Showing 18001 words to 21000 words out of 25466 words

Chapter 7 - Saurayina Book Compelet Writing Mrs Sadauki

yi kyau ma sha Allah,ganin ki kawai
ya sa na ji duk fushin da nake yi da ke ya ɓace” sai ya zo kuma yayi hugging ɗina ya na son
sumbatata na kauce ai kuwa ya riƙe ni gam ganin in na yi wasa kissing ɗin nawa zai yi kawai na

ɓoye fuskata cikin ƙirjinsa ina ce masa “ban so! Ban so!” bai kula ni ba sai kuma na ji wani
sabon salo hannunsa kan fatar cikina.Kuka na fashe masa da shi sai ya sake ni,“ina wayar ki
kullum ina kiran ki ba ki ɗagawa?” ya tambaye ni.
Na turo baki na ce “ta na hannun shi”
“Wa?”
“Ya Mubshar!”
“Mubashar ɗin ne ya koma Mubshar?”
Na gyaɗa masa kai ya ce “ok koma ciki zan fita waje su na jirana”
“Har yanzu ba su tafi ba?”
“Eh! Amma an kama wurin da za su tattauna ɗin abin da aka tsayar kenan sai su faɗa miki ” na
jinjina kai kawai .

Sai da ya kawo ni har bakin ƙofar shiga falo sannan ya fice.
Abun mamaki Mubashar na tarar a zaune cikin dangina sai jansa suke da hira duk da alamu
sun nuna shi fa ya matsu ya tafi.Muka haɗa ido da shi na ga ya na ƙare min kallo,can kuma ya
miƙe ya fice na bisa da kallo ina juyowa kuma muka haɗa ido da Mama.Ɗakina na wuce na bar
gun,na ma rasa abin da ke damuna.Sai can cikin dare ƙawayena suka dawo da uban kaya
niƙi-niƙi ,dogayen riguna ne iri ɗaya duk suka sayo uwanda za su saka a gobe kan
amarya,kuɗin da aka basu suka nuna min Ramlah ce babbar ƙawa wannan ya saka komai na
hannunta.


A can bangaren Mubashar kuwa shi dai haka yake jin ahalin Mama tamkar danginsa yanayin
yadda suka ja shi a jiki kamar sun san shi kuma suka nuna ma soyayya ƙarara.Ya lumshe ido a
karo na barkatai ya na ƙara shaƙar ƙamshin SHARIFA da har yanzu bai bar jikinsa.Ya na nan
zaune saƙo ya shigo wayarta,ya duba ya gani hankalinsa ya tashi ganin lambar FAHAD ce .......

Ga masu son fara payment 500 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ku turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[29/04 à 13:12] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻


LoVe and HoRrOr story💔☠️


```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________
________________________

Page 8


Jikin Mubashar har rawa yake yi lokacin da ya karanta saƙon.A zuciye ya fara neman layin
FAHAD ɗin,ya na ɗaga wa ya fara mayar masa da martani “in ka fasa zuwa sace ta daga tsaye
uwarka ta haife ka,zo ka ɗauke ta tun yau ba sai gobe ba” ƙittt ya kashe kiran kwanyarsa na
mugun sarawa,wato ya fahimci muddin budurwa ta yi rashin dace da saurayin albarka to tabbas
rayuwarta na cikin kwata.A daren sam bai rumtsa ba,da zullumi biyu ya kwana ya rasa wacce
yake so ga kuma wani banza na son jefa ta cikin matsala.
Washegari tun asuba ake ta hidima ,Mubashar na dai ta dauriya amma sam ya kasa
nutsuwa.Sheikh ma ya zo saboda mahaifiyarsa Mami da ta matsa har yanzu ba ta gansa
ba,Mama ta sanar da ita Mubashar ɗan Sheikh ne amma ko kaɗan ba ta yi kuskuren shaida
mata wai ya na son Sharifa ba so take abun kar yayi nisa musamman da ta hango mugun son
Mubashar a idonta kasancewar shine ɗa tilo gun Sheikh.



Iyayen ango sun zo domin ƙara jadadda godiya,ambaton sunan Ali kawai ana jona shi da na
Sharifa tafasa zuciyar Mubashar yake.
A hankali ya matsa kusa da Sheikh ya ce “Daddy yanzu za a iya samun jirgin da zai tashi?”
Bai basa amsa ba sai kawai jansa da yayi suka nufi mota,hakan kuma ba ƙaramin daɗi ya yi wa
Mubashar ɗin ba.Direba ne ke jansu su kuma su na baya,ya lumshe ido ya na hango fuskar
Sharifa wacce ta sha ado da kayan kwalliya na zinare tamkar wata matar indiya.Waya Sheikh
ke yi amma bai tsinci komai a ciki ba,ya dai ji mota ta tsaya sai ya ga suna cikin filin jirgi.Dama
komai na cikin mota tun daga paspo har ticket,Mubashar yayi tunanin shi ɗaya zai tafi sai da
aka zo shiga jirgin ne ya ga Sheikh ma ashe zai bisa.


A wannan gaɓar ne yake jin wata irin soyayya da ƙaunar Sheikh na ƙara huda ɓargon jikinsa.Ya
sa hannunsa cikin nasa ya ce “na gode sosai Daddy ka bani kulawa wacce ko mahaifina ne kai
sai haka” murmushi kawai Sheikh yayi gudun kar ya buɗa baki zuciyarsa ta rufe.
Daga nan cikin jirgi Mubashar ya rubuta wa Ali text kamar haka «ina taya ka murnar mallakar
ƙaddara mafi daraja a duniya ta,don Allah ka riƙe Ifa amana kar ka cutar da ita sannan ka jona
mata tsaro na musamman ta yadda FAHAD ba zai ƙara shiga rayuwarta ba.Ka kula sosai yayi
ikirarin zai sace ta a yau wurin kan amarya, wannan dalilin ne yasa ma na ƙi bata wayarta» Da ya aika saƙon sai ya nuna masa ya ƙi zuwa,hasali ma layin ya sauka sai alamar jirgi✈️ a
zuci ya ce ‘ashe har yanzu baƙauye ne ni wato in ana cikin jirgi sauka komai yake’ sai kuma ya
miƙe zai fita Sheikh ya tsayar da shi “ina za ka je?”
“Zan tura saƙo mai muhimmanci ne” ya basa amsa tare da fita,sai da ya tabbatar saƙon ya tafi
sannan ya koma ciki.

SHARIFA

Dukkan amare su na farin ciki ne a irin wannan babbar rana wacce ƴan magana kan kira ranar
farin ciki! Sai dai ni akasin haka ne a wurina.Baƙin ciki ,tsoro da fargaba sun yi wa zuciyata
ƙawanya.Duk hidimar biki da ake yi sam ba ta gabana,lokacin da aka fitar da ni domin gaishe
da iyayen Ali ji na yi kamar na zage su ko ƙila Allah yasa ya sake ni.A ɗan nesa da ni na hango
fuskar Mubashar wacce ba sai an faɗa ba ka na gani ka san bai cikin farin ciki.Da tunanin mike
damunsa na wuni,ana tsaka da cin biki kuma labari ya riske mu wai ya tafi Misira wurin karatu
babu sallama ba komai.


Da dare aka shirya ni kamar kowacce amarya,bayan na sha nasiha ƙanwar Mama da kuma
wasu daga cikin dangin Papa suka ja ni izuwa waje.
Yadda aka baza sojoji ta ko ina kai ka ce juyin mulki ne za a yi,ina kuka ina ƙari aka shigar da ni
motar.
Aka ce ko an yaudari kowa banda zuciyar da ta kamu da soyayya,a hankali na soma buɗe
mayafin da rufe min fuska saboda ƙamshin turaren FAHAD da na ji ya cika motar amma sai dai
sam ba shi ne a mazaunin direban ba.Ƙofofin hancina na buɗe ina shaƙo ƙamshi tabbas dai
nasa ne,a zuci na soma magana ‘ Allah sarki masoyina yau zan tafi gidan wani wanda ba
kai,lamarin da bai taɓa zo min ko a afarki ba ballantana na yi tunanin haka.Fahad ka cutar da
mu duk laifin ka ne yasa hakan ta faru,kai kuma Ali tsakanina da kai Allah ya isa ka raba ni da
farin cikina ’ sai na fashe da kuka.
A haka dai aka miƙa ni gidana da ke can unguwar plateau,irin uwar dukiyar da Papa ya zuba
min kai kace ƴar minista ce ni amma sam duk munin su nake gani saboda ban auri wanda
zuciyata ke so ba.
Lokacin da kowa ya watse ƙarfe ukun dare ta gota,irin rakiyar nan da ake yi wa ango sam Ali
bai same ta ba shi ɗaya kawai ya zo.
Duk yadda yake ƙoƙarin ɓoye damuwarsa sai da na san akwai matsala,ban tambaye shi ba na
dai bi umarninsa ne na je na yi alwala.Bayan ya ja mu sallah ya gabatar da abin da ya shigo da
shi,da hannunsa yake bani ni kuma sai imagination nake in na ganin FAHAD ne a gabana
wannan ya saka na saki jiki na ci na ƙoshi muka sha madara. Wani salon soyayya irin na FAHAD da Ali ke yi min ya ƙara shagaltar da ni na ji na yarda kawai
da Fahad nake tare.Ban dawo hayyacina ba sai da na ji ya na ƙoƙarin raba ni da budurcina,“a'a
Had ban so kar ka yi wannan!” na faɗa ina jan numfashi.


Ali ya kunna ƙwan fitilar da tun farkon hawan mu gado ya kashe,tsoro ne ya kama ni ganin
yadda ya ɓata zanen gadon da ke shimfiɗe.Abu ko shiga bai yi ba wai amma ya samu
nutsuwa,abin da ya fi ban mamaki kamar ma ya ji daɗin haka.Na dire daga kan bed na wuce
toilet,shower na sakarwa kaina ina jin sanyin ruwan na ratsa ni.

A can bangaren Ali kuwa lokacin da yayi niyyar kusantar Sharifa ji yayi duk wani desir ɗinsa ya
tawo gaba ɗaya kafin ƙyaftawar ido.In ya ce bai ji daɗi ba to yayi ƙarya,amma sosai yayi
mamakin yadda ko shigar ta bai yi ba amma abun ya zube.Ya ɗan ja ajiyar zuciya a fili ya furta
“ƙila don ita matar aurena ce ba kamar sauran matan ba” sai kuma ya saki murmushi ya sauka
ya cire zanen ya shiga toilet.



Da sauri na juyo jin an buɗe ƙofa,jikina na soma rufe wa ina kallonsa.Ali kuwa ji yayi kamar
numfashinsa zai ɗauke ganin ainahin surar Sharifa a cikin ƙwan lantarki,ɗazu ma ya kashe ne
saboda kar ta yi zargin ko ya san mace kafin ta.
Wata irin muguwar buƙatuwa ce ya ji ta na bijiro masa haɗi da game duk illahirin jikinsa sai dai
kash ya na isa kusa da ita ya ji wani irin sanyi ya rufe shi.
Tun da na ga Ali na nufo ni na rumtse ido gam,ina jiran in ji ya fara wasa da jikina na ji tsit
hakan yasa na buɗe ido.Gabana ya faɗi ganin mugun al'amari,ban gama ma fita daga wancan
mamakin ba kuma yanzu ga wani ya ƙara shayar da ni.
A zuci na ce ‘ko dai bai da lafiya ne?’ sai kuma kawai na jawo towel na ɗaura tare da fice wa.


Ali kuwa wannan karon ya ji tsoro sosai,sai ya fara tunanin kar dai ace cikin matan da yake
holewa da su ne wata ta yi masa asiri amma kuma sai wata zuciyar ta rarrashe shi ta ce masa ‘
ta yiyu dai don Sharifa matar ka ce ta sunnah ka ƙara gwada wa ka gani’ a haka dai yayi wanka
ya jefa zanen gadon a mashine ya wanke.


Tun da na fito na rataya doguwar rigar na haye doguwar kujerar da ke nan gefen gado sai
bacci.
Ina tsaka da hutawa ta ya tashe ni lokacin sallah asubah yayi,haka na miƙe na je na yi alwala
na zo na gabatar.
Sanyin AC na ƙara sannan na haye bed wanda na ga tunu Ali ya sake masa shimfiɗa,yadda ya
zo ya wani jawo ni ƙirjinsa yasa na buɗe ido tarau.Kamar wani tsohon maye haka ya dinga
bibiya ta, wannan karon da yayi yunƙurin kusantata sai jini ya ɓalle min a dole ya haƙura.


Cikin jin haushi na wuce toilet na haɗa ruwan zafi na gasa jikina,abun mamaki jinin ya
ɗauke.Ina fitowa na shirya cikin riga da zane na atamfa na fito falo ina ta tunani iri-iri,ina nan na
ji ana buga ƙofa na je na buɗe Ramlah ce tsaye hannunta riƙe da basket.

Murya ƙasa-ƙasa ta ce “na zo ɗaukar zanen gado ne”
Na ƙyaƙyace da dariya na ce “ango ya wanke abinsa sai in ni za ki gasa ”

Ita ma dariyar ta yi ta na mai shigowa ta ce “inda an karɓe budurcin ai ba zan gan ki a nan ba”

“Hum! Mi kika kawo mana?”
“Ni ma ban sani ba,Mama dai ta ce na zo na kawo kin san can na kwana”
“Ok buɗe ki zuba mana bari na kira Ali”
“Ke fa ba ki da mutumci da sunansa za ki kira shi?”

“Eh mana ko FAHAD ai ɗan guntile sunan ne na yi”ina faɗar haka fuskar Ramlah ta canza kafin
ta ce “hum! Ai jiya ya sha na jaki tun da taurin kansa yayi yawa”
“Ban gane ba?”
“Ina fa za ki gane jiya ki na ta kuka ai ba za ki sanin abin da ya faru ba,duk fa uban sojojin nan
haka FAHAD ya ratsa ya shiga motar da za ta ɗauke ki hum wai sace ki zai yi don ƙarfin hali
har da saka kakin soja ko gidan uban wa ya same su oho”


Tun da ta fara zuba na kafe ta da ido,saitin zuciyata na dafe da nake jin ya na tsarga min.Idona
kuwa tuni sun fara tsiyaya, sama-sama nake jin muryar Ali ya na banbami ya na cewa wa ya ce
Ramlah ta sanar da ni.
Da na buɗe ido ne na ji ni tsudum cikin ruwa sai na fahimci ashe suma na yi,fashe wa na yi da
kuka haɗi da ɗora borin sai an kai ni gun FAHAD .
Cikin zuciya irin tasu ta sojoji Ali ya ce “wane FAHAD ɗin? Ba ki da hankali ne ina matsayin mijin
ki shi ne za ki kira min sunan wani banza”


Idona sun rufe har ban san lokacin da na ce “wallahi Had ba banza ba ne shi ɗin *SAURAYINA*
ne kuma shi nake s....” ban dire zancen ba Ali ya zuba min yatsunsa biyar har sai da na ga
taurari na gilma min.
Ya sa kai ya fita,ni ma na miƙe na take masa baya na buɗe murya sosai na ce “ don Allah kar ku
cutar da shi,ba laifinsa ba ne laifin son da yake min ne”
Cak Ali ya tsaya tare da juyo wa ,a hankali kuma na ga ya soma takowa ya zo gare ni.
“Ki na son na bar shi ya tafi kar a sake dukansa?”ya tambaye ni,na gyaɗa masa kai ya ce “ok je
ki sako hijabin ki ” ban musa ba na koma ɗaki har tuntuɓe nake yi na je na ɗauko ko ta kan
Ramlah ban bi ba wacce ke faman goge ɗaki.


A mota Ali ya ɗauke ni ,bayan mun sharara gudu muka isa Company ɗin su.Ina biye da shi har
muka isa wani part mai duhu,da fitilar wayarsa ya haska nan na hango Fahad yashe a ƙasa ya
na fitar da numfashi dakyar in aka ce ya sha duka to mai sauƙi ne sai dai ƙirɓar gumba.
Tako ɗaya kawai na yi Ali ya riƙe ni,ya ce “zan sa a bar shi yayi tafiyarsa amma ki sani ko ke ko
shi duk wanda ya sake tunanin ɗayanku zan sa a yi masa dukan da ko uwar da ta haife shi ba
za ta gane shi ba”
Ina kuka ina ƙari haka nake kallon yadda ƙananan sojawa ke yi FAHAD wanka da ruwa sai jan
rai yake,dakyar ya iya tashi ya na gwalar ido Ali ya kunna ampoule ɗakin ya gauraye da haske

mun haɗa ido ya rairafo ya kama ƙafafuna.....


*Yayana Laminou Gonda ina kawo gaisuwa*🌚

My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822
[01/05 à 09:30] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻


LoVe and HoRrOr story💔☠️


```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________
________________________



Page 9




Ban san lokacin da na zube kan gwiwaina ba,ina shirin jawo FAHAD jikina Ali ya wani ciro ni
sama kafin ya soma tafiya da mu da ƙarfi.Waiwayen FAHAD nake wanda yake ta kallona da
kumbararun idonsa uwanda suka kusa rufe wa saboda uban dukan da ya sha,sai a bakin mota
Ali ya dire ni da kansa ya shigar da ni ciki ina ta kuka a haka muka koma gida.

Ko ciki bai shiga ba ya ƙara fita,ina shiga falo na tarar da Ramlah ta rabka uban tagumi.Jikinta
na faɗa na shiga koro mata bayani masu taɓa zuciya dangane da halin da na tarar da
Fahad,rarrashina kawai take ta na kwantar min da hankali amma sam na kasa yin haƙurin
wannan lamari.A nan ta wuni sai yamma ta yi tafiyar ta bayan ta min girki da gyaran gida,dakyar
na aro jarumta na je na yi wanka na saka doguwar riga ta less.Mai kawai na shafa sai
turare,kusan mirror na yi tsaye ina ƙarewa halittar da Allah ya min kallo.Ina da tsayi amma ba
sosai can ba,ban da ƙiba kuma ba za a kira ni ramamiya ba,tsayin hanci dogon hanci da
manyan idona wanda gashinsu da na gira ta su ne suka ƙara masu kyau baƙaƙe wuluk kamar
doguwar sumar kaina wacce take har gadon baya.Laɓana sirara ne sun ɗan canza kala su ba
jajaye ba su ba pink ba,ina da albarkar Fulani da lafafen ciki hakan yasa shap ɗina ya fita kamar
coca cola.

Tunanin Mubshar ne ya faɗo min a daidai kuma wannan lokacin na ji ƙafata na min wani irin
ƙaiƙayi.Da sauri na je bakin bed na zauna ina sosa gun,ina shirin cire sarƙoƙin Ali ya shigo da
sallama kawai sai na fasa cirewa ina mai tashi tsaye ban amsa ba na zuba masa na mujiya.



Ya je kusan drower ya fara rage kayan jikinsa,ni dai ina tsaye ina kallon murɗaɗen jikinsa
wanda ka na gani kasan ya na ɗaukar ƙarfe . Toilet ya wuce yayi wanka ya fito,a inda ya bar ni
ko motsi ban yi ba.
“Ki zo ki shafa min mai” ya faɗa ya na wani zama gefen gado.
“Ban zo don shafa maka mai ba” na samu kaina da furta wa ina mai kafe shi da ido haɗi da
jifarsa da kallon tsana.
“Ki zo ki shafa min,ba zaɓi ba ne umarni ne” ya sake faɗa ya na haɗe rai.
Na taɓe baki na ce “in kuma ba haka ba?ko ni ma dukan nawa za ka yi kamar yadda ka yi wa
SAURAYINA? ”


Shiru yayi ya na kallona kafin yayi ƙyaci ya miƙe,a gabana ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0