Showing 21001 words to 24000 words out of 35296 words

Chapter 8 - Hira Da Matattu Complete Book By Jamila Umar Tanko.txt

shigo, haka da daddare idan ya taso sai ya biyo ya duba ta kuma ya biya asibiti maqudan kudade. Ana dai cin kudi bana wasa ba amma dai ana ganin kulawa.
Abin mamaki da rana misali qarfe goma sha biyu, Aliyu ya dade da tafiya, samira ta tafi gidan Samha dan ta dafa abinci, yayin da Mama kuma sun tafi yobe ita da Ana's gaisuwar mutuwa. Daman su ne kadai suka san tana asibiti,su kadai ne suke zuwa duba ta.
Sai ta ji an yi sallama an murda qofa an shigo.Ta dauka ma'aikatan jinya ne wato (Nurses) amma ko su ne ai yanzun nan su ka fita. Me su ka manta, su ka dawo kuma?
Wannan tunani na ta ba daidai ba ne wata mata ce ta shigo sanye da atamfa ruwan hoda da gyale shima ruwan hoda (pink color), ta na daga kai su ka hada ido da Sharifah.
Yadda ka san bom ya fashe haka karar bugun zuciyar Samha ta kasance. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ta fada a bayane. Yayin da Sharifa ta taya ta suka karasa tare.
Dan neman magana sai ta qi zama a kan kujerun da suke dakin ta zata zauna a gefen gadon kusa da Samha.
Samha ta koma ta kwanta yayin da take numfashi sama-sama.Sharifah ta dauka duk a cikin ciwo ne, sai ta zabura ta riqe ta tana yi ma ta sannu.
Ta dora da cewa "haba Samha kada ki dinga jefa kanki a cikin damuwa mana, alhali kina dauke da ciki na 'yan biyu ba ma guda daya ba."
Samha ta sake gigicewa, ko ita kanta sai a daren jiya aka fada ma ta cewa tagwaye ne a cikinta. Ta ina Sharifah ta sani? Ita fa ba ciwo ba ne matsalarta, daman Sharifah ce matsalar. Ga matsalar da kanta ta zo har da karin wata babbar matsalar ma, ta kawo ma ta.
Samha ta sirnano da hawaye ta na magana cikin sanyin murya ta ce "Sharifah! Ya kamata ki fada min gaskiya, maimakon ki bar ni ina ta wahala. Shin menene labarin karen da ya cije ki har ya zama shine ajalinki kika mutu kika dawo? Yaya ake kike sanin boyayyen al'amari? In har ke mutum ce ba za ki iya sanin ina nan ba. Waye ya sanar miki yara biyu ne a cikin cikina? Sharifah idan na mutu wallahi ke ce sila ba zan boye miki ba, ki na bani tsoro na kasa yarda da ke. Duk sanda na cirewa raina zargi akan ki sai ki aikata wani abu da kwakwalwata zata kasa dauka. Shin kin shiga wata kungiyar matsafa ne da kike iya bacewa ki ke ganin abinda baa fada miki ba?"
Sharifah ta kwashe da dariya har kamar za ta shide. Samha ta sake sankarewa a kwace, ta yi saranda ta fitar da rai daga ci gaba da rayuwa.
Sharifah ta jawo hannun Samha ta riqe, yayin da jikin Samha ya hau karkarwa.
Sharifah ta ce "in har kowa bai yarda da ni ba, na san ke ce kadai a duniya za ki yarda da ni. Ba zan fada miki yadda na san kina nan ba amma lokaci zai fada miki, ba zan fada miki waye ya sanar da ni kina da cikin tagwaye ba amma mu na zaune za ki sani."
Samha ta ce " na godewa Allah da Ya jarrabe ni da ciwo. Allah Ya bani mafita.
Sharifah ta ce " za ki sauka lafiya ki haife kalau ma in sha Allah."
Takaicin da ya sake addabar Samha shine har yanzu Sharifah ta kasa ganewa cewa itace ummul aba isin ciwonta. Idan ta fita daga rayuwata zata warke.
Aka jima babu wanda yake magana, Samha dai ta saka hannu ta dafe goshi kamar mai ciwon kai yayin da hawaye ya yi ma ta qawanya daga ido zuwa bayan kunne.
Sharifah ta tashi cimak ta linke gyalenta ta ajiye tare da jakarta a gefen kujera.
Gami da cewa "an ce in zo in wuni tare da ke, in yi miki hira, in dauke miki kewa."
Sai hankalin Samha ya tashi ta kalli Sharifah da gefen ido dan bata da kuzarin waiwayowa.
Ta fada cikin sanyin jiki "waye ya ce ki zo ki zauna da ni? Ko dai kin zo ki tare ni ne, nima zan zama ku?"
Sharifah ta ce "Mu su wa kenan? Ciwonki ai nawa ne Samha, dan haka ina nan har dare."
Samha ta ce " na gode amma da kin tafi gida dan ki kula da yaran nan kanana."
Sharifah ta yi dariya ta ce "Ah babu kowa a gidan sun tafi ziyara daga su har Hamidah sai gobe zasu dawo."
Samha ta sake fashewa da kuka ba tare da Sharifah ta tabe dan ta juya baya tana ta salati tana fatan ta cika da imani. Wayarta ta dauko ta turawa Aliyu sako ta ce ya yafe ma ta da wuya ya dawo ya same ta da rai.
Bai karanta ba sai da aka dade sannan ya kira a gigice.
Tambayoyi yake ta jero ma ta ama ta kasa amsawa kasancewar Sharifah ta tsura ma ta idanuwa b ata ko qifatawa. Wa ta magana ya fada sai da Samha ta girgiza.
Ya ce "saboda zaman kadaici ne ya sa na je gidan su Sharifah na fada ma ta baki da lafiya, ta zo ta taya ki zama ku wuni tunda Mama ba ta nan yau. Samira kuma in ta tafi sai an ganta dan kada a barki ke kadai babu dadi.
Sannan kuma akwai wata tambaya da kika yi min akan Sharifah toh bani da amsar na san a cikin magagin bacci kika yi ta. Na tabbatar ba zai wuce labarin da Sharifah take ba ki ne, ba ku gama ba shine abin ya tsaya miki rai. Kika ce min baqin kare ne ya ciji Sharifah sai ta kwanta ciwo. Ni ba na so ki dinga saka abu a rai shiyasa nake so ta zo ta karasa baki labarin baqin karen."
Haushin Aliyu ya rufe ta yayin da suka tsurawa juna ido ita da Sharifah. Duk da ma dai ta san Sharifah bata jin abinda yake cewa
Samha ta kasa cewa komai. Wato Aliyu ne da hannunsa ya dauko ma ta ajalinta ya kawo ma ta. Ai shikenan zai ga karshen labarin baqin kare kuwa idan zuciyarta ta karasa fashewa, zai zo ya dauki gawa.
Samha ta kashe waya ba tare da ta iya bashi amsa ba. Ya sake kira sai ta qi amsawa, da ya kira a karo na uku sai Sharifah ta dauka ta amsa
Ta na dauka ta ce " Aliyu ina tare da ita kada ka damu, yau zamu sha labari da kawata. Ka ci gaba da aikinka ga ni ina kular maka da ita."
Ya yi godiya ya yi ma ta sallama cikin jin dadi.
"Tashi ki zauna in baki yogot ki sha, na ga ga kaji ma ga fruits. Da yake a gigice na taho ban tsaya na saya miki komai ba amma kada ki damu gobe zan kawo miki kwadon zogale, kin ji qawata."
Samha ta qi tashi ta zauna, sai da Sharifah ta dame ta da magiya sannan ta tashi ta zauna. Sai ta ji tsoron da take tsananin ji na Sharifah ya ragu, tunda yanzu ta san wanda ya bawa Sharifah labarin tana asibiti da kuma tagwayen da suke cikinta.
Tare suke shan kayan marmarin akan gado suke zaune, su na fuskantar juna
Samha ta ga gara ma ta tsaya ta saurari labarin Sharifah akan ta mutu saboda zulumi.
Samha ta kalli Sharifah da gefen ido cikin rashin fara'a ta ce " ki bani labarinki da na Fanna, Musamman yadda baqin kare ya cije ki."
Sharifah ta yi murmushi ta ce "tabbas na yiwa mijinki alqawari yau zan zame miki radiyo mai jini za ki sha labari kuwa kala-kala, da na nan da na can ."
" Can ina? Samha ta tambaya cikin rashin tsoro. Dan abin ya zame ma ta dole ma ta tsaya ta ji.
Sharifah ta ce "duniyar rayayyu da duniyar matattu."
Samha ta gyada kai ta ce " na shirya sauraro. "
Ta na rufe bakinta Nana Anmad da Maryam Alqali ne suka murda kofa suka shigo hannayensu dauke da fulasan abinci.
Da faraa suka shigo sai kawai aka yi ido hudu da Sharifah da Samha da su.
Su Nana suka yi turus sula ja da baya su na zare idanuwa su kalli Sharifah su juya su kalli Samha.
Nana ta zabura ta ce " A a ba wannan dakin muke nema ba."
Sharifah ta ce "Nana nan ne mana ku shigo."
Ta taso da sauri za ta tare su. Wani uban tsalle da wuntsulawa gami da zubar da fulasan hannu su su ka yi sannan su ka fafara da gudu.
Sai Sharifah ta daga da fulasan daga qasa, Allah Ya sa basu bude abin ciki ya zube ba. Ta bude kofa da sauri ta leqa, babu su babu kamanninsu.
Sharifah ta juyo ta kalli Samha cike da mamaki ta ce "kin san idanuwana ba sa gani sosai, kamar Nana Ahmad da Maryam na gani."
Samha dan dariya har sai da ta kwanta, ta san abinda suka gani suka gudu.
Samha ta fada a ranta "Su ne mana, amma nima na yi mamakin yadda ta gansu. Ban san wanda ya fada musu ba ma ina asibiti.
Sharifah ba ta damu ba amma tabbas ta gane abinda ya sa suke gudu. Ta bude fulasan biyu sakwara ce a daya, dayan kuma miyar agushi ce ta sha kaji da kifi.
Samha ta ce a zuba ma ta za ta ci sai Sharifah ta zubo musu tare. Samha har yanzu dariya ce take cin ta, amma sai ta dinga kunshe baki tana yi a ciki-ciki.
Su na cikin cin abincin, wannan karon a kan kafet suka zauna suna ci.
Kamar daga sama Sharifah ta ce "su Nana Ahmad da Maryam Alqali kenan. Manyan gari Hmmmmm. Na gane su fa tun ba yau ba."
Samha ta na ta kawar da maganar dan bata so a yi amma Sharifah ta ci gaba da yi.
Ta ce " basu san Sharifah ba ne ganinta kawai suke yi nesa-nesa amma nan gaba za su santa."
Samha shiga gyara magana sai murmushi kawai Sharifah take yi.
Sharifah ta ce "labarinmu mun tsaya a daidai in da na ce na amsa kira kotu ta biyu da ya kaini aka ce ana qarata ne akan in dawo masa da yara saboda ina da aure dan haka raino ya saraya a kaina. Ba ni da lauya ni kadai nake zirga-zurga daga wannan kotun zuwa waccan. Dukka dangina wasu 'yan mata ne guda biyu da muke uba daya su ne suke tare da ni, sauran kowa ya yi shiru har ta da Bello ya koma gefe ya zuba min ido, shi ya fi so in bar masa yaransa kawai ni kuma na ce ba zan taba bari ba.
Cikar dangina da batsewarsu babu wanda ya kira Adamu ya ce masa bai kyauta ba akan wulaqancin da yake yi min ba, sai ma wasu sababbin informations da zai yaqe ni yake ta samu daga gare su.
Ikon Allah kawai na tsaya ina kallo, na yi ta tunanin laifin da na taba aikatawa dangina na cancanci wannan hukuncin. Amma sai aka ce min wadaka da kudi yake yi musu, amma ban taba dauka cewa kudi zai sayi zumunci ba.
Kuma ban taba sanin Adamu mai kudi ba ne dan na ga gidansa bai wadata ba ni ce ma nake yin aikinsa da bai sauke ba. Saboda a bi bayansa dan ya wulaqanta ni kudi yake ta rabo da kayan abinci da kayan dadi, har da ragunan sallah.
Aka yi min wata irin Shari'a wacce ban gane ba zuwa biyu kacal mu ka yi, aka ji ta bakina sai kawai aka yanke hukunci aka ce an ba ni mako guda kacal in kwashi yara in mayar da su tsakar gidan ubansu.
Lallai kuwa tunda na kima hijabi har qasa, gashi na kode na jejjeme ai dole su yi zaton bagidajiya ce. A take na bude baki a gaban kotu na ce ban yarda da wannan hukuncin ba, kuma ina neman kwafin Shariah zan daukaka kara."
Wannan kalma tawa ce ta tabbatar musu da na san abinda nake yi ashe.
Samha ta tafa hannu ta ce da kyau 'yar gidana na jinjina miki."
Sharifah ta yi dariya ta ce "na rantse da ubangijin Musa da Haruna a lokacin na fara jin wani qarfi da rashin tsoro. Tabbas na ga mata a kotu su na ta wahala, ga rashin ilimi, ga rashin karfi, ga rashin wayewa kuma su na da gaskiya an danne musu haqqunansu amma basu da lauya basu da cikar kamalar da zasu iya tsawa su yi bayani. Abin tausayi, ya kamata idan akwai lauyoyi musamman lauyoyi mata da zasu dinga leqawa irin wadannan kotuna su na bibiya su taimakawa irin wadannan matan.
Ina fitowa bakin kotu na hadu da mazigin nan da na fada miki a baya mai suna Idris, ya na murna sun yi galaba akaina.
Na ce masa "ka gama murna amma ka sani babu kotun da ta isa ta raba ni da yaran nan. Ka je ka fadawa Adamu ni da shi sharia yanzu muka fara."
Na fada da karfi cikin daga murya sai da kowa na cikin kotun ya waiwayo. Muryata radau har cikin kotu kowa yana ji. Bana tsoron kowa a lokacin banqi duniyar ta kife ba."
Samha ta gyara zama ta ce "toh yaya aka yi kuma?"
Sharifah ta ce "na shiga ofishin wani abokina lauya da yake babbar kotu wato high court a fusace na rufe shi da fada na ce ka na garin nan amma samun lauya daya da zai tsaya min ya gagara. Kai me kake yi da ba za ka tsaya min ba?"
Ya ce "ni lauyan gwamnati ne ba zan iya tsaya miki ba amma ki kwantar da hankalin zan hada ki da wani lauya mai mutunci, malami ne, mai tsoron Allah shine na tabbatar idan ya ce zai yi zai yi, ba zai taba yarda su siye shi ba."
Na yarda da maganarsa tunda ya ce tabbas shi mai tsoron Allah na san na gama dacewa. Ya kira shi a waya su ka yi magana sanan ya bani lambar wayarsa da addireshin ofishinsa wannan lauya shine Inuwa Ahmad. 'Yar uwata ce ma take ta kuka a lokacin, ni kuma na ce wallahi ba zan yi kuka ba, na daina bata lokacina in yi kuka akan mutumin da bai san darajar matar da ya aura da 'yayan cikinsa ba. Wallahi in raina zai salwanta a cikin yaqin nan, na yarda akan ina raye ina kallon yaran Shariqah su na wulaqanta.
Dan shi ba irin uban nan da na san zai kula da yaransa ba ne, haka gidansa ba irin gidan da zaa kai yaro ba ne ya rayu, matar da bata kula da na ta yaran ba ma tayaya zata kula da yaran wata. Wacce ta tsana ma basu zauna lafiya ba.
Ya na yi ne dan ya wulaqanta ni sai dai Allah bai wulaqanta ni babu mahalukin da zai iya wulaqanta ni.
Ki hasko min maganar jifa irin na asiri, bana duba ba na zuwa a duba min amma Allah Ya na nuna min komai a mafarki, ka na taba ni zan ganka. Ko a suffarka ko a suffar wata dabba mai cutarwa amma a ko wanne hali ko da dakyar ne dai ina kubuta, baa samuna na. Ina da nacin addu'a da kuma tsarkakekkiyar zuciya. Ban cuci kowa ba Allah ba Zai bari a cutar da ni ba .
Masu bani shawara su na bani shawara akan in bazama neman magani a wajen malamai, in tashi tsaye da addu'a akan in yi rinjaye akansa a Shari'a, bayan haka kuma kowa ya dube ni ya san ana jifana da asiri asiri a jikina
Ba na kuraje amma a lokacin wasu kuraje suka feso min, ciwo kala-kala da kasala da bacin rai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login