Showing 1 words to 3000 words out of 18747 words

Chapter 1 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf

27 Feb 2026

399

ZEENATU BOOK COMPLETE
Hausa Novels Document
Daga Alƙalamin Boss Bature✍️*


ZEENATU�





Tana a zaune saman swing chair dake a cikin katafaren garden din gidan, fuskarta sam babu
walwala sai tarin damuwar da tayi mata katutu acikin zuciyarta, ta yi zurfi cikin tunaninta
idanunta suna akan Peacocks din da ke shawagi cikin garden din..







Da matsakaicin gudu motar Alhaji Musa ta kunno kai ta cikin main gate din gidan ta nufo
parking space, yana hakimce a backseat din motar idanunsa suka hango mashi ita ta cikin
glass window, umarni ya ba drivernsa ya tsaya kusa da ita.



Horn ɗin motar ne ya razanar da ita, a firgice ta ɗago da idanunta da suka kaɗa sukai ja ta dubi
motar da a daidai lokacin tayi parking, fitowa yayi daga cikin motar, like always fuskarsa a
murtuke ya ɗauki wankan suit.

Ya saba idan ta ganshi da gudu zata nufe shi tayi hugging dinsa amma yau ya sha bamban,
tunda ta kalle shi sau ɗaya ta kawar da idanunta gefe ɗaya, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin sa
ya yi ba.

Daga gefenta ya zauna tare da ɗaura tafin hannunsa saman kanta ya janyota a hankali ya
kwantar da kanta saman kirjin shi, sai lokacin ta samu damar fitar da abunda ke ranta, fashe
mashi tayi da kuka.

A ruɗe ya soma shafa bayanta da tafinsa, tare da tambayar ta meke damunta? Wa ya ta6a
mashi babynshi? Ko bata jin dadi ne.

Lokaci ɗaya duk yabi ya rude saboda ko kaɗan baya son damuwar Zeenatu.

Cikin shesshekar kuka ta ce, "Daddy, Yaya Shureim.."

"Meya yi maki?"

"Daddy, he stopped paying attention to me bana jin dadin share ni da ya ke yi, I don't know what
I did to him, he's completely changed towards me" tun da ta fara magana ya haɗe rai kamar bai
ta6a yin dariya ba

"Aunty Benazir ma ta rage kula ni, ni gaba daya zaman gidan bai yi min daɗi daddy, mommy
ma bata da lokaci na, in ta dawo daga office agajiye bata kulani sai ta shige daki ta kama bacci,
da anjima kuma in ta farka bata fira da ni, sai dai ta je gurin mommy Layla su yi fira, shima ya
Shureim din baya fira da ni da aunty Benazir ya ke yi kullum suna a tare, kaima idan ka tafi sai
tsakar dare kake dawowa lokacin na riga da na yi bacci, ni gani nake kamar baku sona, baku
damu da ni ba, baku bani kulawa yadda ya kamata..." Ta ƙarashe maganar cikin shesshekar
kuka.



Bai ji dadin halin da take a ciki ba, ya fahimci kaɗaici ne ke damun ta, har cikin ranshi bai ji dadi
ba.



Shafa sumar kanta yayi cikin sigar lallashi ya ce "Stop thinking that way, my princess, bana so
kina sanya damuwa a ranki, you're more important to us than anything, please ki daina fadin
ba'a sonki ko ba a damu da ke ba, sanin kan ki ne bani da abu mafi soyuwa da ya wuce ke, ko
da kowa zai juya maki baya ki tuna ni ina atare dake, koda bana nan kina a cikin zuciyata..."


kalamai masu tausasa zuciya ya dinga faɗa mata har ya samu ta ɗan lafa da kukan.



Tighting dinta ya yi a kirjinshi ta yi lamo fuskarta sharkaf da hawaye sai faman sauke ajiyar
zuciya ta ke yi.



"Daddy yaushe zan cigaba da karatu? Ka ce sai nayi aure zaka barni in cigaba, dan Allah daddy
ka yi mini auren, saboda inaso in dinga zuwa makaranta harma in haɗu da ƙawayen da zamu

dinga zumunci atsakanin mu, saboda na fahimci babu tsara na agidan nan shiyasa ba'a zama a
yi fira dani...."

Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, ya lura da akwai abun da ya 6ata mata rai shiyasa take
fadin ta cikin ta.



"Kada ki damu, Nayi maki alkawari ƙarshen shekarar nan, zan aurar dake, kuma zaki cigaba da
zuwa makaranta"

Murmushi ta saki saboda taji dadin maganar sa, ba karamin ɗebe mata kewa yayi ba, ya bata
lokacin shi sosai sun daɗe suna fira kafin suka sauko daga kan kujerar, hannunsu cikin na juna
suka nufi falo.



Lokacin da suka shigo falon, A dining Suka hango mutanan gidan sun hallara suna cin lunch din
su, ran Alhaji Musa Ya 6aci ganin yadda su ke yin walwala, hakan yasa shi yarda da maganar
Zeenatu, wato basu damu da Zeenatu ta ci abinci ko bata ci ba.


Fusgar hannunta ya yi ya ja ta suka nufi dining din, takun tafiyarsa ne ya ja hankulansu ga
duban shi, har saida gabansu ya fadi ganin yadda ya murtuke fuska.

Yana ƙarasowa ya sanya hannu ya damƙi table cloth din da aka shimfiɗa kayan lunch din
saman shi, ya hankade shi gaba daya kayan abincin suka 6are kan floor, a sukwane suka miƙe
suna kallon shi cikin ruɗu.

A tsorace Zeenatu ta la6e bayansa jikinta na kerma..



Hajiya layla da ranta ya 6aci ta watsa mashi harara tare da cewa, "Wannan wani irin wulakanci
ne? Ta ya muna cin abinci zaka 6arar da shi kamar wani ƙaramin yaro.."

Bata ƙare maganar ba ya daka matsa tsawa tare da nuna ta da yatsan shi, "Karki kuskura ki
sake min magana idan baso kike in 6ata maki rai ba..."

sakin baki ta yi sototo tana kallon sa, hankalin hajiya Sarah ba karamin tashi ya yi ba, sai yarfa
hannayenta take yi tare da marairaice masa fuska don yayi haƙuri.

"Haba Musa, wani irin almubazzaranci ne wannan? Yanzu abun da kayi ka kyauta fisabilillah?
Laifin me mu ka yi maka? Meya sa zaka zubar mana da abinci?" Alhaji Ubaid ne ya faɗa cikin
fushi,

Harara ya watsa mashi rai a 6ace ya ce, "In har Zeenatu ba zata ji dadi a gidan Ubanta ba, to
kuwa babu wanda zai zauna lafiya a cikinku! Saboda rashin hankali kuna nan hankalinku
kwance, kun bar min yarinya a waje cikin kaɗaici? Wato baku damu da ita ba, babu ruwanku
cikinku kaɗai kuka sani ko!"
Da tsawa ya ƙare maganar kamar zai doke su, Benazir da Shureim sun saki baki suna kallon
ikon Allah, sam sun kasa magana..

"Babe, wllh ba haka bane, bansan me Zeenatu ta faɗa maka ba, amma wlh bamu manta da ita
ba, ka tambaye su ka ji saida na aika Tani bedroom dinta don ta kira ta tazo ta ci abinci, bayan
Tani ta dawo ta ce min Zeenatu tace ba zata ci abinci ba, wai bata jin yunwa, dama kwanan nan
fama na ke yi da ita, na rasa gane kanta, da kaina na je ɗakin na matsa mata akan ta zo mu ci
abinci amma taƙiya shiyasa na ƙyaleta, na jira saika dawo in sanar da kai..." Harara ya watsa
musu, tare da jan dogon tsoki, ya juya yana cika yana batsewa ya nufi part dinsa..

Hajiya layla ji take kamar tabi bayan shi ta shaƙe shi, saboda haushinshi da ya cikata,

"Wlh Musa bai da mutunci, ni wlh na gaji da wulaƙancin da ya ke yi mana, don kawai muna
zaune agidansa...?

Bata ƙare maganar ba, Hajiya Sara ta juya tabi bayan shi, bayan tafiyar ta Shureim da Benazir
suka haɗu suna rarrashin mommynsu, Zeenatu dake kallonsu duk tasha jinin jikinta ganin abun
da ta ja musu...

Fashewa ta yi da kuka tare da juyawa jikinta na kerma ta nufi hanyar ɗakin ta, bata kaiga
ƙarasawa ba Dr. Shureim ya bi bayan ta da sauri ya taso ƙeyarta ya dawo da ita dining din,
zaunar da ita ya yi kan kujera ya tsareta da tambayar me ta faɗa ma uncle Musa, cikin
shesshekar kuka ta zayyana musu komai, cike da takaici Benazir ta ce, "Haba Zeenatu, me
yasa zaki mana haka? Idan mu muka 6ata maki rai why ba zaki faɗa mana ba uhum? Kinsan
halin uban naki, yanzu gashi kin ja ya zubar mana da abinci hankalinki ya kwanta ko? Kin shiga
tsakanin mu da shi..."

Fashewa ta kuma yi da kuka, Alhaji Ubaid ya ce, "Ya isa haka pls, ni banga laifin Zeenatu ba,
gaskiya bakwa kyautawa, ku yakamata ace kuna jan ta a jiki, tunda ku kaɗaine ƴan uwa dake a
kusa da ita, bayan haka yarinya ce sai kuna haƙuri da ita.."

Ta6e baki hajiya Layla ta yi, "Ni Zeenatu bata yi mini komai ba, in ita bata da cikakken hankali
ai shi uban nata da hankalinshi ko? In ba rashin wayau ba meye na ɗaukar maganar yaro? Ta
ƙare maganar tare da jan tsoki ta juya ta bar dining din, da sauri Alhaji Ubaid yabi bayanta don
ya lallashe ta.

Cikin shesshekar kuka ta ce, "Am really sorry, idan na 6ata maku rai, ni ban faɗa masa don yayi
maku faɗa ba, Aunty benazir am sorry, yaya Shureim kaima ka yafe min.."

Tausayinta ne ya kama su, har su ka ji basu kyauta mata ba, lallashinta su ka koma yi.



"Nasan nine na 6ata maki rai ko?" Ya tambaya yana kallon ta, yamutsa fuska ta yi tare da
sunnar da kanta ƙasa,

Kallon Benazir ya yi suka haɗa ido, tashin hankali! gaba ɗaya sun gane inda Zeenatu ta dosa,
gashi a halin yanzu Dr Shureim baya jin sonta, tun ranar da Allah ya haɗa shi da Aisha, ya gane
ba son aure yake ma Zeenatu ba, rashin Aisha ne yasa har ya kula ta da sunan soyayya, amma
a zahirin gaskiya baya jin zai iya haɗa Aisha da wata mace a duniyar nan, bai ma ta6a lura da
Zeenatu tayi masa ƙaranta ba sai ranar da idanunsa suka yi mashi tozali da Juliet ɗinsa.


Ƙumshe dariya Benazir tayi, don ta riga da ta gane me ya Shureim ke tunani aransa, ɗan ja
gefe ya yi yadda zai kauce ma Zeenatu kada ta ji mi zai ce don yasan zata iya fahimta, cikin
harshen larabci ya ce, "Ya zanyi Benazir? Wlh tun da na ga Ummi na ji kamar ancire mini son
Zeenatu, yanzu soyayyar da nake mata ta ƴan'uwantaka ce bata aure ba."
Itama cikin harshen larabci ta ce, "Ya shureim sau nawa ina kokarin ankarar da kai akan
Zeenatu uhum? Saida na ce maka tayi maka ƙanƙanta, ba sa'ar auranka bace, duk da ba
haramun bane don ka yi soyayya da ita, amma ni dama nasan mace ɗaya ce a cikin zuciyarka,
ka so zeenatu saboda rashin Aisha, yanzu kuma Aisha ta bayyana, in ka ji zaka iya haɗawa
biyun tau, ka dai san Zeenatu da kishi, kuma tsakani da Allah da raini ka haɗa Aisha da
Zeenatu yar cikin ta.."

Ta faɗa tana dariya, gaba ɗaya maganganun da suke yi Zeenatun bata fahimtar abun da suke
fadi saboda basu ɗaga murya ta sadda kanta ƙasa.

"Ka daure ya Shureim, kada ka karya mata zuciya, ko da ba za ka aureta ba, ka taimaka ka
kwantar mata da hankali, wlh tana sonka, kaga ta fara shiga damuwa, in ya so daga baya zamu
san abun yi..."

Jinjina mata kai yayi tare da mayar da hankalinsa kan Zeenatu ya matsa wurinta, cikin
sanyayyar muryar nan tashi ya ce, "Am really sorry rabin raina, na gane kuskurena, ke ce baki
fahimce ni ba Zeenatu, taya zan daina kula abar kaunata uhum?" Murmushi ta ɗan fara saki..

Ruƙo hannunta Benazir tayi a cikin nata, "Pls Zeenatu, ki daina biyewa zuciyarki, wallahi babu
abun da ya canza na daga kaunar da mu ke yi maki, mun damu dake, muna son ki rabin ranmu,
daga yanzu komai a tare zamu dinga yi in sha Allah, mu ci abinci atare, muyi fira atare, muyi
kallo atare, mu yi gym atare, kai har tilawar alqur'ani zamu dinga yi kullum tare da ya Shureim."
Murmushin farin ciki ta saki ga wani dadi da ta ji.

"Yanzu ma ba zamu barki da yunwa ba.." ta faɗa tare da kwala ma Tani kira, jim kaɗan sai gata
ta nufo su, tana ganin kayan abincin da aka 6arar a ƙasa ta daura hannu akai tana tambayar
meya faru..



"Pls ki kwashe kayan abincin da ya zube ki canza mana wani, sannan ki turo wata maid din ta
goge floor din, muna jiran ki."

Benazir ce ta fada, jikin Tani na 6ari ta amsa da toh ta zuƙunna tana tattara kayan abincin,
bayan ta gama jera su a tray ta nufi kitchen....



______________UNCLE MUSA



Bayan ya shiga bedroom dinsa yana ƙoƙarin fara rage kayan jikinsa, wayarsa ta ɗau ruri.

zaro ta yayi daga cikin aljihun wandonsa yayi picking tare da kara wayar a kunnansa...

"Sir, har yanzu bamu gano shi ba, a binciken da mu ka yi, ba shi kaɗai ya gudu daga estate din
ba, hada yar uwarsa ba'indiyar nan.."

Tsoki ya ja cike da takaici ya ce, "Na raina kokarin ku, tayaya har sakaran mutumin nan ya
gagare ku ganowa um!" Ya fada a fusace..

"Sorry Sir, we'll do our best to locate..."

Bai ƙare maganar ba ya daka mashi tsawa yana faman cije le6e ya ce, "Idan har baku gano
inda ya 6uya ba nan da one week, ku kuka da kanku! sannan bana buƙatar shi araye da shi da
yar uwar ta shi, just kill them all and bury them where no one can find their bodies!"

"An gama sir," Rejecting call din ya yi, sai faman fitar da numfashi mai ɗumi ya ke yi, ran manya
ya 6aci...

Wani layin ya kira tare da kara wayar a kunnansa,

"Mark, how's his condition? Has he recovered from the coma?"


On the other hand Dr. Mark ya ce "He still hasn't regained consciousness, amma ka kwantar da
hankalin ka, yana samun kulawar likitoci, nan bada jimawa ba zai farfado, kasan aminin nasa
baya wasa da lafiyar sa"

cije le6ensa yayi tare da jan numfashi ya furzar da shi.

"Ko da zai cire ran shi yaba Omar don ya rayu, bazai ta6a burge ni ba, bana son alaƙar su
kwata kwata, sai kace shi na haifa ma shi, Omar ya jima yana baƙanta min rai saboda Owais,
shi ya raba ni da shi, ya mallake min ɗa, amma nasan maganinsa dole in shiga tsakaninsu
wlh..!"
Bai ƙare maganar ba, ya tsinkayi muryar Hajiya Sarah,

"Babe..."

Nan da nan ya haɗe rai, da sauri ya katse kiran tare da jefa wayar saman mattress, afusace ya
juyo yana kallonta tana daga tsaye bakin kofar ɗakin,

"Ban hana ki yi min la6e ba idan ina waya?"

Marairaice masa fuska ta yi, "Am sorry, ba la6e nake yi maka ba, dama na biyo kane don inji
meyasa ka yi mana haka pls?"



"Oh! kin biyoni ne don kiyi min faɗa kan abunda na yi halan? Ya fada yana ɗage mata gira..



Ƙwarjini yayi mata hakan yasa ta kasa faɗan ta cikinta..



"In har zaku cigaba da 6ata ma zeenatu rai, nima bazan daina 6ata maku rai ba, yarinya da
gidan ubanta ace kowa ya juya mata baya babu mai kula da ita!"

"Bai kamata kana ɗaukar maganar Zeenatu ba, har yanzu fa yarinyace, babu abunda aka yi
mata fa, ita ce ta ƙuntata kanta.."

Bata ƙare maganar ba ya katse ta, "Pls, fuce ki bani guri, bana son takura.." gyaɗa kai tayi
maganarsa ta 6ata mata rai.

Dama da haushinshi aranta, kwanakin nan kwata kwata baya bata hakkinta yadda ya kamata,
in ya fita sai cikin dare ya ke dawowa gidan kamar aljani, tayi ta jiranshi baiwar Allah, har sai
bacci ya dauke ta, kuma in ta farka ta gansa ta nemi ya kulata sai ya kama yi mata faɗa yana
faɗin ya gaji ita bata da hakuri ne, bata ga a gajiye ya dawo ba, kawai ta kyalesa bacci zaiyi,
baiwar Allah zaman hakuri kawai ta ke yi da shi.



"Abincin naka fa?"

"Bazanci ba" Cike da 6acin rai ta ce, "Kada Allah yasa ka ci Musa, ka cigaba da yi min abun da
kaga dama, ni da kai in har akwai wanda ke cutar wani Allah zai saka masa ne ka jira ka gani,
don kawai ina haƙuri da kai sai ka yi ta min abunda kaga dama..."


A ruɗe yake kallonta cike da mamakin ina ta samu kwarin gwiwar gaya masa magana ido cikin
ido batare da jin shakkar shi ba..

"Ƙaddara ce tasa na aure ka, amma wlh nafi ƙarfin ka, koda yake ba laifin ka bane, nina ja ma
kaina, shiyasa har ka samu damar wulaƙantani son ranka..."

Juyawa ta yi a fusace ta nufi room door din, batai aune ba taji ya damƙi wuyanta, a tsorace ta
kware baki zata fasa ƙara, ya yi hanzarin sanya tafin hannunsa ya toshe bakin nata.

Saitin kunnnanta ya kai bakinsa da wata irin murya mai cike da shu'umanci ya furta,
"Matsoraciya..." Ajiyar zuciya ta sauke tana faman haɗiyar yawu...

"Faɗa min a ina kika samu kwarin gwiwar nan ne?" Ya faɗa yana leƙen fuskarta..



"Ka 6ata min rai ne, ni kawai bana jin dadin abun da ka ke yi min ne, basai na fito fili na faɗa
maka ba ka riga da ka sani .."

"Am sorry my queen, mother of my princess, na kar6i laifina, bazan ƙara ba, nima bada son
raina hakan ke faruwa ba, ayyukane su ke yi min yawa amma zan gyara in sha Allah." ta ɗan yi
mamakin yadda yayi mata magana cikin tausasa harshe.

"Muje ki taimaka min in yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login