Showing 3001 words to 6000 words out of 18747 words

Chapter 2 - Kurkukun kaddara Book 2 Complete by Boss Bature.pdf

27 Feb 2026

402

wanka, mun kwana biyu bamu yi wanka atare ba.." Bai jira amsarta
ba, cikin sigar yaudara da jan hankali ya É—auketa kamar jinjira ya nufi bathroom da ita.


_______________________________


Lokacin da Taj ya je ma Ummi da zancen neman ta da Chief ya ke yi, hankalinta ba ƙaramin
tashi yayi ba, zullumi da fargaba suka cika zuciyarta, ta yi ta tunanin meyasa ya ke nemanta?



Kasa fita tayi daga dakinta, har saida Taj ya kirata a waya ya ƙara tunasar da ita game da kiran
da Chief ya ke yi mata yace ta same shi yanzun nan a sitting room dinsa tukunna, ta zumbula
dogon hijabi ta fito cike da É—ar-É—ar ta nufi sitting room dinsa, saida ta tsaya bakin door din ta
daidaita nutsuwarta, kafin tayi sallama cikin nutsastsiyar muryarta.
Daga ciki ya amsa mata sallamar, ya na daga zaune kan sofa ya É—aura kafarsa É—aya kan É—aya
yayin da idanunsa ke akan Apple ipad dinsa da ya ke daddanawa, shiga ciki ta yi, tunkan ta
ƙaraso ya nuna mata kujerar dake fuskantar sa, table ne ya raba tsakanin su.


Bayan ta zauna ta sunnar da kanta ƙasa cike da jin nauyin sa gaba ɗaya ya yi mata kwarjini.



"Ina fata kin wuni lafiya."



Da ƙyar ta furta, "lafiyalou, ya kake, ya aiki, ya family ɗin ku"


"Alhamdulillah ina lafiya, suma family ɗina suna cikin ƙoshin lafiya,"

Shiru suka É—an yi na wani lokaci, daga bisani ta tsinkayi muryarsa a cikin kunnanta,



"Na kwaÉ—aitu da son jin tarihin rayuwarki.."

Zare idanu ta yi, har ta fara tunanin ko dai ya ji komai agurin su Benazir ne.

Bai damu da yanayin ta ba ya ci gaba da maganarsa, still bai É—ago ya kalle ta ba, idanunsa na
akan apple ipad dinsa da yake cigaba da dannawa,



"A ranar da ƙawayenki suka zo gidan nan, Taj ya faɗa min halin da kuka shiga lokacin da kuka
ga juna, kuma ya ji a bakin Ex-wife din sa cewa ke aminiyarsu ce..."

Har ya ƙarashe maganar bai ɗago ba, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa tsantsar 6acin rai da
damuwa, kwata-kwata bata son kowa yasan labarinta, saboda tana jin kunyar a sani, bayan
haka bata son ta fama tsohon raunin dake a cikin zuciyarta, abun da ya É—aure mata kai meyasa
Chief ya ke son jin labarin ta? Ko Taj da suka fi shaƙuwa da shi bai nemi ya sani ba sai shi da
bai ta6a shiga shirgin ta ba hakan yasa ta dan ji shakkun ta faÉ—a masa..



"Kin yi shiru ba ki ce komai ba,"



Kamar mara gaskiya ta kama yi mashi yan kame kame, muryarta kamar ta mai in'ina ta ce, "Sir,
I'm sorry to say why do you want to hear about my life?"



"Saboda ina son in sasanta tsakaninki da ƙawayenki, cos a fahimtana kun samu sa6ani ne,
kuma akwai wani abu da ya faru wanda yayi silar raba ku. "

Yamusa fuska tayi kwata kwata babu walwala ta furta, "Ina ganin girmanka yallabai, bana fata
Allah ya nuna min ranar da zaka nemi wani abu agurina in kasa yi maka shi, amma ina mai
baka haƙuri, ni bazan iya baka labarina ba..."

Gently ya É—ago da reddish eyes dinsa ya É—aurasu akan fuskarta, tuni ta ji wata nutsuwa ta shige
ta, wani irin kwarjini yayi mata wanda hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar tata.



"Pls ki faÉ—amin, In har kin yarda da ni, amma idan kina ganin da takura ki bar shi..."

Yanayin yadda yake yi mata magana cikin kwantar da murya yasa ta dinga jin kamar yaya
Shureim ne ke yi mata magana, hatta fuskarsa sai ta dinga koma mata irin ta Shureim, batasan

sa'adda ta fara bashi labarin rayuwarta ba, tiryan tiryan ta labarta masa komai daya faru da ita
har izuwa lokacin data bar gidan mahaifin ta.

Idanunta cike tab da ƙwalla ta ƙare maganar, lallashin ta ya yi cikin nuna tausayawarshi gareta
har ya samu ya shawo kanta.



"Tayaya akai kika bar ƙasar nan? Ki ka koma America da zama, bayan kin canza rayuwarki?"

Sunnar da kanta ƙasa tayi cike da jin nauyin ta fada.



"Zan fahimce ki Ummi, tun kafin ki fara yi mana aiki mun riga da mun san komai game da
rayuwarki a America, don haka kada ki ji komai, abun da ya faru da ke jarabta ce daga Allah..."

Kalamai masu dadi ya faÉ—a mata har sai da ta ji zata iya fada masa komai saboda ta yaba da
hankalinsa ta kuma aminta da shi, a tsanake ta fayyace masa komai da ya faru bayan
rabuwarta da mahaifin ta.



Daƙyar ta ƙarasa labarin ganin yadda hankalinsa ya tashi matuƙar sosai, jikinshi har kerma ya
ke yi saboda tsabar bacin rai da fusata, bai ta6a jin tsanar mutun kamar yadda ya ji ya tsane sa
ba, zaluncin sa yayi yawa, bayan ya rabata da kowa nata, ya kuma maida ta karuwa, cikin fushi
ya daki gaban table dinsa da hannunsa.


Hankalinta a tashe ta ce, "Sir meke damunka? Ko labarin dana baka ne baiyi maka dadi ba..!"



"Har yanzu kina atare da Uncle din nata?"

girgiza kai ta yi, "Mun rabu da daÉ—ewa,"

Wani kallo yayi mata da ya sa tasha jinin jikin ta, batasan ya san komai ba.

"Ki ji tsoron Allah, Ki faÉ—a min gaskiya!"

Tamkar zata fashe da kuka ta ce, "Pls kada ka tilasta mini, bazan iya faÉ—a maka amsar
tambayarka ba, ka yi haƙuri kawai.."

Murmushin takaici ya yi tare da cewa, "Okay, Kin taba haihuwa da shi?"

AruÉ—e take kallonsa jin wata tambaya mara ma'ana, ba dan tana ganin girmansa ba da ba abun
da zai sa ta zauna yana mata tambayoyi kamar É—an jarida,

"A'a, amma na ta6a samun cikin shi, wanda silar zubar da cikin da na yi yasa muka samu
sa6ani da shi, har ya ɗauke ƙafa da kawo min ziyara, abun da yasa nayi hakan saboda bana so
in 6ata shape din jikina sannan bani bukatar in ƙara haihuwa, ƴata dana bari ta ishe ni in ƙarasa
rayuwata, ashe ma Æ´ar da nake ta hauka akanta ta mutu batare da na sani ba...."
Fashewa tayi da kuka ya dinga lallashinta har ya samu ta yi shiru..



"Amma meyasa baki taba kar6ar tayinsa na aure ba?"

Tana cikin share ƙwalla ta ce, "Saboda ban ta6a son shi da aure ba, bayan haka a duk lokacin
da yayi mini magiya akan in amince in auresa, da zarar na amince muka fara shirye shiryen
auranmu toh bazai ƙara lafiya ba, har sai ya fasa zancen auren, wannan dalilinne yasa har ila
yau bai aure ni ba."

Duƙar da kanta kasa ta yi jikinta yayi sanyi da ganin yanayinsa, duk sai taji ta muzanta, saboda
tayi zaton haushin rayuwarta ya ke ji, tuni idanunta sun cicciko da ƙwalla,



"Kayi hakuri, idan labarin dana baka ya 6ata maka rai, shiyasa tun farko banso ka matsa min
akan in fada maka ba.."

A hankali ya buÉ—e idanunsa da suka kaÉ—a jawur ya girgiza mata kai, "Ba abunda kike tunani
bane Ummi, labarin ki ya karya min zuciyana, na ji tausayin rayuwar ki..." hankalinta ne ya
kwanta jin ba abun da ta zata ba ne.

"Nagode da kika aminta da ni har kika faÉ—a min sirrinki" ÆŠan murmushi ta yi.

"Amma kai ma kamar kana da damuwa, kada ka ce na sanya maka ido, wlh ka rame, babu
karsashi a jikin ka"


Murmushin yaƙe ya ƙaƙaro akan fuskarsa, "Kada ki damu da ni, zazzabine ke damuna amma
na ji sauƙi..." Girgiza kai ta yi, "Yallabai, halin da ka shiga yafi ƙarfin zazzabi, kada ka boye min
pls, tun da har na aminta da kai na baka labarina dayake sirrina kaima ya kamata ka sanar dani

taka damuwar, ko da bazan iya sama maka mafita ba, zan tayaka da addu'a." marairaice masa
fuska ta yi.



Shiru yayi jim yana tunanin ya zata É—auki abun in ya fada mata,

Cikin sanyin murya ya ce, "Ummi mun fara gano su wanene Elders na gidan Kurkukun ƙaddara!
Kuma muna zargin uncle din ƙawarki Benazir yana ɗaya daga cikin su..."

Bai ƙare maganar ba ganin yadda ta zare idanunta, walwalar fuskarta ta ɗauke tamkar bata
ta6a yin dariya ba.

A dabarbarce ta ce, "Sir ka san me ka ke faÉ—a kuwa? Wallahi ba dan ina ganin girmanka ba da
ba abun da zai hana..." Kasa ƙarasawa ta yi, can kuma ta ce, "Bazai yiwu ba, big boss baya
É—aya daga cikin su, saboda shi ba matsafi bane kuma ba mugu bane, ni nasan wanene big
boss! Nasan halinsa ciki da bai, pls ku sake bincike akan shi zaka tabbatar da abun da nake
faɗa maka!" Rai a ɗan 6ace ta faɗa, ta haƙiƙance akan gaskiyarta.



"Ke baki tunanin mutumin nan da wata mummunar manufa yake atare dake Ummi? Ke fa
malama ce, kina da tarin ilimi akan ki, kinsan mai kyau da mara kyau, taya zaki yi tarayya da
fasiƙi kuma har kina kare sa daga laifin da ake tuhumarsa...?"


"Baki tunanin saboda kin nuna baki son shi dr. Shureim kikeso shiyasa ya ƙulla makircin da ya
shiga tsakanin ki da shureim ya kuma raba ki da mahaifinki saboda yasan bazai bari ki aure shi
ba tunda baki son shi, sannan bayan kin gudu da tsakar dare tayaya akai har kika haÉ—u da shi a
wannan lokacin? Shi Aljanine baya bacci ne? Ba yadda za'ayi ya fito in the midst of the night
batare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, gaba ɗaya plan dinsa ne Ummi..."

Shiru tayi jim ba tare data furta kalma ba, bata san tayaya zata fahimtar da Chief ba, gani take
kamar ya fara zarewa.


"Kiyi amfani da hankalinki Ummi, meyasa ya ɗauki nauyin karatunku a ƙasar germany? ya kuma
kama maku hayar gida, bayan haka duk weekend sai ya kawo maku ziyara har ya kwana
agidan ku," ya faÉ—a yana kallon cikin idanunta.

Gaba É—aya tabi ta ruÉ—e, sai dai kwata kwata bata gasgata maganarsa ba, saboda ta yarda da
Uncle Musa fiye da kowa tun da ita ya yi mata hallacci, ya so ta a lokacin da kowa ke gudunta,
ya zama danginta a lokacin data rasa dangin da zata jingina da su.

Murmushin takaici ya dan saki, saboda ya fahimci ta cikin sauƙi bazata yarda da shi ba,

Zura hannunshi ya yi cikin front pocket na jallabiyarsa ya zaro hotuna,

Kamar daga sama ta ji ya ce, "Nasan har yanzu kuna a tare Ummi, saboda akwai ranar da ya
kira ki a waya kin shiga toilet, Batool ta gani ta É—auka batare da sanin ki ba, a yanzu haka ina da
hujjojin da za ki gasgata magana ta.."

She was utterly perplexed, but she didn't believe his words at all.

Ya ƙarashe maganar tare da ɗaura mata hotunan akan table dinsa, lokacin da ta daura idanunta
akan hotunan wata irin firgita ta yi, gaba daya tabi ta rude, muryarta da mamaki ta ce, "Sas.. Sir
ina ka samu waÉ—annan hotunan?"

Ta tambaya aƙagare da son jin amsar shi, bai tanka mata ba, har saida ya zaro ɗayan hoton ya
jera shi da sauran hotunan..



Lokaci ɗaya ta ƙara ruɗewa, labbanta na kerma ta furta, "Baby preety, Sir Ina ka samu hotunan
su um??"



Numfasawa yayi kafin ya ce, "zan faÉ—a maki inda na samu hotunan amma ki fara faÉ—a mini miye
alaƙar dake atsakanin mutanan dake a cikin hotunan nan?" Jinjina mashi kai tayi kafin ta fara
kora masa bayani,



"A tare na san shi da Natasha, sun daÉ—e a tare, karuwarsa ce kuma baturiyar england ce, ita
kuma baby preety rainon ta ya kawo mata tun tana jaririya, amma lokacin da ta kai shekara sha
shidda ta ce min ya kar6e ta, ya mayar da ita gurin mamanta da ke anan Nigeria.."



Runtse ido chief Owais yayi saboda takaicin da ya turnuke zuciyarsa, aransa ya ayyana hakan
na nufin Æ´an biyu ne ita da Æ´ar wurinsa! Kamar yadda su ka yi tsammani, Ya sadaukar da É—aya,
ita kuma É—ayar tana agurin mamanta.

"Sir meya faru um? Dan Allah tun da na amsa maka tambayarka, nima ka fadamin a ina ka
samu hotunan su! Na ƙosa na ji."

Miƙa hannu yayi cikin table drawer din gabansa ya curo diary ɗin Unaizah ya ɗaura mata akan
table din, "kinga inda na samu hotunan, Kuma diary din nan mallakin É—aya daga cikin fursinonin
kurkukun kaddara ne, nasan ba zaki manta yarinyar da Unaisah ta bada labarin mahaifinta da
ya yaudareta ya sadaukar ita gidan kurkukun kaddara a matsayin Korean School...?"




Wani irin faduwar gaba taji daram dararam kamar ana buga gangunan yaƙi a ƙirjin ta.

Yatsun hannunta na kerma ta buÉ—e diary din ta soma karanta shi,

Wa'iyazubilla! tana karantawa yayin da brain dinta ke tariyo mata fuskar yarinyar, tabbas ta
yarda diary din mallakin baby preety ne babu tantama saboda yawanci duk abunda ta rubuta a
cikinsa ta ta6a jin labarin a bakin Natasha.




Bata ƙarasa karantawa ba, ta rufe diary din tare da kifa kanta saman shi, wlh bazan iya misalta
tashin hankalin da ta shiga ba, She was completely bewildered and shocked, unable to believe
it, Aranta tana jin ba zai yiwu uncle Musa ya iya aikata rashin imanin nan ba, mutun mai tsoron
Allah da tausayi irin sa would never do such terrible thing, amma kuma ta fara kokwanto saboda
in har ba a diary din baby preety ba, to kuwa babu inda za'a samu hotunan Big boss da Natasha
da kuma na baby preetyn, sai dai bata so ma zargin su akanshi ya zamana gaskiya.

"Yanzu kin yarda da maganata ko kuwa kina akan bakanki"

Jinjina mashi kai ta yi, "Bani da matsaya, amma na yarda da big boss, kuma na yarda da kai,
sai dai bazan iya yarda da abun da ka fada akansa ba, wadannan hotunan na yarda a cikin
diary din baby preety aka same su amma bana tunanin itace yarinyar da Unaisah ta bamu
labarin ta, please na roƙe ka ku sake bincike akan shi.."

Duk yadda Chief ya so ya kwatanta mata cewa ba mutumin kirki bane taƙi yarda, tana akan
bakanta saboda ta aminta da mutuminta, yadda kasan wadda aka asirce, kwata kwata bai ji
haushinta ba saima tausayinta da ya mamaye zuciyar shi saboda ya lura ta ruÉ—e ne sosai kuma

bata son zargin da suke yi ya tabbata akan shi saboda halin da zata shiga, shiyasa tun farko
baima yi tunanin faÉ—a mata komai game da babynta ba saboda gudun halin da zata shiga.




"Ummi, Zan baki lokaci kije ki yi tunani akan abun da na faÉ—a maki, sannan ko da baki yarda ba,
Inaso ki bamu hadin kai please..."

Girgiza kai ta yi, "Ka yi haƙuri ba zan iya ba, nayi masa alkawarin bazan ta6a bari wani ya san
muna a tare ba, in har ya ji na karya masa alkawari bazai ji dadi ba, zaiga kamar na ci
amanarsa ne, ni ko maganarsa bana son yi da wani." Zuciyarsa ta sosu ransa yaso ya 6aci, sai
dai bai nuna mata a fuska ba..



"Zaki iya tafiya..." Har zata miƙe ya tsayar da ita, "Zan gargaɗe ki, Kada ki kuskura ki bari
mutumin nan ya gane abunda muke zargi akansa! bama shi ba, ko da ƙawar nan taki ce, idan
har na ji maganar nan agurin wani, hmm, ba abun da zai hana in garƙame ki a cell kuma kema
zaki shiga cikin zargin da muke akan sa, sannan kada ki canza masa ku cigaba kamar yadda
kuka sa6a."

Maganarsa ta ɗaga hankalinta, dama da biyu ya yi mata barazana, fuskarta ta jiƙe sharkaf da
gumi, kwata kwata babu walwala atare da ita, Ya rudar da ita ba kaÉ—an ba, Ya kuma tsoratar da
ita.


Hanky ya miƙa mata, "Share zufar dake akan fuskarki, don bana so wani ya gane halin da kike
a ciki."

Cikin rawar hannu ta kar6i hanky din ta soma share gumin fuskarta, har ce mata yake yi, "Ki
share da kyau fa.." tace toh, bayan ta gama ta juya zata tafi da hanky É—in ya dakatar da ita,
"Bani abuna.." miƙa masa hanky din ta yi, ko waiwayensa bata yi ba saboda a ƙagare take da ta
bar sitting room din nasa..
Lumshe idanunshi yayi tare da jingina bayan shi jikin kujarar, bawan Allah abun duniya ya ishe
shi, saboda gujewa tunanin da zai haifar masa damuwa yasa baya barin zuciyarsa hakanan
batare da yayi tasbihi ba 💔



Bayan fitar Ummi daga dakin, jikin bango ta jingina bayanta, yayin da zuciyarta ke tariyo mata
wasu abubuwa da suka haifar mata da kokwanto akan mutuminta! bakomai ta fi tunawa ba face

ranar data fara ganin Danish babu shirt a jikinsa! zanen tattoo dinsa ya tsaya mata a rai, har
yau bata manta ba, saboda sak irin na big boss ne, kamar anyi photo copy dinsa an É—aura
masa abayansa, kuma tun da take mu'amala da americans bata ta6a ganin mai irin tattoo dinshi
ba, sai akan Danish shiyasa ranar data ganshi al'ajabi ya kamata, bayan haka maganganun da
Chief ya faɗa a game da shi sun tsaya mata a ƙahon zuciya, tabbas diary din baby preety ne,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login