Showing 24001 words to 25466 words out of 25466 words
Chapter 9 - Saurayina Book Compelet Writing Mrs Sadauki
riga da wando irin na tura wa ya ce na saka ya na son ganina cikin su,na yi
murmushi tare da karɓa na ce “yaushe ka saye su?”
“Sun ɗan jima! Ko na buɗe miki sauran akwatinan ki gani? Kayan lefen ki nake haɗa wa” ya
bani amsa tare da taimaka min na sa kayan ai kuwa tamkar wata baturiya haka na fito.
Ɗaya bayan ɗaya haka FAHAD ya buɗe min duk na ga komai,sosai na ji daɗi ina jin ƙaunarsa
na ƙara haɓaka.Falo muka wuce,Sulvi ta kawo mana abinci ya fi iri goma ina zaune raɗam kan
cinyar shi ita kuma ta na sanar da shi sunayen abincin.
“Zuba min shinkafa da miyar biri,babyna ke mi kike so?”
Da mamaki na dube shi na ce “biri kuma? Yaushe aka halitta mana cin Biri kuma?”
Wani kallo ya min wanda ban san na mine ne ba kawai sai na ji ma kamar na manta tambayar
da na yi.
“Zuba mata acake da kifi” ya ba Sulvi umarni,plate biyu ta ɗauka ta zuba wa kowa nasa sai a
lokacin na zauna kan kujera.Bayan mun gama ne na ce masa ina son zuwa gida,na saka
hijabina muka fito.
A hanya ne yake ce min “na yi tunanin nan za ki zauna sai dare ki koma amma da alamu duk
kin damu ki zo baƙin gidan nan”
Na ce “gobe ake karrama mu a makaranta shi yasa”
“Ok amma gobe a gidana za ki kwana”
Na yi shiru ban ce komai ba,“ko ba za ki zo ba?” ya tambaye tare da min shegen kallonsa
wanda ban san yaushe ya koye shi ba amma sam bai da daɗi sai nake ganin ma kamar idonsa
su na canza wa.
Na haɗiye yawu na ce “zan zo”
“Tun da kin yi alƙawari na yarda,in ma ba ki zo ba da kaina zan shigo har gidan na ɗauke ki” ni
dai ban ce komai ba har ya kawo ƙofar gidana,sai da ya min kiss kafin na fice.
Ina shiga na tarar da Ramlah ta cika ta yi fam kamar za ta fashe,na ƙyalƙyace da dariya na ce
“fushin na mine?”
“Ban sani ba tun ɗazu kin samu wuri kin yi zaman ,daga ina kike ma wai?” ta tambaye ni ta na
wani kallona,sai da na ja ajiyar zuciya na ce “zan faɗa miki ba yanzu ba” sai kawai na wuce
bedroom.Kan gado na haye bayan na cire hijabi,na lumshe ido ina tuna moments ɗinmu.
“Ina kika samu uwannan kayan?” na ji muryar Ramlah daga bayana.Da sauri na tashi zaune
muna kallon juna,tambayar ta sake maimaita wa ni kuma ba tare da wani ɓoye mata ba na ce
“Had ya saya min”
“Wane Had ɗin?”
“Fahad mana”
“Yaushe suka dawo Nijar?”
“Wallahi ban sani ba ni ma yau dai na haɗu da shi kasuwa”
Ramlah za ta yi magana kenan ,Ali ya shigo bakinsa ɗauke da sallama da sauri ta fita yayin da
shi kuma ya tsure ni da ido.Sanin halinsa ba ƙaramin aikinsa ba ne ya nuna min na jaki ba yasa
na kawar da kaina,“daga ina kike? ”
“Kasuwa na tafi”na basa amsa .
“Mi kika siyo? ”
“Kayan da zan sa gobe ko?”
“Su na ina?” ya watso min tambaya.
Na yi shiru ina tunani ,tabbas na bar su a motar FAHAD.
“Ba ki ji abin da na ce ba?” ya daka min tsawa ya na ƙara matso wa,bakina na rawa na ce “su
na cikin drower” tare da nuna masa da yatsa.
Ali ya je ya buɗe drower nan take ledodi suka faɗo,ya ɗauko su tare da buɗe wa ya na duba wa
haɗi da karanta reçu/ receip .Ni kuwa mamaki ne ya kusan kashe ni ganin kayan da na bari a
mota ga su kuma a ɗakina.Ya mayar da kayan ya fice,na ja wata wawiyar ajiyar zuciya ina mai
cewa “to ya aka yi suka zo nan?” sai kuma na soma tunanin ko na shigo da su ne,ganin zan
sawa kaina ciwo kawai na share na soma baccin gajiya.
Ali kuwa ya na fita direct kitchen ya wuce inda yake jin motsin Ramlah.Wani irin finciko ta yayi
ya ce “daga yau in na sake jin banzan shirmen ki wallahi ni da ke ne.Kin san aikin da nake yi ne
kika taso ni ? Kawai saboda banzan kishin ki a dole so kike mu yi faɗa ni da matata”
Ramlah ta fincike hannunta ta ce“oh matar ka ce? Shi ne ta kasa yi ma komai ina ce ni nake
sauƙe duk buƙatun ka sama da shekara ɗaya.Ka na ji Ali wallahi na gaji kawai ka aure ni ko
kuma na tona ma asiri” Ramlah ta faɗa ta na jin wata irin da na sani,saboda cin amanar ƙawar
ta da take yi ita da mijin ta wanda ba komai ya jawo hakan ba sai yadda SHARIFAr ke bata
labarin sirrin aurenta sannan kuma da kwaɗayi da hassadar ƙawarta ta auri wanda ya fi
masoyinta Kb.Tun lokacin auren Sharifa bai wuce wata biyu ba Ramlah ke shige da fice har sai
da ta ja hankalin Ali,ta yi hakan ne don cin kuɗinsa tun da Sharifa ta tabbatar mata ya na da
muguwar sha'awa sai dai fa ko kafin akai ga yin sex komai ke lalace wa.Ta zata za ta ci bulus
sai kogo ya juye da Mujiya Ali ya karɓe budurcinta ta mummunar hanya,ta yi kuka har ta gaji a
ƙarshe kuma ta shafe idonta da toka suka dinga holewar su kai kace wasu ma'aurata har da
ɗaukar maganin tsarin iyali.Burin ta guda a yanzu shi ne Ali ya aureta,shi kuma ya tabbatar
mata har abada ba za a yi cin amana da shi ba sai dai in bai auren Sharifa, wannan hujjar ta
saka Ramlah a doli sai ta samo laifin da zai sa Ali ya saki Sharifa har wani ta samu wanda zai
dinga bin bayan Sharifa duk inda za ta je.
Ali ya dubi Ramlah,kallo irin na ba ki da hankali kafin ya ce “na aure ki? Mi za ki min wanda
yanzu ba ki min ba? Ki na ji na ko? Ki buɗe kunnuwan ki babu aure tsakaninmu” ya na gama
faɗa ya ficewar shi.
FAHAD
Tun bayan haɗuwarsa da Sharifa yayi dubarar haɗa wani plan kanta ,na kula da duk wani
motsin ta da abin da ya shafe ta.Ya na tsaka da driving ya ji ledodi na motsi daga
bayansa,kallonsu kawai yayi ya fahimci abin da ke faruwa.Umarni kawai ya basu ya na mai
furta wata kalma kawai suka ɓace suka kai kansu cikin drower Sharifa.
Cike da annushuwa ya isa gida,tun bayan rabuwarsa da ita bai taɓa samun nutsuwa ba sai yau
kuma da idonsa suka sake tozali da ita.
Ya na isa gida ya hau bene,bai tsaya ko ina ba sai bakin ƙofar da ta sha banban da kowacce
ƙofofin da ke jere,don ita hatta pentin ta daban yake .
Bayan ya buɗe ta na ya soma shiga da baya-baya har zo tsakiyar ɗakin wanda tsabar duhunsa
ba ka iya ganin komai amma a haka FAHAD yake yin wani yare.Kyandirori ne suka kawo jar
wuta kamar jini,hakan ya ɗan haskaka ɗakin wanda komai nasa ja ne in ka cire baƙin capet ɗin
da ke shimfiɗe a duk illahirin wurin.
Gumki da ke tsaye ƙiƙam FAHAD ya je ya yi wa sujuda kafin ya tashi ya yanka yatsansa ya kai
bakin shi.Kamar wani mutum mai rai haka ya dinga zuƙar jininsa na tsawon minti biyu kafin ya
saki yatsan,a nutse FAHAD ya soma yin magana “Gourou ka cika min alƙawari,na samu
masoyiyyata silar shiga ta ƙungiyar asiri.Ka faɗa min wane irin tukuici zan yi ma domin nuna
godiya ta gare ka?”
Kamar daga sama gumkin ya buɗa baki ya ce “ita nake so! Sharifa nake so ka kawo min ita ina
son shan jinin ta!”.
Ƙarshen free page !
*Ya aka yi FAHAD har ya shiga ƙungiyar asiri? Ta wacce hanya ce? Shin zai kai bayar da
Sharifa ɗin? Mine ne makomar Ramlah? Shin ina labarin MUBASHAR ?*
Mu haɗe a PAID GROOP duk za ku mu ji ainahin abin da ya faru shekara ɗaya da ta
wuce,sannan za mu ji yadda gourou gumkin da FAHAD ke yi wa tsafi za su kaya.
Mai son shiga group only 500 ne via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500 .Ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta
500f,sai ku tura shaidar biya ta WhatsApp +22795045822.
Ga account nan kawai ki yi payment ki turo min evidence haka ma masu turo kati,wacce ta san
ba ta da niyyar biya ta yi wa Allah kar ta min magana na gode!
MRS SADAUKI Nijar í ¼í·³í ¼í·ª