Showing 9001 words to 12000 words out of 18747 words
Chapter 4 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf
ya ƙi sanar da ni...." Nan ya labarta musu
abun da suka tattauna tsakaninshi da baba Obie.
Kallon kallo suka jefawa junan su cike da tashin hankali, Agent Jabeer Osman ya ce, "Akwai
sauran rina a kaba kenan, In har bamu yi gaggawar kamasu ba zasu iya mayar da hannun
agogo baya, nasan iwar haka suna nan suna shirin kawo mana farmaki."
Gaba ɗaya sunyi amanna da maganarsa, Agent Zahra ya ce, "Ni damuwana ina zasu farmaka?
ya tambaya yana duban su,
"Hankalina ya fi karkata akan fursinonin da muka baro a Csh."
Taj ya ce,"Asibitin yana da tsaro tunda na sojoji ne, amma fa kada mu dogara da hakan, mun
riga da mun san su wanene Evil Giants, in har suka farmake mu da su, toh Allah ne kaɗai zai
iya ƙwatar mu, za su iya amfani da sihiri su kashe sojojin dake tsaron su, su kwashe yaran
abunda ba a fata, amma menene mafita...?"
gaba ɗaya suka zurfafa tunaninsu kowa na tunanin abun da yakamata a yi.
"Kuskuren da muka yi tun farko shine barin makaman da grandma ta bamu, da mun sani mun
taho da su, saboda da su kaɗai ne za'a iya yaƙar su.."
A cewar Captain..
Cike da takaici Canal ya daki gaban table dinsa yama rasa abun cewa..
Jackson ya ce,"Akwai gagarumar matsala, dole fa mu fara kai masu farmaki kafin su kawo
mana idan ba haka ba, ba zasu yi mana da dadi ba, bamu san ina zasu farmaka ba!"
Lieutenant Thompson ya ce, "Ni dai a nawa ganin shawara ɗaya ce, Chief grandpa shine
mafita, shi kaɗaine makamin da muke da shi a yanzu, tun da ya ce zai mika wuya toh ya
taimaka ya faɗa mana komai idan ba haka ba, ba zamu iya cin galaba a kansu ba, a kowani
lokaci zasu iya kawo mana farmakin bazata..."
Girgiza kai Chief Owais ya yi, "mu yi hakuri mu nemi wata mafitar, saboda ba irin magiyar da
ban yi masa ba amma ya ƙi fada mun, ya ce a dokar aikinsu wani baya tona asirin wani,
alkawari ne suka ɗaukarwa junansu, kuma shi ba zai ci amanarsu ba, tun da har ya fadi hakan
bai duba ƙaunar da yake yi mini ba, toh wlh ba zai ta6a bamu hadin kai ba, koda zamu azabtar
da shi ne, amma a maganarsa ya ce in har aka kawo mana farmaki mu sanar da shi, amma
wannan ba mafita bane, tayaya za a yi mu san za'a kawo mana farmakin?"
Da damuwa ya jefa musu tambayar, gaba daya sun shiga tashin hankali..
"Ni a ganina mu fara nemo wadanda grandma ta fadi sunayen su? In ya so sai muci ubansu mu
azabtar da su har sai sun faɗa mana su wanene sauran Elders din..." Taj ne ya fada yana huci
zuciya ta kai wuya..!
General Noah ya ce, "No ba zamu iya kama su ba, har yanzu bamu da isassun hujjojin yin
hakan!"
"Sir, muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su..."
Gaba ɗaya suka maida hankali akan Taj da ya yi maganar har suna haɗa baki gurin tambayar
wata hujja ce? Bai jira Chief ya bashi umarnin ya faɗa ba, ya fara zayyana musu komai da ya
faru tun daga kan labarin Ummi har izuwa labarin da Benazir ta bashi akan Alhaji Musa.
Lamarin ya ɗaure musu kai, basu gama shan mamaki ba, sai da Chief ya samu ƙwarin giwar
tunawa da wata hujjar da yake da ita, nan shima ya labarta musu komai da ya gano game da
shi tun daga kan hotansa dake a cikin diary din Unaizah, ya ƙara da cewa, "Har yanzu bai rabu
da Ummi ba, bayan ya rabata da kowa nata ya maidata karuwarsa, shine ya tafi da ita
America..." A rude U.s armies suke jefawa junansu kallo mai cike da tsantsar al'jabi, Ummi dai
da suka sani tantiriyar karuwa yau sun ji asalin labarinta da kuma azzulumin da ya yi silar
canza rayuwarta, gaba ɗaya basu ji daɗin abun daya faru da ita ba, tausayinta ne tsantsa a kan
fuskokinsu, ba su kaɗai ba hatta General Noah dana hannun daman Chief sun nuna
tausayawar su a gare ta, labarinta ya taba zukatansu, kuma basu taba ganin mugun mutun irin
Musa ba, labarin yarinyar da ya sa su zubda ƙwalla ashe shine Ubanta, sun ma riga da sun
yanke ma kansu shine JAN WUYA mutumin da suke nema ruwa a jallo..
Chief Owais bai dakata ba, ya ɗaura da basu labarin da Sheikh Imam ya ba shi ...
Taj ya ce, "dama sai da raina ya bani, sune suka kashe Uzair..." Ya faɗa cikin ƙunci da baƙin
ciki.
General Noah ya ce, "Wai ni Musan nan bashi bane former president ba? Mahaifin Ddg? Kuma
ƙanwarsa tana auran daddynka ko?" Jinjina mashi kai Taj ya yi.
Cikin fushi Noah ya buga saman table rai a 6ace ya ce, "Babu tantama zai aika, Ni dama bai
ta6a burgeni ba, mutun sai girman kai da izza ashe dukiyar tasa ta kungiyar asiri ce, shi dama
karen yan siyasar nan na daɗe ina zargin sa saboda mugun munafuki ne.."
CI ya ce, "Zai yi wuya in ba daga tsatson fir'auna ya fito ba, mutun ba imani ba tausayi! Zalunci
da mugunta kaɗai yasa gaba, aikuwa dubunsa ta cika, daƙiƙin kwata kwata baya amfani da
kwakwalwarsa, gashi nan cikin rashin sani ya tabka kuskuren da ya yi silar tonuwar asirin sa..."
Coo ya ce, "Wlh ikon Allah ne, ka duba yadda ya daɗe yana sheƙe ayarsa tsawon lokaci batare
da an iya kamasa ba, wai a haka har matsayin president ya taka, ko da yake ya samu ɗaurin
gindi ne..." Bai ƙare maganar ba, Taj ya yi masa gyaran murya tare da furta "Hattara dai.." Cike
da jin kunyar Chief CI ya sunnar da kansa, bawan Allah Chief ɗan murmushi ya saki tare da ɗan
girgiza kan kanshi.
"Sir, Yanzu meye abun yi tunda muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su? Taj ne ya faɗa
yana dubansu..
Commender James ya ce, "Babu bukatar 6ata lokaci, mu kama su kawai su fara kar6ar
sakamakon zunubin da suka aikata..."
General Noah ya ce, "da shi ɗan iyan, da Musan, da pravin da aminnan grandpa, da likitocin da
momma ta faɗa suna da sanya hannu suma a kama su, sannan kada a kuskura abar pravin ya
ƙetare kasar nan, nasan iwarhaka yana neman hanyar da zai gudu, watakil ma ya gudun,
shiyasa banso kuka ɗauki lokaci baku sanar damu ba, wlh da kun faɗa mana tun ranar da abun
ya faru zamu bi diddiginsa mu kama ɗan iskan, amma na yi maka uziri nasan alhinine ya hana
ka sanar mana..."
Chief ya ce, "Mun tattauna da Uncles dina, suma zasu bada gudummuwarsu..." Nan ya labarta
masu abunda suka tattauna da Uncles ɗinsu, sunji dadi kuma sun ƙara jin kwarin gwiwa a tare
da su..
"Bayan haka tun ranar da ya gudu nake ta trying layinsa a kashe yake, har jaraba bin diddiginsa
na yi amma ban iya gano komai ba, ina tunanin ya jefar da wayar ne don kada mu bi
diddiginsa."
Agent Zahra ya ce, "Zai iya yiwuwa ya canza layi, in kuwa yayi kuskuren zuwa yin register zamu
iya samun bayanansa."
"Ita yar'uwar tashi ka kira layinta ne?" James ne ya tambaya..
"A ɗaki tabar wayar, na kar6i number dinta a hannun yan uwanta maids, dana kira sai na gano
location din wayar a cikin gidan ya ke, da kaina na shiga na dudduba dakin har na gano wayar
nata."
Taj ya ce, "Za mu iya haɗa baki da abokan aikin nata, ita Hajjatyn zata iya yin kuskuren kiran
wani daga cikin su tun da ta yarda da su atare suke aiki, ko basu ba mu nemi aminiyarta ta ƙut
da ƙut, wadda muke da tabbacin zata iya kiran ta, sannan mu haɗa baki da ita, da zarar ta kira
ta tayi hanzarin sanar damu, mu kuma sai muyi kokarin bin diddigin su..." Shawarar da Taj ya
kawo ta yi masu daɗi..
Ya kuma cewa, "Amma ni abun da ya ɗaure mun kai, Ita hajjatyn tasan abun da ya aikata kuma
ta bi shi suka gudu? Ko dai dama a tare suke aikata 6arna ta bayan fage..."
Amma da kamar wuya saboda Hajjaty mutuniyar kirki ce .." Wani marayan kallo Chief ya yi
masa..
"Mugu bashi da kama Taj, abun da ya faru da ni ya isa yasa ka dauki darasi, ba kowani nagari
bane mutumin kirki, akwai masu fuska biyu, a fili Musa a zuci fir'auna, ni bana zargin ta, amma
ta aikata babban kuskure da ta haura ƙafa ta bi shi suka gudu, in har muka gano da sa
hannunta akan abun da ya faru da auntyna, kuma tasan abunda yake aikatawa wlh na lahira sai
ya fi ta jin daɗi, dole mu hukuntata daidai da abun da ta aikata, babu wanda zamu ragamawa
kamar yadda bazan raga ma kakana ba, dole kowan nan su ya gir6i abun da ya shuka..."
Ya faɗa tare da bugun kan table din gaban su, gaba daya idanunsu akan fuskarsa, maganarsa
ta burge su, suna alfahari da shi, ya cancanci su yaba mashi saboda jajircewar shi akan
gaskiya, a dai yadda duniyar nan ta baci da rashin son gaskiya, da wani mai son kan ne idan
yasan nashi ne yake aikatawa 6oyewa zai yi, ko ya bashi hadin kai ya gudu don kada a kama
sa, ko kada su kunyata a idon duniya, gaskiya samun mutun mai irin zuciyar chief zai yi wuya a
fadin duniyar nan, he's a true leader, ba karamun mai tsoron Allah bane zai yi hakan...
Almost one hour suna tattauna yadda zasu kama Elders, kowa yana kawo idea dinsa, a karshe
suka yanke shawarar zasu tuntubi Ummi saboda ta hanyar ta ne suke sa ran za su damƙi Musa
ta cikin sauƙi. Chief ya ce su bar komai a hannunshi ya riga da ya yi mata magana amincewarta
ya ke jira, zai ƙara yin magana da ita duk yadda su kai zai sanar da su..
*PRAVIN❗*
Aje Motarsa yayi a haraban wani gida, fitowa yayi jikinsa sanye da suit ya rufe fuskarsa da
mask, hatta hannayensa da ƙafafunsa ya saka musu safa, sai yan waige waige ya ke yi daga
gani yana a cikin fargaba, zagayawa yayi ta baya ya buɗe boot din motar, ya janyo ƙaton buhun
dake a ciki ya aje ƙasa, kafin ya bude backseat ya sungumo baƙar jakarsa ya rataya ta kan
kafaɗarsa, da sauri ya ja buhun ya shige da shi ciki, kulle door din ya yi da code kafin ya nufi
Ciki.
Shigarshi falo keda wuya ya soma jiyo kakarin aman da ta ke yi, hankalinsa a tashe ya zame
jakar ya jefar kan sofa ya saki buhun cikin sauri ya nufi bedrom din da take.
Yana shiga ciki bai same ta a saman gadon ba, sai dai bargonta dake a yashe ƙasa, cike da
fargaba ya bangaje kofar toilet ya shiga yana haki saboda gudun da ya yi, lokacin idanunsa
suka sauka akan ta yayin da take a gaban sink tana kwarara amai tamkar yan hanjin cikinta
zasu zazzago, ta daddafe bakin sink din da hannayen ta.
Ƙarasawa ya yi da sauri ya dafe kafadarta yana yi mata sannu. Bata ko kula shi ba sai da ta
gama amayar da komai da ta ci, ta kunna faucet ruwa ya wanke aman.
Kokarin daukarta ya yi don ya sauwaƙe mata tafiyar, cikin bacin rai ta bangaje shi ya yi taga
taga zai faɗi yai saurin tsayar da kansa yana kallon ta.
Tsantsar bacin rai ne akan fuskarta, idanunta sun kumbura sun kaɗa jawur saboda kukan da
take sha, gown din dake a jikin ta tayi squeezing kamar an ƙwatoto daga bakin kura, doguwar
sumar kanta ta cukuikuye kamar ta mahaukaciya, mace mai tsafta ta zama ƙazamar karfi da yaji
saboda rashin lafiya da damuwa..
A hankali zafafan hawaye suka soma zarya kan kuncin ta, labbanta sun bushe ƙamas sun ɗan
faffashe ga jikin nata har yanzu ba sauƙi..
Cike da bacin rai ta furta, "Karka kuskura ka ƙara matsowa kusa da ni, i don't want to see you
Pravin, ka nisanta kanka dani, idan ba haka ba zan yi ma kaina illa!" Bai ta6a ganin Hajjaty a
cikin fushi irin na yau ba..
A hankali ya sanya hannu ya cire mask din dake akan fuskarsa, cikin yan kwanakin nan saboda
zullumi da fargaba har rama ya yi, tun ranar da ya gudo da Hajjaty, bai nufi ko'ina ba sai guest
house dinsa da ya daɗe da mallakarsa, babu wanda yasan yana da gidan.
"Ba halin ki bane, bansan ki da fushi ba, na rasa gane kanki cikin kwanakin nan, duk abun da
kika ga ina yi saboda in kare ki ne, amma kin kasa fahimta na.."
Harara ta watsa mashi, cikin bacin rai ta ce, "Idan ba halina bane to kai ne ka sauyani Pravin, ni
bazan cigaba da yarda da munafuki ba, na gaji da sauraran ƙarairayin ka! ka faɗa min gaskiyar
abun da ya faru, ka raba ni da mutanan da nake rayuwa da su ka kawo ni wani gida ka boye ni
a cikin sa! Kullum na tambaye ka sai ka yi shiru, wai me ka ɗauke ni ne? Don ina da hakuri ba
hakan yana nufin bani da hankali ba! Zan iya jure komai amma wallahi bazan jure rainin wayon
ka ba...."
Tuni ya sha jinin jikinshi jin yadda Hajjaty ke masa faɗa kamar uwarsa, tana magana tana
ciccije le6enta saboda radadin da take ji..
"Tayaya kake tunanin zan cigaba da zama da kai? Bayan baka ɗauki iyalinka da muhimmanci
ba sai ni Pravin? Wani laifi ka aikata ne da yasa har ka gudo da ni? A ranar kafin in fita
hayyacina na ji muryar Hajiya Saratu a cikin kunnena, ta shigo daki na, duk da ban ji abun da ku
ka tattauna ba amma raina ya bani ta gano abun da muke yi shiyasa har ta shigo ɗakina, kuma
na ji lokacin da ta bangaje mu muka faɗi daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba..."
Dakatawa ta dan yi tana jan numfashi idanunta a cikin na shi, ya yi zuru zuru ya rasa ta ya zai
shawo kanta, kwanakin nan basu jituwa saboda yaƙi faɗa mata laifin da ya aikata, ta ƙi kwantar
da hankalinta balle har ta ji sauƙin abun da ke damunta..
Girgiza kai ta yi idanunta suka cicciko da ƙwalla...
"Ka kasa kare kanka saboda baka da gaskiya shiyasa ka yi shiru ko? Ni ina ji araina wani laifi
ka aikata musu shiyasa ka gudu da ni, saboda hujjar daka bani bata gamsar da ni ba.."
Sunnar da kanshi kasa ya yi, jikin shi ya yi sanyi lakwas, baisan ya zai yi ba, ya jefa rayuwarsu
a cikin bala'e da masifa, ya yi danasani tafi sau a ƙirga, yana matukar jin kunyar Hajjaty, yana
jin nauyin tasan miyagun laifukan da ya aikata wa'iyazubillah!!
Bata ƙara yin magana ba, ta juya ta nufi kofar fita da sauri ya bi bayanta, shigowa cikin dakin ta
yi, jikinta na kerma ta nufi bedside drawer ta soma kwashe magungunanta tana jefa su cikin
dustbin din dakin, shigowa ya yi da sauri ya damƙi hannayenta, kokoyi suka kama yi..
"Pls ki saurare ni, zanyi maki bayani, ki daina zubar da maganinki, da tsada na siye su saboda
lafiyarki..."
Wani kallo ta wurga masa, "Ban damu ba Pravin, bana son lafiyar tawa, nafi son na mutu,
saboda wanda na yarda da shi yana neman ya karya min zuciyata..."
Bai san sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, duk yadda ya so ya dakatar da ita abun ya
ci tura, ƙarfi yasa gurin ɗaukarta ɗungurugum ya kwantar da ita kan gadon, ta dinga kuka tana
bubbuga mattress da hannayenta, bin ta ya yi saman gadon ya janyota jikinshi tana turjewa, ya
rungume ta kan ƙirjin shi, duk yadda ta kai ga jin haushin shi da ya yi mata hakan sai da ta ji
sassaucin damuwarta.
Cikin sanyin murya ta ce, "Pravin dan Allah ka fadamin meyasa ka gudu da ni? Meyasa ka bar
Obie estate? Wani laifi ka aikata? Kada ka yi min karya Pravin, babu sirri atsakanin mu, kasan
bani da kowa in ba kai ba, kaine majinginata, ƙashin bayana, bana so ka ci amanar yardar da
na yi maka Pravin, dan Allah ka faɗamin na yi maka alkawarin zan rufa maka asiri kuma zan
taya ka neman mafita.."
wani irin tsantsar sonta da tausayinta ne ya mamaye zuciyar shi, tsoma yatsun hannayensa ya
yi a cikin sumar ta yadinga cakuɗa gashinta kamar yana mata susa,
Cikin sanyin murya ya ce, "Ki yi hakuri na boye maki ne saboda bana so na ɗaga maki hankali,
amma gaskiyar abun da ya faru, Hajiya Saratu ta gano ina zuwa dakin ki, harma in kwana,
bayan mun dawo an fara shirye shiryen family meeting, sai na shiga ɗakinta don in canza kayan
dake a jikina, ina kokarin cire riga na jiyo muryarta a cikin toilet tana yin waya ƙasa ƙasa kamar
bata so aji, saina lallaba na je bakin ƙofar dakin na yi mata la6e
a nan na ji tana faɗin wallahi bazata sa6u ba, dama ta jima tana zargin kin asirce mata miji
saboda yadda kike gayu, wallahi ba zata ƙyale ki ba, sai ta kashe ki da poison..."
Zare ido Hajjaty ta yi,
Pravin ya sha mur ya ci gaba da zabga mata ƙarya, "Da na ji haka gabana na faduwa na fara
tunanin me yakamata