Showing 15001 words to 18000 words out of 35296 words
Chapter 6 - Hira Da Matattu Complete Book By Jamila Umar Tanko.txt
ta runtse ido ta qi dagowa. Daga nan ta bace min da gani, na yi ta duba ta ban kara ganinta ba."
Sai Samha ta dafe kirji ta ce " Ya salam! A bakin wacce rijiya kuma? Da safe ko da daddare?"
Sharifah ta ce " gab da magrib. Daga nan na fara tunanin akwai abinda ake yi wanda ba ta so.
Ina tare da yaranta zuciyata na quna na rasa karamar kanwata, na rasa babban yayana wanda nake ganin shine namijin da zai tsaya min a dukkannin lamurana.
Rayuwa ta tsananta a lokacin ba na so in ga kowa ko in yi magana da kowa. Lokacin mutuwar tana tsaka da cin zuciyata na tana cin zuciyar Hamidah sosai kowa a cikinmu babu kuzari. Yaran Shariqa musamman masu wayon su na cikin alhini su kan shiga daki su kwanta akan kayanta su na kuka. Ina ta faman amsa tambayoyin kananan yaran, su na tambaya ta cewa Muminsu ta na asibiti amma me yasa har yanzu baa kai su sun duba ta ba. Ina iya kokarina wajen kawar musu da hankali. Ina ta shirya karya kala-kala wajen kwantar musu da hankali.
Kowa da irin yanayin da ya fi so ya kasance idan ya shiga damuwa, wani ya fi son ya zauna yayi shiru, wani ya fi son yayi ta barci, wani ya fi son yayi ta kuka, wani kuma ya na son ya shiga cikin mutane, wani baya san ya ga kowa a kusa da shi.
Nawa yanayin na fi son in zauna shiru a daki, bana so in yi magana, ba na so ayi min. Idan na kebe ni kadai a lokacin nake iya yin kuka ba tare da wani ya ganni ba.
A daidai wannan lokacin da bana so in ga kowa in yi magana da kowa shi kuma mijin Shariqah ya kafa zarya a gidana yana kulafucin yaransa. Ya na ciyar da su yadda ya kamata abubuwan da bai basu a baya ba ma a yanzu yana kawowa, komai baja-baja amma bai dame mu ba.
Babu mai iya ci, mai aikina ce da wasu kalilan daga cikin yaran ne ma ke iya ci. Dinar da Hamidah ba komai ne yake burge su ba sai sun zaba.
Dokoki dai na takura barkatai alhali a lokacin bana son a takura min ko kadan abinda yake damuna shi yake damuna. Wannan dalilin ya sa ma na yanke alaqa da dukkannin kawayena ban sanar da su rasuwar ba ma dan bana so a dinga zuwa inda nake. Sauran kawayena wadanda na saba da su daga baya a harkar kasuwanci ko a gari su ma na guje su, babu wanda ya san a ina nake mo me nake ciki.
Abinda zai ba ki mamaki zai daure muku kai shine na baro dukka abinda na mallaka na kasuwanci a hannun abokiyar kasuwancina Fatima kt. Ni ce karfin tsayawa har kasuwancin ya kafu, jarina ne ya fi yawa. Na rantse da Allah matar nan da yake bata tsoron Allah sai ta hada dukka ta cinye. Bayan ta fada min bakaken maganganu ta yi blocking dina a dukka wata kafa da zan same ta.
Na sayi ticket zan je in hado kayana amma matsalar Corona ta ballo kai babu shiga babu fita. Haka aka soke tikitin ban Sami tafiya ba.
Ashe bala'i ya na gaba, dukka wannan wasa ne. Ina zaune ina ci gaba da kula da yara su na zuwa makarantu islamiyya da boko ga kanwata ga mai aiki kowa yana iya kokarinsa.
Ban San yadda ake raino ba dan ban iya shi ba ma, saboda nawa rainon Shariqah ce ta yi min.
Yanzu Allah Ya juya lamuransa ni ce nake yi ma ta rainon. Daman haka aikin alkhairi yake idan ka yi abin alkhairi ko bayan ranka za ka tsince shi a gaba. Ga shi dai yadda ta yi min wahalar raino ba tare da ta yi tunanin zan biyata.
Duk duniya banda yaran Shariqah babu wanda zan iya riqewa haka. Na salwantar da duk abinda nake da shi na yarda in rasa komai, na yarda in takure rayuwata in zauna waje daya dan kawai in kula da yaranta.
Akan maganar auren Adamu da Dinar Allah shine shaidata na kira Dinar na zauna da ita na bata shawara akan ta nutsu ta yi tunani ta gani ko za ta iya yin wannan jahadin ta aure shi dan ta riqe yaran 'yar uwarta.
Amsar da ta bani ita ce ta sa ban sake shiga maganar ba, ta ce dani ta rantse da Allah ko kwana daya ba za ta iya auren mutumin nan ba. Ta zayyano min wasu daga cikin mugayen halayensa wanda ta gani kuma wasu ta ji labarin wasu.
Na ce ma ta amma ai ya ce ya tuba zai gyara halayansa, daga yanzu mace za ta sami 'yanci.
Ta ce min "haba Aunty ko watanni uku baa yi ba fa da na je gidansa aka boye ni dan idan ya gan ni kora ta zai yi. Mutumin da ina matsayin kanwar matarsa uba daya amma bai san ni ba ban san shi ba, tsabar bai dauki danginta da muhimmanci ba."
Na gasgata maganata, maganar kyautawa sam bai kyauta ba, amma yaya zaa yi tunda zuri'a ta hada, yara ba ba daya ba ba biyu ba har guda biyar.
Ni kaina ina neman mafita ne dan ba zan iya zubar da yaran nan in tafi ba, in dai ba na sami takamaimai in da na tabbatar zaa kula da su ba ne. Idan kuwa babu dole in zauna da su, in hakura da komai nawa na rayuwa.
Wannan shine ma abinda zai fiye min kwanciyar hankali tunda 90% na tabbatar bayan uwar da ta haife mu ni da Shariqah babu mai riqe yaran nan kwatankwacin uwarsu irina.
Saboda haka ko da ace aurensa da Dinar ya tabbata ba zan ba ta yaran dukka ba sai dai in ba ta masu dan wayon su biyu zuwa uku kanan sai dai in riqe su. wala in zauna da su a kasar nan ko in tafi da su kasar da nake zama. Wanda na san halinsa ba zai yarda ba sai dai in an kai ruwa rana.
Mu na cikin wannan hali maimakon dangina su shiga maganar a sasanta.A' a sai zuga da ake ta kai masa, gulma kala-kala, sai da aka bata a alqata da shi gaba daya.
Wata rana ya zo ya same ni ya ce yana so akai masa yaran weekend su dukka har yar karamar da bata shiga makaranta ba. Na ce manyan dai su uku banda kananan ya ce su dukka yake so.
Hamidah ta ji hankalinta bai kwanta ba ta ce da ni "Mama kada ki bayar da su dukka kada ya hana su fa."
Na ce haba dai shima ba zai fara ba. Haka kuwa aka yi lahadi ta yi lokacin da ya kamata ya dawo da su yayi wato ranar lahadi da yamma saboda akwai makaranta ranar litinin. Wayarsa na ji ya kira ni ya tambaya ko ina gida? Na ce na fita amma ina hanya, idan yaran zai kawo su Hamidah na gida. Sai ya ce ba yaran ba ne magana ce da shi akan gado in hado musu takardun dukka gidajenta in bashi, yaransa kuma ya kwashe."
Sharifah ta yi shiru saboda radadi da zugin da zuciyarta ke yi, yayin da Samha ta yi shiru ita ma zuciyarta ce ke tafasa, dan takaici da tausayin Sharifah.
[3/3, 9:43 AM] Jamila Umar Tanko: 5
Samha ta ce "Sharifah na san ki a baya ki na da zafi bakya daukar raini. Yaya aka yi har mutumin nan ya sami dama yake taka ki yadda ya ke so?"
Sharifah ta yi murmushi ta jingina a jikin kujera ta rufe ido kamar mai tunani har zuwa wasu 'yan lokuta sannan ta dago ta dubi Samha ta yi dariya.
Ta ce " ba ke kadai ba ma ko 'yar da na haifa Hamidah ta yi min irin wannan tambayar. Samha wato na ga rayuwa, na tabbatar babu wanda ya Isa sai Allah, babu wani mai iko sai Allah. Dan Adam ba komai ba ne. Na qara yin imani, na koyi hakuri, na koyi tawakkali, ina so in gyara mu'amulata da Ubangijina, da kuma sauran jama'a. Me ya yi saura kuma a duniyata? Babu Mama, babu Baba, babu Yayana Bellocity, babu Shariqah. Na dogara ga Allah gaba daya na miqa maSa wuya, ina ganin kamar rayuwar matattu ta fi irin rayuwar da nake yi yanzu dadi. Na karkata gaba daya na fuskanci kabarina, kullum ina jiran isowar layi ya zo kaina.
Samha me kika sani akan mutuwa? Me ki ka sani akan rayuwa? Me kika sani akan halayyar dan Adam? Ana ganin idanuwan iyayenki ba zaki taba gane masoyinki ba sai ranar da aka ce yau babu ran mahaifa za ki ga rashin kara da rashin kunya.
Ko a sanin da kika yi min ada Samha, ba na neman fada ko kadan. Ina takatsantsan dan kada in shiga harkar wani in bata masa amma kuma bana so a shiga harkata a takura min. Idan na takura ne sai in fashe toh idan na fashe ba ta yin kyau.
Ai Adamu bai kai rabin neman rigimar mijina ba amma da ya kaini karshe bai ji da dadi ba. Na kan bawa mutum dama mai yawa kafin in gaji.
Ai yanzu na ke ba ki labarina da mijin Shariqah za ki ji yadda ta kaya. Sai ya tabbatar min ya kwashe yaran ba zai kawo min kuma dan rashin kunya ya kira ni yana yi min maganar gado.
Bayan tun lokacin da aka yi sadakar arba'in ake ta bin kansa ya zo a zauna ya qi. Ashe shi niyyarsa babu rabon gado daman shine zai gada daga shi sai yaransa, idan ya auri Dinar sai ya dauki yaransa, ya karbe gado, sai ya yi gaba shikenan ya gama da shafinmu. Sai ya je ya ci gaba da mulkinka.
Kuma daman dukka kara da bin dokar da nake yi akan kada ya kwashe yaran ne, yanzu kuma me yayi saura tunda ya kwashe?
Na rikice ta inda na shiga ba ta nan nake fita ba, wani yanayi na shiga wanda ni da kaina ba yin kaina ba ne, har sai da Hamida da Dinar suka kwace wayar. Ina ganin bai taba jin maganganun da ya ji a ranar ba.
Daga nan ya tabbatar ko ya sha giyar wake ba zai iya takowa ya zo gidana ba. Sai ya nemo Bello a waya. Sai ga kiran Bello ya na tambayata abinda ya faru sabanin abinda Adamu ya fada masa masa har ya shirya min wani sharri da karya karya kala kala.
Daga nan fa fada ya fara a tsakanina da Adamu. Ya boye yara ba sa gidansa ba sa gidan iyayensa ya kai su ajiya. Ki duba fa ki gani wai yaran da suka rasa uwa yake yiwa wannan wulakancin alhali ga inda aka san darajar ake kaunarsa ya dauke su.
Mu ka yi samame mu ka je gidansa babu yaran, wata 'yar uwata ta nemo lambar mahaifinsa saboda dattijo ne mun yi tunanin bai san rashin arzikin da dansa yake aikatawa ba. Amma sai kalamansa su ka nuna shine ma yake zuga shi akan ya kwato yaran.
Tsohonsa ya yi rantsuwa su babu wanda ya isa ya riqe mu su yaransu, su ne masu alhakin rikewa. Ashe ma dai shine ya dora shi akan wannan karatun na ya sace yaran.
Amsar da na bayar ita ce daga kaina kuwa za ku sauke wannan salon."
Samha ta gyara zama ta ce "ikon Allah wannan wacce irin rayuwa ce? Daman ana yin haka?"
Sharifah ta langwabar da kai ta ce " Wallahi Samha tunda daga ranar da aka kwashe yaran nan Shariqah ba ta sake kwanciya a labarinta ba, kuma ba ta barni na kwanta haqarqarina ba."
Samha ta zazzare ido ta tambaya a gigice "Kamar yaya?"
Sharifah ta sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani, ta ce " duk in da na jefa kafata Shariqah sai ta jefa ta ta qafar. Bi na a baya kawai take take yi. Sai in juyo in tambaye ta Shariqah menene? Sai ta yi shiru ba ta magana. Babu safe, babu rana, babu dare, Sharqah na biye da ni.
Sai daga baya na gane bin nan da take yi min ya na da alaqa da yaranta da aka kwashe ne fa, take so in karbo ma ta. Satin yaran nan uku cur baa san inda suke ba kuma ya qi fada. Haka itama ba ta taba yin fashin barina ba, koda yaushe ina ganinta.
Ta biyo ni daga cikin gida mu ka fito kofar gida na shiga mota na zauna sai ta tsaya a bakin get, na ce ma ta ta zo mu tafi mana, sai ta tsaya ta qi ta shigo cikin motar. Ta san na gane abinda take so ta nusar da ni, wajen yaranta take so in je dan haka ba ta biyo ni ba."
Kan Samha fa ya daure gaba daya, har hayaqi yake yi na rashin fahimta.
Ta sosa goshi cikin in-line ta ce " Sharifah da tsaya pls me kike cewa ne akan Shariqah?"
Sharifah ta yi murmushi ta ce "abinda kika ji ina fada shine dai abinda nake nufi. Ke dai ki biyo ni kawai ki ji karshen labari.
Masana su ka bani shawara akan in kai shi qara wajen hukumar sulhu ta musulumci, su ne masu yin sulhu dan Allah da kuma fadar qur'ani.
Da tambaya har na sami inda ofishinsu yake, na je na shigar da korafi. Nan da nan suka neme shi a waya, dakyar ya zo bayan ya gama kamun kafa da wani da ya sani a wajen. Amma maganar gaskiya kuma maganar cikin qur'ani baa canjawa.
Aka ce ya dawo min da yara ni na fi cancanta na riqe su. Babbar matsalar da ta afku ita ce, a daren zaa fara kulle gari wato lock down, a lokacin Corona ne kuma a ranar zaa tashi da Azumi.
Aka yi ta fama da shi akan ya dawo min da yaran dukka biyar din, saboda ana kan teburin sulhu ne ba kotu ba ce amma ya dage shi bai yarda ya kawo da su dukka ba sai dai ya dawo da kananan guda biyu.
Kasancewar dare yayi zaa rufe gari aka tafi akan hakan amma bayan sati biyu zaa bude gari aka ce mu dawo.
Yara biyu su na wajena, guda uku su na wajensa sai, ya fito da su daga inda ya boye su ya dawo da su gidansa.
Anan ma na sake ganin Shariqah, ta ce min in zo in gani. Ina biye da ita har mu ka isa wani gida mai qofofi guda biyu. Ta bude qofar farko sai na ga haske sosai ga ranta guda biyu wadanda suke wajena kenan, su na ta bacci a cikin ni'ima. Sai ta bude qofa ta biyu sai na ga duhu na hango ragowar yaranta guda ukun da basa wajena, a cikin duhu da damuwa. Daga nan sai ta bace.
Kin ga kenan ta na nuna min ga halin da wadancan suke ciki, kuma ta na so lallai-lallai su ma a dauko su kenan."
Samha ta fada a bayyane " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah wai me kike cewa ne?"
Sharifah ta qura ma ta wasu jajayen idanuwanta da suka cika da kwalla ta ce "wai me kika ji ina fada ne? Abinda nake fada shine kike ji."
Samha ta shafa jikinta don ta tabbatar ko tana raye. Eh tana raye tabbas dan ruhinta da gangar jikinta su na tare kawai dai ta na HIRA DA MATATTU ne.
In har Sharifah mutum ce toh ba za ta dinga ganin matattu a fili haka ba, sai dai idan ita ma ta mutu din ne.
Samha ta sadddakar asan ita kadai matattun nan su ka zaba suke bi suke so a dole sai ta ji labarinsu. Dan haka ya zama wajibi ta sallama ta zauna ta saurare su.
Daga nan kuma ta san karshen zancen zasu tafi da ita ne kawai. Ta