Showing 6001 words to 9000 words out of 18747 words

Chapter 3 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf

27 Feb 2026

404


agurin ta kaɗai za'a samu hotunansu, wani abu da ya ƙara ruɗar da ita nickname dinsa da ta
gani a rubuce cikin diary din Preety, kuma a labarin da Unaisah ta basu ta fadi sunan mahaifin
Unaizah yar gidan daddy, gaba ɗaya dai kanta ya ɗaure tamau, kwakwalwarta ta rikice sai tufka
da warwara ta ke yi.



"Ummi, kun gama magana da Chief dinne?" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Taj, a firgice ta
dube shi yana zaune kan wheelchair dinsa, danne damuwarta ta yi ta kakaro murmushi kan
fuskarta, "Eh mun gama magana da shi, shine ma ya ce min in tafi.

Sarai ya lura akwai damuwa atattare da ita sai dai kawai ya basar.


"Yakamata ka ajiye wheelchair din nan, tun da ka fara samun sauƙi, idan ba haka ba zaka
manta yadda ake yin tafiya da kafafu," Ta faɗa da zolaya.

Murmushi ya sakar mata, "wlh iya yine irin nawa, kinsan ance sabo turken wawa, ɗan hawan ta
da nake yi yasa har na saba da ita.." ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa, A hankali ya samu ya tsaya
kan kafafunsa, murmushi ta yi mashi, "in shigar maka da kujerar ciki?"

"No, bana so Unaisah tasan na samu lafiya, tafi ji da ni Allah, duk in zata ganni ina gungura
kujerar jikinta na 6ari take kamamin ta tura ni.."

Duk da halin damuwar da take aciki hakan bai hana tayi dariya ba, maganarsa ta bata nishadi
ashe lambon ciwo yake ma Unaisah.

Bayan ya shiga sitting room din Chief, Jiki asanyaye ta wuce bedroom dinta, tana kallon
Unaisah da Batool zaune kan rug, sun baza textbooks dinsu da alama karatu take koyawa
Batool, bata bi takansu ba, cikin sanɗa ta wuce don kada su ganta saboda a halin yanzu tafi
bukatar kadaici..



~___________�_____�________________________~

ISOD HEAD QUARTER AT MEETING ROOM..

Meeting Room ba lafiya, tun da suka hallara, Chief ya zabga tagumi da tafukansa biyu, hakan
ba ƙaramin daure musu kai ya yi ba, kiran gaggawa ya sa aka yi musu don su yi meeting, kuma
sun zo ya kasa magana ko kallonsu bai yi ba, cike da ruɗu suke ta kallon fuskar sa, daga
yanayinsa suka fahimci baya jin dadi ganin yadda ya faɗa, kuma akwai wani abu dake
damunsa, duk da sanyin A.c ɗin ɗakin wani irin gumi ne ke keto mashi....Cikin kunnuwanshi ya
tsinkayi muryoyinsu sama sama suna yi mashi magana cikin harshen turanci tamkar raɗa,

"Sir Are you Okay?"

"Sir meke damunka? Baka da lafiya ne"?

"Sir pls, gaba ɗaya mun damu da kai, ka faɗa mana in akwai abun da ke damunka.."

Dafa Kafadarsa Commender James yayi, "Owais, meke faruwa da kai ne uhum?"

Sai lokacin ya ja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya zame tafukansa daga
kan kuncinsa, ya zube hannayensa saman laptop keyboard din gabansa, a hankali ya ɗago da
raunannun idanunsa da suka kaɗa juwar ya bi su da kallo.

Na hannun damansa ne zazzaune kan kujerun dake a gefensa na hagu, daga bangarensa na
dama U.s Armies ne tare da General Noah da Taj, wannan karon hada shi Chief ya yi inviting..

"Owais, mun fahimci akwai damuwa atare da kai, daga yanayin ka muka fahimci baka da
kwanciyar hankali, Pls, in ba damuwa ka faɗa mana mu nema mafita a tare, mun riga da mun
zama ɗaya..." Cikin kulawa General Noah ya yi maganar yana dubansa.

Bawan Allah, kallonsu kawai ya ke yi shi kaɗai yasan meke damunsa, baisan ma tayaya zai fara
yi musu bayani ba! Ya za su ɗauki abun idan suka ji cewa kakansa ne Elder! Ya Ilahi, fargaban
da ya ke yi kenan shiyasa yake ta jin zullumin ya faɗa abun da ya tara su, abun da takaici.

Numfasawa yayi a hankali ya soma magana,

"Abun da ya sa na tara mu anan, saboda in taya mu murnar cigaban da muka samu a binciken
da mu ke yi akan Elders na gidan kurkukun ƙaddara, ina yi maku albishir na gano wanene
shugaban kurkukun ƙaddara..." Zare idanu suka yi cike da tsantsar al'ajabi jin abun da ya ce, ya
basu mamaki matuka don basu taba zaton nesa zata so musu kusa ba...
"Chef ta yaya akai ka gano Elder? Abun da muke tunanin ba zai samu cikin sauki ba....?"
Commender ne ya faɗa da mamaki akan fuskarsa..

General Noah ya ce, "Amma dai ka shammace mu Chief, ka yi matukar bamu mamaki..." Ya
faɗa da murmushi akan fuskar.

kwata kwata basu lura da yanayin sa ba, Taj ne kaɗai ya fahimci babu lafiya, aransa ya ayyana
zai yi wuya in ba wani nashi ba ne Elder, duba da yadda ya rame ga damuwa tsantsa akan
fuskarsa, hakan yasa bai nuna farin cikin sa ba..

"Sir, ba dan daga bakinka na ji maganar nan ba, da sai na ce ba gaskiya bane, saboda na
razana da jin ka gano mana tantirin dan ta'addan nan, amma tayaya ka gano sa? Kaina ya
kulle, banyi zaton zamu iya gano sa ta cikin sauki ba.." CI ne ya fada..

COO ya ce, "Allah yasa ba mafarki nake ba, Chief pls ka fada mana wanene ɗan iskan mutumin
nan uhum? Wani shegen ne? Wlh na ƙosa na ji harna fara tunanin azabtarwar da zamu yi
masa, kai mutumin nan ko kotu ba zamu kai shi ba, saboda bana tunanin zasu iya yanke mishi
hukuncin da ya dace, mu zamu haɗa baki mu murkushe ɗan iska a cikin cell, But, sir sauran
Elders din fa?"

Wani raunannan kallo ya ke binsu da shi, sai farin ciki suke yi suna ɗurawa Elder ashariya basu
san grandpa din sa ba ne, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji wanene Elder din sai tambayar shi
suke yi yayi shiru yana kallonsu,

Agent Zahra ya ce, "Zan so inga idon azzalumin mutumin nan, ƙarya ta ƙare masa, ko ya zaiji
idan muka ɗamke sa, amma kuna tunanin kamasa zaiyi mana sauƙi kuwa? Tun da basa jin
makamin mu, zai iya amfani da tsafi ya 6ace..." Ya faɗa da damuwa akan fuskarsa..

A hankali Chief ya dubi Taj dake ta kallonsa, ruwan hawayen da ya gani kwance a cikin idanun
Chief ya ɗaga hankalinsa, girgiza mashi kai ya ɗan yi alamar kada ya karaya, cike da damuwa
ya yamutsa pink lips dinsa tare da cizon lower lip din da hakoransa.

Cike da rashin kuzari ya miƙe daga kan kujerar da yake ya fuskance su tare da zuba
hannayensa cikin aljihun wandonsa, gaba daya suka bi shi da kallo a ƙagare da son jin me zai
ce.


Nauyin haɗa idanu da su ya ji, a hankali ya fito daga gaban kujerar ya juya masu baya lamarin
ya ɗaure musu kai,

Ya ji zafi aranshi fiye da zafin ƙunar wuta, surutan da suka yi akan kakansa sun ta6a zuciyarsa,
ina ga kuma sauran al'umma idan komai ya fallasu, Allah kaɗai yasan cin zarafin da za a yi
musu.

Haƙiƙa Baba Obie ya cutar da su, ya ja musu zagi da cin mutunci a idon duniya, sai da ya yi
silar ɗaukakar su tukunna ya tarwatsa darajar su..

Gwauran numfashi ya ja, cikin karyayyar murya, mai matukar rauni da ƙarfin hali ya furta, "Ina
baku haƙuri da abun da zaku ji daga gare ni, I'm really disappointed, an karya min zuciyata,
zallumi da fargaba ne suka hana in sanar da ku tuntuni..."

A ruɗe suke kallon kallon a tsakaninsu, nan take ransu ya fara basu kodai na jininsa ne Elder
ɗin? Wataƙil cikin uncles ɗinsa ne, kwata kwata ba su kawo ma ransu zai zama kakansa ko
mahaifinsa ba.

"Kada ka ji komai Owais, ka faɗa mana zamu fahimce ka.."

Commender james ne ya faɗa..

Cikin rawar murya ya ce, "Ba mahaifina bane, Ba kuma cikin Uncles ɗina bane, amma wanda
ya yi silar zuwan su duniya shine Elder shugaban Kurkukun ƙaddara...."

Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, Tunkan ya ƙarasa maganar A kiɗime suka zabura tare
da miƙewa tsaye, a lokaci ɗaya suka ɗaura hannayensu saman kawunansu, Idanunsu azazzare
cike da tashin hankali haɗi da al'ajabin da ya kamasu! Lamarin ya gigita su.

Duk da sanyin A.c din dake ratsa fatar jikinsu hakan bai hana gumi wanke gaban goshin su ba,
wlh sun karaya matuka, Hankalin maza ya tashi.

A sukwane General Noah ya zame hular kakinsa dake a kansa ya kifa ta saman table dinsa..

A dabarbarce Commender James ya furta, "Owais, kana cikin hayyacinka kuwa? Kasan me
kake faɗa? Ko ka sha giya ne uhum? Kakanka fa ke nan, Kana nufin Obinna, anya ka yi bincike
da kyau? Ta ya ma hakan zai yiwu?"

Girgiza kai CI yayi cike da takaici ya ce, "Sir am sorry to say da wani ne ya faɗamin maganar
nan Allah sai ya ci na jaki, Hakan ba zai ta6a yiwuwa ba, ba gaskiya bane, Baba Obie bazai
aikata munanan ayyukan nan ba, Owais ka bani mamaki, ban taba zaton zaka iya furta wannan
maganar akan kakan ba, kafi mu sanin wanene shi, amma ko mu kanmu da muke abokanka
mun yi imanin baba Obie bashi bane Elder, Mutumin mai kyawawan halaye da tausayi irinsa
bazai iya aikata abun da Elders suke yi ba...

"Ni dai danasan zaka fada mana wannan almaran da ba abun da zaisa in halarci meeting ɗin
nan, sai dai ka yi hakuri Chief amma yau ka 6ata min rai, ka ce Elder ne kakan ka, Wanda ya
haifi baba, gaskiya sir kwakwalwarka bata aiki yadda ya dace kana bukatar a duba ka.." Coo ne
ya fada tare da zame glass din kan fuskarsa ya zaro hanky yana sharce gumin dake tsastsafo
masa.

Kasa juyowa ya yi ya fuskance su, baisan taya zai yi musu bayani ba, baba Obie ya cuci kansa
ya yaudari mutanan da suka yarda da shi, gayanan duk wanda aka faɗamawa sai anyi da
gaske kafin ya yarda..

Taj Tuni hawaye sun wanke fuskarsa, dama saida ranshi ya bashi hakan, wata irin karaya ya ji,
baba Obie ya bashi mamaki, ba tun yanzu ba ya jima yana al'ajabin dukiyarsa da ɗaukakar
ahlinsa ashe bana Allah da Annabi bane, haƙiƙa bai kyauta ma rayuwarsu ba, ya zalunce su
wata shari'ar sai A lahira...
"Tun da nake daku na taba yi maku ƙarya? Mutumin nan kakana ne nafi ku sanin wanene shi!
Miye ribana in na mashi kazafi? Tun da na ce maku shi ne ku yarda kawai, kakana ne Elder!"

Ya faɗa cikin shesshekar murya ba tare da ya juya ya fuskance su ba,

Wannan karon kusan suman tsaye suka yi saboda sun fara karaya da maganarsa jin kamar
yana shesshekar kuka...

"Ba shaye shaye na yi ba, da hankalina da tunanina, Ni ba mahaukaci bane, ba kuma kazafi na
yi masa ba, zan sake maimaita maku, Kakana Obinna shine Elder, azzalumin da ya ke azabtar
da rayuwar yaran da ba su ji ba basu gani ba a gidan kurkukunsa, mutumin da muke nema
ruwa a jallo, ashe daga tsatsonsa na fito, ban ga laifinku ba da kuka kasa yarda da maganata
saboda muma lokacin da muka ji hauka ne kaɗai bamu yi ba, na yi fatan ace ban kai wannan
lokacin a raye ba, gaba ɗaya mun yi danasanin kasantuwar mu jininsa, amma ba yadda zamu yi
haka Allah ya ƙaddara mana, Allah yana fitar da rayyayye daga jikin matacce, Ga misali nan
akan mu, Kakanmu gurbatacce ne, mai fuska biyu, mu kuma ba haka muke ba, gaba ɗaya
uncles dina da mahaifina babu sa hannunsu a ciki, hasalima basu taba jin wani abu mai suna
kurkukun kaddara ba, a ranar da asirin ya tonu, abun ya daure mun kaina, sai na ga kamar ban
ma taba sanin shi ba saboda na ji abubuwa game da kakana wanda ni ko iyayenmu babu
wanda ya taba sani..."



Jikin taƙaura fa ya yi la'asar, tuni annurin fuskokinsu ya ɗauke duff kamar basu taba dariya ba,
zuciyarsu ta karaya, ga baƙin cikin da ya mamaye su, hankalinsu ya tashi, har basu san sa'adda
suka cire hulunan kakin da ke akansu suka ɗaɗɗaura su gaban table ba, a ɗimauce suka koma
kan kujerun suka zauna tare da sadda kansu ƙasa..
Har tsawon mintuna ashirin cuf babu wanda ya furta kalma daga cikin su saboda matsananciyar
damuwar da suka shiga, kwata kwata meeting din yau bai yi musu dadi ba, saboda jin abun da
basu taba zata ba, basu ji dadin maganganun da suka faɗa akan kakansa ba, wannan ne karo
na biyu da suka ga raunin Chief, ranar da Danish ya faɗa rijiya da kuma yau, wlh sun tausaya
masa sosai, sun ma ga kokarinsa da ya iya jurewa in wani ne tuni zuciyarsa zata buga ya mutu
ko ya halaka kansa saboda baƙin ciki..


Miƙewa Commender ya yi ya nufe shi tare da ruƙo hannunsa ya juyo da shi, hankalinsu ya tashi
da ganin siraran hawayen dake zarya kan kuncin sa.

_Zaunar da shi kan kujera Commender ya yi, tare da zaro Hanky ya share mashi ƙwallar shi,
mikewa sauran suka yi gaba ɗaya suka kewaye sa duk da raunin da suka yi hakan bai hana su
ƙarfafa zuciyarsu gurin lallashin shi da bashi baki akan ƙaddarar data same su, babu wanda bai
tofa albarkacin bakinsa ba gurin kwantar masa da hankali, su ka ce ya yi hakuri ya jure radaɗin
da ya ke ji, sun san abun da ciwo, dole zai shiga mawuyacin hali amma ya yi hakuri, kada ya ji
komai su masu fahimtar shi ne, tabbas su kansu sun karaya sun kuma razana da jin cewa
kakansa ne, amma ya zasu yi babu wanda ya isa ya canza abun da Allah ya riga ya kaddara
faruwarsa, wlh saboda tausayin da ya basu da suna da halin da zasu cire mashi damuwar shi
da ba abun da zai hana su yi hakan kodan su sauƙaƙa mashi radadin da yake ji, amma ba zasu
bar shi ba, zasu kasance a tare da shi, No matter what, shi Chief dinsu ne na har abada, su sun
yarda da shi fiye da yadda suka yarda da kansu, don haka kada ya ji komai, laifin kakansa ba
zai taba shafarsa da ahlinsa ba, zasu tsaya masu tsayin daka don ganin basu tozarta a idon
duniya ba, bashi kadai zai yi fadan ba, ya sani yana da su zasu taya shi yin fighting ɗin duk
wani wanda yayi yunkurin cin zarafin ahlinsa ta hanyar amfani da abun da kakansa ya aikata!
Bayan haka basu san rauninsa, yana ɗaga masu hankali, abun da suke so da shi ya yi ƙoƙarin
cire damuwar da ke aransa, saboda zata iya haifar masa da rauni wanda kuma hakan faduwa
ne a gare su, sun san Chief ɗinsu jarumin namiji ne, mai dakakkar zuciya, kuma mai tawakkali,
basu so ya canza daga yadda ya ke a da, ya sawa ransa cewa zai iya, ya manta da cewa
kakansa ne Elder, ta haka ne zai kore damuwarsa har su samu su ƙarasa aikin su."_

Maganganu masu daɗi da ƙarfafa gwiwa suka gaggaya masa har saida
ya ji karfi a jikin shi, sun faranta ranshi, kuma dama abun da ya kamata kenan idan mutun ya
shiga wani hali a tausaya masa, a ja shi a jiki, bawai a dinga cuzguna masa ba saboda wata
ƙaddara ta same shi, wasu har daɗi suke ji su dinga bullying ɗinka don su baƙanta maka rai, su
ja depression ya kama mutun daga haka har ya lahanta kan shi, wa'iyazubilla..
Tun suna share mashi ƙwallar da ke gangarowa kan kuncinsa har ta kai ga sun fara tsokanar
shi, baisan sa'adda ya fara sakin murmushi ba, saboda dadin da ya ji har godiya ya yi musu, su
ka ce kada ya damu hakkinsu ne su bashi kulawa, yanzu tunda sun fahimci ba ya jin dadi yana
bukatar ya ga likita saboda lafiyarsa, don haka zasu ɗaga meeting din, zuwa lokacin da zai ji
sauƙi.


Ya ce masu bai ƙi shawarar su ba, amma bazai yiwu a ɗage meeting ba, akwai muhimman
abubuwan da yakamata su tattauna akai idan ba haka ba zasu iya fuskantar matsala,
hankalinsu ya tashi da jin hakan, suka ce tun da haka ne, zasu tafi hutun awa uku saboda sun
damu da lafiyarsa suna so ya huta...
A cikin yan mintuna suka kira Isod docs suka bincika lafiyarsa anan cikin medical room ɗin su,
bayan sun tabbatar da ciwon dake damunsa ya gargaɗe su akan kada su faɗa musu
sakamakon saboda baya son kowa ya sani...

Lokacin da suka koma zaman meeting din, ba laifi sun ga ya ɗan saki jikinshi da walwala akan
fuskarsa, A tsanake ya fayyace musu komai da ya faru bayan zuwan Khala..

Sun yi matukar mamakin jin cewa kakarsa ce, kuma Obie ne ya yi ƙaryar mutuwarta ya kai ta
kurkukun kaddara, duk ba wannan ba, abun da ya basu haushi da takaici abun da Pravin ya
aikata, ashe shima Elder ne na gidan kurkukun kaddara, lallai Obie Family sun haɗa giggan ƴan
ta'adda acikin su.
Bayan sun taya shi murnar ganin grandma ɗinsa, da jimamin abun da ya faru da familyn sa
Commender James ya ce,

"Yanzu ta ya za'ai mu iya gano sauran Elders? Kana ganin grandma ɗinka zata iya samun sauƙi
nan kusa!" Girgiza kai ya yi, "Bakowa ta sani a cikin su ba, yanzu haka da ita da aunt ɗin nawa
an kwantar da su asibiti basu san inda kansu yake ba, amma suna samun kulawar likita.."

"Me zai hana mu tuntubi shi Elde...Au, afwan sir grandpa nake so na ce,..." murmushi chief ya yi
tare da kallon CI da ya yi maganar. "Duk yadda ma ka faɗa daidai ne CI, already na yi masa
magana akan ya fada mun sauran Elders din amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login