da yaran, ban ce komai ba amma na fadawa lauyana duk abinda ya faru. Sai ya riqe Hamid dan yaron nan da nake yawo da shi wanda ya fi kowa sona a cikinsu, nima na fi shakuwa da shi. Sai ya riqe shi dan ya san abin zai taba min zuciya. Ya yi karya wai yaron bashi da lafiya, ashe har a makaranta ya saka shi."
Samha ta ce "Adamu fa ya sami matsala, ya rasa yadda zai yi da ke ne yake wannan kame-kamen."
Sharifah ta yi dariya ta ce "ya raina mata ne, bai dauki mace a komai ba sai ga shi ya takalo fada da mace ta hana shi bacci. Akwai mata ai kuma akwai mu na mata.
Bayan nan aka dinga zamansulhu amma an kasa cimma matsaya. Bar.Aisatu har tausayi ta bani, tana ta kokarin yin sulhu amma abu ya ci tura. Ta na da abubuwa da yawa a gabanta, kullum a na layi a ofishinta, ga gidajen radiyo da dama su na yin hira da ita, haka take kashewa ta saurare mu amma mutumin nan ya dinga yi ma ta wasa da hankali.
Bar.Aisatu ta dube ni ta yi shiru can ta ce " har misali nake yi da ke, kuma na fadawa mijina labarinki ya yi miki addua. Tunda nake sulhunta cases ban taba haduwa da wacce ta jajurce akan sai ta riqe yaran 'yar uwarta ba sai ke. Saboda idan dan wani abin duniya kike yi an zo lokacin da ko ciyar da su ma ya daina, amma baki gaji ba kullum na ki ake ci ma.
Na sha ganin uwa da uba an rabu yana cewa ba zai riqe yaran ba ita ma tana cewa ba za ta riqe ba, sai mun shiga tsakani mun yi musu sulhu sai a raba yaran gida biyu kowanne a bashi.
Amma ke gashi ba komai kike nema ba, a baki yaran 'yar uwarki ne kawai kike so ki riqe, tabbas na jinjina miki."
Sai ta sirnano da hawa ta yi min addua."
Samha ta langwabe kai ta ce "wallahi abinda nake ta tunani kenan a raina, nake cewa ko idan na mutu na bar yara nima anya Samira zata iya irin wannan jajurcewar kuwa ta riqe min yarana? Gaskiya ba kowacce 'yar uwa ba ce za ta yi maka haka bayan ka mutu ba. Allah Ya saka miki da alkhairi Sharifah, kin yi zumunci ba za ki taba wulaqanta ba kuma ba zaki yin kukan babu ba, har abada da yarda Allah."
Sharifah ta ce "Amin . Allah Ya ara mana tsawon rai da lafiya da abinda lafiya za ta ci. Yara kuma Allah Ya sa masu albarka, Allah Ya raya su su zamanto sadakatul jariya ga uwarsu da mu ba ki daya.
Bayan wannan tsohon alqalin da mu ka je da ke da na ce miki ya rasu daga baya, daman ai bashi kadai ba ne su ke handling case din ba, akwai wani dattijon arziki amma shi yana da zafin rai sosai.
Ana gobe zamu koma zaman sulhu sai na koma wajensa na sanar ma sa maganar sulhu fa ta gagara. Daman shi bai yarda da maganar wani sulhu ba, ya fi so a daukaka kara a kawo mu su case din gabansu can babbar kotu. Ya ce babu maganar a raba hankalin yara su yi kwanaki anan su koma can gidan su yi kwanaki baya cikin tsarin raino.
A daren ne na washe gari zamu koma wajen sulhu da tsakar dare ina kwance sai na ga Shariqah a kwance a kusa dani.
Da qasusuwa a cikin bakinta, ta tauna ama ba ta zubar ba.Ta hada fululluka na kwanciya har guda biyar ta tokare kanta. Kin san duk wanda ya jera fulo da yawa ya kwanta ai kinga ai ba zai iya kwanciya ya yi balance ba, sai dai ace yana zaune ya tukaro kai da su.To a haka na ganta, cikin daki mai duhu-duhu da haske kadan, ga wundon dakin a bude wanwar.
Ni kuma ina kwance a gefe bakina ya na ta addu'a amma ko yatsana na kasa dagawa.
Ta cikin budadden wudon nan na ga mage ta shigo, ta zo daf da fuskata ta na kokarin ta yagushe ni, amma ta kasa ina ta tofa mata suratul Falak, nas, samad, hasbunallahu , da Auzubillahi minal shaidanur rajim.Tayi-tayi ta taba ni ta kasa, sai ta fita ta windo.
Sai ga biri ya shigo shima haka zai taba ni ya kasa, ina ta addu'a, amma fa na sankare babu inda yake motsi a jikina sai bakina. Shima ya kasa taba ni, ya fita ta windo.
Ya na fita sai kurwata ta dawo jikina. Na miqe zaune da sauri, na dinga tashin Shariqah dakyar ta farka. Na ce ta je ta zubar da qashin da yake bakinki ta, ta tashi ta je jikin windo ta tofar, na ce ta sake tofarwa da dukka sai ta zubar da su dukka.
Sannan na ce ta zo ta gyara kwanciyarta ta kwanta.Ta zo ta sauke fululluka ta rage saura guda daya, irin yadda kowa yake kwanciya ta kalli gabas da bangaren dama ta kwanta.
Da gari ya waye na cewa Hamidah da Bello yau sulhu zai zo karshe, Shariqah ta koma ta kwanta lafiya.
Kin ga ban ma san a ranar mai duba shari'a ya je kotun yayi magana ba, a ranar zamu yi zaman sulhu a ofishin Bar.Aisatu muke zama da misalin karfe hudu aka ce, shi kuma da karfe uku ya shiga kotun. Shi kuma ya je da misalin karfe uku, lokacin ya rage saura awa daya mu fara zaman.
Ya na shiga kotun ya sami kujera ya zauna, sai ya ce a bashi file din shariar Sharifah da Adamu.
Ni da lauyana mu na can mu na ta jiransu a ofishin Bar. Aisatu. Daga baya itama ta karaso sai ta ke fada mana cewar su Adamu fa sun yi mata waya, wai Adamu ya ce azumi yake ba zai samu damar zuwa ba.
Mu na cikin maganar ta nuna mana itama fa abubuwan gabanta take kashewa ta takura kanka sannan take iya zuwa ta zauna, amma kalli yadda suke wahalar da mu kullum.
Ko bakinta bata rufe ba sai dai kawai mu ka ga Adamu da lauyansa sun shigo a gigice., bayan wayar da su ka yi su ka ce ba zasu sami damar zuwa ba. Daga dukka alamu mai sharia ne ya fafaro su ya ce lallai su zo a gama sulhun nan a yau, dan shima ya samu ya huta ina ta turo masa inspectors daban-daban ."
Samha ta tsurawa Sharifah ido ta yi tagumi tana kallo Allah ne kadai ya san lissafin da zuciyarta take yi. Kanta ya daure tamau idan aka zo maganar matacce ya bayyana a duniya ana jira da shi..
Sharifah ta ci gaba da cewa "yaro bai san wuta ba sai taka, nan da na suka nutsu aka gama magana a ranar, abinda aka shekara ana jan magana. Nima ta roqe ni da in yi hakuri da wasu abubuwan ta san zan takura amma in sassauta in rabu da shi ya je dan kansa.
Ya amince ya bar yaran a wajena su yi makarantar islamiyya da ta boko, amma zaa raba hutu gida biyu rabi a wajena rabi a wajensa.
Sannan kuma za su dinga zuwa gidansa duk ranar juma'a su dawo gidana ranar lahadi.Daman tun farko akan wannan zuwa weekend ne da ban yarda ba ya sa ya kai ni kotu, saboda abinda nake yiwa yaran hange shine zasu rasa makarantar islamiyyarsu ta yamma a ranakun asabar da lahadi. Yanzun ma a hakan ake, yara su na asarar karatunsu an a ta wuce su. Amma kuma na yi ma sa uzuri dan bai san darajar karatun ba ne.
Aka zayyano ma sa abinda zai dinga basu duk wata karshen wata n abinci, ya zauna ya na ta Jan magana ana ta musu da shi.
Yara har guda biyar amma ko abincin yara biyu baya kawowa. Bayan rashin kyau da inganci na abincin amma ban damu ba, fatana Allah Ya kara min budi in kula da su, ya je dan kansa.
Babu yadda ya iya da ni na fi karfinsa kuma na ci galaba akansa. Da shi da tawagarsa sun ji kunya kuma ya wahalar da kansa da dukiyarsa a banza bai sami yadda yake so ba. Alhamdulullah."
Samha ta ce "tabbas kin gama magana. Harkar tsiya ce ace ka kasa ciyar da yaranka amma kana can kana burgewa a waje. Kada ya dauka ya ci banza, yaran su na kallon duk abinda yake yi ba zasu manta ba. Toh yaya maganar daya shariar da ya dauko gidanki ya ce na su ne?"
Sharifah ta ce " ina zamana lauyana ya kira ni a waya ya ce ga Adamu da lauyana sun ce in zo a yi sulhu akan gidan nan nawa, ya yarda gidana ne ciko kawai zan yi ma ta. Sun yarda in basu cikon in riqe gidana.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login