Showing 18001 words to 18747 words out of 18747 words
Chapter 7 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf
mike a kidime jin ƴarsa da ya binne Uncle Musa
ne ya dauke ta, yama kasa magana sai zazzare idanunsa ya ke yi gaba ɗaya ya ruɗe, nan ta ke
ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru a baya, lokacin da ya je ya tone
ƙabarinta ya ga ƙasusuwa saida ya yi zargin wani abu, just in two weeks da ya binne ta har ta
zama ƙashi, bayan haka ya daɗe yana ji aranshi tana a raye saboda bai ta6a mafarki da ita a
mace ba, Ya Ilahi! Yanzu ya gane komai.
Jirin tashin hankali ne ya ɗebesa yayi taga taga zai kife, Alhaji ubaid ya yi saurin miƙewa ya
tallabo shi, tare da rungume shi kan kirjinshi, kukan baƙin ciki ya fashe da shi kamar ranshi zai
fita, tuni zazzabi da ciwon kai sun kama shi.
Sheikh Imam ya ƙara shiga damuwa daga shi har Aisha jin rashin imanin da Uncle musa yayi
ma Benazir saboda kawai ta nemi ta tona masa asiri don ta ƙwatarwa Aisha hakkin ta.
Cikin shesshekar Kuka Hajiya layla ta dinga ɗura mashi ashariya tana tsine masa albarka,
dama da ƙiyayyarsa aranta, bata ta6a son shi ba, kwata kwata baya burgeta saboda izzarshi, ta
tsane shi ta tsani komai nasa.
Ƙwallar bakin ciki ce ta cika idanun Alhaji Ubaid, cikin rawar murya yake ambaton duk wata
addu'a da ta zo bakinsa don ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa.
Abie da ke zaune a gefensa dafa kafadarsa ya yi batare da ya iya furta kalma ba, kowa ya
razana da jin abun da Musa ya aika ta.
Babu wanda zuciyar sa bata karaya ba..
"Har yanzu baku fayyace mana komai ba, Ina so in san wace irin sadaukarwa ce Musa ya yi da
yarinyar Shureim da kuma yarinyar Benazir? suna a raye ko sun mutu?"
Cike da fargaba Abie ya yi tambayar, saboda yana son yasan in duk a tare suke da ɗan Iya.
Shiru su ka yi saboda basu da amsar tambayar da zasu ba Abie.
_Taj Ka faɗa masu komai, yanzu lokaci ne da kowa yakamata yasan gaskiya, Illa iyaka kowa ya
yi hakuri da abun da zai ji_
Zuciyarsa ce ta raya ma shi.
Gyaran murya ya yi hankalin kowa ya dawo kan shi.
falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, baka jin sautin komai sai na muyar Taj dake basu labari..
Ya fara ne daga kan labarin leƙen asirin da suka yi wa matsafa shi da Uzair, rabuwarsa da
Unaisah da hannun da kowan nan su ya faɗa, Alherin da Chief Owais ya yi masa da kuma
haɗuwarsa da ƴarsa bayan shekaru..
Lokacin da ya fara basu labarin gidan kurkukun Ƙaddara, saida suka yi danasanin jin labarin
shi, saboda matsanancin tashin hankalin da suka shiga, sun ruɗe sosai, sun razana, zuciyarsu
ta tsinke da jin irin azabtarwar da ake yi wa yaran da basu ji ba basu gani ba. Babu wanda bai
share ƙwalla ba acikin su, kuka ne ya kubcewa Benazir da Anila kamar ransu zai fita, Hatta
Hajiya Layla da Mami saida suka yi kuka na fitar hayyaci, shi Alhaji Ubaid ma kukan zuciya mai
radadi ya kama yi, shi da Abie, musamman da ya zo kan labarin Unaizah abin ya ta6a zuciyoyin
su.
Jin abun suke kamar ba a gaske ya ke faruwa ba saboda ruɗun da suka shiga.
Bayan ya ƙarasa basu labarin, ya juya ya nufi sitting room din Chief ya ɗauko diary din Unaizah
wanda tun shekaran jiya da ya shiga ɗakin ya gan shi akan table.
Bayan da ya dawo hannunsa ruƙe da diary din, ya Miƙa masu ya ce yana so kowan nan su ya
dubi hotunan dake a cikin diary din da kyau.
Alhaji Ubaid ya fara mika mawa hannunsa na kerma ya kar6a tare da bude shafin farko, wata
zabura ya yi ya mike a firgice yake tambayar diary din wanene? Mai ya kawo hoton Musa da na
ƴarsa Zeenatu a cikinsa.." Da jin wannan maganar yasa Benazir ta mike cike da rashin kuzari ta
nufe shi, hajiya Layla ma tuni ta mike tana leƙa hoton ta furta, "Kai! Ai Zeenatu ce wannan! Da
Musan! Me ya kawo hotunansu anan? Wace ce kuma wannan baturiyar?" Ta tambaya a ruɗe.
Kowa sai da ya duba hotunan, bayan da suka gama kallo, Taj ya fayyace