Showing 15001 words to 18000 words out of 25466 words

Chapter 6 - Saurayina Book Compelet Writing Mrs Sadauki


Mubashar ya ɗan saki murmushi kawai,nan dai yayi musu sallama kafin ya ɗauki hanyar
komawa Niamey.



SHARIFA

Furucin Mubashar abu ne da ban yi tunani ba,ko kaɗan ban taɓa kawo hakan a raina ba
wannan yasa kawai na gudu na barsa.Da na shiga ciki kuwa kuka kawai nake yi,anty Maimuna

ta yi tunanin na murna hakan yasa ta yi ta buɗa ta na min waƙar amare.Sai da na gaji don kaina
sannan na daina,sallah kawai na iya yi amma sam na kasa cin abinci.A gidanta na kwana da
tunanin Mubashar,da safe yunwa ta tayar da ni na je na ɗora ruwan zafi na haɗa Lipton da citta
da menthe na sha.Ina nan zaune falo Anty Maimuna ta fito ta na sanar da ni Sheikh bai da
lafiya,kuma Mubashar bai kwana gida ba.
“Wa ya faɗa miki bai kwana gida ba?” na tambaya hankali tashe.
“Mama ce! Zo mu haɗa abincin da za mu kai daga asibitin sai mu wuce gida na ga lefe”

Na ja tsuki na ce “wai lefe!” anty Maimuna ta saki baki ta na kallona,na ce “ni fa ban shirya aure
ba gaskiya karatu ne gabana ”
“Sai ki je ki sanar da Papa,ko kuma bari na kira Ya Mustapha sai ki faɗa masa” ta na gama faɗa
ta wuce kitchen,ni kuwa ɗakinta na wuce na ɗauko wayarta kiran lambar Mubashar na yi ta yi
amma ya ƙi ɗagawa.Ina nan kwance ina saƙe-saƙe har anty Maimuna ta zo ta sanar da ni na je
na shirya .Wanka na yi ta fiddo min doguwar riga fara sol na saka ,hijabin na wurgar na ce “ki
ban kallabin rigar mana”
“Ki na matar auren?”
“Don Allah Anty ki ban”

Ta miƙo min na ɗora shi a kai,sannan muka fita ita ke ɗauke da ƙaramin basket ɗin abincin har
muka je bakin titi muka samu taxi.
Tun da muka ɗauki hanyar asibitin gabana ke wani irin bugawa,har muka isa.Muna shiga ciki na
tsaya cak ina kallonsa ya na mai fitowa daga cikin mota ,anty Maimuna ce ta kira sunansa sai
ya juya muka haɗa ido da shi.Ban sani ba ko idona ne amma gani na yi kamar ya rame,ban
taɓa ganinsa da uwannan kayan na jikinsa ba duk da ba wasu tsadadi ne ba amma ni dai ya
min kyau .
Iskan da ya fara kaɗawa ne ya sa na lumshe idona,sam ban damu ba da kallabina da ya sauka
daga kaina ba duk da ina jin gashina na taɓa min fuska alamun iska na kaɗa shi.
“Sai ki buɗe idon don ya tafi” na ji muryar Anty Maimuna,ai kuwa ina buɗe wa babu
Mubshar.Takaici na ji,a haka muka ƙarasa ciki inda muka tarar da danginmu an dubiya sai dai fa
shi Sheikh ɗin an ɓoye shi.
Ina ƙoƙarin wuce wa don samun wurin zama na take ƙafarsa,wajen na yi sauri na janye sulɓi ya
kwashe ni na faɗi ƙasa na buge baki na saki ƙara ina mai ɗagowa na kalli Mubshar da ya ƙi tare
ni har na faɗi.......





*Jummah Mubarak*😶‍🌫
[28/04 à 10:15] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻


LoVe and HoRrOr story💔☠️

```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________
________________________



Page 7



A kunyace na miƙe ina shafar inda na buge ɗin ko zan ga jini amma babu komai.Kowa yayi min
sannu amma banda shi,gefen anty na zauna ina satar kallonsa sai wani ƙara haɗe rai yake ya
na haɗiyar yawun da ban san ko na mene ba kawai dai ina ganin maƙogoronsa na motsawa.Ya
juyo muka haɗa ido sai kuma ya ƙi kauce wa kallona ni ma haka na yi masa ƙur,yadda ya kafe
bakina yasa na shafa gun sai na ji ya ɗan kumbura.Na shagwaɓe fuska kamar zan yi kuka ina
mai ci gaba da kallonsa,ya kawar da kai gefe.Ana cikin haka ne kawai muka ga an turo Sheikh
Muhammad bisa gadon maras lafiya an nufi wani ɗakin da shi duk sai muka tashi muka bi
bayan su.
Idonsa biyu sai kllonmu yake ɗaya bayan ɗaya,Mubashar ne ya matsa kusan kansa ya na cewa
“Sheikh ya jiki?” bai basa amsa ba sai hannunsa da ya kamo ya na ɗan matsa shi.Mubashar ya
buɗe baki zai yi magana Sheikh ya tari numfashinsa “alhamdullah ai na samu lafiya! Ya kake ?
Ina ka tafi na yi ta kiran wayar ka amma ba ka ɗauka ba ka sa duk hankalina ya tashi?” yadda
Sheikh ke magana cike da kulawa yasa tsikar jikin Mubashar tashi sai yake jin ina ma ace
wannan ɗin mahaifinsa ne? Rana ɗaya tak da bai ji ɗuriyarsa ba ya ɗaga hankali amma shi
mahaifinsa bai taɓa ma nemansa ba duk tsawon rayuwarsa.

Sheikh ya katse masa tunanin da yake ya ce “ kar ka sake yin nisa da ni ! Kai ne na fi jin farin
ciki in ina tare da kai kaf cikin yarana ” Mubashar ya lumshe ido,sanin duk yaran da Sheikh ɗin
ke magana ba biologique ƴaƴansa ba kawai zumuncin musulunci ne .
“In sha Allah Dadd...am Sheikh ” Mubashar ya furta a rarrabe,saura ƙiris ya kira shi da Daddy
amma sai kuma ya canza .
Sheikh ya ɗan murmusa ya ce “ya ammyn naka ta na lafiya ko?”
Ya jinjina kai ya ce “lafiyarta lau”



Da taimakon Mubashar ya tashi zaune sai a lokacin ya fara amsa gaisuwarmu amma banda ta
Mama,ina lura kuma da ita sai ta sunne kai.
Hajiya Balkis ce ta shigo sai baza ƙamshi take,direct kusan mijinta ta je ta zauna ta na mai

tambayarsa jikinsa ya amsa sama-sama kafin ya dubi Mubashar ya ce “ina son jus!” da to ya
amsa kafin ya fita ni ma na take masa baya ina kiran sunansa amma yayi banza da ni haka na
koma a kunyace.

A nan bakin asibiti Mubashar ya siyo jus ɗin ya dawo,anty Maimuna ce ta bayar da kofi aka
tsiyaya masa ya sha bayan nan ya lumshe ido kafin ya ce “Mubashar kira min likita ya zo ya
sallame ni ”
“Wane irin a kira likita ka ga kuwa halin da aka ɗauko ka? Kawai ka bari har ka ƙara samun
lafiya” cewar Hajiya Balkis wanda hakan ne ya tsayar da Mubashar, Sheikh ya dube shi kallo
irin mi ka tsaya jira shi kuma ya ce “da dai ka ƙara haƙuri zuwa an yamma”
“To Allah kai mu”


Da rana abincin da muka kawo ne aka zuba aka ci,wanda ni sam na kasa ma tantance daɗinsa
saboda yadda Mubashar ke wani hura min hanci sai shan ƙamshi yake.Bayan sallar azahar ne
muka wuce gida ni da anty Maimuna,a hanya take tambaya abin da ya haɗa mu da Mubashar
amma na ƙi bata amsa.Da muka isa gida haka ta yi ta duba kayan da ke ciki ta na yabawa ni
dai ina gefe ina kallonta haɗi da tunanin wai yanzu gaske na zama matar Ali.



A can asibiti kuwa yamma na yi likita ya sallame Sheikh Muhammad bayan an yi masa gwaji an
ga jikin nasa yayi sauƙi sosai.
A mota Mubashar ne ke tuƙi, Sheikh na zaune gefensa a can baya kuma Mama ce da Hajiya
Balkis hira suke kan zancen lefen Sharifa da aka kawo ita Hajiya Balkisun ce ke sanar da Mama
ai Ali ɗan ƙawarta ne da dalilin da ya hana ta zuwa wurin kawo lefen.
“Amma Sharifa ta yi dacen miji don Ali babu ruwansa da ƴan mata duk kuwa kuɗinsa” Mama dai
ba ta ce komai ba sai murmushin yaƙe,“amma ba da ita zai tafi ba ko? Ko da yake na ji uwarsa
na cewa a bari sai Sharifar ta gama karatu ban sani ba ko Ali ya yarda”yadda Hajiya Balkis ta
ƙure Mama da ido yasa a doli ta bata amsa da “juma'a mai zuwa za ta tare don ba wani
babban...” maganar ce ta yanke sakamakon sakin mota da Mubashar yayi ya na ta ƙoƙarin
danne burki amma ya kasa sai da Sheikh ya taimaka masa.Cak motar ta tsaya, Mubashar ya ja
wani dogon numfashi kamar ransa zai fita kafin ya aro jarumta ya lalubo nutsuwa ƙira'a ya saka
ya ƙure volume kafin ya ci gaba da tuƙin.
Sheikh ya juya ya kalli Mama kafin ya maido dubansa kan titi,lokaci zuwa lokaci kuma ya na
ankare da Mubashar har suka isa gida.Da taimakonsa Sheikh ya isa har ɗakinsa,Mubashar zai
fita amma ya tsayar da shi ya na mai cewa “ka je ka yi wanka wani zai zo ku tafi wani gun ”
“To bari na je gida”
Sheikh ya rumtse ido tuna har yanzu fa Mubashar gidan Mama yake da zama,“ok ka yi sauri ”


Mubashar na fitowa Mama ta miƙe suka fita ,shi ya tuƙa ta har gida amma babu wanda ya cewa
wani komai.

Wanka yayi ya shirya kafin ya koma can gidan Sheikh ɗin,tuni mutumin da za su tare ɗin ya zo.
“Ina katin ɗan ƙasar ka yake?” mutumin ya tambaya, Mubashar ya fiddo ya nuna masa sai suka
yi wa Sheikh sallama suka fito.
Shi ke tuƙi Mubashar na gefen shi,sai nasiha yake yi masa har suka isa inda ake paspo ba su
wani ɓata lokaci ba aka yi wa Mubashar duk abin da ya dace kafin a sanar da shi nan da kwana
biyu ya dawo ya karɓa.


Mutumin ya maido shi gida,sai a lokacin Mubashar ya samu lokacin yin tunanin da bai yi ba
.Yadda Sharifa ta bugu ba ƙaramin zafi yayi masa ba amma sanin ta haramta gare shi yasa bai
yi yunƙurin tare ta ba.Hawaye suka ciko idonsa ji yake kamar yanzu ne Mama ke cewa juma'a
mai zuwa za a kai Sharifa gidan wani ƙato namiji wanda ba shi ba.Rurin wayarsa ne yasa shi
dawowa hayyacinsa,Ammy ce da sauri ya ɗaga .
“Ina ta jira ka kira ni amma shiru,ya ne ka sauka lafiya ya mai jikin?”
“Da sauƙi Ammy,har ma mun dawo gida”
“To ka bani shi na yi masa ya jiki”
“To kashe in na shiga bangaren shi sai na kira ki”cewar Mubashar kafin ya fito daga ƙarƙashin
innuwar mangoro ya wuce ciki. A zaune ya tarar da Sheikh a falo ya na duba wasu takardu,cikin
girmamawa ya sanar da shi Ammy na son magana da shi. Sai da yayi ɗan jimmm kafin ya
amince, Mubashar ya kira bayan Ammy ta ɗaga ne ya miƙa masa,“assalamu aleykum ustaz ya
gida ya ƙarfin jikin?” sai da Sheikh ya lumshe ido saboda jin muryar da ya jima ya na jin
ƙishirwar ta ,“Alhamdullah jiki yayi sauƙi na gode sosai ” ya furta muryarsa na rawa.
Ammy ta ce “ni ke da godiya Alhaji , Allah ƙaro afuwa yasa kaffara ne” ya amsa da “amen Ya
Rabb na gode!" Kafin ta miƙa wa Mubashar wayar ba don ya gaji da muryar ba a'a sai don jin
wani yanayi wanda ya tunatar da shi ashe har yanzu namiji ne shi.



“Ka tsaya ina son yi magana da kai” Sheikh ya tsayar da Mubashar da ke ƙoƙarin fita “ammy
zan kira ki daga baya” bayan ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sai ya zo ya zauna gabansa.


“Ina son fitar da kai waje domin ci gaban karatun ka wace ƙasa kake son zuwa?” Sheikh ya
tambaye shi .
“Duk wacce ka zaɓa ta yi”
“Zaɓin ka shi ne nawa” Sheikh ɗin ya faɗa ya na tsure shi da ido kafin kuma ya turo masa
takarda mai zanen ƙasashen duniya.
Idon Mubashar suka ciko da hawaye,wai yau shi ne ake neman zaɓinsa domin zuwa wani gun
da mota ba ta zuwa sai jirgi kamar ba shi ne almajirin nan ba wanda yake kwana bakin titi.


“Daddy ka zaɓa min” ya furta muryarsa na rawa, Sheikh ya saki wani murmushi mai sauti ya na
jin zuciyarsa fara sol Mubashar ne farkon wanda ya kira shi da sunan Uba duk da Sheikh

yaransa ke kiran shi.
Ya sauka daga kujera ya rungume shi ya na bubuga bayansa “ya isa haka! Yi shiru zan zaɓa
ma ai dama haƙi ne na Uba ya aika ɗansa wurin da ya dace da shi”


Hajiya Balkis da ta fito daga kitchen tun ɗazu ta taɓe bakinta kawai kafin ta wuce ɗakinta baƙin
ciki fal zuciyarta .
Tsawon lokaci Sheikh ya sake shi suka koma zancen karatu ya na yi masa tambayoyi shi kuma
ya na basa amsa.





FAHAD

Ji yake matakin da ya ɗauka shi ne daidai,duk da kuwa ya na cutuwa da rashin Sharifa.Iya
romance kawai ke shiga tsakaninsu amma ya fi samun nutsuwa da ita kan sauran ƴan matansa
da suke sheƙe ayarsu.
Sannu a hankali soyayyar shegen ɗansa ke ratsa zuciyarsa,har yau ba a yanka masa rago ba
sunansa dai Jamilu.Kusan kullum ya na fita aiki don samo kuɗin sayen madara,babur ɗinsa
kuwa tuni ya aika abokinsa Kb ya ɗauko masa shi a gidan su Sharifa.

Yau ya na zaune a gida ya na hutawa kwatsam Kb ya aiko masa hoton Sharifa da Ali ga
akwatinan aure a tsakiya.Zumbur ya miƙe zuciyarsa na bugun tara-tara,ya mirza ido ya fi sau
goma don tabbatar da ko idon ne nasa ke masa gizau amma tabbas Sharifar dai ce .Sam bai
taɓa tunanin ko saurayi ta saurara ba ballantana ta kai su da zancen aure. Karon farko kenan da ya kira ta tun bayan da uban dukan da ya sha,sai da ya jera kira wajen
bakwai kafin a ɗaga,FAHAD dama tuni zuciyarsa ta yi rauni kawai sai ya fashe da kuka ya na
cewa “Rifa dama akwai ranar da za ki manta soyayya ta har ki amince da auren wani? Wallahi
duk duniyar nan babu wanda ya fi son ki sama da ni har su munafukan iyayen naki masu hure
miki kunne ki na ji na ko? Don Allah kar ki amince na san tabbas auren doli ne za su miki ni
kuma da na bar sauraren ki shine kika amince,to ki yi haƙuri ki fito mu gudu mu....” Mubashar da
zuciyarsa ke tafarfasa ya yi saurin katse shi “kai banza ka cika min kunnuwa da shirmen
ka,alamu sun nuna ka manta dukan da na yi maka har yasa ka buɗe ƙazamin bakin ka kake
wani cewa ta fito ku tsere to tsaya na faɗa maka billahil azim ko ka yi saurin cire wannan
banzan tunanin daga kan ka ko kuma haɗuwa ta da kai hummmm” sai kawai kashe kiran.
Fahad ya kalli wayar ya na ƙara jin wani tashin hankalin,hoton ya sake dubawa ya ga dai ba na
Mubashar ba ne wannan soja ne.
Babu shiri ya fito ya zuri takalmi kamar wani mahaukaci haka ya ɗau mashin ya nufi gidan su
Sharifa.Yayi niyyar ko kirɓin gumba za a yi masa sai ya je,ya na shiga layin ya ga motocin
sojawa su ma duk sayen suke da kakin soja wanda babu tantama abokan angon ne.Gefe guda
kuma ƙawayen amarya ne kowacce ta ci ado,can ya hango Ramlah wacce yake jin haushinta

don ya san babu ta yadda za a yi ace ba ta san an kawo kuɗin auren Sharifa ba ga dukkan
alamu ma har an fara shagalin biki.



SHARIFA

Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka na koma,duk wani shirye-shirye ƴan gida kawai
ke yinsa.Mama ma sam ba ta wani damu da ta yi min gyara ba, babu abin da take ban na sha
ballantana gyaran fata.Yau muna ranar Alhamis wacce ita ce jajibir ɗin ranar tarewa wata,anty
Maimuna tun safe ta zo ta shafa min dilka a dukkan jikina haka ta dinga haɗa min kayan gyaran
fata ina wanka za ta yi min wani.Tuni na yi fresh na yi kyau,da na dubi kaina ga madubi sai da
na ji takaicin ina ma gidan Fahad ne za a kai ni ba na Ali ba?


Wuraren ƙarfe biyar na maraice duk ƙawayena suka hallara gidanmu don sai yau ne kawai za
su yi réunion su da abokan ango wanda a bakin anty Maimuna ne nake samun labarin shi ma
zai shigo gari.
Ina nan zaune cikin dangin Mama da suka zo tun daga Agadas sai ga Ya Mustapha ya
shigo,gaishe su yayi kafin ya mayar da hankalinsa kaina ya ce “ki fita zuwa lambu Ali na son
ganin ki” kai kawai na jinjina masa amma banda niyyar miƙewa.
Tun da aka kawo lefe ba mu yi magana da shi ba,don Ya Mubashar ya ƙi ban wayata hasali ma
ya bar barin hanyarmu ta haɗu da na sanar da Mama kuma ta yi kamar ba ta ji ba dole na barsa
da ita.
“Ke ba magana nake yi miki ba?” ya Mustapha ya daka min tsawa,da sauri na miƙe ina gyara
zaman sahari na da ke barazanar kwancewa na nufi ƙofa da sauri.


Ina ƙoƙarin bin hanyar da za ta kai ni lambu na kai masa karo na yi baya zan faɗi ya jawo ni na
faɗa kan ƙirjinsa.Iya ƙamshin jikinsa kawai na ji na fahimci wane ne,ban san lokacin da na fashe
da kuka ba na ce “Ya Mubshar shi ne kake fushi da ƙanwar ka a lokacin da ta fi buƙatar ka.Kai
fa malamina ne babu abin da ka koya min na dangane da zaman aure ko da yake ba son shi
nake ba” na ida furicin ina mai ɗan ja da baya don na ji tun ɗazu yake kiciniyar raba ni da
jikinsa.


Cikin idonsa na kalla wanda suka yi zurfi suka faɗa,ya motsa baki dakyar ya ce “Mijin ki na jiran
ki” sai kuma ya kauce ya bar ni nan tsaye ,ban gusa ba sai da ya ɓace wa ganina juyowar ga da
zan yi na ga Ali tsaye cikin kakin soja ya harɗe hannuwansa.A tunanina ko ya gan ni jikin
Mubashar ne sai na ji kunya na sunne kai,“amarya babu lalle?” na ji muryarsa daga sama. Na ɗago na dube shi,sai ya sakar min murmushi ya ce “kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0