Showing 30001 words to 30509 words out of 30509 words
Chapter 11 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi
ma Abba yana kiranta.
Cikin haka sukayi jarabawa suka sami hutu, inda Uncle ya zo ya ɗauke ta Hajiya Jummai kuwa
wadda rashin mutuwar A'isha yasa ta yi wurjan-wurjan, tamkar ta zare saboda tashin
hankali,tana jin cewa yau A'isha zata dawo bata yi ƙasa a guiwa ba gurin fito da dukkan asiran
da ta tanada na gurin bokaye daban-daban ta shiga zuba su wasu na binnewa ne wasu kuma
na yarfawa,kai har toilet ɗin A'isha sai da ta saka asiri cewa tayi wai ya buɗe ɗakin za a share
mata, kafin ta iso,shi ko har da sa mata albarka.
Yanda yaga A'isha ta ɗan murmure har wasu ƴan mazaunai ta yi sannan ƙirjinta ya ɗan yi tudu
ta riga sai kurum ya samu kanshi da sha'awar kusantarta. Ya kasa manta yanayin da ya ji a
ranar da ya riƙe hannunta.
A'isha ba ta manta da addu'ar shiga gida ba,da ta ɗaki tana aje jaka ta shige toilet ɗauke da
addu'a a cikin bakinta, ta yo wanka ta fito. Uche ya gabatar mata da abinci. Bayan sallar isha'i
tana zaune Uncle ya shigo ya zauna bakin gadonta yini ya yi yana tunanin ta ina zai ɓullo mata?
Ko ya sanar da ita ƙudurinshi game da ita? Kai in ya yi haka ƙila ta daina ganin girman shi,to ko
ya....ta katse shi, lafiya Uncle? Ya ce zaki iya gyara min shinfiɗata? Ta yi ƴar dariya haba dai
shinfiɗa kawai zan kasa gyarawa kuma na ke gyara nawa ma? Ya ce kin san fa gado na ba irin
naki bane yana da girma,ta ce zan iya,ya ce to kiyi shirin baccinki kawai sai kije ki gyara min
hope zaki iya? Ta ce why not, Uncle zan iya mana. Sam bata san nufin shi ba,don haka sai da
ta gama shirinta tsaf na bacci har tana Uncle ya kawo min dabara ina dawowa sai in ƙwanta yau
dai zan ga kalar wannan gado da Uncle ya ke cewa ba zan iya gyara shi ba. Hajiya Jummai
tana zaune a falo lokacin da A'isha ta fito sanye da kayan bacci riga ce doguwa in and out.
A'isha ta yi mata sannu, sannan ta wui. Sam A'isha bata san kishi ba sannan bata san ƙudirin
Uncle ɗin nata ba,don haka kai tsaye ta shige ɗakin tare da sallama.
Jummai tana kallonta,kishi da baƙin ciki ya sa ta faɗawa ɗakinta da gudu,nata ganin A'isha ta yi
haka ne don ta ɓata mata rai don ta nuna mata itama ta san daɗin namiji.amma da ta tuna
bokan gindin tsamiya da na kan dutse bakinsu ya zo ɗaya,kan cewa in dai tayi amfani da
maganin da suka bata ya yi amfani da ita ya koma ya yi da A'isha to an gama komai, kuma ita
ta yi duk yanda zatayi yau da asuba ya kwanta da A'isha lallai ta san gawar A'isha kawai za'a
ɗauko, domin bata da ja da maganar bokayen nan guda biyu dan sune abin dogaronta,
wa'iyazu billa,shin hakan ta kasance?......
Mu haɗu a littafi na biyu.
Taku:-
K/Mashi.