Showing 24001 words to 27000 words out of 35296 words

Chapter 9 - Hira Da Matattu Complete Book By Jamila Umar Tanko.txt

Samha kin san ni nima na sanki, bin malamai da bokaye ba aikinmu ba ne. Ko da an takura ni na yarda na je to sau daya zan je kuma ba zan koma ba, sai in ga kamar na zubar da gaba daya imanina ne sai na yi sabuwar kalmar shahada.
Abu daya na riqe shine in tashi cikin dare in roqi Ubangijin da Ya busa min numfashi, Ya raya ni, wanda raina ke hannuns
Sa kuma idan na mutu gare Shi zan koma. Shi yake da wuta kuma yake da aljanna.
Tunda kuwa na yi imani da haka na watsar da neman taimakon kowa, na daina bacci cikin dare, na dingi tashin dare ina rokonSa, Shine sarkin sardauna.
Nayi imani da Shi, abu na farko sai na daina fargaba, na daina tsoron kowa. Duk wanda ya dogara ga Allah Shi kadai baya tsoron faduwa sai dai nasara a komai. Haka baya neman taimako daga wajen kowa sai Allah dan haka ya wuce wulaqanci. Baya gudun ko wani zai iya cutar da shi. Zai ji kamar duk duniya ya na daidai da kowa ko da kuwa bashi da ko Sisi ko wani mai karfi. Zai ji a ransa zai iya tunkarar kowanne irin bala'i da ake binsa da shi. Zai ji zuciyar ta washe babu haushin kowa. Baya tsoron talauci ko ya ce wani zai juya masa baya ya hana shi wani abu. Baya tantama ko kokonto akan abinda ya saka a gaba.
Kawata na ga aya, na ga mu'ujuza da isa irin ta Ubangiji. Da na matso kusa da mahalaccina Allah da Shi nake magana cikin dare ke kya ce ina ganinSa a gabana tabbas Shi Yana kallona idaniyata bata ganinsa amma ruhins da zuciyata su na tare da shi 100%.
Bayan na yi sallar nafilfili ina yi masa kirari da kyawawan sunayensu tsarkaka guda casa'in da tara, sai in yi tawasali da kyawawan aiyukan da na aikata daga ni sai shi, bayan na tuba kuma na yiwa masoyi salati SAW sai in yi magana da Ubangiji ke kya ce ina ganinSa, tabbas shi Ya na ganina amma zuciyata tana hasko shi. Buwayi gagara misali.
Na ce "Ya ubangijin kai ka halicce ni, bani da kowa bani da komai sai kai kuma da kai kadai na dogara, kai ne ka ce mu roqe Ka, za ka amsa mana. Allah ka tsaya min da kanKa kada Ka bar ni da iyawata daidai da kiftawar ido dan ba zan iya ba."
Samha ta ce : Allahu akbar! kawata na ji har tsikar jikina tana tashi. Tabbas ba kowa ya gane wannan sirrin ba. Dogara ga Allah Shi kadai babbar nasara ce."
Sharifah ta ci gaba da cewa "Allah Ya nuna mu su Shine Allah kuma baYa mantawa da bawanSa a lokacin da bawa Ya tuna da mahalaccinSa, na rantse da Allah Samha mai Shari'ar farkon nan kacokan aka dauke shi daga alkalanci ba zai sake alqalanci ba ma a duniya.
Shi kuma dayar kotun da ya ce zai kwace yara shine kika ganni a high court a sanadiyyarsa ne, yakardar da na cike ta kai can sama. Sannan ni da sabon lauyana mu ka fara shirye-shiryen daukaka kara.
Nan fa ma su duba sharia suka dinga zaryar zuwa group-group kowa ya zo sai ya ce a bashi kwafin shari'ar Sharifah da Adamu ya gani.
Daga nan ya tabbatar na maka karansa a can sama ne. Nan da nan aka dakatar da ni da lauyana daga ci gaba da yin Appeal, sai aka hada mu da wata kwanciyar lauya mai kare hakkin mata da kananan yara mai suna Bar.Aisatu.
Ya ce ta shiga tsakiyarmu ta yi mana sulhu akan yaran, an fasa kwace su daga hannuna.
Adamu ya sha takaici ya dinga bacin rai, sai da aka fi shekara baa gama sulhu ba. Dan an yi zama da yawa basa zuwa kuma ya daina ciyar da yaran ko kadan. Sai da ya shekara bai ga yaran da idanuwansa ba, ya daina nemansu.
A wannan shekarar ni ce cinsu, ni ce shansu, suturarsu, ni ce school fees dinsu islamiyya da boko. Ni ma na rabu da shi ban neme shi akan taimakon komai ba. Ko Bello ba ya taimaka min da ko sisi haka a dangina babu wanda ya taba dauko kwayar taliya daya ya bani ya ce in ciyar da su.
Amma fa ina zuwa gidajensu in ganin irin kayan alatu da Adamu yake kai musu kyaututtuka amma yaransa ya qi ciyar da su. Manufar ita ce idan na ji wuya zan mayar masa su da kaina.
Amma ina? Ya manta ko su waye Sharifah da Shariqah ne? Ai yadda ba zan iya daukar Hamidah in 'yar da ita ba, ba zan taba iya daukar yaran Shariqah in zubar ba. Idan bara nake za mu yi tare mu ci abinci.Idan a titi nake kwana zamu kwana tare da su.
A wannan lokacin rigimar nan hankalin Shariqah a tashe yake, kusan kullum sai ta zo min.
Ina yawan ganinta wataran ta yi magana wataran ba ta yi amma tabbas ranta a bace yake, shari'ar nan da ake yi akan yaranta na damunta."
Samha ta maimaita " ranta a bace yake kuma? Shariqah da kika ce."
Sharifah ta yi murmushin qarfin hali ta ce "kwarai kuwa, ba za ki gane abinda nake nufi ba ne, sai nan gaba. Hmmm Samha! Sai a wannan karon ne na tabbatar Sharifah ba ta da dangi, daga sama ta fado saboda babu mutum daya daga cikin dangin uwata da na ubana da ya dauko kwayar taliya daya ko shinkafa kwano daya ya ce ki dafawa yara.
Ba na so in zobe ladana amma na yiwa dangina bauta, da jikina da dukiyata. Amma sai su ka yi kamar ma basu taba sanin mu na shari'a ba saboda ya toshe bakinsu da abin duniya. Ko mun hadu babu wanda zai yi min maganar case dina da Adamu kuma ana hango shi a gidajensu ana zuwa ana fada min da duk abinda ya kai musu.
Wai mutumin da bai wadata gidansa ba shine yake bin dangina ya dinke bakunansu da abin duniya, yana ta rabo kai kace dan takarar gwamna ne.
Sun bani mamaki wannan abu ba zan taba mantawa da shi ba, shine na sake gasgatawa ka saki mutum ka kama Allah Shi kadai kawai saboda mutum mugun ice ne."
Samha ta yi tagumi ta ce "kaina fa ya daure, innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Da ma kin tabo ni kawata sai ki ga bare ya taimake ka jininka bai taimake ba."
Sharifah ta gyada kai ta ce "daman na dade da sanin haka, yawanci duk abinda na zama a rayuwa ta hanyar bare ne ba dai dangina ba.
Amma na girgiza matuqa kawata, sai da aka zo babbar sallah lokacin da kowa yake yanka rago, wasu shanu wasu rakuma. Har ana gobe sallah ga ni da yara basu da aiki sai loqawa makwabta su na ganin raguna, su na dawowa da gudu su na bani labari. Mu a gidan babu ko kazar da zamu yanka kuma bani da kudi.
A daidai wannan lokaci kuma mahaifinsu yana can yana raba raguna kuma ma rabon a gidajen dangina yake rabawa, kowa yayi kulas babu wanda ya fada min ko ya labari, balle ma su tare shi su ce ya kamata a a kaiwa Sharifah da yaranka."
Sharifah ta yi shiru ta sunkuyar da kai kasa dan radadin da zuciyarta ke yi.
Samha ta girgiza kai ta ce "an ci amanar zumunci. Wani irin zamani ya zo wai dan uwanka, jininka ne yake so ya ga ka tozarta. Yaya kika yi kuma?"
Sharifah ta dago ta kalli Samha ta yi murmushi ta ce "kin manta ina da Allah? Wanda Ya rike Allah babu shi babu cewa na shiga uku. Na yi addua cikin dare na roqi Allah Ya rufa min asiri kuma Ya bani yadda zan yi Alfarmar yaran nan ya fitar da ni kunya.
Na rantse da wanda Ya zabi Annabi Muhammad S.A.W Ya fifita darajarsa fiye da ta dukkannin halitta. Alert din dubu dari na tashi na gani, na wani tsohon bashin tikitin da na ce miki na biya zan koma turai in dauko kayana aka rufe ko ina saboda Corona.
Kudin ya fi dubu dari uku na tambaya har na gaji dan shima an so a cinye min Allah Ya kwatar min wannan, ba dan komai ba sai dan Ya yi alqawari idan mu ka roqe Shi zai amsa mana."
Samha ta yi kabbara ta riqe hannun Sharifah ta jijjiga ta ce "na baki kambun jarumta, haka na baki kambun wacce ta yi jahadi saboda zumunci. Allahu akbar duk kin shiga wannan tsanani ba dan jin dadin kanki, ba dan na 'yarki ba sai dan 'yaya 'yar uwarki saboda zumunci. Ba za ki wulaqanta ba in sha Allah. Nasara na tare da ke kawata."
Sharifah ta gyada kai ta ce "na tashi da asuba na ga wannan kudi sai na yiwa Allah sujjada na yi maSa godiya banda Shi babu wanda Zai yi min haka.
Bayan mun je sallar idi mun dawo gida, akwai wani bawan Allah da muke mutunci da shi tun Mamana ta na raye muka saba da shi, a Makka yake zama da.
Shine ya zo da mota ya dauke mu ni da Hamidah mu ka tafi can hanyar Wudil kasuwannin kauye, lokacin raguna sun karya cikon kudi kadan na yi akan dubu farin nan na sami raguna guda biyu manya-manya.
Mu ka zo muka yanka yara su na ta murna, mu ka yi layya kamar kowanne gida. Abinda ya bani mamaki har aka yi sallah aka gama bubu wanda daga cikin dangina ya aiko min da tsokar nama ko kwaya daya tal. Ashe da ban yi layya ba babu me bani nama. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun."
Samha ta ce "ikon Allah. Amma na cika da mamaki. Tabbas ke din Jaruma ce dan ba kowacce mace ba ce zata iya daukar abinda kika dauka. Ke a maza ma ba kowanne namiji ba ne zai iya irin wannan tawakkalin ba. Kin rasa kowa daga cikin makusantanki, sannan kowa ya juya miki baya. Yaya sharia ta kasance?
Sharifah ta yi dariya ta ce "sharia ta farko wato ta rabon gado an cire me sharia an kawo wani wannan shariar ai an ja ma ta layi sai ya bibiyi abinda aka yi a baya. Fiye da wata shida bai waiwaye mu ba ma.
Ta biyu kuma da ya kai ni dan a kwace yara, ita wannan shari'a ai babu ita tunda an mayar da ita teburin sulhu, tare da wannan matar barista Aisata da na baki labari a baya, da aka ce ta yi mana sulhu.
Mu na zuwa ni da lauyana shima da lauyansa amma fa sai mu yi zuwa uku su sai su ki zuwa dan ba haka suke so ba, su so suke a kwace yara a basu wanda ba zai yiwu ba kuma."
Samha ta ce " sannu kawata shari'a har guda biyu, ya maka ki a kotuna daban-daban."
Sharifah ta tabe baki ta ce "na fada miki waccan kotun da ya dauko gidana ya hada da na su ya ce dukka nata ne kuma an goyi da bayansa, har an saka ranar da zaa zartar da hukunci. Allah Ya yi ikonSa, kacokan aka dauke mai shariar aka kawo wani.
Dan haka nasarorin da Adamu ya hango ya fara samu kacokan sun juye, kai a kasa kafafuwa a sama. Haka duk abinda ya kashe ya yi asararsu.Dangina da suka ci kudinsa babu abinda zasu iya taimakonsa da shi. Ko sun sha giyar wake dai babu wanda ya isa ya zo gabana ya zage ni balle ya fada min bakar magana akan riqon da nake yiwa 'yayan Shariqah.
Tunda dai su sun manta duk wahalar da ya bawa 'yar uwarsu, a haka kuma su ke bude baki su ce su na kaunarta.
Na yi addu'a Allah Ya tsare ni daga dariyar makiya da mahassada. Allah Ya rufa min asiri kada in tozarta kuma har yanzu a haka nake, babu tozarci kullum asirina a rufe yake.
Hamidah da na haifa har ta gane tabbas Allah Ya na tare da ni a koda yaushe. Tun tana damuwa har ta daina idan na tashi bani da kudi sai ta shiga damuwa ta tafi makaranta jikinta a sanyaye amma wallahi tana dawowa sai ta bude wayata ta duba ko tantama babu zata ga kudi an turo min.
Yanzu har abin ya zamar ma ta jiki, idan na ce bani da kudi sai kawai ta yi dariya ta ce "Mama ke 'yar baiwa ce, Allah ba ya hana ki."
Samha akwai wani bashi da ya rikito min kudi ne mai yawa, cikin dare na tashi na yi sallah, na yi doguwar sujjada ina addu'a. Kawai ina idarwa sai na jawo wayata na duba. Wallahi Samha alert din dubu dari biyar na gani. Kafin ma in duba in ga daga ina kudin ya zo sai kawai na turawa wacce take bi na bashin kudi, sannan ma na bincika daga ina alert din ya zo."
Su duka su ka yi kabbara a lokaci guda.
Samha ta ce "dan Allah Sharifah ki bani sirrin addu'oin nan . Da gaske kike? Waye ya turo miki kudin?"
Sharifah ta yi dariya ta ce "daman wasa ne ya tara mu anan? Wallahi daga CBN, kudin nan da ake rabawa na tallafin corona."
Samha ta ce " kin bani satar amsa in sha Allah zan tattara lamurana waje daya in miqawa Ubangijina Allah. Wato ma mutum ya daina neman shawara ko fadawa wani matsalarka, dukka bata lokaci ne da tonar asiri.Gara kawai ka kalli gabas ka fadawa Allah."
Sharifah ta ce "sosai Samha. Ga rashin lafiya dan a lokacin idan kin ganni ba za ki gane ni ba, kawai kuraje suka dinga feso min, idanuwana ciwo, wani lokaci har bana gani sosai. Idan ina tafiya sai in fara haki, har ana so a dora min ciwon zuciya. Sanda kika ganni ma me ai na ji sauki akan da.
Addu'a kawai na tsaya ina ta yi, abinda na cewa Rabbil samawati shine Ya Allah zuciyata ba zata kamu da ciwo ba saboda a cike take da tsoronka da son matsayinka Annabi Muhammad S.A.W. dan haka zuciyata babu ciwo. Ya Allah kada ka kaddara zuciyar da ta cika da son Annabi ta kamu da ciwo.
Ina zuwa gwaji zuciya babu ciwo Samha, alhali ada komai na alamun ciwon zuciya ya tabbata. Kai duk wanda ya ce babu Allah bai yarda da Allah ba, tabbas ya na cikin asara babba."
Samha ta yi kabbara ta ce " gaskiya kin kama babbar madafa. Ina tare da ke 'yar uwa."
[3/6, 5:15 PM] Jamila Umar Tanko: 7
Lokacin sallar azhar ta yi dan haka su ka katse labari, Sharifah ta shiga bandaki don dauro alwallah.
Samira ce ta shigo a gigice har sai da Samha ta ji tsoro.
Samira na ganin Samha sai ta yi ajiyar zuciya ta dafe kirji, har da wata kwallar farin ciki ce ta sirnano.
Samha ta tambaya a gigice "lafiya? ina su Mama?"
Samira ta ce " ba maganar Mama ba ne, ita yanzu ma mun yi waya sun isa lafiya. Kawayenki ne su Aunty Nana suka zo gidanki nemanki, na fada mu su ki na asibiti. Daidai lokacin na gama sakwara sai na basu su taho miki da ita dan an kira ni a BUK ance mu kai wani wani assignment da aka bamu.
To ina can makaranta tare da kawayena mu na yi sai su ka hana ni sakat su na ta kira na a waya wai in kira Yaya Aliyu da 'yan uwa a je asibiti, sun baro ki kina cikin wani hali kina neman taimako. f
Fatalwa ta saka ki a gaba bakya iya magana bakya iya daukar waya, kuma ba lallai ba ne ma likitocin su ganta ke kadai kike ganinta."
Samha ta jawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login