Showing 9001 words to 12000 words out of 35296 words
Chapter 4 - Hira Da Matattu Complete Book By Jamila Umar Tanko.txt
dube ta.
Ta lalubo wayar ta kunna sakonnin Fanna ne ya shigo har guda uku.
Sako na farko ta ce "kin kira kina so ki ji labari kuma kin kashe waya."
Sako na biyu ta ce " ki kunna waya mana."
Sako na uku ta ce "in kina so in baki labarin matattu da fatalwa ki kira ni ki ji."
Ta na karantawa sai ta zabura. Aliyu ya tsaya ya na kallonta.
Can ya tambaya ya ce "kun sami zuwa gidan Sharifah kuwa? Me ya faru? Ko wata fatalwar kika gani ne na ga kin susuce?"
Samha ta zazzare ido ta ce "fatalwa kuma? Ai an wuce wannan babin. Ba mu sami damar zuwa ba. Amma za mu saka wata ranar."
Da ya ci gaba da yi ma ta kallon tuhuma sai ta yi gaggawar barin falon don kada ya gane ta.
*** *** ***
Bayan kwana biyu da rana misalin karfe biyu, Aliyu yayi tafiya, Samha na zaune ita kadai a falo ta na kallon talabijin. Sallama ta ji a bakin qofar falonta ba tare da ta ji an taba get ba, duk da ma dai get din a bude yake amma tana jin karar sa idan an taba.
Muryar da ta ji ta daga ma ta hankali, ta yi kama da muryar Sharifah ko Shariqah ko Hamidah. Sai ta zabura ta miqe ta koma bayan kujerar lungu ta tsaya, ba tare da ta iya amsawa ba.
Ta ga an bude labule an shigo sai ga Sharifah ta bayyana muraran, hannayenta dauke da manyan fulasanta na abincin da suka kai ma ta.
Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu sannan Samha ta tuna ashe bakuwarta ce, kuma sannu da zuwa da murmushi ake yiwa baqo.
Samha ta washe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "yau Sharifah a gidana? Sannu da zuwa, ki zauna."
Sharifah ta yi murmushi sannan ta sami kujera ta zauna. Yayin Samha ta shiga kicin hannunta na rawa ta dauko lemo da ruwa ta kawo ma ta. Sannan ta sami kujera daga nesa-nesa ta zauna. Kirjinta na faman dukan uku-uku.
Bayan sun gaisa Sharifah ta ce "daga makabarta nake wallahi, na ce dai bari in biyo in ajiye miki fulasan nan in yi miki godiya."
Samha ta dafe kirji ta maimaita "makabarta kuma? Me ake yi a makabarta? Waye ya rasu?"
Sharifa ta shafa kai ta ce " na je ziyara ne. Na jewa Shariqata visiting. Kin san ana je musu visiting da guzurin addu'a ko?"
Samha ta gyada kai cikin matsanancin tsoro ta ce "eh haka ne. Ina zuwa."
Ta shiga daki ta dauko takarda da biro ta rubuta wasiyya.
Ta ce "idan kun tsinci gawata ko an rasa ni na bace toh Sharifah ce, ta zo gidana ga mu mu na tare daga ni sai ita a gida."
Kamar daga sama ta ji Sharifah ta kwalla ma ta kira, sai ta fito a gigice.
Sharifah ta kalle ta ta yi dariya, ta ce "canza min tasha ina so in kalli wani horror fim a MBC 2, zasu maimaita yau. Jiya na fara kallo na yi bacci. Fim din Matattu ne, su na fitowa daga kabarurrukansu. Daga sun ciji masu rai sai su ma su zama su."
Samha ta ji gabanta ya fadi da alama yau ta zo ta cije ta itama ta zama su. Hannunta na rawa ta dauko remote ta miqawa Sharifah yayin da ta yi wuqi-wuqi da ido, ta yi baya-baya ta zauna daga nesa da ita.
Ana gama fim din da ake yi yanzu zaa fara wancan fim din na matattun da take so.
Sharifah ta na ta yi ma ta hirar yadda abincin yayi dadi, sun sha santi.
Har aka gangaro hirar su ta rannan akan rayuwarta. Samha ta fara sakin jiki akan babu yadda za ta yi dole ne ma ta sake.
Samha ce ke tambayarta akan a ci gaba da labarin rannan amma da alama ma yau Sharifah ba ta son hirar.
Samha ta ce "Su Nana sun ganki a wajen yayanta Barista kin je rannan sai suka ji tsoron yi miki magana saboda sun fi son su zo har gida su baki hakuri. Sun yi miki laifi ba dadi su baki hakuri akan hanya."
Sharifah ta galla ma ta harara har sai da gaban Samha ya fadi. Sharifah ba ta bata amsa ba, ta ci gaba da kallon talabijin.
Sai can ta ce "ai kun zo har gida kuma ku ka sake guduwa."
Samha ta sunkuyar da kai ta kasa bada amsa.
Sharifah ta kwashe da dariya har sai da Samha ta tsorata sannan ta ce " ku na bani mamaki, amma ba abin mamaki ba ne dan har yanzu ba ku san mutuwa ba ne ba ne, ba ku taba rasa wani makusancinku ba shiyasa har ku ke tsoron mutuwa da matattu."
Samha ta gyada kai ta ce "har da wannan ma."
Sharifah ta gyara zama ta ci gaba da cewa " Na tsaya a inda na ce a lokacin ina zama a kudu ni da mijina. A dalilin rashin lafiyar Shariqah na ji gara kawai in dawo kano in zauna a kusa da ita. Na kauro Kano na kama haya a kusa da unguwar da gidan Shariqah yake bai wuce naira hamsin a adaidaita sahu ba, na samowa Hamidah makaranta ta ci gaba."
Samha ta ce maigidanki fa?"
Sharifah ta tabe baki ta ce "a can na bar shi yana zuwa ina zuwa daman zamana da shi babu dadi na fi sha'awar mu rabu saboda daga ni har 'yarsa ba ma jin dadin zama da shi. Baya tsinana mana komai da albashinsa. Komai ni nake yi a gidan.Ya qi yin saki kuma baya kyautata min. So yake mu yi aure irin na 'yan duniya mu daki juna, mu zagi juna sannan mu fito titi mu tarawa kanmu mutane sai kuma mu koma gida mu bawa juna hakuri mu ci gaba da zama.
Da na fahimci haka yake sai na ja masa layi ba na kula shi sam, abinda na sani shine aure bautar Allah ne aljannar mace tana karkashin tafin kafar mijinta, idan haka ne ba zan taba samun aljanna ba a irin wannan rayuwar ta mu ba."
Samha ta gyada kai ta ce "wannan gaskiya ne, kin yi daidai."
Sharifah ta ce "Dan haka na dinga baya-baya da shi dan kada ya illata mu. Na matso kusa da 'yar uwata dan na kula da ita kuma na taimaka ma ta sosai da kudina da kuma jikina da shawarata.
Kwatsam wata dama ta samu ni da shi daman mun nemi tafiya turai Allah bai yi ba sai daga baya damar ta samu mu ka yi shawara mu kaura kawai.
Na bar Hamidah a gidan da na kama haya na dauko wasu daga cikin dangina suka zauna da ita. Ina so ta gama sakandire sai in zo in tafi da ita kawai.
Mu na can har mu ka shekara daman kamar yadda na fada miki a baya zamana da mijina a cakude a waje daya matsala ne, kullum fada.
Abin ya zamanto har da cin amana kuma na gano shi ya fara son wata kawata acan, na gane abinda ke faruwa kawai na sallame shi mu ka rabu, na kama gaba na ya kama na sa gaban.
Daga baya ma ya kasa zama ya dawo Nigeria ya ci gaba da lalacinsa. Ni ce daman me zafin neman na ci gaba da gina sana'a ta a can ni da wata kawata mai suna Fatima kt mu na zaune tare. Ina samun abin rufin asiri ina turowa gida ina taimakon 'yata da 'yan uwana musamman Shariqah.
*** *** ****
A satin da Shariqah za ta rasu na sami mai zuwa nan Turai na ce ta aiko min da gyararren wake da gyadar kunu. Kasancewar na san ba ta da kudi sai na turo ma ta da kudi na kashewarta da kuma wanda za ta sayi komai. Aka ce ita ta gyara min da hannunta, dan tayi-tayi da mai aikin ta yi ta qi mayar da hankali, dan haka sai ta yi da kanta.
Ta rame sosai kasancewar ciwon ya na ta cinta. Na yi ta fama da ita akan ta turo min hotonta in gani amma ta qi, ashe ba ta so in ga yadda ta zama ne ta san hankalina zai tashi. A waya dai ga muryarta nan tangararai ashe jikin ba dadi.
Koda yaushe muna hira a whatapp da sabuwar wayar da na turo ma ta, ta sare gaba daya ta ji a jikinta zata rasu.
Muna hira na ce ma ta kwana biyu sai in ji zuciyata babu dadi, gabana ya na ta faduwa. Budar bakinta sai ta ce "ko ni ce zan mutu?"
Na rasa amsar ma da zan ba ta yayin da hankalina ya sake tashi.
Ana cikin wannan hali kwatsam Hamidah ta kira ni tana kuka ta ce min " Mama sai in ji na kasa bacci kirjina yana ta bugawa, zuciyata na tsinkewa."
Nan ma na ji hankalina ya tashi matuka, na cewa Hamidah ta yawaita yin addu'a sosai da yawan alwalla da sadaka.
Shariqah ta bani labari a waya ta ce ta kasance tana yawan yin barci mai nauyin gaske a koda yaushe, ba dare ba rana ba safe. Baccin da kowacce irin hayaniya ake yi ba ta ji, sannan kuma ayi ta tashinta ana girgiza ta dakyar take tashi.
Ta tabbatar min wata duniya take tafiya, tana ganinta tana biye da wani mutum. Mutumin ya na hawa saman duwatsu, tana biye da shi. Sai ta waiwayo ta dubi bayanta sai ta ga 'ya'yanta guda biyar din nan dukka a warwatse wancan a wani lungu wancan a yashe a wani waje daban, sai ta zo ta na ta kokarin harhada su a waje daya amma sun ki haduwa. Sai ta hada wadannan sai ta sake hango wancan a can wani a wani waje, in ta dauko shi sai ta ga wancan a wani lungun. Tayi-tayi ta hada su a awaje daya ta kasa.
Da ta fada min sai na yi shiru dan akwai tashin hankali babba a cikin labarin mafarkinta.
Nima ina can ina yin nawa mafarkan, na ga daki guda ya kama da wuta, sai na fito a gigice da yara guda biyu a hannuna.
Da na fada ma ta sai ta ce "ko dai mutuwa zan yi"
Ban san ciwon ta ya kai haka ba, har nake ta kokarin ba ta kwarin guiwa, na ce ta fara yin business zan turo ma ta da kayan yara da takalma ta fara siyarwa. Ta amince nan da nan take ta murna.
Akwai wani gidana karami da na taba siyar ma ta, ba ta fada min kai tsaye cewa mijinta ya qi kai ta asibiti ba amma ta ce min in karbi gidana in mayar ma ta da kudinta har ma ta yi mun ragin 500k hakan ya nuna a matse take da kudin.
Ashe lafiyarta ta ke so ta tafi ta nemo. Na Amince har na tura ma ta wasu daga cikin kudin na fara biya.
Hamidah ta dauke ta a hoto ba tare da ta sani ba ta turo min "innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Ashe babu Shariqah, a kashi goma saura kashi uku, Shariqah ta kare ta rame sai kashi ga gayo tana yi. Karfin hali kawai take yi da take iya magana, ba ta daina aikin girki da yiwa miji wanki ba.
Bayan kwanaki biyu Hamidah ta kira ni a gigice ta ce ga Muminta Shariqah babu lafiya, ta zo gidan ta same ta a yashe a kasa a falo, mijin ya fita bayan yaran sun je da gudu sun fada ma sa ba ta da lafiya, ya zo ya kai ta a asibiti. Ya ce baa fada masa da wuri ba, shi yanzu fita zai yi. Ko leqawa bai yi ya ga yanayin jikin ba.
Bayan Hamidah ta wuni a makaranta ta je gidan sannan ta iske ta a cikin wannan hali. Daga ita sai yara kanana da mai aiki.
Na cewa Hamidah ta samo adaidaita ta kai ta asibiti, yariyar nan karama ita ta saka ta a cikin adaidaita sahu su ka tafi.
Kowanne asibiti baa karbe ta ba saboda babu gado kuma ba su da na'urar oxygen din da zaa saka ma ta saboda numfashi ya dawo sama-sama.
Hamidah ta kira su Bello da sauran dangi aka hadu da su aka dinga fama. Mijin nan bai dauki waya ba har dare, babu irin kiran da baa yi ma sa ba ya qi dagawa.
Karshe dai suka kai ta wani asibitin kudi, tunda babu gado ana gwamnati kasancewar a lokacin ana wani irin anobar zazzabi. Aka ce sai can da daddare mijin ya zo ya na ta yi ma ta tsawa.
Wasu daga cikin dangi su ka hau kansa da fada sannan ya sassauta. Da kyar lokitoci su ka ceto rayuwarta, ta samu ta warware kadan, har muka yi magana a waya da ita.Bayan kwana biyu tana asibitin jiki ya sake rikicewa, na kira su a waya yadda na ji kowa a rikice na san Shariqah kuma babu.
Na yi addu'a, na yiwa Allah SWA bakance, na yi sadaka, na saka dukkannin Malamai bayin Allah da na sani su sauke ma ta qur'ani akan Allah Ya jinkirta ma ta, Ya tashi kafadunta. Na yi tawasali da dukka kyawawan ayyukana da kaunar da nake yi wa Annabinmu dan gatan Allah Muhammadu Rasullulah (S.A.W)."
Sharifah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa yayin da hawaye ke zuba kamar an kunna famfo.
Samha ma sharce hawaye take tayi ta yi dan yaqi tsagaitawa. Ta miqawa Sharifah tissue ba tare da ta iya magana ba. Sharifa ta karba ta goge ta face hanci, ta dago ta dubi Samha da jajayen idanuwanta
Ta ce "Allah sarki Samha na zo na ba ta miki mood dinki, na tayar miki da hankali, na saka ki kuka."
Samha ta ce "in ban tsaya na saurari labarinki ba ba zan taba yafewa kaina ba."
Sharifah ta gyada kai ta ce "Na gode da kulawa sosai."
Samha ta ce "ci gaba da labarin ina sauraro."
Sharifah ta cije baki ta ci gaba da cewa " Wane mutum, babu gudu babu ja da baya idan lokaci ya yi, ko sakon daya Allah ba zai qara ma ka ba.
Duk duniya babu mai iya hanawa, me afkuwa ta afku. Ba zan taba manta da yadda na ji baqin labarin nan ba. Shin mafarki nake yi zan farka ko da gaske ne? Haka nake shafa jikina dan in tabbatar.
" Innalilahi wa inna ilaihi òrajuun." kawai na ke ambato. Kamar in yi fuffuke in diro Nigeria haka na ji.
An sanar min ga Hamidah ta suma ga Bello ya dimauce. Babu abinda zan iya yi, nima ta kaina nake yi, ni kadai a kasar da ba tawa ba, sai ni sai kawaye da abokan arziki ne ke kewaye da ni su na bani hakuri.
Na kasa kuka ma sai kirana ake ta yi a waya, daga ko ina a fadin Nigeria saboda ni na fi cancanta a yiwa jaje akan rasuwar Shariqah.
Ban qi in kwashe dukkannin kudina da na mallaka a duniya dan in sayi sabon tikiti ba, in har zan samu tafiya a ranar.Mutumin kirki wani Alh. Musa ya yi min dukkan kokarin da zai yi, na hau kan return ticket dina ba tare da an kashe wasu kudi da yawa ba.
Ta rasu cikin dare ta yi kwanan kaso da safe aka yi ma ta Jana'iza, ana sanar min da komai a waya. An fadi irin taron jama'a da suka sami halattar jama'izarta, ana yi ma ta kyakykywan zaton samun rahamar Ubangiji. Bayan ta cika da kalmar shahada kowa ya budi baki kyawawan halayanta ake ambato, fara'a, da kyauta,