Showing 6001 words to 9000 words out of 25466 words
Chapter 3 - Saurayina Book Compelet Writing Mrs Sadauki
gobe!” ta na gama faɗa ta kwantar da ni kamar wata ƙaramar yarinya
kafin ta fice,na bi bayanta da kallo kafin na ƙoƙarta na rubuta wa Fahad saƙo sai kuma na
kashe wayana.
MAMA
Ta na fita ta wuce ɗakin Papa wanda bai jima da dawowa ba,jiki a sanyayye ta zo ta zauna.
Ya ɗan dube ta ya ce “ya dai?”
“Akan auta ne!” Mama ta faɗa dakyar.
“Ina jin ki”
“Alhaji na ce mi zai hana ka sassauta lamarin nan ka ce Fahad ya kawo duk abin da Allah ya
sawwaƙe masa ka aura masa ita hankalin kowa ya kwanta”
Papa ya ɗaure fuska ya ce “duka nawa Autar take? 22years ne fa? Sai na yi mata aure ko
karatu ba ta gama ba kuma da wancan yaron?”
Mama ta ce “in an yi auren....” yayi saurin katse ta da “ba za a yi ba!”
Cikin jimami Mama ta fito daga ɗakin ta koma nata ta fara saffa da marwa,tun ranar da ta ɗora
idonta kan Mubashar ta gamsu da nutsuwar shi, abu na gaba kuma shi ne yadda ya bata
laƙanin yadda za ta tsare mutumci ƴarta.Ta ja wani dogon numfashi ta ce “rashin uwa ke sa a yi
uwar ɗaki! Da dai in bari Fahad ya ɓata miki rayuwa gwara na bai wa Mubashar auren ki kowa
ya huta” daren nan sam Mama ba ta rumtsa ba sai da ta samo wa kanta mafita,ta kira babban
Yayanta Sheik Mohammed ta sanar da shi burinta.
Washegari
Wuraren ƙarfe goma na safe ina kwance kan gado Mama ta shigo cikin shirin fita,dakyar na
buɗe baki na gaishe ta.
“Zan fita ki shiga kitchen ki ɗora girki”
Na ɗan shagwaɓe fuska na ce “Mama don me Saude ba za ta yi ba?”
“Ke nake so ki yi! ” ta na gama faɗa ta fice.Toilet na shiga na yi wanka na kimtsa kafin na fita
falo,babu kowa sai ƙaton tv da ke ta magana shi ɗaya.Table na nufa na haɗa tea na sha kafin
na wuce kitchen,tuni Saude ta fara gyaran kayan miya da taimakon ta na yi komai.
A ɓangaren Mama kuwa ta dai ce Mubashar ya kai ta wani wuri ba tare da ta yi masa bayani ba
har suka isa.
A tare suka shiga har babban falon kamar yadda ta buƙata,su na ta gaisawa da mutanen gidan
kafin Sheikh Muhammad ya fito cikin shigarsa ta kamala dogo ne fari tasss ya ɗora gemunsa ka
na ganinsa ka ga ahali sunnah.
Bayan sun gaisa ne Mama ta ce “wannan ne dama nake yi maka zance a jiya,ya na hadda
alƙur'ani sai dai na Warshi ne irin na ƴan allo to Yaya ina son ya koma kamar dai kai haka a
koya masa karatun litattafan Musulunci ”
“Ai duk ɗaya ne karatun Warshi da Habsi,amma in sha Allah za mu yi abin da ya dace.Ya sunan
ka?” cewar Sheikh Mohammed.
Mubashar da sai yanzu ne ya san dalilin zuwan nasu wato gata Mama za ta yi masa kenan ya
basa amsa da “Mubashar ne sunana”
Nan ya fara yi masa tambayoyi game da makarantar da yayi,kamar yadda ya shaida wa Mama
haka ya maimaita yanzun ma ba tare da ya ɓoye komai ba.
“A Borno na yi karatu,a can ne kuma aka koyar da mu wasu laƙanin,wanda da farko muna dai
taya malaminmu ne in an kawo masa aikin tsibo daga haka yayi ta koyar da mu amma ban taɓa
gwada wa ba sai sau ɗaya a can Tilabery da wani ya ce ya na son wata na masa aiki kuma ya
ci.A ranar da ya zo yi min godiya ne Ammyna ta fahimci al'amarin da ke faruwa shine ta ƙone
duk kayan aikin sannan ta hane ni da juya ilimina domin sana'a, wannan dalilin yasa ma na fito
neman aiki har Allah ya haɗa ni da Hajiya Mama”
Sheikh Muhammad ya jinjina kai bayan ya gama sauraren shi kafin ya ce “Allah yafe mana baki
ɗaya ka ci gaba da yin istigfar.Gobe za ka fara zuwa makarantarmu ban sani ba ko ka taɓa jin
ana cewa Imam Malik ba? To sunanta kenan.Makaranta ce mai koyi da sunnah da kaucewa duk
wani abu da ya saɓa ma koyarwar manzonmu” sosai Sheikh Mohammed yayi masa bayani
yadda zai fahimta,kasancewar Mubashar bai da girman kai haka ya tsaya ya saurare shi.
Da za su koma haka ya basa wasu littattafan,a hanya ya na zuba wa Mama godiya har da yin
kukan farin ciki.Su na isa gida Mama ta wuce can ciki,shi kuma Mubashar ƙarƙashin innuwar
mangoro da ke tsakar gidan ya je ya zauna tare da danna kiran Ammy.
Bayan sun gaisa ta ce “jiya ina ta jira ka maido shiru,ba ka bani amsa ba na ce yarinyar....” yayi
saurin katse ta ya na mai cewa “Ammy akwai abun murnar da nake son sanar da ke fa”
“Wanda ya fi wannan?” ta tambaya.
“Eh Ammy! Hajiyar da suka ɗauke ni aiki ce ta biya min makaranta irin ta ƴan gayu,gobe zan
fara” nan ya yi mata bayani,sai ga Ammy ta na kukan murna “Alhamdullah! Allah na gode ma
dama ya ce in ka yarda da shi zai maka ni'ima ta inda ba ka zato.Ka bani lambar Hajiyar na kira
na yi mata godiya, Mubashar ka je hankali ka yi karatu Imam Malik duk Nijar babu makarantar
da kai ta,domin har Larabawa ke da kwai cikin masu karantarwar”
“In sha Allah Ammy! Zan sake kiran ki” sai ya kashe tare da nufar ɗakinsa.Ɗan ƙaramin
akwatinsa na ƙarfe ya buɗe ya zaro wata sarƙa wacce suke shige da wacce ya bai wa Ammy a
shekaran jiya.Sai da ya ɗan juya ta kafin yayi Bismillah ya buɗe lular tsakiya,garin magani ne a
ciki wanda Allah kaɗai ya san surkullen da aka yi masa. “Daga yau ba zan sake yin imani da duk wani abu da ya shafi abu kamar haka ba” ya furta tare
da sauke ajiyar zuciya sai ya je ya ƙone su daga ƙarshe.
FAHAD
Abokansa suka haɗa wasa a wani gidan gona ,sanin Sharifa ta na cikin period kuma ba zai
samun yadda yake so ba yasa shi fara kiran ƴan matansa uwanda sun fi goma a haka yayi ta
nema har ya samu wacce ta yarda su je su watse ɗin.Lokacin da Sharifa ke ta gwada kiransa
shi kam bai da lokacinta ,sai dai ya na da niyyar kiranta a gobe . A gajiye ya buɗe idonsa saboda sam bai rumtsa ba ya samu ƴar mutane ya na ta hole wa da
ita,tun dare har asubah abu ɗaya suke.
Fahad ya jawo wayarsa da ke can gefe ya duba,saƙon Sharifa ya gani «Had gobe ka zo gida
Mama na son ganin ka,da dukkan alamu lokacin aurenmu ne ya zo» ya na gama karanta saƙon
ya ida ture budurwa da ke kan ƙirjinsa ta na sharar bacci.Kayan jikinsa ya fara nema a cikin
kayan da ke zube na abokan shiriritar tasa.Ya na gama kimtsa wa ya fice ko ta kanta bai bi
ba,babur ɗinsa ya hau ya na tafe ya na gwada kiran lambar sharifa amma ba ta shiga a haka
har ya isa unguwarsu inda ya tarar da cincirindon mutane a ƙofar gidansu.Bai kai ga tambaya
ba ya hangi motar ƴan sanda ga Umma a zaune ta na sharar ƙwalla.....
[21/04 à 09:07] MRS SADAUKI í ½í±‘: *SAURAYINA*í ½í²…í ¼í¿»í ½í²…í ¼í¿»í ½í²…í ¼í¿»
LoVe and HoRrOr storyí ½í²”☠️
```MRS SADAUKI```✍í ¼í¿»
Dedicated to Autar Manyaí ½í±‘
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________
________________________
Page 4
Da azama Fahad ya nufi motar ƴan sandar,sai dai kafin yayi magana ya ji muryar Nana na cewa
“yawwa Maman ga shi nan ya zo” inda sautin ya fito ya duba,sai yayi tozali da Nana hannunta
riƙe da jinjirin yaro sabuwar haihuwa.Gabansa ne ya faɗi ras ,ya haɗiye wasu yawun tsoro kafin
ya ce “ uwar mi kike nema a gidanmu?” Mahaifiyarta ce ta basa amsa da “uwar abin da ka shuka ta zo miƙa ma tsiyar ka.Ke miƙa masa
shegen ɗansa,miƙa masa na ce!” ta ƙarashe faɗa cikin ƙaraji hakan ya janyo hankalin dukkan
mutanen da ba su hankalta ba.
Umma ta fito daga mota ta na kallon Fahad wanda ya rungume jaririn,sai rarraba ido yake ya
rasa mi zai cewa Ummar.Nana da mahaifiyarta kuwa tuni sun bar gun su da motar ƴan
sanda,“ka kyauta kuma na gode” cewar Umma ta na mai shigewa cikin gidansu na laka.
Cike da kunyar jama'a Fahad ya ratsa su ya bi bayan Umma,bai taɓa tunanin akwai ranar tonon
asirinsa ba sai yau.
“Umma don Allah ki yi haƙuri wallahi tsautsayi ne kuma ba ni ɗaya ba na kusance ta...” ko kafin
ya dire zancensa Umma ta zuba masa yatsunta biyar kan kunci .
“Ban son jin komai! Ka san tun yaushe ake neman ka? Tun jiya zuwan da suka yi ya fi cikon
casbi,duk tunanin su na ɓoye ka ne shi yasa yau suka zo da motar ƴan sanda ta yadda asirinmu
zai tonu ana zunɗenmu a unguwa.Dama ka san ba aurenta ba za ka yi shi ne har da wani bani
labarin ta?”
Fahad ya ajiye jaririn da sai baccinsa yake kafin ya ce “wannan fa ba Sharifa ba ce! Dama ƴar
iska ce kawai don ban son tsiyar gumi shi yasa na karɓi yaron nan amma ki bar ta da ni take
zancen”
Umma ta jefe shi da kallon masheƙan aya ta ce “ko makaho ya dubi jaririn nan ya san ɗan ka
ne,abin da nake so da kai dai shi ne ka bar yawon banza ka san ciwon kanka don na ji labarin
jiya wasa kuka shirya shi yasa ma ba ka kwana gida ba”
“Umma ni fa ban son yaron nan...” bai ƙarasa faɗa ba sai ga abokinsa Kb ya shigo gidan
hankalin tashe don ko sallama bai yi ba .
“Abokina yanzu aka kira ni aka ce babu lafiya,na zo kuma na ga kamar hankalin ka kwance ”
cewa Kb.
Umma ta yi caraf ta ce “eh mi zai sa ya tada hankalinsa tun da ita ƙaddara ta san ɗakin kowa
,kuma ai ba gare shi farau ba ballantana ya ƙare kansa” daidai nan jinjirin ya fara canyara
kuka,Kb sam bai damu da zantukan Umma ba don tun ba yau ba ya san da ba ta son taren shi
da ɗanta Fahad sai dai babu yadda zai yi Allah ya haɗa jinin su.
Fahad ya girgiza kai kawai kafin ya buɗe ɗakinsa ya ce wa kb ya wuce ciki,yayin da Umma ta
ɗauki ɗan ta na ririga shi “Fahad ya kamata fa ka nemo madarar da za a basa ya sha”
“Banda ko sisi aljihuna ki ara min in na samu sai na baki” ya bata amsa.
Kb ya ce “akwai a wurina bari na je na siyo” sai ya fasa shiga ɗakin ya fice .
Fahad ya dubi mahaifiyarsa ya ce “ Umma don Allah ki bar nuna zallar ƙiyayyar ki ga Kabiru shi
ɗin...”
“Ya isa haka! Wuce ka yi wanka dubi yadda fuskarka take a yamutse” Umma ta faɗa ta na bai
wa jaririn ruwa.
Bokiti ya cika da ruwa ya je yayi wankan,ya na fitowa shi kuma Kb na shigo wa.
Madarar gwangwani ce sai biberon inda za a dinga kaɗa madarar,sai da ya nuna wa Umma
yadda ake haɗa wa sannan ya wuce ɗakin abokin nasa.
“Fahad ka ga abin da nake guje maka ko? Wannan rayuwar da ka ɗaukar wa kan ka sam ba ta
da tabbas” Kb ya faɗa cikin rashin jin daɗi.
Fahad ya ja numfashi kawai,sai da ya gama shirya wa cikin ƙananan kaya sannan ya ce “sau
ɗayan wahala ne kawai ka ji abokina”
“A'a tun ba yau ba kuke tare da Nana ni a tawa shawarar kawai ka aure ta”
“Allah tsare ni da auren ƴar iska!” cewar Fahad ya na haɗe rai.
Kb ya murmusa ya ce “to kai mine ne?”
“Irin ka ne ni ko ka zata ban san ku na holewa kai da Ramlah ba?”
“Ita ɗin wacce zan aura ce kar ka manta haka.Kuma babu abin da ya shiga tsakanina da
ita,ranar nan ma da ka gan ta ɗakina wani dalilin ne ƙwaƙwara ya kawo ta”
Sai da Fahad ya sheƙe da dariya ya ce “to a faɗa wa kaji zabi hira suke! Ka ga tashi mu je ka yi
min rakiya gidansu Sharifa”
“Ba zan je ba! Ni ma gidan tawa amaryar zan je!”
“Okay!" Ya faɗa ya na mai maƙe kafaɗu.A tare suka fito,Umma sai wanka aka yi wa baby Kb
yayi mata sallama maimakon ta amsa sai cewa ta yi “saura kayan sawa na baby ” bai ce da ita
komai ba ya zo ya ja motarsa ya wuce gidansu Ramlah wacce ke can ta na jiransa tun ɗazu .
Sai da ya shiga ya gaida iyayenta sannan ya fito ya zauna cikin mota,jim kaɗan ta fito cikin
adonta.Yadda ta haɗe rai alamun ta yi fushi yasa shi cewa “sorry Hajiyata ba gani na zo ba?”
Ramlah kamar za ta yi kuka ta ce “saboda Allah mi ya tsayar da kai?”
“Fahad ne mana”
“Ka ce ciwon kan ka” Ramlah ta faɗa ta na taɓe baki.
Kamar suɓul da baka Kb ya ce “ai kuwa yau ma ya kwaso jan aiki,wata yarinya ya yi wa ciki
yanzu har ta haihu yau ta kawo masa ɗansa”
Ramlah ta dafe ƙirji “ciki?” ta faɗa da ƙarfi sai a lokacin Kb ya tuna ya yi katoɓara musamman
da ya san ita ɗin ƙawar Sharifa ce.
Cikin son kawar da zancen ya ce “wane gida za mu fara zuwa?”
“Duk inda ka kai mu” Ramlah ta faɗa ta na fiddo wayarta ta na dadana wa a haka suka fara
ziyar dangi da abokon arziki inda a ƙarshe ta ce ya kai ta gidan su Sharifa.
#Gidan Papa
Muna gama girki ni da Saude muka jera kan table ɗin cin abinci.Wanka na je na sake yi sannan
na kunna wayata,saƙon Fahad ya ta gwada kirana aka turo min na lumshe ido ina jin wani irin
sanyi na ratsa ni wanda ba komai ya janyo haka ba sai don ganin Fahad ya damu da ni tun da
har ya gwada kirana sama da goma sai kuma na wata baƙuwar lamba marar suna. Simple kwalliya na yi kafin na feshe jikina da turare na fito falo,tuni Yayuna Munir da Sharif sun
fito su na ma cin abinci.
Na turo baki gaba na ce “ba a ko jira har na fara ci shine kuka zuba”
“Ke wa?” muryar Ya Mustapha ta katse ni wanda shi ma ya fito cikin shirinsa sai baza ƙamshi
yake .
“Yaya wasa fa nake!" Na faɗa cike da shakku.
“Su ɗin sa'anin ki ne?” na girgiza kai idona na cikowa da ƙwalla.
“Na sake jin banzan shirmen nan ki ga ikon Allah.Mi yasa kika kashe wayar ki ne? Ali ya ce yayi
ta kiran ki bai samu ba” sai a lokacin na ɗago na dube shi,wato tuni shi ma sun gulmata masa
abokin mijin anty Maimuna na sona.
“Wayar ce ta mutu sai yanzu na caza ”
“Yau zai zo sai ki shirya tarbarsa,sannan ki aje hankali ki nutsu da kyau da zarar kun fahimci
juna zan basa auren ki”
Tamkar saukar guduma haka na ji furucinsa,babu tsoro sam a idona na kafe shi da su na ce “shi
kuma Fahad ɗin fa?”
Ya Mustapha ya ɗaga hannu da niyyar mari na amma Papa ya dakatar da shi.Da gudu na koma
ɗakina ina kuka,ban ma san lokacin da Mama ta dawo ba.
Ina cike da ƙuncin nan ƙawata Ramlah ta shigo,“ke lafiyar ki?” shi ne abin da ta faɗa ta na buga
bayana.Na tashi zaune ina dubanta da kumburarun idona,ban wani ɓata lokaci ba na koro mata
bayani tun da ni da ita ba mu ɓoye wa juna sirrinmu.Maimakon na ga damuwa kan fuskarta sai
akasin haka,“ai wallahi gwara ki cire Fahad a ran ki don sam ba ku dace ba,kin ga fa yanzu Kb
ke faɗa min ya yi wa wata ciki an kawo masa baby.Yanzu irin wannan mijin za ki aura?”
“Ban gane ba ki yi min gwari-gwari!” na faɗa don sam ban fahimce ta ba,sai da Ramlah ta sake
maimaita min sannan na gane.
Nan wani sabon kukan ya kubce min,maimakon ta rarrashe ni a'a kawai sai ta yi ta ɓata Fahad
ana cikin haka ne kiransa ya shigo.Sanin shi ɗaya ke da irin wannan ringing ɗin yasa na ɗaga
kiran ko screen ban kalla ba,“ga ni a ƙofar gidan naku mai gadi ya hana ni shiga” jin muryarsa
cikin damuwa sai na ji tawa damuwar na barazanar ɓacewa.Ko kallabi ban tsaya sakawa ba na
dire daga bed na fice,a tsakar gida na gamu da Mubashar ina jin ya na tambayata ina zan je
ƙafata babu takalmi kuma ba mayafi amma na yi masa banza.
Ina isa bakin get mai gadi ya tare ni ya na cewa “hajiya umarni Oga Mustapha ya bayar kan
cewa kar na saki na bari ki fita, sannan wancan ma ya ce kar a bar shi ya shigo”
“Ja ka bani wuri in ba so kake na mare ka ba” na faɗa ba tare da na duba yawan shekarunsa
ba,da na ga bai da niyyar ja na yi wani ƙuuu doli ya kauce min na fita.
Fahad na ganina ya sauko daga kan mashin ya nufo ni,ya buɗe baki zai yi magana na wanke
shi da mari sai kuma na cakumi kwalar rigarsa ina jijiga shi.Cikin kuka na soma magana “ Had
mi na yi maka ne har haka? Don mi? Akan wani dalili za ka je ka yi wa wata ciki ta haifa ma ka
ɗa? Ni mi na kashe maka ne? Mi yasa ba ka yi min cikin ba madadin ta?