Showing 9001 words to 12000 words out of 30509 words
Chapter 4 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi
kwantar da hankalinki" ta ce "zan yi ƙoƙari."
Yana saka kaya ta shigo da sallama. Ta ci gayu cikin shadda mai kalar ja, ƙyan shaddar da
tsarin ɗinkin shine ya toni asirin tsadar kayan,ƙamshinta ya cika ɗakin,cike da salo ta iso
gurinshi ta amshi (Nect tie) ɗin tana gyara mishi tare da faɗin, "ka ganka kuwa Alhajina? Kai ka
yi ƙyau." Bai ce mata komai ba, haka nan bai saki fuska ba, kuma bai katse ta da gyara mishi
(Nect tie) ɗin ba, sai da ta gama yana kallonta,ta ɗauko turarenshi Matador ta fesa mishi kaɗan,
sannan ta ce sauran ka (break) ya ce na ƙoshi,ta dube shi da sauri ban gane ka ƙoshi ba? Kana
nufin ba zaka ci ba zaka fita?"
Ya soma tafiya,tasha gabanshi cikin yanayin tausayi,ta ce "Haba Alhajina, kayi haƙuri na san
ban ƙyauta ba laifin kishi ne, sonka ne ya sani na yi maka haka." Ya tsaya yana dubanta,
sannan ya ce "Don kina kishina sai ki min rashin kunya? Har kina gaya min cewa ni macuci
ne?" Ta zube ƙasa guiwa biyu.
"Kai min afuwa,ba zan sake ba." Ta soma hawaye, mai tausayi ne musamman ga mata,don
haka ya ce "naji tashi shi kenan, amma kada ki sake,batun Break kuwa na yi latti,in na dawo
zan ci na dare" cikin shagwaɓa ta ce,"ka kula min da kanka." Ta rakashi zuwa ƙofar falo,yana
fita ta ce,zaka sani ne, tunda ka ce mata kasa gaba.
Hajiya Kari ta dubi Hajiya Jummai.
"Ina jin ki."
"Wai kin san da ya ya ma ya faɗa min sunanta?" Ta ɗan dakata,kafin ta cigaba "sai da siyasa,na
ce haba Alhaji ko baka huce ba ne? Kana ji ina tambayarka sunan ƙanwar tawa amma ka min
banza."
"To me zan ce miki" haka fa ya ce min sai daga baya yake ce min "A'isha." Yaƙi gaya min ma
lokacin bikin."
Hajiya Kari ta ce, "ki bar shi,ai dai in lokacin ya matso dole muji, tunda mun samu sunanta shi
ne kawai abin buƙata, yanzu kuma mun ji."
Yanzun sai mu sa ranar tafiya maguzawan, "To yaushe ne zuwan? Inji Hajiya Jummai,ta cigaba
"Kuma sai dai mu je da direbanki, kamar kowane lokaci" "Eh,ai ina sane ba zamu bar wata kafa
ko ya ya take wadda zata tona mana asiri ba,ke dai ki shaƙi kuɗi don bokan dutse yanzun
idanunshi sun buɗe da son kuɗi,da, ko akan dubu biyar ma sai ya yi kisan rai." Jummai ta ce,"A
sosai ma kuwa, ɗan iska ni har yau ma ban sai mashi motar da yake naci ba". Hajiya Kari ta ce
"ke dai bar ɗan iska ko ina ruwan wanda ke cikin daji da mota?" Jummai ta ce,"nima shine na
gani, shiyasa na share shi,rabo na da zuwa gun shi tun aikin ƙarshe da ya yi mana,na matar
ƙarshe da Alhaji ya aura." Hajiya Kari ta ce, "ƙyale shi wannan karon sai ki sai masa ko ƴar
starlet" Hajiya Jummai ta ce "hakan za mu yi" nan dai suka ci gaba da shirya ranar da zasu tafi.
Da gudu suka rungume juna suna murna.
*A'isha Mustapha kin ɗan rame." Inji Suwaiba Ringim.
"Nayi rashin lafiya ne, Zainab K.T bata iso ba?"
Sam, A'isha ba tayi niyyar sanar da Aminan nata batun auren nata ba, saboda kunya take ji,
duk cika bakin da takeyi na cewa ita karatu zatayi kamar ba gobe,don Doctor zata zama yanzun
ma har Doctor Aisha suke ce mata,in ko suka ji ta san zata sha tsokana, sai dai su shafa su ji
bata dawo ba, Zainab ma ta iso kuma sun duƙufa karatu babu wasa.
Alhaji Saddiƙ ya yaba da yanda Abba ya tsaya tsayin daka, aikin kamfanin ya kammalu. Guri ya
yi ƙyau duk mutane sun yaba,don haka shima bai yi wasa ba wurin kawo duk wani abu da
kamfanin ke buƙata don fara aiki.
Alhamdulillah,tuni kamfani ya soma aiki, Abba kuwa ya samu kujerar manaja, yanzu sunturi
yake yi tsakanin Dutse da Jigawa, Alhaji Saddiƙ ya ce mishi ya nemi gida nan Jigawa sai a siya,
sannan ya saya mishi ƴar mota,ba a jima ba suka samu gidan suka dawo Jigawa.
[12/1, 19:47] Ummi Tandamaí ½í¸‡: ____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 6*
Aisha tana makaranta ba ta san ana yi ba.
Gurin Abba Alhaji Saddiƙ ya ji cewa satin da zamu shiga ne visiting day ɗin su mutuniyar shi,ya
ce "To Friend ka bari ni zan je mu da Nafisa" Abba ya ce,"shiyasa na sanar da kai don tasan
cewa magana tana nan.
Waya ya yiwa Nafisa cewa,ta shirya zasu je visiting tana jin haka ta soma murna. Sun ɗau
hanya in da Yahaya direban shi yake jan su. Aikin shi yake yi a bayan mota cikin laptop,
harkokin business ɗin shi yake ta yi. Nafisa ko sai dai kallon ƙauyuka take yi, sai da suka isa
garin Kano sannan suka tsaya bakin Sahad Store ya yi mata tsaraba mai ban mamaki, sannan
suka ɗauki hanyar Munjibir.
Da tambaya suka isa makarantar,Henesy baƙa wul tana ta sheƙi,ta ɗauki hankalin da yawan
ƴan makarantar,gilashinta masu duhu ne,don haka suke ganin mutane. Ya dubi direbanshi ya ce
"Yahaya fita ka samo mana ofis ɗin (PC) ɗin makarantar."
"To ranka ya daɗe" inji Yahaya.
Jim kaɗan ya dawo.
"Ranka ya daɗe ga ofis ɗin can, har ma na yi mishi bayanin cewa maigidana yana son
ganinshi,kuma ya ce mu shigo" "To ai shi kenan." Inji Alhaji Saddiƙ, tare da Nafisa suka fito.
Ƙwarjinin Alhajin ya sa ya zama abin kallo gurin ɗaliban tare da masu ziyara. Kai tsaye ofis ɗin
(PC) ɗin suka nufa,suna shiga shima (PC) din ya miƙe tare da ba Alhaji Saddiƙ hannu,don daga
ganin shi ya jiƙe da Naira. Sun gaisa, sannan suka zauna kan wasu kujeru da ke gefe,ya nuna
ma Nafisa wata kujera ya ce, "Bismilla Malama" shi ko Yahaya cewa ya yi,bari ya koma gurin
mota.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"mun zo ziyarar yarinya ne."
"Ya ya sunanta?" Inji P.C.
"A'isha Mustapha, daga Gumel ta jihar Jigawa."
P.C ya ce,(S.S) take ko JS?"
"S.S one." Inji Alhaji Saddiƙ.
"Ok" ya miƙe yana fita ya kira shugabar ɗalibai ya aike ta neman A'isha,ya dawo ya ce bari a
kira ta.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"Ba komai" ya zauna tare da cewa, "Ranka shi daɗe ƴar ka ce?" Alhaji
Saddiƙ ya amsa da cewa "Eh,ƴar abokina ce", wayarshi ta shiga ruri,ya ɗauka yana magana.
Shugabar ta gano A'isha ne tare da ƙawayanta Zainab da Suwaiba,in da Yayan Zainab ya kawo
mata ziyara daga Katsina, ta ce kece A'isha Mustapha ko?" Ta amsa da "eh,ni ce."
"To ki zo inji P.C"
A tsorace ta ce,"lafiya?"
Nima ban sani ba" ta ce "Ina jiran ku" ta nufi ofis ɗin shugabar ce ta shiga,ga ta nan Sir,ya ce ta
shigo, nagode miki ta fita sannan ta ce A'isha ta shiga, ita kuma ta tafi. Tana shiga ta ji hancinta
ya shaƙi daddaɗan ƙamshin turaren Uncle,gabanta ya faɗi amma ta daure ta shiga,sanye take
da wando da riga haɗe da gyalen su, kayan mutanen Pakistan masu kalar sararin samaniya, kai
tsaye teburin P.C ɗin ta nufa, inda ta gaishe shi cikin harshen Turanci, sannan ta ce gata,ya
nuna mata Alhaji Saddiƙ da ke waya.
"Ga masu visiting na ki." Ya miƙe "Bari na barku, ku gaisa ko?" Ya fita.
Duk sai taji kunya ta rufe ta, har ma ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskarta. Ta dubi Nafisa,ga
zatonta matarshi ce. Cike da dariya Nafisa ta ce, "zo mu gaisa A'isha." Ta isa gurinta ta zauna,
sannan ta ce "Ina yini? Ya ya hanya?" Nafisa ta ce "lafiya lau,hope kema kina lafiya?" A'isha
kanta a ƙasa ta ce "lafiya ƙalau." Nafisa ta ce "Hajiyarmu da Alhajinmu sun ce mu gaishe ki"
A'isha ta ce, "ina amsawa, na gode."
Dai-dai sannan Alhaji Saddiƙ ya gama waya ta ɗan saci kallonshi da gefen ido. Wata jiƙaƙƙiyar
shadda ya saka kalar ƙasa,ya yi ƙyau sosai ta zamo daga kan kujera don ta gaishe shi.
"Ina yini Uncle?"
"Bana cin miƙe A'isha, daga nan za ki gaishe ni?".
Ta saka gyale ta rufe fuskarta, sannan ta miƙe taje gefenshi ta tsugunna,muryarta ƙasa-ƙasa ta
sake gaishe shi. Ya amsa yana dariya.
Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta burge ta, A'ishan ta mata ƙyau,sai dai yarinya
ce ƙwarai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi A'isha ya ce, "Ga ƙanwata Nafisa." Ta
kuma duban Nafisan.
"Sannu da hanya"
"Yauwa," Nafisa ta amsa da fara'a.
A'isha ta miƙe tana kallon Nafisa, "Bari na kira ƙawayena." Har za ta fita, ya ce "Zo" Ta dawo ta
tsugunna.
"Wa zaki ce musu ya zo?"
Ta rufe fuska,tana ɗan murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu labarina ne?"
Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle ɗina ne." Ta miƙe ta fita da sauri. Dariya
Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddiƙ duk da A'isha yarinya ce kun matuƙar dacewa, Allah dai ya
yi mana jagora tare kuma da shige mana kan matsalarmu." Ya ce "Amin sister."
Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle ɗinta ne daga Katsina, suka shigo suka
gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ƴar garinmu? To sannuku,ku
dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na gode." Suka fita suna mamakin
dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba ta taɓa gaya musu ba? Zainab kam so take ta
tuna inda ta san shi.
Nafisa ta miƙe, "A'isha bari na bi ƙawayenki na ɗan miƙe ƙafa," A'isha ma ta miƙe ta fito, kira ta
ƙwalawa su Zainab.
"Ga baƙuwa ko zaku je school shop."
Suka ce, "To" ta dawo ofis ɗin ta zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da godiya,
shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda aikin shi ya koma
Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga Dutse?" Ya ce "Haka ne,to
yanzu yaushe ne zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar zuwa shida." Ya ce, "To so nake a
shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a ɗaura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe
fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce, "Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya ce, "wannan
babu komai, sai makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya
ce, "No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."
Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C ya rako shi har gun motarsa.
A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan Zainab,ya zo ya bi su
Uncle ɗin ta mana tunda suma Katsina za su je.
Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ƙwalaye a ƙasa daga boat ɗin motar,Sani
yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddiƙ K.T. mutumin da ya yi kuɗi da jinin
mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu yana son shan jinin
ƴan makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.
Alhaji Saddiƙ ya miƙa ma Nafisa bandir ɗin kuɗi yace ba ƙawayan nata. A'isha ta leƙo tana
cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ƴan garin." Ya ce, "Ni fa ko Nafisa kaɗai ki ka sani?"
Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai je". Alhaji Saddiƙ ya ce, "To ya shiga
mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina
da aboki nan cikin Munjibir,ta je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.
Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle ɗin ki?
Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."
"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji Saddiƙ Usman K.T ɗin ne baki sani ba."
Zainab ta dafa ƙirji da ƙarfi.
"Kana nufin me kuɗin jini?" Ya ce "shi ne mana."
A'isha ta zaro ido,me kuɗin jini kuma?" Sani ya ce, "tabɗi,ke da baki san halin Uncle ɗin na ki
ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."
Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min gaske ne?"
Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo mu ƙwashe kayan nan." Ta ce, "ai ni bazan
ɗauki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da Zainab har ma da Sani suka shiga
ƙwashe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin baƙon al'amarin, har suka raka Sani suka
dawo.
Zainab ta zauna kusa da ita, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-aure ya ke
yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma, uwargidan ce kaɗai bai cinye
ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka
zuuu sai dai ka ganka a cikin wani ɗaki a gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a
cikinshi, ko ba ki san gidan ba?"
A'isha cikin tsananin tsoro ta ce "ban taɓa zuwa ba".
Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ƙyan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne wani mahaukacin
gida ga bishiyoyi."
A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk kayan da ya
kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ƙwana uku ta ƙwanta ciwo,ƙwananta biyu ta ɗan
samu sauƙi. Amma duk ta rame su Zainab sun yi ta matsa mata da son jin gaskiyar lamarin ta
da Alhaji Saddiƙ don sun ga yanda ta ɗauki abin da zafi ƙwarai. Ta gaji ta gaya musu cewa
Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da
addu'a, Allah ya shiga tsakaninta da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.
A daddafe dai suka yi jarabawa, Abba da Abdulrahman ne suka zo ɗaukanta, Abba ya dube ta,
"A'isha ciwo ki ka yi haka? Na ganki ne babu ko ƙyan gani?" Hawaye ya soma zubo mata, cikin
sanyi murya ta ce "Abba nayi ciwo ne sosai."
Sun isa Jigawa misalin ƙarfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon sabon
gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa iyayenta suna cin
kuɗin ƴarsu ne. Nan take hawaye ya soma zubo mata,ta shiga ciki.
#######
[12/2, 08:00] Ummi Tandamaí ½í¸‡: ____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 7*
Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani tsararren kitchen ta hangi Umma, Umma tana
juyowa ta yi arba da ƴarta, da sauri ta fito tana cewa ga ƴan makaranta ga ƴan makaranta."
A'isha ta faɗa jikin Umma tana kuka.
Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da Abdulrahman
suka shigo, Abba ya ce, "ƙawallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga yanda ta ƙare?" Umma ta
ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai
duk jikina ne bana jin daɗin shi. Suka shiga falo kan kujera ta ƙwanta tana ƙara kallon yanda
aka tsara falon da kuɗin jini, duk sai ta samu kanta da ƙyanƙyamin komai na gidan. Umma ta
zubo mata abinci ta tasa shi ta kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ƙi cin komai.
Hankalin Iyayen ya tashi, cikin dare zazzaɓi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole
da safe suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka yasa
mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.
Ƙwananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba ta magana. Umma ta matsa
mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke damunta. A'isha
tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi kuma ya yi faɗa. Ko ma
ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.
Abba yana zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma ta shigo
ɗakin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika ɗaki da kaya bane tunda
cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce kana nan na fito ban ganka
ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin a gabana in gani," Umma ta ce "to nima
dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ƙoƙarin
ganin ta ci abincin,ko don hankalin iyayenta ya ƙwanta, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji
Saddiƙ ne?" Da sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba
ne Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai mun
gama