Showing 24001 words to 27000 words out of 30509 words

Chapter 9 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi

09 Jul 2025

1301

ta cin
abinsa da alamu ya saba da shi, wayoyinsa suka soma ringing lokaci ɗaya ta miƙe ta ɗebo
mishi su, sannan ta koma gefe ta sha ruwa ta zauna tare da tsura ma guri ɗaya idanu da
alamun ta faɗa cikin tunanin nata,kusan minti talatin yana amsa wayoyi, sannan ya kira Uche ya
kwashe kayan ya dubi A'isha, "Beby tunanin ko?" Ta sunkuyar da kai ya miƙe ya isa gurin T.V
wanda ke manne a jikin bango ya kunna sannan ya shiga neman tasha,MBC 3 yasa sannan ya
dube ta ga irin naku ko Beby? Ta kalla Cartoons suke yi na Tom & Jerry tana son cartoon,sai dai
ta kula shi Uncle ya maidata wata ƴar mitsitsiyar Yarinya. Nan ko ta gyara zama ta shiga
kallonta, shi ko ya jawo laptop ɗin shi ya shiga al'amuranshi na kasuwanci daga bisani ta ji bacci
yana fizgarta,don haka ta hau gado bayan tayo alwala ta zauna ta jero addu'o'inta sannan ta
kwanta bacci kuwa ya yi gaba da ita,sam bata tare da fargaba irin na amaren nan game da
angwayensu, uku dai-dai ta farka har lokacin yana gaban laptop alwalla tayo ta zo ta soma na
filfilu, hankalinshi ya yi nisa sai daga baya ne ya ji motsinta, nan shima ya yo alwalla.

Hajiya Jummai tana da tabbacin ango ya kwana ɗakin amarya fatan ta dai Allah yasa sun sadu .

Da safe har ɗaki A'isha taje ta gaida Hajiya Jummai ta same ta tare da su Sofy, cikin fara'a ta
amsa ma A'isha, sannan ta ce dasu Sofy ba za ku gaida Antyn taku ba? Har suna haɗa baki

gurin jan tsaki, haka da A'ishan ta gani yasa ta gaishe su ba su amsa ba, A'isha ta fito tana
tunanin su kuma waɗannan su wanene? Tana shiga ɗakinta ta soma gyaran gado,ta gyara
ko'ina sannan ta shiga toilet tana wankewa ya shigo cikin shirin fita motsin da ya ji a bayin ya sa
shi tsayawa ya san tana ciki,jim kaɗan ta fito. Ya ce na zaci wanka ki ke yi? Ta ce a'a ina wanke
bayin ne. Ta durƙusa ina ƙwana? Ranshi ya yi fari sannan ya ce lafiya lau tashi na gode. Ya ci
gaba ni zan fita ne don Allah kada ki yi kuka ko tunani sannan ki ci abinci kuma wannan aikin da
ki kayi yanzu akwai masu gyaran ɗakunanku. Zan sanar da ke komai sai in na dawo yau da
yamma zan haɗa ku da Jummai, ta ce to, har ya soma tafiya ta ce Uncle ka....sai kuma ta yi
shiru,ya dawo har kusa da ita, nayi me? Sanar da ni mana. Ta sunkuyar da kai tana wasa da
yatsunta sannan ta ce ina nufin kayi break fast ne? Ya yi murmushi, abinda Hajiya Jummai ba ta
taɓa damun kanta a kan ya yi ba kenan, haka gaisuwar da A'isha ta yi mishi ya sa shi jin cewa
shi ɗin maigida ne. Ya ce A'isha bana yin break a gida saboda baƙwa karyawa da wuri ni ko
bana son mutane su yi ta jirana a Ofis," ta ce "to acan ana saida abu ne? Ya ce zan sha copee
a Ofis da rana kuma muna kusa da gidan cin abinci," ta ce "to sai ka dawo Allah ya bada Sa'a"
ya ce amin Bebyna,na gode miki kiyi kallonki kin ji? Zan kira ki" ta ce to,ya fita ta bishi da kallo.
A zuciyarta tana tunanin duk in da Abbansu za shi komai sauri sai Ummanta, ta mishi Abinda
koda ba zai ci ba saboda sauri zai riƙe.



######
[12/6, 07:59] Ummi Tandama😇: *📗 Page 14*


Shi ko ya fito ne yana jin daɗin yanda A'isha ta nuna kulawarta kanshi, ƙaramar yarinya kenan.
Sai sha ɗaya sannan aka kawo mata abin kari tea kawai ta iya sha domin hatta dankalin
ɗanɗanonsa bai mata ba.

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi tana zaune kan abin sallah tana karatun Alkur'ani tun bayan da ta
idar da sallar azahar, Hajiya Jummai ta shigo tare da ƙawarta Karima, ta miƙe tana musu sannu
duk cikin fara'a suka amsa. Karima ta ce wayyo ashe ma yarinya ce ƙarama.

Ita dai A'isha kanta yana ƙasa. Jummai ta ce eh, yarinya ce,sai wayar Jummai ta soma ringing
sai ta fita ina zuwa bari in yi magana Alhaji ne ya kira ni ku gaisa ina zuwa,tana fita Karima ta
matso kusa da A'isha, "yarinya ni dai zan miki nasiha ne ki riƙe mijinki ki mishi biyayya, kada ki
zama cikin irin matan nan masu gudun miji,kin ga haihuwa yake so kiyi maza ki cika mishi gidan
da ƴaƴa kin ji?" Zancan ya yi ma A'isha nauyi,don haka ta kasa ɗago kai, sai dai ta kaɗa kai
alamun to. Ta ƙara ƙasa da murya,kin ga dai kishiyarki aminiyatace ko? To wannan ba zai sa in
kasa gaya miki gaskiya ba, ita bata so kowace mace ta haihu tunda ita bata haihu ba,don haka
zatayi ta zuga mijinku kan cewa kada ya kusance ki,ke yarinya ce in kin ji tana haka ki mata
shiru, amma da lokacin ƙwanciya ya yi ki tafi gurin mijinki kin ji? Sai Hajiya Jummai ta turo ƙofa
tare da sallama, sai Karima ta ja baya alamun bata son Jummai ta ji, amma yanda A'isha taga
sanda suka haɗa ido suka yi wata alama da gira sai jikinta ya bata cewa ƙila sun shirya wani

abu ne.

Yinin ranar ta amsa wayar Uncle kusan sau taƙwas, duk dai dan yaji halin da take ciki. Ta kira
Umma da Abba da kuma Yaya Abdulrahman, shida saura ya shiga ɗakinta amma daga gani ya
fara zuwa ɗakinshi, domin ya canza kayan shi daga suit zuwa jallabiya fara kar. Ta ce sannu da
dawowa,an dawo lafiya? Ya ce lafiya lau Beby,ba dai wata damuwa ko? Ta ce eh,ya ce to bari
muyi sallah, ta ce to. Wanka tayi tasa riga da siket na atamfa,bata damu da yin wata ƙwalliya
ba, domin shafa wannan shafa wancan ba damuwar ta bane. Ta yi sallah tare da nafila raka'a
biyu,ta zauna tana yin azkar ɗin yamma. Ayatul kursiyu ake fara karantawa, sannan falaƙi da
Nasi da ƙulhuwallahu, sannan ta ce "am saina wa amsalmulkulilahi Rabbana as aluka khairan
mafiy hazihil lailati wa khaira ma ba a daha,wa'a uzubika min sharri mafi hazihillailati wa sharri
ma ba a daha, sannan ta ce:-

Allahumma bika amsaina wa bika asbahna,wabika nahya wa bika na mutu,wa ilaikal masir.

Allahumma anta rabbii laa ilahaaha illa anta kalaƙatani,wa'ana abduka wa anna ala ahdika
wawa'aduka mastaɗa'atu a'uzubika min sharri ma sana'atu abu'u laka bi ni'imatika alayya wa
abuu'ubi zanbi fagfirlii fa innahu la yagfiruz zunuba illa anta.

Haka ta yi ta kawo addu'o'i har zuwa isha'i ta yi sallah tare da yin shafa'i da wuturi,tana zaune
tana tasbihi, Uncle ya shigo da sallama. Ta amsa, sannan ta yi mishi sannu da shigowa, ya
amsa ya ce in kin gama zo muje,dama ta gama ta yi addu'o'inta ta shafa shima ya shafa tare da
cewa Allah ya karɓa ta yi ɗan murmushi sannan ta ce Amin. Ya ce me kika roƙar mana? Ta
dube shi, sannan ta sunkuyar da kai ta ce alkhairi, ya ce kin sani a ciki? Ta dube shi, "na manta"
ya ce "to daga yau in kin yi sallah ki dinga saka ni cikin addu'arki, Allah yana saurin amsar
addu'ar mace a kan mijinta, haka nan ta mijin akan matarsa. Ta ce to, ya juya zo muje, ta bishi
suka ratsa falon shiga cikin wani labule, sai ga gurin cin abinci,dinning ne na glass mai kujeru
shida,can gefe ga wani mai kujeru taƙwas,gurin ya tsaru gwanin sha'awa.

Hajiya Jummai ta shigo ta wata ƙofa bata hanyar da suka biyo ba, ashe kitchen ne, da fara'a ta
shigo,ta dafa A'isha wadda tunda ta shigo ta soma jin wata muguwar faɗuwar gaba,ta rasa dalili
duk lokacin da Hajiya Jummai ta zo inda take sai gabanta ya dinga wata muguwar faɗuwa.

Hajiya Jummai ta ce, ƴar ƙanwata kin fito? Cikin in-ina A'isha ta ce, in in ina yini? Jummai ta
zauna tana cewa, lafiya lau, Alhaji Saddiƙ ya yi murmushi sannan ya ce,gata nan sai kunya da
tsoro,dubi yanda duk ta rikice daga shigowar ki.

Jummai ta ce, daina tsorona ko kunyata,ni ƴar'uwarki ce kin ji ko? Ta jawo plate ta soma zuba
ma Alhaji shinkafa fara da miyar ganda,ta tura mishi, ita ko cous-cous ta zuba sannan ta ce me
zaki ci ne ƙanwata? Shiru A'isha ta yi Uncle ya ce zuba mata shinkafa itama. A'isha dai tana jin
su ba ta ce komai ba, domin ita ƙamshin abincin ma bai mata ba,tana ɗan tsakura tana korawa
da ruwa kaɗan kaɗan,ya dube ta Beby ba ki cin abinci fa, ta ce ni dama bana cin abinci sosai.
Jummai ta ce ki ci fa nan gidanki ne.

Bayan sun gama, ya dubi Jummai ya ce, to Jummai ga dai ƙanwa nan sai kiyi ta haƙuri da ita
saboda yarinya ce, duk da na san A'isha tana da hankali da biyayya, duk in tayi ba dai-dai ba ki
gyara mata, sannan ki nuna ta ga ma'aikatan gidan nan, ta ce insha Allah.

Ya dubi A'isha, Beby kin ga ƴar'uwarki nan kiyi mata biyayya sannan da akwai masu aiki babu
abinda za ki yi hatta gyaran ɗakinki da wankin bayinki duk za su yi akwai mai girki,wato Uche
kenan. Sai dai duk abinda ki ke so ƙya iya sanar dashi ga kitchen ɗin nan,za kuma a zo a saka
miki wayar cikin gida a ɗaki saboda kiran masu aiki,in kin yi baƙi haka,ko dai wata
matsalar,aikinki ɗaya ne jal shi ne gyaran ɗakina,wato shinfiɗa ta, to amma na ɗauke miki
wannan tukunna don ba zaki iya ba.

Ta dube shi kamar zata yi magana, amma sai tayi shiru,na ta ganin menene abin wuya a gyaran
gado? Nata ganin komai girman gado zata lailaye shi. Jummai ta ce, gaskiya kam, amma dai ka
raba mana kwana saboda ko bata gyara maka shinfiɗar ba, saboda ƴan matsalolin ta kaga sai
ka rinƙa ji,ya ce haka ne.
Bayan sun gama jawabansu, tana dai jin su,ta ƙosa ta koma ɗaki don jinta take tamkar kan
ƙaya,ba don komai ba sai don Jummai,don haka ta soma hamma,ya ce je ki ƙwanta ai kafin ya
rufe baki har ta miƙe ta nufi ɗakinta.

Jummai ta dube shi, Alhaji ni ko nawa ganin ba yi bane kace zaka ƙyale ta,ka san yaran yanzun
da wayonsu sarai,mu da muke son yara ka tsaya renonta? Ya yi shiru, sannan ya ce ni
abubuwan ne sun min yawa dubi fa yarinyar zan cutar da ita,ƙirjin ma babu komai sannan sai in
dinga ganin tamkar in na ƙwanta da su ne suke mutuwa,shi yasa nake tsoro.
Jummai ta zaro idanu "kada fa asirinta ya tonu,ta ce mishi haba dai to da haka ne dani yanzun
sai dai labarina ka daina wannan tunanin." Shiru ya yi yana nazarin maganarta,sai dai shi kam
nashi ra'ayin ba zai taɓa ɗanɗana nauyin juna ba yanzun a tsakaninsu,yana ganin in ya ɓullo da
haka ɗan sakin jikin da take mishi zata daina, amma sai ya bar wannan a ranshi don sirrinshi
ne. Ya dubi Jummai ya ce haka ne,shi kenan sai ku riñƙa yin ƙwana bibbiyu in na gama
ƙwanakina cike da jin daɗi ta ce Allah ya taimake mu ya bamu Sa'a, ya ce amin.

Abinda ya soma ɗaga hankalin Jummai shi ne,yau satin amarya biyu, kullum tana jiran ta ji
Alhaji Saddiƙ ya ce jama'a ku zo, har yau shiru. In ta kira Karima ta mata magana sai ta ce bata
da haƙuri ne sun taɓa yin wannan abin ya yi musu gaddama? Ta ce ko dai har yanzun bai
ƙwanta da ita bane? Jummai ta ce oho amma yau zan bugi cikinta. Matsiyaciyar yarinya kina
ganinta haka na kula zata yi salo don yanzun kin san kullum daga Ofis sai ya aiko an karɓar
mishi wani zoɓo da take mishi?" Kari ta ce daina bani labari, zan dai zo gidan gobe.

A'isha kam yanzun tafi ƙosawa da karatunta,don haka sai ta ɗebo littattafan ta na makaranta
tana ta karantawa, Uncle ya shigo ta ajiye ta miƙe tare da yi mishi sannu da zuwa,da sha'awa
ya dubi takardun me ki ke karantawa ne Beby ? Ta ce ina ɗan duba books ɗina ne na school,ya

ce kin tuna min,an kusa a koma hutu ko? Ta ce ni da jiya ma zan koma Sunday. Ya zauna kina
son makarantarki ne ko in samar miki wata? Ta yi shiru sannan ta ce duk yanda kace bani da
zaɓi Uncle,daɗi ya ji sannan ya ce to shikenan,nan da ƴan ƙwanaki zaki ƙara zama student ko
Bebyna? Ta yi dariya har kumatunta suka loɓa. Abinda yake burge shi sosai.
A'isha tana ta gyaran ɗakinta domin tunda take sau ɗaya ƴar aikinta ta taɓa zuwa ta gyara mata
daga nan bata dawo ba,don haka sai ta ci gaba da aikinta,dama ba ta ɗauke shi aiki ba,ta gama
ta jona na'urar da ake saka turaren wuta,ta zuba nan fa ƙamshi ya soma tashi. Hajiya Jummai
da Hajiya Kari suka yi sallama,ta amsa nan take gabanta ya shiga faɗuwa ta soma karanta
Allahumma kafihim bima shi'ita,domin yanzun addu'ar da ta koma karantawa Jummai kenan.

Suka shigo ta zauna ƙasa ta sunkuyar da kai,su kuma suka zauna bakin gado. Ta gaishe su
kanta yana ƙasa suka amsa cikin fara'a, sai kurum suka ji an bugo ƙofa a tsorace A'isha ta ɗago
kai. Suwaiba ce cikin rashin kunya ta ce Hajiya ki zo kinyi baƙi,me kike yi ne ɗakin wannan ƴar
ƙauyen? Jummai ta miƙe tana cewa ubanki nake yi kin ji ko? Ta bita suka fita. Hajiya Kari ta
girgiza kai tare da cewa, Allah wadaran irin wannan tarbiyya da Jummai ta koyawa yaran nan,
ta dubi A'isha ƴar nan sai fa haƙuri kin dai ga abinda nake gaya miki nan,ta sake matsowa gaya
min yanda kuka yi da Alhajin naki,baki dai gudun shi ko?" A'isha ta ɗaga kai amma zuciyarta
cike da tsanar matar, ta ce yauwa ƴar nan,to ya ya kukeyi ɗakinshi ki ke zuwa? Ran A'isha ya
ɓaci ta yi mata banza tana ta tambayarta A'isha tayi shiru, da ta matsa mata sai ma ta saka
kuka.

Hajiya Karima ta ce yau na shiga uku daga tambaya? To yi haƙuri,wayar A'isha ta soma ringing
ta share hawayenta ta ɗaga Uncle ne ya ce na turo direba, ya amshi zoɓon nan na ji shi shiru,
ta ce bai zo ba ko ƙila yazo bai samu wanda zaya aiko ba, ya ce to bari na kira Uche ya amsa
ya bashi,ta ce to sai ka dawo, ya ce ba wata matsala ko? Ta ce a'a babu komai ta ajiye wayar
bayan ta kashe ta kalli in da Karima take, tana nan zaune ba ta koma ta kanta ba, sai kawai ta
shiga haɗawa Uncle ɗinta zoɓon da ta riga ta haɗa cikin wani ɗan ƙyakƙyawan ƙwando,yau har
da cin-cin da diblan ta haɗa irin na bikinta ta zuba cikin wani ɗan ƙwanon tangaran saiti ne da
jug ɗin ta zuba kofunan jug ɗin Uche ya ƙwanƙwasa ƙofar ta buɗe mishi sannan ta bashi tana
juyowa taga Hajiya Kari ta miƙe ta ce, to sai anjima tunda kin ƙi mu yi hira A'isha can ƙasan
maƙoshi A'isha ta ce to ta shige toilet.



########
[12/6, 16:20] Ummi Tandama😇: *📗 Page 15*



Cike da al'ajabi Kari ta isa ɗakin Hajiya Jummai da sauri, Jummai ta miƙe ta ce ta sanar dake
komai? Karima ta ce, ina fa, wannan yarinyar tana da shegen wayo, na lura muna mata kallon
biri ne ita kuma tana mana kallon ayaba.

Jummai ta dafe ƙirji ya ya ku kayi ne? Karima ta zauna,yarinyar da na matsa mata sai kurum ta
saka min kuka,can kuma in gaya miki sai Alhajin ya kira ta,zo kiga kashe murya don sanabe
Uncle ma take ce mishi an haɗa su soɓo da cincin an kai mishi.

Jummai ta ce,ni yanzu zama bai ganni ba,Kari shirya kawai mu nufi maguzawa in ko Boka na
kan Dutse ya yi kuskuran aikin nan ne to ya cuceni,Kari ta ce daina wannan zancan kema kin
san ba zaya ƙi yin aikin nan ba sai dai in tanan ne aka samu mishkila, amma yanzun ki bari sai
gobe mu je muji dalili. Jummai ta ce bana bacci fa Karime, kullum sauraron ganin gawar
yarinyar nake yi. Kari ta ce ki dai haƙuran ma goben.

Washegari tun safe ta fice ta riga maigidan fita, gidansu Kari ta nufa, shi dama ba'a ɗakin ta ya
ƙwana ba, amma ga tsarin shi ko ba kece da shi ba zai shigo har ɗaki ku gaisa. To ya shigo
ɗinne su Suwaiba suka ce mishi ta fita. Ya kalli agogon hannunshi,baƙwai da ƙwata ya dube su
ina taje? Suka ce ba su sani ba,ya yi tsaki sannan ya fita. Ya samu A'isha tana gyaran gadonta,
ya ce a'a Beby ina mai aikin naki ne? Ta ce Uncle ni na ce ta barshi bana son zama bana aikin
komai shi ne dalilin,ya ce good,ta rusuna ta gaishe shi, ya ce zai fita,yau dai ta daure ta ce to
Uncle kace ma Uche in aiki ya yi mishi yawa ni zan dinga taya shi, domin bai dace kana fita
baka karya ba, kallonta ya dinga yi some times tana ɗaure mishi kai in tayi wata maganar domin
sai ya ji tafi Jummai wadda ta haifeta hankali. Ya ce Beby kina son in dinga karyawa a gida ne?
Ta ɗaga kai alamar eh,ya ajiye jakarshi ta Ofis ya zauna kan kujera je kitchen ki haɗo min ko
menene zan ci,ta ce to amma kana ganin Anty Jummai ba zata ga kamar na canza mata tsari
ba? Nan ma kallonta yake yi,ya girgiza kai sai ta saka takalmi to bara na zo ta fita ya bita da
kallo zuciyarshi tana ta kai kawo an ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0