Showing 15001 words to 18000 words out of 18747 words

Chapter 6 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf

27 Feb 2026

407

nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko
maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk
garin da take
Our Chadian aphrodisiacs are.
Beejay fire
Sata jagab honey
Wetness and sweetness combo
Daka
Great A sabaya
Breast engagement powder
Ciccibi
Gumbar madara
Gumbar dabino
Bita Zaizai

08093772168.




~____________________________________í ¼í½í ¼í½í ¼í½~









*Me ya Faru Bayan shigar Sheikh Imam Malik*?

Ko sallama bai yi ba saboda 6acin ran da ya ke ciki, dakatawa ya yi yana tunanin meyasa Taj ya
kira shi a irin wannan lokacin? Menene dalilin kiran nasa? Me kuma ya kawo Alhaji Ubaid da
iyalinsa gidan?"



Yasan dai ba su da wata alaƙa da Chief Owais, zuciyarsa ce ta raya mashi ko dai sun kira sa ne
saboda sun ji komai da ya faru tsakaninsa da Æ´arsa, shiyasa suka kira su Alhaji Ubaid don su
sasanta su.


Ƙunci ne ya mamaye shi, har ya juya zai fuce ya tsinkayi muryarta mai tattare da sautin kuka a
cikin kunnanshi..

"Baba! Dan Allah kada ka tafi, ni nasa ya kira mini kai saboda ina son ganin ka, ina bukatarka a
kusa da ni, ina so na yi magana da kai..."


Jin muryar gudan jininsa ya sa shi dakatawa da yin tafiya, ya manta when last ya ji muryar Æ´arsa
yayin da take kiran shi da sunan babanta.


Ganin bai da niyar juyowa ne yasa ta nufe shi tana kuka ta zube saman gwiwowinta a bayan
shi, ta rurruƙe ƙafafunsa da hannayenta da ke kerma.


Ba zai iya misalta yanayin da ya shiga ba, ya ji wani irin abu da ba zai iya kwatanta shi ba, sam
ya kasa magana.


Shesshekar kukan Aisha ya kashe mashi jiki, ya kuma fama masa raunin dake a cikin zuciyar
shi, shekara goma sha takwas rabon da jikinsa ya haÉ—u dana gudan jininsa, Æ´arsa É—aya tilo da
ya kora daga gidansa tare da jinjira a tsakar dare ba tare da ya yi tunanin wani hannu zasu faÉ—a
ba, akan laifin da bata ji ba bata gani ba, wanda har yau idan ya tuna yana jin baƙin ciki mara
misaltuwa.



Dakyar ta iya miƙewa ta rungume shi ta baya, tare da kwantar da kanta saman kafadarsa ta
zagayo da hannayenta saman cikin shi.


Duk yadda zuciyarta ta kai ga tafarfasa da baƙin ciki sai da ta ji sanyi ya ratsa ta, jin ɗumin
mahaifinta a jikin ta.

Hannayenta da ta ƙanƙame cikinsa da su ya bi da kallo, sai ya rinka tuna ranar da mahaifiyarta
ta haife masa ita, ta damƙa masa amanarta tana atsaka da fuskantar ajalinta, hakika ya ci
amanar malama Batool.


Hawayen da suka cika idanunsa ne suka fara zarya kan kuncinsa.


"Baba! meyasa baka ta6a nemana ba, tsawon shekara goma sha takwas, bakasan irin rayuwar
da na yi ba, hankalinka a kwance ka ke gudanar da rayuwar ka, baka ta6a tunanin wani hali
nake a ciki ba, ina lafiya ko bana lafiya, ina raye ko bana raye, duk da abun da ka yi min hakan
bai hana zuciyata tunanin ka ba, kullum ina sa ran zaka neme ni, amma shiru har sai da na
fidda rai da ina da uba a duniyar nan, ka yi min iyaka da kowa nawa, baba hankalinka a kwance
kake rayuwarka bayan Æ´arka É—aya tilo da kake da ita tana rayuwa a wani wurin, ko har yanzu
fushi ka ke da ni? Baba ka ta6a danasanin abun da ka yi mini? Ka kuwa san halin da kasa na
jefa rayuwata?"



Maganganunta sun karya zuciyar shi, duk yadda ya kaiga jurewa saida kuka ya kubce masa,
jikinsa na kerma ya ruko hannunta tare da zagayo da ita, ya rungume ta akan ƙirjinsa da
hannayensa biyu ya tallabe bayanta.


Komai dake faruwa akan idanun Alhaji Ubaid da iyalinsa, haka zalika akan idanun Abie da
iyalinsa, da kuma Taj wanda ke a tsaye gefe É—aya.

Idanun kowan nan su ya cika tab da ƙwalla saboda tsantsar tausayin Aisha da mahaifinta,
kamar sun samu tv haka suke ta kallon su.


Cikin shesshekar kuka da rauni ya furta, "Ki yafe mini Aisha, hakkinki ne ke bibiyar rayuwata, na
ci amanar mahaifiyarki, na cuce ki na kuma cuci kaina..."

ya É—an dakata yana mayar da numfashi, fuskarsa har kerma ta ke yi.


Daƙyar ya ɗaura da cewa, "Taya zan guji gudan jinina kuma in zauna lafiya? Allah shine
shaidata, wallahi na yi danasani tun a daren ranar dana kore ki na gane kuskure na, bansan
meyasa nayi maki haka ba Aisha! Bana a cikin hayyacina Aisha, bayin kaina bane, ina tsaka da
bacci na farka da tsanarki a zuciyata, na ji kin fita araina, kawai bana son ganin ki, kamar ana
tunzura ni, a lokacin ji nake in har ban kore ki ba zan iya rasa raina, na daÉ—e ina tambayar kaina
meyasa na yanke maki É—anyen hukunci! Bayan nafi kowa sanin wacece Æ´ata, Aisha, bazan iya

misalta maki mawuyacin halin da na shiga ba bayan dana neme ki na rasa, na yi kukan da ban
ta6a ƴinsa ba arayuwata, na tsani kaina, na ƙuntata rayuwata, na ji rayuwar duniyar ma ta sire
mini, mutuwa nakes o kawai na yi, Aisha gidan mahaukata ne kawai ban je ba, amma na yi
haukan rashin ki, har kulle kaina na yi tsawon kwanaki ba asan inda nake ba ba ci ba sha, na yi
rashin lafiyar data yi silar kwantar da ni asibiti, na yi jinya kamar bazan rayu ba, bansan wa ke
akaina ba, saida ta kai ga sunanki kaÉ—ai nake fada a cikin sambatuna, Aisha yanzu haka da
nake maki magana ina da ciwon zuciya, Allah ne bai ƙaddara zan mutu ba, shiyasa na kawo har
wannan lokacin a raye..."


Shesshekar kukan Benazir da Anila ne ya cika kunnuwan kowan nan su.

"Aisha ban manta dake ba, da ke nake kwana da ke na ke tashi araina, addu'ar da nake maki
kullum a cikin sallata ban daina ba, kamar yadda ki ke sa ran zan neme ki nima haka nayi ta sa
ran wata rana zaki dawo ki neme ni, amma baki ta6a tunanin kiyi hakan ba, shiyasa zuciyata ta
karaya na yi tunanin ko kin mutu ne ko kuwa abun da na yi maki ne yasa baki ta6a nema ba..."
Ya É—an dakata yana mayar da numfashi.


"Bani da kwanciyar hankali saboda zullumi da fargaban a wani hali kike a ciki, kullum saina kira
layinki amma ban ta6a samun shi a kunne ba, kuma ban fidda rai ba, kullum addu'ata idan kina
a raye keda jinjirarki Allah ya kare mun ku a duk inda ku ke, Ya zama gatan ku, Ya kuma haÉ—a
ni da ku, idan kuma baku a raye Allah Ya jikanku da rahamarsa, ban ta6a gajiyawa ba da
neman ku, saboda ku na sha zuwa aikin hajji don in yi maku addu'a..."


Kasa karasa maganar ya yi saboda raunin da zuciyarshi ta yi, baiwar Allah ta yi kuka kamar
ranta zai fita, bata taba tunanin ya damu da ita har hakan ba, ta yi zaton yana sane ya yi watsi
da ita shiyasa bata ta6a tunanin ta dawo gida ba tun da bai neme ta ba, ta yi zaton har yanzu
fushi ya ke yi da ita.



Tallabo fuskarta ya yi da tafukan sa, idanunsu da ke tsiyayar da kwalla suka haÉ—u cikin na juna.


"Aisha, saboda ke na ajiye aikina na rabu da kowa nawa, a karshe ma da na yi jiran shiru baki
dawo ba, sai na bar ƙasar ba tare da sanin kowa ba."


Numfasawa ya yi tare da girgiza kansa cike da danasani ya daura da cewa, "A ranar dana fara
ganin ki a gidan nan, wani irin farin ciki mara misaltuwa na ji, kamar anyi min albishir da gidan
aljanna, saboda na ji daÉ—in ganinki da ranki da lafiyarki, duk da na shiga tashin hankali saboda

sauyin da na gani a tare dake, daga yanayin shigarki, na gane kin canza hali, har saida na yi
kokwanton anya Aisha nane?"

Amma saboda jinina dake yawo a jikinki yasa ban musa ba, a lokacin dalilin da yasa ban yi ma
ki magana ba, saboda ina jin kunyarki, kema kuma sai kika nuna kamar baki taba sanina ba,
shiyasa jikina ya yi sanyi, amma bayan na koma gida saboda farin ciki ban iya runtsawa ba,
kwana na yi ina nafilfili don nuna godiyata ga Allah da ya bayyanar min da ke, har so nake Chief
ya gayyace ni don in zo gidan nan saboda kawai zumudin in ganki.. "

komai saida Imam ya fayyace mata na daga halin da ya shiga bayan rabuwar shi da ita.


Bai ƙare maganar ba, Ya saki fuskarta da ya tallabe, ya tattare ƙasan jallabiyar Jikin shi da niyar
ya zuƙunna kan gwiwowinsa don ya nemi yafiyar ta.


Lura da hakan yasa ta yi saurin ƙanƙame shi tana rokonshi akan kada ya zuƙunna mata, ya
bari, kada ya yi, idan ma akwai wanda ya cancanta ya nemi yafiyar wani atsakanin su toh ita
yakamata ta nemi yafiyar sa, yana kuka ya ce mata ta barshi ya zukunna, idan har baiyi hakan
ba bazai ta6a yafe ma kansa ba, koda ta yafe masa, saboda ya dade yana yi ma kanshi kallon
mugun Uba, mara imani, saboda rashin adalcin da bai yi mata ba.
Ta fashe da wani sabon kukan ta ce, "Baba babu yafiya atsakanin mu, abun da ya faru bayin
kanka bane, haka zalika abun da ya faru tsakanina da yaya Shureim bayin kan shi bane, a yau
na ji komai baba. Na ji abun da ya É—aga hankalina ya kuma karya zuciyata, Baba ashe dama
makirci ne aka kulla min saboda a É—auki fansa akanka?"
Kaitsaye maganar ta ratsa kunnuwansu, a ruÉ—e suke kallonta.


Muryarsa na rawa ya furta, "Bangane me kike nufi ba? ki yi min bayani yadda zan fahimta!"

Gajiya ta yi da tsayuwa, hakan yasa ta zauna shima ya zauna yana fuskantarta, yayin da
sauran mutanan dake a falon suke atsaitsaye babu alamun gajiya a tare da su.



"Ke nake sauraro Aisha.." A ƙagare da son ji duk da yana fargaban abun da ya daɗe yana zargi
ya zamana gaskiya.


"Baba, zan faÉ—a maka, amma zan roke ka, dan Allah ka yi min alkawarin zaka jure komai da za
ka ji daga gare ni, kuma duk abun da zan faÉ—a maka ya riga da ya wuce, kuma anyi ne don a
cusa maka baƙin cikin da zai yi silar mutuwarka, sannan kuma a lalata martabarka da ƙimarka,
in har ka tada hankalinka akan abun da za ka ji toh zai yi nasara ne, shiyasa bana so ka sanya

damuwa a ranka, nasan za ka ji raɗaɗin da yafi na ƙunar wuta zafi a cikin zuciyarka amma ina
so ka tuna komai ya faru a rayuwar mu mukaddari ne daga Allah, ka É—auki hakan a matsayin
jarabawa da Allah ke yiwa bayinSa muminai, mu yi hakuri da cutarwar da aka yi mana, In sha
Allah zamu ga ribar hakurin da muka yi, kuma Allah zai yi mana sakayya"


Cikin sanyin murya ta ƙarasa maganar tana kallon fuskar mahaifin nata dake kallonta da
rinannun idanunsa.


Unexpectected ta ji ya furta, "Musa!"

kowa da ke a falon sai da gabansa ya faÉ—i da jin sunan da ya ambata.


Ba ta yi mamakin Jin ya canki sunan shi ba, dama tasan dole ya zo masa a rai tun da shine
babban maƙiyinsa a duniyar nan.


"Ki faÉ—amin shine ko? Shine ya shiga tsakanina da ke ko?" Cike da damuwa ya tambaya,


Fargaban amsa mashi ta ke yi saboda zullum halin da zai shiga, tasan mahaifin nata da zuciya
komai zai iya faruwa.



Daƙyar ta jinjina mashi kai cikin raunanniyar murya ta ce, "Shine baba, uncle Musa, ya daɗe
yana ƙulla makirci atsakanin mu, ban ta6a ganin azzalumin mutun irinsa ba, ya karya mini
zuciyata, ya ha'ince mu, wata shari'ar sai a lahira, amma ya cutar da rayuwar mu..."


kamar a mafarki suke sauraron maganar Aisha, gaba daya sun kasa tantance wani Musan take
magana akan shi, Taj ne kaÉ—ai ya san komai, sai kuma Benazir da Anila.


Sauran da ke a falon sun ruÉ—e sosai, sun rasa gane inda ta dosa.


"Aisha kada ki ji komai, ki fadamin kawai, bazan karaya ba, nasan zai aikata saboda ya kullace
ni a ranshi, dama ni saida na yi zargin dasa hannunsa a cikin abun da ya faru, kawai don bani
da hujjar da zan tuhume sa ne.."

ya faÉ—a cikin karfin hali kamar zai iya jurewa.


Ƙarasa shiga cikin falon suka yi, saboda su samu damar jin komai, a saman sofas kowan nan
su ya samu wuri ya zauna suka nutsu suna kallon Aisha da baba Imam, kwata kwata basu san
da zaman su ba, saboda hankalinsu ba akansu yake ba, basu san ma sun shigo falon ba.


Numfasawa tayi cikin karyayyar murya ta soma zayyana masa komai da Uncle Musa ya faÉ—a
mata, tiryan tiryan abu É—aya da ta boye masa saboda gudun halin da zai shiga, shine
karuwancin da ta yi a America da kuma haramtacciyar alaƙarta da Musa tasan in ya ji wannan
komai zai iya faruwa ita kuma ba ta so Musa yayi nasara akan mahaifinta, ta dai sakaya ta ce
shi ya kaita America ya É—auki nauyin komai nata saboda ya kawar da tunaninta akan dawowa
gida.


Tunkan ta ƙarasa labarta mashi Hajiya Layla ta miƙe tsaye tana tafa hannayenta a kiɗime take
zabga salati, Alhaji Ubaid dake a zaune sai jinjina kansa ya ke yi yama kasa furta komai saboda
ƙuncin da zuciyarshi ta yi mashi, ina ga Dr shureim dake neman zaucewa saboda tashin
hankalin da ya haifar masa da raÉ—aÉ—i mara misaltuwa a zuciyarsa, bai ta6a zaton Uncle musa
zai iya yi masa haka ba, saboda yasan shi ya cutar da rayuwarshi shiyasa ya dawo da shi gidan
shi da zama, haka lokacin da ya ke neman taimako yaita kiransa baya shiga ashe blocking
É—insa ya yi, kowa dake falon sai da ya razana ba kaÉ—an ba, Musa ya karya zuciyoyinsu, basu
ta6a tunanin shine munafukin da ke ƙulla musu makirci ba.

Saboda bacin rai da fusata yasa shekh Imam zubda gumi akan fuskarsa, ba a ta6a cin galaba
akanshi ba sai wannan karon, Musa ya cuce shi, wani laifi ya yi masa da yasa shi yanke masa
mummunan hukuncin nan?"

Kawai saboda ya hana shi auran Aisha? Saboda baƙin zalunci da rashin imani ya shiga
tsakaninta da shi, yayi mata kazafi bayan ya shiga tsakaninta da Shureim, abun da yafi bakanta
ransa tsawon shekarun da ya raba shi da Æ´arshi, ashe yana a tare da ita, saboda zalunci irin na
shi, yanzu ya gane komai da ya faru da Aisha shi ya ja mata, tun da akan shi yake É—aukar
fansa, bata ji ba bata gani ba. Ruƙo hannayenta ya yi a cikin nashi, saboda kerma da jikinshi ke
yi itama nata jikin ya kama kerma idanunsu a cikin na juna yana kuka tana kuka ya ce, "Allah Ya
yi maki sakayya Aisha, Allah ya bi maki hakkin ki. Wlh bamu ya cuta ba kanshi ya cuta,
la'ananne, In sha Allah sai rayuwarsa ta wulaƙanta tun a gidan duniya, na yi danasanin sanin
shi a rayuwata, dama wasu mutanan Allah yana hadamu da su ne don ya jarabcemu da su,
wasu kuma don su zama alkhairi a cikin rayuwarmu.."


kasa ƙarasa maganar ya yi saboda kululun bakin cikin da ya tokare makoshin shi, ya ji zafi a
ranshi, bakin ciki ya cika shi kamar zai haÉ—iyi zuciya ya mutu.

Kwantar da kansa ya yi saman kafaÉ—ar Ummi, ya É—aura hannayensa a saman bayanta.

Cikin sigar lallashi yake dan bubbuga bayan nata, tsananin tausayinta ne ya kama shi, saboda
gaba daya rayuwarta a cikin jarabta ta ke, kowa dake a falon sai da ya tausaya masu, Hajiya
Laila ta yi danasani, sai cizon yatsa take yi, gani take kamar hada laifinta komai ya faru, idan
har Musa yana sarrafa Alhaji Ubaid da sihirinsa toh ita da hankalinta take yin komai.
A fakaice ta dinga share kwalla tana satar kallon Aisha da mahaifinta..

Cikin ruÉ—u Alhaji Ubaid ya ce, "Har yanzu na kasa yarda da abunda kunnuwana suke jiye min!
Dan Allah ku fahimtar da ni! Kaina ya ɗaure, Wani musan kuke nufi? Ƙanina musa ko wani
musan ne daban?"



Hajiya Layla ta yi saurin cewa, "Wallahi zai aika! Fiye da haka ma, ai baida mutunci ko kaÉ—an,
mutun sai bakar zuciya kamar ta kafuran farko, na daÉ—e ina zargin ba mutumin kirki bane Musa,
kuma dukiyarsa bata Allah da Annabi ba ce, Ai ni bazan ma Musa ba..."..



Benazir ta kar6e da cewa, "Abun da Aisha ta faÉ—a gaskiya ne daddy, na dade ina jiran wannan
ranar da zan fadi ta cikina, ku yi hakuri da ban ta6a sanar da ku ba, na boye maku ne saboda
nasan zai yi wuya ku yarda da ni a wannan lokacin, saboda ku kan ku sai yadda ya yi da ku...."


mayar da hankalinsu su ka yi akan Benazir..

A tsanake ta labarta masu komai da ya faru tun daga lokacin data ta kama shi yana yin waya
agidan shi, har izuwa kan asirin da ya yi mata..

Daura hannu biyu Hajiya Layla ta yi akanta.

Mami ta zabga salati, Dr Shureim ya zabura ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login