Showing 12001 words to 15000 words out of 18747 words
Chapter 5 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf
in yi saboda nasan mugun halinta na kishi wlh tsaf zata kashe ki, ni
banma san wani munafukin bane ya kulla maki makirci, na so inji da wa ta ke yin wayar, ina jin
alamun ta gama yin wayar na ma fasa canza kayan, jiki na na kerma na baro dakin nata, na
nufo ɗakin ki don in faɗa maki abunda ke faruwa, shigowata keda wuya ina kokarin in tashe ki
na ganki a kudundune cikin bargo, kwatsam na jiyo muryar hajiya Saratu daga waje tana
tambayar maids ina ne ɗakin ki? da sauri na la6e bayan labule ina jira inga me za ta yi maki,
tana shigowa ɗakin ta nufi gadonki hannunta ruƙe da poison..."
Dafe kirji Hajjaty ta yi jikinta ya hau 6ari, daɗi ya ji acikin ranshi ganin ta fara yarda da
maganarshi..
"Ji nayi bazan iya bari ta cutar dake ba saboda nasan ba imani gare ta ba, saboda tashin
hankali banma san lokacin dana yi wuff na fito daga bayan labulen ba tana jin motsi na ta juyo
mu ka yi ido biyu, ta ware baki zata fasa ƙara na shaƙeta tana ta sambatu tana faɗin maciya
amana, zarginta ya tabbata akanmu, wlh saita kashe mu, da na ga ta turje ta ƙi saurarena kawai
saina sumar da ita, na sungumeki na bar estate ɗin da ke, don nasan muddin ta farka kwanan
mu ya ƙare..."
Cike da damuwa Hajjaty ta ce, "Banji dadi ba, amma koma wanene ya ƙulla mana makirci Allah
ya isa tsakanin mu da shi, mutane basu tsaron Allah. Amma hajiya Saratu bai kamata tana
daukar zigar wani ba, ko da ya ke dama ta tsaneni, tasha faɗamin saita raba ni da gidan
ubanta, amma bansan tsanar da ta yi mini ta kai har haka ba, kuma dama kwanaki ko hanya
bata son haɗawa da ni, abinci ma indai ni na dafa bata cin shi.."
Pravin ya ce, "Hmmm, ɗan adam fa ba abun yarda bane, indai ka biyewa mutane zasu kaika su
baro ka, kuma dama bata sonki ta sha saka ki kuka, ta ƙuntata maki saboda tana jin haushin
zaman da kike yi agidansu, ni kaina da nake mijinta bata ƙyaleni ba, kullum saita goranta mini
saboda ina zaune gidan ubanta. Saratu bata da wayau, sakarya ce, kwata kwata bata da halin
kirki, zaman hakuri kawai nake yi da ita, amma ni kaina ba sona ta ke yi ba, wahalar da ni ta ke
yi, taita juyani son ranta." Yana magana yana yamutsa fuska,
"Amma pravin meya kamata mu yi yanzu? Ni ina ga kawai mu je mu basu haƙuri mu faɗa masu
gaskiya, In ba haka ba za su mana kallon mutanan banza kuma maciya amana.."
Waro idanunsa ya yi, "Ke! Kina hauka? Tab lallai, ay wlh muddin muka koma estate din nan sai
sun hukunta mu, sai ka ce kin manta irin yadda baba Obie da yayyanta suke ji da ita?
"Pravin, koma me zai faru mu ne masu laifi, mutanan nan sun yi mana hallaci, sun yarda da mu,
tsawon shekara da shekaru muna rayuwa acikin su basu ta6a gudun mu ba, amma mu muka ƙi
fada masu alaƙar dake atsakaninmu, bamu kyauta ba, kuma nasan zasu fahimce mu in har mu
ka je muka basu haƙuri muka kuma faɗa masu akwai aure a tsakanin mu za su yafe mana,
koda hajiya Saratun bata yarda ba nasan za su yi ƙoƙarin sasanta mu da ita, tun da su din
mutanan kirki ne suna da hankali da kuma tausayi...."
Bata ƙare maganar ba ya tari numfashinta da cewa, "Hmmm, na lura har yanzu baki san halin
hajiya Saratu ba, nasan mutanan kirki ne amma wlh akan Saratu zasu iya komai, kin manta
labarin dana baki lokacin da ta zo da ni don inga danginta? Ƙiri ƙiri suka nuna basu sona sun
tsaneni saboda ni ba jinsin su bane, kuma bani da asali da arziki irin nasu, a lokacin ba don
baba Obie ya goya mini baya ba ai da basu bani auranta ba..."
Dafe kai ta yi da hannu ɗaya, "Me zai hana mu tuntu6i baban toh? nasan zai taimaka."
"Har yanzu kin ƙi fahimtata, nifa bazan ci gaba da zama ƙasar nan ba, saboda hajiya Saratu ba
zata raga mana ba, ƙwara mu tattara yanamu yanamu mu tafi, don yanzu haka nemanmu suke
yi ruwa ajallo don su hukunta mu.."
Maganarsa ta ɗaga hankalinta, da damuwa ta ce, "Pravin meya kawo maganar barin ƙasa? Ka
san me kake faɗa kuwa? Ina zaka kai ƴa'ƴan naka da matarka? kaima kasan wannan bamai
yiwu bane, kawai saboda asirinmu ya tonu sai mu gudu kamar waɗanda suka aikata wani
mugun laifi...?"
dafe kanshi yayi da hannu ɗaya baisan tayaya zai shawo kanta ba..
"Pravin ka daina wannan maganar, ba zan ta6a baka shawarar ka tafi ka bar iyalinka ba, bamu
aikata laifin daya kai har mu gudu ba, kawai kuskuren mu shine ƙarya da muka yi masu tun
farko muka boye masu gaskiya, in har muka nemi yafiyarsu bayan mun faɗa musu komai wlh
zasu yafe mana Pravin, mun shaƙu da mutanan nan, mun saba da zama cikinsu, sun zama
kamar danginmu da muka rasa! Sun ɗauki nauyin komai namu Pravin, wlh idan muka gudu
baza su ji dadi ba, zasu ga kamar dama da wata manufa muke atare da su shiyasa bayan mun
samu abun da muke so muka tafi, kai baka tunanin halin da ƴa'ƴanka da matarka za su shiga?
Wai kuwa Pravin anya kana jin kanka amatsayin ubansu..."
bata ƙare magabar ba ya toshe mata bakinta da yatsan shi..
Ta rasa meyasa take ji aranta kamar pravin ba gaskiya ya fada mata ba! Saboda yanayinsa da
kuma maganganunsa abun tuhuma ne! Kawai saboda ƙaramin laifin da bai kai ya kawo ba sai
ya gudu ya bar iyalinsa?
Ganin kamar ta fara ɗago shi ya sa shi saurin daidaita nutsuwarshi cikin sanyin murya ya ce,
"Na gane kuskurena, kawai bana so ta cutar dake ne shiyasa na yi wannan maganar, amma ba
har cikin raina ba, ni ba zan iya tafiya na bar iyalina ba, banma san na fada ba, ki yi haƙuri idan
na 6ata maki rai.." Ajiyar zuciya ta sauke, "Yanzu da yaushe zamu je estate din mu nemi
yafiyarsu?"
"Me zai hana mu bari sai an kwana biyu, lokacin da suka yi kewarmu, koma suka neme mu da
kansu don su ji ba'asi sai mu je mu faɗa masu gaskiya,..."
ta aminta da maganarsa saboda a halin yanzu tasan jiran su suke yi.
"Na yarda, amma tayaya zasu neme mu? Bayan babu waya gaba ɗaya mun barsu agidan.."
Yamutsa fuska ya yi, "Kash, sam na manta, amma akwai waya da na siya, nama yi mana hada
siyayyar kayan abinci, da duk wani abu da zamu bukata.."
"Pravin basu da layin da zasu tuntubemu a yanzu."
"Karki damu, ki bari da kaina zan je estate din, in faɗa masu komai in sun hakura suka yafe
mana zan sanar da ke komai." Ta ce, "Toh Pravin, yaushe zaka je ne?" A takure ya yamutsa
fuska, kwata kwata bai son tana yi masa maganar Obie estate, da tasan masifar da suke a ciki
da bata ƙara marmarin ambaton ko da sunan estate din ba.
"Ƙarshen satin nan." Ajiyar zuciya ta sauke, "Toh Allah ya kai mu, amma dan Allah ka kwantar
da hankalinka, bana so in gan ka a cikin damuwa, addu'a yakamata mu yi Allah ya sa abun ya
zo da sauki su yafe mana." Jinjina mata kai ya yi batare da ya furta kalma ba. Ta yi tunanin
hajiya Saratu ce damuwar shi batasan mugun abun da ya aikata ba.
Ruƙo hannunta ya yi, "Mu je in taimaka maki ki yi wanka, yau kwana huɗu jikinki baiga ruwa
ba." Bata musa mashi ba ya ɗauke ta kamar jinjira ya nufi toilet da ita, after mins ya futo dauke
da ita, ta yi ɗaurin ƙirji da towel, ya kwantar da ita kan gadon shi.
Juyawa ya yi ya nufi closet tabi bayanshi da kallo tana mai ƙara jin kaunarsa saboda kulawar da
ya ke bata.
Dawowa ya yi hannunsa ruke da riga da wando na shan iska, tun ranar da ya kawota nan ya
siya masu kaya kala uku uku..
"Za ki iya sakawa ko in taimaka maki?"
Murmushi ta sakar mashi, "Bana so kana wahala, na lura hada damuwar ciwona ke damunka,
kada ka damu zan ji sauki in sha Allah..." Murmushin yaƙe ya yi mata..
Bayan ta kar6i kayan ya fuce daga ɗakin, shiru bai dawo ba, saukowa ta yi daga kan gadon,
bayan ta kammala zura kayan a jikin ta, ta je gaban mirror tana kallon kanta.
Zuciyarta cike fal da kewar Ahlin Obie, ita dai ta kamu da ƙaunarsu tun farko, kuma ba ta jin
zata iya rabuwa da su ko da hajiya Saratu zata hukunta su ne, ta ji zata zuƙunna kan
gwiwowinta ta roƙeta akan tayi hakuri ta yafe su.
Bakomai tafi ji ba face halin da ƴa'ƴansu za su shiga idan suka rabu.
Can kuma ta canza akalar tunanin nata, ta fi jin kewar aminiyarta akan komai, ta so ace akwai
waya a hannunta da ba abun da zai hana ta kira Turai ta faɗa mata halin da suke a ciki tasan
zata fahimce su kuma zata taimaka masu..
Body oil ta shafa ma skin dinta ta dauko comb ta sharce gashin kanta dakyar dakyar saboda
yawanshi ga tauri da ya yi ga kuma jikinta ba ƙwari..
Jin shiru pravin bai leƙo ba ya sa tayi tunanin ko ya fita daga gidan ne.
Hakan ya sa ta miƙe daga gaban madubin ta fito ta shiga falo, ɗan madaidaici ne ya haɗu sosai,
Pravin ya daɗe yana kokarin jan hankalinta da ta dawo gidansa da zama ta ƙiya saboda bata
son rabuwa da obie estate...
Idanunta ne suka hango mata bag ɗinsa da ya ajiye kan sofa, sakamakon jefar da ita da ya yi
lokacin da ya shigo har ta buɗe abubuwan dake a ciki sun zubo waje..
Buhun ta nufa ta soma buɗe shi, ba komai ne a ciki ba face kayan abinci, komai da zasu buƙata
ya siya masu, murmushi ta yi tare da miƙewa har zata juya idanunta suka sauka akan
passports dake ajiye kan hannun kujera.
Zuwa ta yi gaban kujerar, ta kai hannu ta curo Passport din da ta gani, shiru ta yi jim tana
duddubasu aranta ta ayyana me Pravin zai yi da passports dinsu?
Bata kawo komai ba a ranta ta mayar da su cikin jakar ta yi zipping dinta, ƙamshin suya ta fara
juyowa a cikin hancinta, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta jin motsin shi
Direction din da take jiyo motsin ta nufa, dadi kamar zai kashe ta ganin pravin yana girka mata
abinci, daga shi sai short a jikin shi, ya haɗa gumi sai aikin motsa suya yake yi...
Kamshin naman ne ya daki hancin ta, cikin sanda ta shiga ciki ba tare da sanin shi ba saboda
ya bata baya.
Hugging dinsa tayi ta baya, wata firgita da ya yi saida ta yi noticing wani abu,
"Waw.. waye...! " Ya faɗa tare da ɗaga ƙaton spoon din hannunsa da niyyar ya kwaɗe wanda ya
ruke sa..
Ajiyar zuciya ya sauke ganin Hajjaty ce,
"meyasa baki yi min sallama ba?"
"Saboda in baka tsoro." Ta faɗa da murmushi..
"Hmm, zan rama ne Allah."
"Ki koma daki pls, har yanzu babu ƙoshin lafiya atare dake, idan na gama zan kawo maki a
daki."
Maƙe mashi kafaɗa ta yi, "Kaima kasan bazan bari kana yin aikin da ya kamata ace ni zanyi ba,
in har ba zaka bari in taya ka ba, to ka bani in ƙarasa tun da jikin nawa da sauki."
Dakyar ya lallabata har ya samu ta koma falon ta zauna.
Bada jimawa ba ya fito hannunshi ruke da tray, daga saman shi plates ne na chicken pepper
soup, da na shinkafa, ga juice a glasses.." Tunkan ya karasa ta fara haɗiyar yawu..
A saman rug ya a je tray ɗin ta sauko ta zauna shima ya zauna suka tasa tray din a tsakiyar su..
A tare suke ciyar da juna, idan ta bashi a baki shima sai ya bata...
Suna ci suna fira, duk ta ishe shi da santi..
"Da ka yi mini girkin nan har ka tuna min lokacin da muke a gida, kafin mu yi aure, ni dai na yi
dacen ɗan uwa kuma yayana sannan mijina, tun ina ƙaramata kake kula da ni baka ta6a
gajiyawa ba, ci na, suturata, da duk wata ɗawainiyana kaine, baka ta6a bari na da yunwa ba,
koda kai zaka rasa toh zaka nema min ni in ci..." Idanunta cike tab da ƙwalla ta yi maganar.
Jikinsa ya yi sanyi lakwas.
_"Dan Allah Pravin no matter what, kada ka canza daga yadda na sanka, ka ji tsoron Allah ka
kuma kiyaye sa6a masa, da ka zalunci wani ƙwara kai azalunce ka saboda Allah baya yafe
hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, ka kau da ido ga abun da ba halal dinka ba, ka yi haƙuri
da abun da Allah ya baka. Duk abun da ka samu shine rabonka, ita duniyar nan ba matabbata
bace, wata rana zamu mutu mu barta ne, lahira ita ce matabbata kuma dawwamammiya, mu
ruƙa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari, daga kai sai halinka za a binne ka, komai da muka tara
anan zamu bar shi, kowa zai girbi abun da ya shuka, walau na alkhairi ko na sharri...."_
Tun da ta fara yi masa nasihar jikinsa ya soma 6ari, zuciyarsa ta ƙuntata sosai. Bai ƙarasa
sauraronta ba ya miƙe kamar zararre ya nufi daki, yana shiga ya faɗa kan gadonsa ta rubda ciki
ya kwanta..
Da gudu ta bi bayan shi, ta hau kan gadon tana tambayar shi me ya faru? Meke damun shi? Ko
nasihar da ta yi masa ne bata yi mashi dadi ba...
Cikin karyayyar murya ya ce baya jin daɗin zuciyar shi bacci yake so ya yi, saukkowa ta yi daga
kan gadon taje gaban mirror ta dauko tissue box, yago tissue din ta yi, ta koma kan gadon ta
soma goge masa hannayensa da bai wanke ba, bayan ta gama ta daura box din saman
drawer..
Rungume kanshi a ƙirjinta ta yi, tana jin yadda zuciyarsa ke harbawa fat fat kamar zata tsaga
ƙirjinshi. Ta ruɗe da ganin yadda ya razana daga kawai ta yi masa nasiha, sai dai bata kawo
komai aranta ba, a haka bacci ya yi awon gaba da su.
Luxury-incense By Sapnah Borno.
Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da
kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika
zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na
shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da
Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika
akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki
jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada
turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba
kada ku bari ayi babu ku.
Wardrobe balls
Kabbasa spray
Chadian khumra
Hawee
Halud
Gabgab
Sandal sukkariya
Kajinguru
Dilka soap
Ready to use dilka
Karkar oil
Turaren tsuguno
Habil
Dorut
Dorot after period
Brown khumra
Dufr khumra
Body milk
Sudanese kuleccam
Chadian dufr kuleccam
Musk khumrah.
Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada
maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko
maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk
garin da take
Our Chadian aphrodisiacs are.
Beejay fire
Sata jagab honey
Wetness and sweetness combo
Daka
Great A sabaya
Breast engagement powder
Ciccibi
Gumbar madara
Gumbar dabino
Bita Zaizai
08093772168
*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya
ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta
wannan number din 08103884440*
~________________________________________✍️~
Luxury-incense By Sapnah Borno.
Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da
kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika
zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na
shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da
Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika
akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki
jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada
turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba
kada ku bari ayi babu ku.
Wardrobe balls
Kabbasa spray
Chadian khumra
Hawee
Halud
Gabgab
Sandal sukkariya
Kajinguru
Dilka soap
Ready to use dilka
Karkar oil
Turaren tsuguno
Habil
Dorut
Dorot after period
Brown khumra
Dufr khumra
Body milk
Sudanese kuleccam
Chadian dufr kuleccam
Musk khumrah.
Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada
maganin karin girman