Showing 12001 words to 15000 words out of 25466 words
Chapter 5 - Saurayina Book Compelet Writing Mrs Sadauki
yayi sanadiyar rabata
da mutumcin ta.Sai bayan komai ya lafa ne suka farga,haka ya taimaka mata dai ta kimtsa ba
tare da sanin ashe a wannan daren Allah ya ƙaddarar rabo ya shiga”
“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un ! Cikin shege?” kallona yayi kawai,“tashi mu tafi!” na miƙe da
sauri na bi bayansa ina mai cewa “to ya aka yi gaba?” bai ban amsa ba har muka shiga mota.
Kallonsa kawai nake har muka isa gida,da zan fita na ce “Ya Mubshar ka faɗa min mi ya faru
mana”
“Sai in an jima zan sanar da ke ,yanzu makaranta an koma akwai jarabawar da zan yi”
Na turo baki kafin na fice,shi kuma ya ja motar ya tsaya bakin get sai da direba ya shiga kafin
su wuce.
Ina shiga ciki na zube falo ina faman yi wa Mama ƙorafin na gaji.
“An dai kusa yin auren ki na ga ta rakin kin gaji can ai doli ki girka abinci da kuma aikin gida”
cewar Mama.
“Ni dai ban shirya ba sai..” ban kai ƙarshe ba Mama ta ce “in an jima iyayen Ali za su zo ki tashi
ki tafi gidan Antyn ki”
Tamkar aradu haka na ji,ko kafin na yi wa Mama tambaya tuni ta tashi.Ni ma ba shiri na wuce
ɗakina sai a lokacin na tuna kuma wayata na ga hannun Mubshar.Toilet na faɗa na yi wanka,
zuciyata sai matsanancin bugawa take a haka na fito na yi sallah na shirya cikin riga doguwa da
hijabinta .Ƴar ƙaramar jaka na ɗauka na fito na yi wa Mama sallama,maimakon na je gidan anty
ɗin kawai na cewa mai taxi ya kai ni Imam Malik.
Bayan na biya shi ne na shiga daga ciki,sai kuma na rasa wane ɓangare zan bi tsabar girmanta
ina nan ina shawagi a ciki har aka fito sallar Asar nan na ware ido ko Allah yasa na ga Mubshar
ɗin sai dai abun takaici duk mazan jallabiya fara ce da su.Tuni idona ya fara kawo ruwa,kamar
daga sama na ji an ce “ Ifa ” har ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min don shi kaɗai ke
kirana a haka.
Ina ɗan waigawa idonmu ya sarƙe cikin na juna,ban taɓa yi masa kallon ƙure ba sai yau dogo
ne sosai mai faɗin ƙirji.Ya na da doguwar fuska da dogon hanci,idonsa madadaidaita ne ba su
fiya girma ba,bakinsa na ɗauke da laɓa masu kauri baƙaƙe wanda sajensa ya ƙara masa
kyawu.Ban san ya iso gare ni ba sai da na ji ya busa min iskan bakinsa,na lumshe ido hakan ya
baiwa ƙwallar da ta ciko idona damar saukowa kan kumatuna.Tattausan hannunsa na ji cikin
nawa ya na mai cewa “zo nan!” haɗi da jawo ni gefe,sai a lokacin na buɗe ido.
“Mubashar wace ce wannan?” a tare muka juya sai na ga ashe Yayan Mama ne sheik
Mohammed.
Gaishe shi na yi sai na ji ya ce “Kamar Sharifa nake gani”
Na ce masa “ni ce!” sai na ga ya kalli hannunmu da ke cikin na juna,sai a lokacin Mubashar ya
sake ni.
Sheikh Muhammed yayi tafiyarsa ya na mai cewa “lokacin sallah yayi ta je ɓangaren mata ta yi
alwala,in an gama kuma ina son ganin ka a office ɗina”
Na ja wata wawiyar ajiyar zuciya ina saƙa wani abu a raina wanda ban sani ba ko idona ne ba
su gane min daidai ba....
[26/04 à 09:57] MRS SADAUKI í ½í±‘: *SAURAYINA*í ½í²…í ¼í¿»í ½í²…í ¼í¿»í ½í²…í ¼í¿»
LoVe and HoRrOr storyí ½í²”☠️
```MRS SADAUKI```✍í ¼í¿»
Dedicated to Autar Manyaí ½í±‘
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________
________________________
Page 6
Ɓangaren mata Mubshar ya kai ni ya na mai yi min magana cikin taushin murya “ki nutsu ki yi
sallah in kin gama ki jira ni a nan cikin masjid zan zo na neme ki kar ki je ko ina kin ji ko?”
Tsakiyar idonsa na kalla ina mai jinjina masa kai,kamar wata ƙaramar yarinya da ya juya zai tafi
na tsayar da shi .“Ya Mub...shar don Allah kar ka jima ban san kowa ba a nan” ya sakar min
murmushi kafin ya tafi .Toilet na shiga na ɗauro alwala sannan na shiga masjid ɗin mai cike da
mata duk sun sha manyan hijabai har ƙasa.Na shiga sahu na yi tsaye har aka tada sallar,bayan
an gama da ɗaiɗaya duk suka fita na yi saura ni ɗaya kawai sai faman zuba wa ƙofa ido nake
ina jiran shigowar shi.
An ɗauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ya shigo,da mugun sauri na miƙe wani irin abu nake ji kamar
ƙaramin yaro mai neman rarrashin uwa.Wannan yasa saura ƙiris na faɗa jikinsa yayi saurin tare
ni da dukkan hannuwansa,murya a sanyayye ya ce “mu je na kai ki gida”
Idona ya ciko da ƙwalla,ba haka na so ba ! Na yi tunanin zai tambaye ni dalilin zuwana a nan
ɗin amma haka na bi bayansa har muka isa parking special.Wata haɗaɗiyar mota Benz na ga
ya buɗe min gidan gaba,haka na shiga na zauna kafin shi ma ya shiga ya tuƙa mu.
“Ya jikin ki?” na ji ya furta ƙasan maƙoshi kamar ba shi ne yayi maganar ba sai yanzu na tuna
ma da kaina na ciwo.Murya na ɗan rawa na ce “babu sauƙi!” ƙuuuu ya ja ya tsaya,da idonsa ya
kafe ni kafin ya ce “mine ne ainahin abin da ke damun ki?” kuka na fashe masa da shi kafin na
ce “aure za su min Yayaaaa!” Bai ce komai ba sai ya ci gaba da tuƙi,sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ce “ba ki na son shi ba ?”
“A'a ni kawai burge ni yake yi, amma zuciyata Fah....” ko kafin na ida ya buga min tsawa “ya isa!
Kar na sake jin kin furta sunansa domin ba mutumin kirki ba ne bai son ki”
“Ya na sona kawai dai bai da kuɗi ne,ina da tabbacin in ya samu kuɗi sai ya fi faranta min rai da
su fiye da kowa” na furta ina jin wani abu na tsira min a zuciya.
“Saboda ki faɗa min ki na son shi ne kika zo wurina?”
“A'a gidan anty Maimuna za ka kai ni kuma ka ban wayata ”
“Ba zan bayar ba!” ya furta hankali kwance daga nan bai sake furta komai ba har muka isa ƙofar
gidan,sai a lokacin na tambaye shi “motar wace ce wannan?”
Ya ban amsa kai tsaye “ta Sheikh ce”
“Mine ne ya faɗa maka to? Wace magana kuka yi da ya ce ya na son ganin ka?”
“In ji tsoron Allah in girmama wacce nake so kar na yi amfani da so wurin cutar da ita,sai kuma
ya ce na mayar da ke gida” ya bani amsar ya na kallona,na ɗan haɗiye yawu kafin na ce “Ya
Mubshar har yanzu ba ka taɓa nuna min budurwar ka ba ko a hoto ne”
Ya ce “mine ne amfanin nuna wa mutum kansa?”
“Ban gane ba?”
“Wuce ki shiga ciki muna da darasi zan koma makaranta”
“Amma Yaya don Allah ka sanar da ni ya budurwar nan ta yi bayan ta gano ta na ɗauke da
ciki?”
“Ƙawarta ta fara sanar ma,ta bata shawarar a zubar ta ƙi.A ƙarshe dai tun ta na ɓoyo har
iyayenta suka sani,ba su jinkirta zuwa gidan su saurayin ba amma fafur suka ƙi amincewa da
zancen suka ce ƙazafi ne ta yi wa ɗansu tun da kowa ya san ustaz ne”
“Kenan cikin ta zubar?”
“A'a barin gidan iyayenta ta yi ta je can wani gari ta raini cikinta har ta haifu”
“To amma ya labarin su har yanzu su na raye ita da ɗanta?”na tambaya ina jin tausayin su,sai
da ya yi min wani kallo mai wuyar fassarawa kafin ya ce “ga yaron da aka haifa zaune tare da
ke!” kallon ban gane ba na fara binsa da shi kafin na waro ido na ce “wai kai? Kai ne aka haifa?
Ka na nufin labarin Ammy ka ban?”
Bai bani amsa ba kawai dai ya jingina ga kujera haɗi da lumshe ido,daga inda nake ina jin
yadda zuciyarsa ke mugun bugawa.Cikin wata irin murya ya ce “ wannan dalilin yasa nake jin
takaici in na ga budurwa na haukan saurayi musamman irin FAHAD wanda kullum burinsa ya
kusance ki.Ifa na rantse da Allah da ace na yi dogon karatun boko da tabbas zan fito alƙalin
mata ne,duk wanda na samu da laifi kwatankwacin hakan da Allah kawai ya san hukuncin da
zan yi masa”
“Ka yi haƙuri!” na furta dakyar,ya buɗe idonsa ya watso min su kamar daga sama ya jefo min
tambayar “ki na sona?” ji na yi kamar ya buga min guduma,ban basa amsa ba kawai na ɓalle
murfin mota na fita da gudu na shiga gidan ina jin wani iri a jikina.
MUBASHAR
Ya bi bayanta da kallo ya na jin wani irin takaicin kansa ,da ya kasa riƙe sirrin zucinsa har ya
sanar da ita ya na sonta.Dakyar ya iya jan mota ya koma makaranta,ya na isa ya wuce aji don
ya san tuni Sheikh Muhammad na ciki.
Murya kamar ta maras lafiya yayi sallama a bakin ƙofar aji, Sheikh ya juyo ya dube shi kafin ya
amsa tare da basa izinin shigowa.Mubashar ya je ya zauna mazauninsa,sam hankalinsa bai
wurin ballantana har ya fahimci abin da ake a haka har aka gama darasin.Ya miƙe ya nufi
Sheikh da ke zaune ya na duba system ɗinsa,“ga key ɗin motar” ya faɗa cikin sanyi.
“Ka riƙe shi gun ka” Sheikh ya basa amsa ba tare da ya ɗago ya dube shi ba.
“Na kai gida?”
“Ka tafi da ita ka dinga hawa” ya faɗa wannan karon ya na mai ɗagowa ya kalle shi,da sauri
Mubashar ɗin ya sunne kai.
“Lafiya ? ”
“Alhamdullah!” ya faɗa domin ɓoye sirrinsa.
“Okay ka tafi”
“Na gode” ya faɗa kafin ya fice,yau dai ga shi an basa mota special don ya dinga hawa amma
sam bai jin murna.Dakyar ya isa gida,nan ya ƙara tarar da wani sabon tashin hankalin yadda
mutane suka cika tsakar gidan ga kuma akwatina jere ras.
“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un !” Mubashar ya motsa laɓansa,kasa fita yayi daga cikin mota
haka ya zauna ya na kallon yadda komai ke wakana.Can mata suka fito daga ɗaki su na
rangaɗa buɗa wacce ta kusa tarwatsa zuciyarsa, Mubashar ba shi ya fito daga cikin mota ba sai
da ƴan kawo lefe suka watse.Ya na fitowa kuma ana kiran sallar magrib.Sashensa ya nufa ya je
ya yi wanka ko zai ji sanyi kafin ya ɗaura alwala ya wuce masjid,bayan an gama sallah ne ya
wuce can ciki ya gaishe da su Mama.
Papa ne ya sanar da shi zancen kawo lefen,ya yi jarumtar yaɓo murmushi a fuskarsa ya yi
doguwar addu'a kafin ya miƙe zai tafi Mama ta tsayar da shi “ka zauna ka ci abinci tukuna,yau
ya aka yi kuka taso da wuri na zata sai an yi sallar isha'i za ka dawo”
“Dama ina tsayawa ne don ƙara bibiyar abin da aka yi mana” ya bata amsa,Mama ta ce “au! Shi
yasa zo zauna na zuba mana”
“A'a ban jin yunwa! Yanzu ma fita nake son yi”
“Ok in ka dawo sai ka ci”
Da haka Mubashar ya fita,mota ya shiga ya duba yawan petur ya ga kusan ma tankin cike
yake.Kawai ya ɗauki hanyar Tilabery,gudu kawai yake shaɗaɗawa sai ya ɗauki wajen awa uku
kafin ya isa.
Ammy na kwance ta na jan casbi yayin da Fadila ke yi mata matsa ƙafa kawai sai jin tsayuwar
mota suka yi.Babu jimawa kuma Mubashar ya shigo,gaban Ammy ya zube wacce tuni ta tashi
zaune kasancewar akwai hasken lantarki ta gane shi.
“Subahanallah! Yaron kirki mine ne haka?” bai iya cewa komai ba kawai ya kwanta ya ɗora
kansa kan cinyarta kafin ya ɗora hannunsa saitin zuciyarsa ya na fitar da wani huci.
“Fadila ɗebo min ruwa masu sanyi a randa ” cewar Ammy,ta yi saurin miƙe wa hankali tashe ta
ciko moɗa ta kawo Ammy ta karɓa ta yi tofi ciki kafin ta soma yayafa masa su a jiki a ƙarshe ta
buɗe bakinsa ta fara basa ya na sha.Ajiyar zuciya kawai yake saukewa,“ɗauko min fanka ki
kunna” Ammy ta ƙara faɗa,Fadila ta sake miƙewa ta je ta ɗauko ta kunna.Iska mai sanyi ya
soma fita,Mubashar ya lumshe ido kawai tun ya na jin muryar Ammynsa na yi masa addu'o'i har
bacci ya ɗauke shi.
A daren dai babu wanda ya rumtsa,Fadila baiwar Allah sai faman zubar da hawaye take yayin
da Ammy ke ta jan casbi.Wuraren ƙarfe biyun dare Mubashar ya farka,sai da yayi ɗan jimmm
kafin ya fahimci inda yake.Ya tashi zaune kafin kuma ya miƙe ya je yayi alwala,sallar isha'i yayi
sannan ya zo gaban Ammy ya ce “ina wuni Ammy na same ku lafiya?” “Alhamdullah! Tashi ga shimfiɗa can ka shiga ka kwanta” ta nuna masa gidan sauro wanda tuni
an ɗaura shi,bai musa ba ya je ya shige.Lamo yayi ya na tunanin yanzu Sharifa aure za ta yi ta
bar shi? Ita kuwa Ammy jan Fadila ta yi su ma suka je suka kwanta.
A can Niamey kuwa sai dare ne Sheikh Muhammad ya samu labarin zancen kawo lefen
Sharifa.Hankalinsa in yayi dubu to ya watse,duk yadda ya so kiran Mubashar kuma wayar ba ta
shiga.Da ya kira Mama kuma ta tabbatar masa tun da ya fita bai dawo ba,tsohon hawan jininsa
ne ya ji ya na son tashi.Tasbihi kawai yake yi amma ya kasa nutsuwa,matarsa Hajiya Balkis
tambayar duniya ta yi masa amma ya ƙi sanar da ita damuwarsa.Ya jingina jikin kujera ya na
roƙon Allah a zuci ‘ Ya Rabb kar ka jarabce ni da abin da ba zan iya ɗauka ba,a baya na rasa
farin cikina ina tsaka da maraici ka jefo min gudan jinina tsokata wanda nake jin ko cinaka ban
so ya cije shi ballantana wani abu ya same shi.Allah ka tausaya min ka tsare Mubashar a duk
inda yake,ka sassauta masa wannan jarabawar’ haka yayi ta yi sanfarorin addu'o'i har garin
Allah ya waye.
Ƙarfe bakwai na safe Hajiya Balkis ta shaida masa zuwan Mama,ya bada izinin ta shigo.
Ta shigo ta zauna gabansa,ta rasa ta ina za ta soma faɗa wa Yayan nata har yanzu fa
Mubashar bai dawo ba don bai kwana gidan ba.
“Amma ai kin san ya na son Sharifa ko? Shi ne kika yarda wani ya kawo sadakinsa har aka
ɗaura auren duk a jiya....” Sheikh Muhammad ya faɗa ya na jan zuciyarsa da ke barazanar faso
ƙirjinsa ta faɗo,Mama da ba ta fahimci abin da yake nufi ba kawai ta zuba masa ido.
“Karo na biyu kin ruguza farin cikina! Kin kasa kulawa da amanar da na damƙa miki kin kyauta
Aghaisha!” ya faɗa ya na ɗan yin tari haɗi da dafe ƙirji.
“Yaya wallahi ban taɓa sanin Mubashar na son Sharifa ba! Sannan tun kafin na gano ɗan Hawa
Kulu ne na ƙudirta a raina zan aura masa Sharifa. A ranar da na je ɗakinsa zan nemi ra'ayinsa
akan auren a ranar ne kuma na ga hotunan Hawa Kulu, wannan dalilin yasa na ɓoye saboda
muddin ya san ni ce silar barin mahaifiyarsa garin nan zai iya tsana ta ma”
“Wannan duk ba hujja ba ce Aghaisha,a ranar da kika sanar da ni ina ce dai a tare muka yi
alƙawarin nema masa duk wani farin cikin rayuwa ta yadda ko da ya san mu ahalinsa ne ba zai
guje mu ba,amma yanzu mi kika yi? Farin cikinsa wacce nake hango ita ce nutsuwar shi kika
ɗauka kika bai wa wani bare”
Cikin kuka Mama ta girgiza kai ta na mai cewa “ wallahi ba da sa hannuna aka yi auren nan ba
,komai Mustapha ya tsara shi da mahaifinsa kuma...” da sauri katse ta ya na cewa “ya isa haka!
Ki tashi ki tafi ban son jin komai da ace ki na son Mubashar ɗin ya aure ta ai kin sanar da ni
zancen kawo lefen amma kika ƙi har sai da aka ɗaura” sai kawai Sheikh Muhammad ya soma
tari jini ya soma zubo wa ta bakinsa,hankali tashe Mama ta fita ta sanar nan yaran da suke
karatu gidansa suka zo suka ciciɓe shi aka kai shi asibiti.
Cikin ikon Allah dai aka samu aka daidaita igiyar numfashinsa,sai dai an hana kowa shiga ɗakin
da yake.Mama kuwa sai gwada kiran Mubashar take amma wayar a kashe ,haka ta yi ta yi har
Allah yasa ta same shi bayan ya kunna wayar.Cikin kuka ta sanar da shi Sheikh bai da lafiya,ya
kuma shaida mata zai zo.
A bangaren Ammy ba ta takura Mubashar ba sai ya faɗa mata abin da yake faruwa ba.Kawai
dai ta yi masa nasiha mai ratsa jiki,wanda a ƙarshe ya sanar da ita budurwar da yake tsananin
so ce aka aurar.Murmushi kawai ta yi nasu na manya ba don wai ba ta ji ɗacin haka ba a'a sai
don basa ƙwarin gwiwa tare da nuna masa ba komai ne da kake so ba kake samu.“Dama haka
lamarin Allah yake,sai ka so abu wanda shi ɗin ba alkhairi ne gare ka ba in ka yi dace Allah na
sonka sai ya kuɓutar da kai daga sharrinsa.Ka yi haƙuri Allah zai baka wacce ta fi ta” Ammy ta
faɗa ta na kallon Fadila, Mubashar ma haka ya na shirin magana ne kiran Mama ya shigo ta
sanar da shi zancen rashin lafiyar Sheikh.
Da sauri ya miƙe ya ce “Ammy zan koma sai in mun yi waya” har bakin motar suka yi masa
rakiya ,ya sosa ƙeya ya ce “sai dai ban kawo muku komai ba”
Ammy ta ce “ai ba mu buƙatar koman ,kwanaki ma an fidda zakka an kawo mana duk kayan
abinci kuɗin da ka aiko kuma su na nan ko dala ban kashe ba har ina cewa ko na sayo ma
Akuya a kiyaya ma”