Showing 30001 words to 33000 words out of 35296 words
Chapter 11 - Hira Da Matattu Complete Book By Jamila Umar Tanko.txt
Na ce babu damuwa."
Samha ta yi dariya ta ce " wato da dai ya dauka ke banza ce ya shirya miki wulaqanci. Ni kuwa ina bayin Allah nan su biyu da kika ce Babanku daya, su ne kadai suke tare da ke suke bin bayani?"
Sharifah ta tabe baki ta ce "su ma ashe munafukai ne Samha. Hmmm! Har gara kowa ma da su, ashe har gara wadanda suka fito fili tun farko su ka nuna basa tare da ni. Su biyu uwarsu daya ubansu daya. Sun ga Allah Ya rufa min asiri fiye da su, a jikina suka jingine suke samu. Ba na so in tsawaita fadar abin kirkin da na yi mu su saboda dan Allah na yi zan zube ladana. Amma amfanin da na yi mu su ko Shariqah ba ta more yadda su ka more ni ba.
Dayar da ba ta da aure, kacokan a gidana take zaune, ni ce komai na ta duk da tana aiki amma sai ta boye albashinta nawa kawai take ci.
Kwanannan da baa dade ba, cikin dare Hamidah ta farka sai ta ji su a waya su na gulmata. Wai ashe bakin ciki su ke yi min duk tsawon wannan lokaci, musamman da na tafi turai ina samun kudi. Yanzu kuma murna suke yi na dawo ba ni da kudi ba ni da cikakkiyar lafiya, su na ta shewa fa su na cewa ta kare ma ta ai gashi nan ma bata da lafiya. Alhamdulullah. Sun godewa Allah zasu ga yadda zan yi kuwa. "
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Subhanallah. Uba daya fa kika ce. Shin me zumunci ya zama ne a wannan zamanin? Ashe wannan kiyayyar ta 'yan ubancin da ake fada da gaske ne?" Samha ta fada a gigice.
Sharifah ta yi shiru zuwa wani lokaci ta ce "Addu'a nake ta yi a kwanakin kuwa, duk sanda na yi sujjada inaroqom Allah akan duk wanda baya zaune da ni da zuciya daya Allah Ya tona shi ya kuma cire shi daga cikin rayuwata.
Ke kin ji gulmammaki da su ka dinga fitowa daga gidaje daban-daban? kuma wasu ma dangina ne na wajen uwa nan suke zuwa su na yin gulmar. Ashe ma sun dade su nayi tun mamarmu tana da rai suke yi mana wannan baqin cikin saboda Allah Ya rufa mana asiri. Mamana ta fi uwarsu rufin asiri, duk riqon da mu ke yi mu su shekara da shekaru ashe hassada na karkashin zuciyarsu basa kaunarka ko kadan.
Gulma da kage da sharri ko bare ba zai fadi wani abin ba. Na tabbatar mu su duk na san abinda suka ce kuma na fada mu su dukka abinda aka fada min a gidajen da su ka je suka yi gulmar.
Su ka dinga borin kunya, su na ta zage-zage, su ka amayo da kullutun hassadar da bakin cikin da ya dade yana addabarsu, yana ta cinsu, su ka fada da bkinsu kowa ya gane hassadar da suke yi min.
Na ce kuma ta tashi ta bar min gidana ba zan kara iya zama da su ba dan za su kashe ni. Asiri ma su na yi min, wasu na gane wasu kuma ban gane ba amma ban taba nunawa na san ma su na yi ba. Samha wallahi ina sane na zuba musu ido tunda ita wacce mu ke zaune har malamin da ta je wajensa ta ce ayi min asiri ni da 'yata Hamidah ya zo ya fada min da bakinsa da azal ta ci shi, ya tona asiri ina ga kudinsa ne bata cika masa ba da ta ga aiki bai yi ba. Na ce mu su babu komai amma su ci gaba da taba ni haka asirinsu zai yi ta tonawa dan bani da hakkinsui.
Akwai wadanda mu ke uba da yawansu basu da amfani a rayuwata, har almajirin gidana da me aikina da suke yi min aiki ina biyansu kudi amma wallahi sun fi yi min amfani akan su.
Akwai wadanda na hada jini da su har gara ma bare dan basu taba yi min amfanin komai a rayuwata ba. Har jira ake aji wani bala'i ya same ka, su yi murna.
Na san baka da ikon da za ka zabi wanda za ku fito daga ciki daya ba, da ana neman shawaraka ace ka zabi wadanda zaa hada ku, akwai 'yan uwana da yawa da zance kada a hada mu jini daya.Toh Allah ba Ya neman shawarar kowa Shi Ya san dalilin da Ya hada ku kuma ya ce a yi zumunci.
Zumunci ya zama sai kana da kudi yanzu, idan baka da shi tun daga cikin gidanku za ka fara ganin wulaqanci.
Shiyasa mutane mararsa tunani su ke fadawa neman yaki halal yaki haram. Toh maganar gaskiya ni ba zan fita neman haram dan a mutunta ni ba, gara a yanke zumunci da ni tunda ba na miqewa.
Banda mutuwar zuciya ma ka zauna kullum.kana jiran a nemo a baka, ranar da mai baka bai bayar ba ka zage shi. Wannan wacce irin rayuwa ce haka? To kin ji karshen labarina da yadda Adamu ya yi min, da kuma dangina amma ba komai na yafe musu su dukka. Domin Allah Ya na son masu yafiya, idan ka yafe Shi ma sai Ya yafe maka. Dan mu dukka masu laifi ne, amma kada su dauka zan manta, ba zan taba mantawa da rashin adalcin da dangina suka yi min ba kowa ya koma gefe ya zuba ido a lokacin da nake tsananin bukatar kulawarsu."
Samha ta kama hannun Sharifah ta riqe qam sannan ta sirnano da wani hawaye mai zafi.
Ta ce "kin yi abinda Allah Ya ke so, kin zama mai yafiya kuma Allah Ya na tare da ke."
Sharifah ma ta sharce hawaye ta ce "in sha Allah, ina fatan nima Allah Ya yafe min, wadanda na batawa nima su yafe min dan ba zance ni ba na batawa kowa rai ba. Amma abinda sani baa taba dan uwana a gaba in kyale wallahi sai in da karfina ya kare."
Sharifah ta tashi ta tayar da sallar la'asar, sannan Samha ma ta tashi daman dukkansu da alwallarsu.
Bayan sun idar da sallah sun dade su na addua, sannan su ka shafa.
Samha ta kalli Sharifah ta yi murmushi ta ce "kawata yaushe kika zama malama ne? Na ji ki na ta ragargazo addua."
Sharifah ta yi dariya ta ce "ai ni a ko ina nake ba na daina neman ilimi, acan kasar ma na shiga islamiyya haka anan ma na shiga ta ranar asabar da lahadi. Domin Allah Ya ce ka sanni kafin ka bauta min."
Samha ta ce haka ne, da kyau kawata nima zan shiga islamiyya in sha Allah daman Aliyu yana ta fama da ni na qi mayar da hankali in shiga. idan Allah Ya sauke ni lafiya zan shiga. Ki qi ki bani labarin baqin kare dai."
Sharifah ta kalle ta da gefen ido ta ce " ke wallahi kin cika naci kamar mayya. Subhanallah me kike so ki sani ne? Labarin baqin kare wannan ya faru ne tun mamana tana da rai, Hamidah tana karama.
Na rantse da Allah Samha bani da makiyi ko maqiyiya a zuciyata, da zaa rutsa ni da bindiga ace sai na nuna makiyana wallahi ban san su ba dan ban kullaci kowa ba.
Abinda na sani shine idan ka yi min nima zan yi maka a take, daga nan na manta. Toh amma tun ba na yarda har na fara yarda cewa ina da maqiya na boye a duniya, wadanda ba zan iya cewa gasu ba, kuma ban san dalilnsu na yi min wannan kiyayyar ba.
Kamar yadda na fada miki ina da yawan yin mafarkai, za ki ga wani mafarkin tamkar bidiyo ake haska min ina ganin abinda yake faruwa a boye, ko kuma wanda yana daf da zai faruwa nan gaba.
Sai na kasance mai nacin addu'a tunda na fara ganin wasu alamu a mafarkaina. Ina mafarkan kadangaru daman, da kuma karnuka, su na bi na da gudu zasu cije ni dakyar nake sha a cikin mafarkin basa damuna.
Ko baa fada maka ba idan ka yi mafarki marar kyau za ka ji a jikinka ka tashi zuciyarka babu dadi. Har ya kai na fara tambayar masu ilimin fassarar mafarki aka tabbatar min kare da kandangare da miciji maqiya ne da aljanu. Ban kawo a ka ba kawai ina addu'a in kwanta.
Tun ina ganin baqin kare a makabarta yana biye da ni, har rannan ya cije ni a mafarki kuma sai aka haska min kan karyar da ma ga ribbon kenan an nuna min karara mace ce ta cije ni.
Wasa-wasa sai na kwanta ciwo, na kunbura suntum sai an kwantar sai an tayar. Dukka qasusuwan jikina ciwo su ke, ba dan kadan ba.
Aka dinga yawo da ni gari gari asibitoci don neman magani ana ta gwaje-gwaje amma sakamako ya nuna bani da ciwon komai ko malaria babu.
Likitan da ba bahaushe ba ya ce in je in nemi na gida amma na fi shi lafiya a dukka gwajin da ya yiwa kayan cikina da jinina bana dauke da kowacce irin cuta."
Samha ta yi tagumi ta ce "ikon Allah Sharifah duk kika shiga wannan rayuwar amma ba ki taba fada min ba?"
Sharifah ta ce "in fada miki in ce me? A lokacin mu na tare kuwa sai dai mu kan dade ba mu hadu ba.
Ina kwance a national hospital Abuja mu ka tattara muka dawo Kano aka ci gaba da addu'a kawai. In takaice miki na kwanta cikin dare ciwo yana ta damuna. Radiyo a kunne sai na ji wa'azi malam ya fadi falalar karanta suratul qulhuwallahu ahad kafa dari, Karin ka yi barci. Sai na jawo carbi na karanta kafa dari na shafa sannan na roqi Allah Ya ba ni lafiya Ya yi min maganin ciwon nan.
Sai na yi mafarkin Manzon Allah S.A.W ya bani ruwa na sha na shafa na rage dan kadan, sai na farka.
Wallahi wallahi da na farka babu ciwo, Samha shikenan na warke har yau."
Samha ta yi kabbara ta fashe da kuka ta rungume Sharifah.
Ta ce " baiwar Allah Sharifah wallahi ina zaune da ke amma bana yi miki kallon mai ibada ko mai hakuri, ashe ki na da kyakykywar alaqa tsakaninki da mahaliccinki, shiyasa baa yankewa mutum hukunci kuma baa shiga tsakanin bawa da ubangijinSa"
Sharifah ta yi murmushi ta ce "ba na taba bawa kowa wannan labarin dan mutane zasu dauka karya ma kake. kin kuwa san baa karya da mafarkin Annabi haramun ne. Mamana ce da wata kawata su ka dinga yadawa cewa Sharifah ta ga Manzon Allah a mafarki ya bata magani gashi ta warke. Kin san masoyanta ne sosai Mamana ta son Manzon Allah S.A.W Allah Ya sa ya cece mu baki daya.
Na sha ganin irin wannan rubutun yana yawo a social media ban sani ba nawa mafarkin ne ko bayin Allah da yawa su na yin ciwo su ga Annabi Muhammad S.A.W ya basu magani ban sani ba. Amma tabbas nawa na gani kuma na warke Allah Ya kara mana son Manzon Allah S.A.W.
Amma raina yana hannun Allah duk in da aka kai ga rashin kaunata da son ganin bayana idan Allah bai yarda ba dole su ganni su kyale ni."
Samha ta ce "sosai kuwa haka ne. Fanna ta ce da kika yi ciwo kin mutu sai kuma dawo."
Sharifah ta ce "an gama yi min kukan mutuwa tabbas, dan babu wanda zai ga jikina ya yi zaton zan rayu. Mutane kuka kawai suke yi idan suka ganni.
Idan na kwanta sai in mafarkina in ganni a wata duniya dukka ko ina karnuka ne, ni na kuma duk jikina ya lauye na kasa tashi, wash mata sai su zagaye ni su na dariya. Ban sani ba aljanu ne ko matsafa ne ko kuwa mayu ne oho. Ni dai na dogara da Allah kuma Allah Ya warkar da ni ta hanya mai kyau.
Idan ciwon nan daga Allah ne shikenan na ci jarabawa kuma na godewa Allah ban dorawa kowa ba kuma ba zargi kowa ba. Idan aljanu ne ko mutane su ma su je dan kansu. Yaya zasu yi da ni dan wanda ya halicci ni Ya na son ganina a raye basu da rai basu da mutuwa. Kuma in dai wani ne yayi min wannan dai ba zan taba yafewa ba, sai a lahira za mu tsaya a wajen hisabi."
Samha ta ce "hakan ya nuna kin mutu sannan kika dawo kenan?"
Sharifah ta harare ta ce "daman ana mutuwa a dawo? Ai rai daya ne idan ya tafi ya tafi kenan, in kin ga an mutu an dawo daman suma ne ba mutuwa ba. Toh ni ban suma ba amma an cire rai da ni. Wannan hausar Fanna ce ta yi miki sai ki yi ma ta uzuri tunda ba bahaushiya ba ce da ta ce na mutu na dawo.
Amma ita a nata matsalar ta yi ciwo sai ta yi doguwar suma har an hada ta zaa kaita sai ta farfado. Wannan baya nufin ta mutu ta dawo ko ta yi fatalwa."
Samha ta gyara zama ta na daukar ilimin da ba ta sani ba a baya.
Ta ce "Shariqah doguwar suma ta yi kenan baa sani ba aka binne ta tunda tana dawowa duniya kuma ki yi hira fuska da fuska a bayyane."
Sharifah ta yi shiru kamar mai tunani sau ta dauko wayarta tana daddannawa, ashe Bello ta kira a waya.
Tambayarsa ta yi yana ina? Ya ce yana gida yana jin yunwa. Ta ce ya bari zata taho masa da abinci
Samha fa jiran amsa take amma Sharifah ta qi maganar har ta fara hada kaya za ta tafi.
Samha ta jawo hannunta ta zaunar ta ce " wallahi ba za ki tafi ba, sai kin bani labarin yadda kike yin "HIRA DA MATATTU ".
Sharifah ta kwashe da dariya ta ce " hirata da Shariqah ta qarshe ita ce da ta kira ni a waya na hangota a zaune karkashin kasa, ni kuma ina zaune a cikin dakina anan ina duniya. Na ce Shariqah so mu ke mu ganki."
Ta yi dariya ta ce "idan ku ka ganni ai guduwa za ku yi. Yanzu na zama ba irinku ba." Daga ranar ban sake ganinta ba sai lokacin da na fara ba ki wannan labarin, na ganta ta zo kofar gidana, na kamata na kai ta wani gida mai kyawun gaske da gado a wani daki mai haske. Na ce ta kwanta zan koma in kawo ma ta yaranta, sai ta ce a a kada in kawo ma ta su za ta dawo da kaita ta kwashe su amma ba yanzu ba."
Sharifah ta miqe yayin da ta yafa mayafinta ta dauki jakar ta rataya.