Showing 15001 words to 18000 words out of 30509 words
Chapter 6 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi
zai zama mijinki? Duk kin bi kin
ɗaga hankalinki, maimakon ki tsaya kan addu'a Allah yasa ki shiga gidanki cikin Sa'a ko? Ta
miƙe ranta ɓace ta fita falo ta bar ta ɗauke da tagumi tana nazarin yanda ma za'ayi ta iya
ƙwantar da hankalinta.
"Sofy! Sofy," Hajiya Jummai ce ke ƙwala ma ɗaya daga cikin ƴammatan da take ɗaukowa cikin
danginta kira. Sofy ta zo cike da yatsina, ta ce "gani Anty Jummai," ta ce suby fa? Sofy ta yi
wani luu da idanu, sannan ta ce tana bedroom in kirata ne?" Jummai ta ce, "eh kirata aikenku
zan yi yanzun ku fito cikin shiri." Suka fito cikin riga da wando ya ɗame kowacce cikinsu, Sofy
ce ma ta ɗan yafa wani ɗan kucilin gyale, Jummai ta dube su kun yi ƙyau, sai dai kema Suby je
ki yana ko ɗan irin na Sofy ɗin kin san Alaramma yana gari. Haka take kiran Alhaji Saddiƙ in
zata yi wani abu daya hane ta. Ko in ya yi mata nasiha, to ranar yini zata yi tana ce mishi
Alaramma,ko Alagafarta. Soby taje ta ɗauko tana mitar ita bata son wani yafe-yafen gyale duk
takura ne, Jummai ta ce "ya ya zakiyi tunda kina gidan Ustazai,ka ce shi yafi kowa sanin Allah"
ta ce "ga wannan ta miƙa musu wani ƙullin abu cikin tsumma,ku kai ma Hajiya Kari,ku ce mata
ga ƙasar ƙafar nan za kuma mu yi waya.
Sofy ta ce, "motar wa zamu ɗauka tunda ta mu tana gurin gyara?" Hajiya Jummai ta soma
masifa, "ku hau mashin ba zan ba ku motata ba,ku je ku buga min ku ja min asara." Suby ta ja
tsaki tayi gaba tare da cewa, "Sofy ta baki kuɗin mashin ɗin, amma ai ba mutuncinmu bane
hawa acaɓa." Hajiya Jummai ta ce "shegun yara kada ku yi mutuncin mana, tare da jeho musu
ɗari biyu Sofy ta ɗauka tana mita haka suka tafi suna zaginta, da cewa masifaffiyar mata.
Sofy ƴat ƙanwarta ce,Suby kuwa ƴar autar su ce,yaran sam basu da tarbiyya,ba sa shakkar
kowa sai maigidan. Hatta Hajiya Jummai maida mata magana suke yi. Foly suke zuwa da ke
nan Katsina. In kin ga yanda suke ɗaukan kai da shan ƙamshi zaka zata ƴaƴan shugaban ƙasa
ne. Alhaji Saddiƙ kaɗai ke taka musu birki in yana gari.
Hajiya Kari da Jummai cikin motar Hajiya Kari, ita da kanta take jan motar suna hirar yanda
zasu tsara mutuwar Amaryar ta Alhaji Saddiƙ,waton A'isha. Hajiya Jummai ta ce "kin san Allah
Hajiya Kari, (ta cigaba) wannan karon sati ɗaya nake son a aika yarinyar nan barzahu, domin
duk cikin matan da ya yi,yayin auren ban taɓa jin kishin wata ba kamar wannan". Kari ta dube ta
"menene na ɗaga hankali,yarinyar da ƴan ƙwanaki za ta yi ta sheƙa barzahu, har ki ke damun
kanki." Jummai ta yamutsa baki,"ina mugun jin takaicin yanda ya damu da yarinyar, duk
abokansa ya bi ya sanar da su alhalin da a ɓoye yake aurensa, sai in amaryar ta mutu sannan
su ji, amma wannan fa shi da kanshi yake buga musu waya yana cewa,zai yi aure su taya shi
da addu'a,ke wani takaici ma sai suna waya da yarinyar in kin ji yanda yake ƙara saisaita murya
zaki sha mamaki." Hajiya Kari ta ce, "dama ga muryarshi kamar ta mata,anya ma ba salabane
yake yi kuwa?" Jummai ta ce,"shi dai ya sani,ni yanzun damuwata ba ta wuce ya Boka na kan
Dutse ya ganni ba. Kari ta ce "a'a kada ki damu,zai ganki ɗan iska nufin shi zai rama wulaƙancin
da mukayi mishi na aikin ƙarshe da ya mana na ƙin sai mishi motar da ki kayi?" Jummai ta ce
"shiyasa yanzun na taho mishi da makullin motar su Suby,don ba zan sai mishi sabuwa ba,yana
kan tsauni ban da iskanci me zai yi da wata mota?" Kari ta ce "saka ai mata penti ki bashi ya
ƙarata da ita". Jummai ta ja tsaki,"Ni tunanina me zan ce ma Alaramman nawa in ya ce ina
motar su Suby?" Kari ta ja tsaki, "Jummai kina bani haushi,mu da muka nufi gurin masu biyan
buƙata cikin gaggawa shakkar me zakiyi,ai ki sa a rufe mishi baki yanda ba zai tuna motar ba,su
kuma shegun yaran masu ɗan iskan rawar kan tsiya sai kurum ki ringa haɗa su da na Mashinko
direba ya dinga kai su."
https://hikaya.bakandamiya.com/muazzam-babi-na-daya/
*í ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒí ½í²ƒWata garabasa sai tsarin bakandamiya ki sayi littafi daya ki samu damar karanta
littafai sama da arba'in,akwai litattafan manyan marubuta kamar su RUFAIDA UMAR,LUBNA
SUFYAN,MAIMUNA IDRIS SANI BELI,FATIMA DAN BARNO da sauran su,yi kokari kada
wannan garabasa ta wuce ki akan naira 500 kacal,wacce take bukata ta yi magana ta wannan
number 09068032427*
____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 9*
Jummai ta ce, "sun raina Tinau direba, kullum rigima shi yasa fa Alhaji ya sai musu ta su", Kari
ta ce "ƴan iska to su fito da miji mana ki musu aure,ki huta can sa ƙarasa karatun a ɗakunan su"
Jummai ta ce "yaushe suka nutsu har zasu samu mazan ƙwarai? Sai dai masu rarake su kuma
ƙanana sa'o'insu.
Kari ta ce,"nima gidana matsalar kenan,Safina tamkar ƴar Akuya ko ince karya maza wannan
ya aje wannan ya ɗauka". Jummai tasa dariya, sannan ta ce bata yar ba,kin tuna lokacin muna
school?" Kari ta ce "kema ai Allah ne yaso ki gurin cire cikin da Mr.Joseph ya yi miki,mahaifarki
ta nakasa,da ba don haka ba ƴarki ko ɗanki ba ƙaramin tataccen ɗan iska ko ƴar iska za'ayi ba."
Jummai taja tsaki "bar tuna min ɗan iska Mr.Joseph, shi ne ya yi min sanadi da ko ƴan iskan na
samu ai da ban Yi wahalar ɗaukar rayukan jama'a ba,tun da nasan don rashin ƴaƴa ne yake ta
wannan aure-auren." Kari ta ce, haka ne. Suna ta ƴan hirarrakinsu, har suka isa ƙauyen da zasu
je, hanya ce mara ƙyau mai cike da ƙwazazzabai tare da dutsina.
Suna isa suka fito suka rufe motar, sannan suka soma hawa dutsen wata ƴar bukka ce a saman
dutsen nan suka nufa ashar suka zunduma ita ce sallamar shiga gurin Bokan dutse,shima daga
ciki ya ce maraba da ƴan tselan uwa,ku shigo dan abu takazar ubanku.
Suka samu guri gefe suka zauna. Ya dubi Jummai da jajayen idanunshi,kafin ki ce komai ki fara
cika min alƙawarina,don tsakaninmu babu ƴar ɗaga ƙafa yanzun ga wuri ga waina zamu dinga
yi, tunda ke na lura ƴar rainin hankali ce. Dodo ya ce in kin sake kuskure alƙawarinsa za ki sha
mamaki."
Ta buɗe jakarta tana cewa,"kai ko gashi ka cika gajen haƙuri, gashi" ta miƙa mishi makullin
motar, ya ce "riƙe tukunna ina motar?" Ta ce "a'a tana can ni ba zan iya jan zuwa gurin nan ba,
kuma bana son in ce direba ya jawo asirina ya tonu,ko ba haka ba ne? Yace don wannan babu
ji ko su Ifiritu sai su ɗauko, amma sabuwa ce ko?" Suka dubi juna ita da Kari, har suna haɗa
baki gurin cewa dal ma kuwa,ya ce shi kenan. Ya shiga haɗa wasu abubuwa yana surkullenshi
har ya gama ya ce,to ke ma fa kina da aiki a gabanki, domin wannan aikin ya banbanta da na
baya.saboda ita wannan yarinyar tana yawaita ambaton Ubangijin musulunci, saboda haka sai
mun dage."
Jummai ta ce,gara kam a dage Boka, saboda wannan in son raina ne ta mutu a ranar da aka
kawo ta.
Hajiya Karima ta ce "in ma ta mutu ranar ya kiyaye aure," Boka ya ce "ba zata mutu sanda ku
ke so ba, domin Aljani ba zai samu aiwatar da aikinsa ba, sai lokacin da take fashin sallah,
saboda tana tsananta ambaton Ubangiji.
Tana yawan kusanta kanta da Ubangiji, sannan ke kuma zaki daina sallah daga yau har sai
lokacin da Dodo ya ce kici gaba da yi. Ya miƙa mata wani ruwa gashi nan ki yayyafa cikin ɗakin
da za'a saka amaryar, kullum sau uku a rana har tsawon kwana baƙwai. Ya bata wani ɗan
gwangwani,ki binne shi a ƙofar ɗakin amaryar in ana sauran sati ɗaya bikin," ta ce "Boka ko'ina
tiles,ya ya zan yi in saka? Ya ce "ruwan ki in kin matsu ki sa a fasa, sannan zaki dawo in ana
sauran ƙwana tara bikin" ta ce "to sai batun mijina ya ya zanyi na sameshi a hannuna? Ya
ce"wannan ba zan gaji da gaya miki ba,ba zaki taɓa samun shi yanda kike so ba,
kasancewarshi mai tsayuwa akan duk dokokin Ubangijinshi, sannan tun yana ƙarami iyayanshi
suna matuƙar tsaye kan shi, duk bokan da ya ce zai kama miki shi to ƙarya yake yi ba zai iya
ba, sai dai ki haɗa da kissarku ta mata,to zuciyarshi tana da tausayin mace, amma ba dai asiri
ba,in ma ya kamashi ba za aje ko'ina ba, zai karye.
Jummai ta ce, "shikenan zan ga me zanyi. Suka tashi suka fita yana me ƙara tuna mata ban da
Sallah ban da Sallah. Wa'iyazu billa,kaji mushirikan mata.
Alhaji Saddiƙ ya dubi Fatima, "Sister ki duba dai ko za'a ƙara wani abu" cikin dariya ta ce, "sun
yi fa Brother,sai dai in kana son ka ƙara zaka iya." Nafisa ta ɗaga wani takalmi mai igiya ta baya
ta ce, "haba Brother wallahi wannan takalmin ya yi ma A'isha kaɗan na yara ne fa?" Ya dube ta
kaji ki to ai itama yariyar ce,she is fourteen or fifteen,sa'ar ƴarki ce fa sister" ya dubi Fatima.
Nafisa ta ce "amma ai tafi Nana tsawo," ya ce "to ai Kuma Nana ta fita ƙiba ma," ya miƙe yana
cewa, "kisa direbanku ya ƙwasa ku kaima Hajiyarmu,in ta ce komai ya yi shikenan,sai kusa
ranar tafiya tunda gaba ɗaya yau sauran kwana sha shida bikin. Suka ce "To" bayan ya fita suka
soma dariya Fatima ta ce "ni nama rasa me zan ce ma Brother babu fa brezia ko ɗaya,ya dai
saka pants da skat zuwa su bess, amma babu bra. Nafisa ta ce "nufin shi bata da nonon
sakawa ne ko?" Suka sa dariya, Fatima ta ce "kin san shi da kanshi ya siyo undes ɗin, zannuwa
da sauran kayan duk ni ya ba zaɓi amma ko takalma sai gashi da su" Nafisa ta ce "shikenan in
ta zo gidan ya siya," suka soma shirin ƙwasar kaya don zuwa gidan Hajiyarmu.
A'isha tana ƙwance kan katifa, zuwa yanzu ta gama sadaƙarwa ta dangana ta kuma ɗauki
ƙaddara, sannan ta amince ƙwananta ne ya ƙare. Don haka ko yaushe zaka same ta da
casbaha tana ja. Istingifari ta ke yi, domin Allah ya yafe mata zunubanta.
Wayarta da ke gefanta ce take ruri, bayan ta ɗauka tare da sallama, ya amsa, sannan ta ce,
"ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby, baƙin sun taso na san yanzun ma sun sauka a Kano,
saboda jirgin Kano suka hau, ta ce "Allah ya kawo su lafiya," ya ce "Amin" ya ɗan yi shiru
sannan ya ce "Beby duk abinda be yi ba cikin lefen ki gaya min kin ji ko? Saboda bata son
dogon bayani sai kurum ta ce "To" ya ce "shikenan sai na kira ko? Ta ce,to na gode, ya ce nima
haka.
Gidan cike yake da ƴan'uwa ta gefen Umma da kuma gefen Abba. Shi yasa yawancin baƙin duk
ƴan Gumel ne, sai ƴan Garki, sun zo ne don karɓar lefe kamar yarda akayi waya aka sanar da
su. Anyi girke-girke don tarbar baƙin Katsina. Su kan yiwa amarya tsiya da cewa duk gudun
auren ne ta ƙara ramewa, ita dai tana kallon su tana kuma jin su,nata addu'a ne a zuci, Umma
ma dai tana ƙarfin hali ne domin kada ta karya ma A'isha guiwa.
Sun iso cikin motoci guda uku fararen Acadami su uku motar farko matan abokanshi ne na
Kano,ta tsakiya kuma kaya ne a ciki, sai direba ta bayan mata huɗu ne Fatima a gaba, sai
Nafisa sai kuma ƙanwar Hajiyarmu, da ƴaƴarta Talatu.
Ƴan unguwa da suka taru da kuma ƴan'uwa sun sha mamakin ganin kayan da aka kawo, suma
sun sha tarba kuma sun ga karamci sun kuma yaba. Nafisa kuwa ɗakin A'isha ta shige lokacin
A'isha tana wanka. A'isha tana fitowa taga Nafisa zuciyarta tana son Nafisa. Ta saki murmushi
tare da cewa "dama har da ke aka zo? Ta ce,eh mana aini Brother ya yi ma ƙawance. A'isha ta
zauna tana shafa mai, Nafisa na kallonta, lallai kam yanzun nononta suke fita ashe ya kula ne.
Ta ce, Nafisa ya ya Hajiya fa dasu Aunty Fatima?" Nafisa ta ce, "ai tare da Anty Fatima, muka
zo Hajiyarmu kam tana gaishe ki ba ki ce ina Uncle ba? A'isha ta ɗan yi murmushi kawai.
Nafisa ta ce, "Naga kin rame ne" A'isha ta ɗan yi murmushi, sannan ta ce "Na sha jinya fa tun a
school har yanzu." Nafisa ta ce Allah sarki, to Allah ya ƙara lafiya. Amin inji A'isha, tare da zura
wata duguwar riga, sannan ta soma ɗaura ɗan ƙwali. Nafisa ta ce Allah yasa ki haifa mana
Beby mai irin gashin nan naki. A'isha dai ta sunkuyar da kai, Nafisa tayi-tayi ta zo su gaisa da
su Anty Fatima, amma ta ƙi,Fatiman ce ma tace ai nima ƙanwar ta ce, bari naje mu gaisa,Talatu
ma tabi Fatima dan su ga A'isha.
A'isha ko rufe fuskarta ta yi, har dai suka gaji suka tafi, Nafisa ma nan ɗakin ta ci abincinta,
Abba yayi-yayi su ƙwana amma suka ce a'a, Kano zasu ƙwana don zasu shiga kasuwa goben
da safe,sai su wuce. Da zasu tafi an basu tukuici suma yanda ya kamata. Nafisa ta raɗa ma
A'isha a kunne, cewa ki rage bacci,ki tsaya kan addu'a.tsayuwar dare zaki dinga yi kina roƙon
Allah alkhairin da ke cikin auren ya kuma kare ku da duk masu sherri da hassada kin ji ko?
A'isha ta ce, na gode Nafisa zan kiyaye insha Allah.
Ya fito daga wanka,wankan da ya zama mishi ƙa'ida, duk dare koda da ya yi shi ne zai kusanci
matarshi ya fi gane yayin in yaso ya sake. Matsawar bai yi wankan nan ba,to ko ba zai samu
bacci ba, kasancewar yanayi ne na zafi shiyasa. Yana fitowa ya warware (AC) turarukan shi na
ƙwanciya ya faffesa, sannan ya saka kayan baccin shi riga da wando.
Ya zauna bakin gado yana son jin muryar A'isha ne kawai,yau ƙwana biyu kenan ba su yi waya
ba,bai san mene ne yasa yake son Yarinyar ba,yana tsoron fa kada Yarinyar ta mutu tamkar
sauran matanshi. Ya soma neman layin yarinyar,yana yi yana kallon agogo goma ta gota a
ranshi, ya ce ko kin yi bacci zaki tashi. Dai-dai lokacin ko ita tana kan darduma, nafila take yi
sanda ta sallame sannan ya sake kira.
Ta ɗauko wayar ta ɗaga tare da sallama, ya ce "oh sorry Bebyna, na tashe ki kina bacci ko?" Ta
ce, "a'a bana bacci, ya ce me ya hana ki? Ta yi shiru, ya ce to ko abinda ya hana ni bacci ne
kema ya hana ki? Ta ce um,ya yi ƴar dariya kin san abinda ya hana ni ne? Ta ce a'a, ya ce in
gaya miki? Ta ce eh,ya ce ni tunanin kine ya hanani ke fa? Ta yi shiru ya ce Beby kina ji na
kuwa? Ta ce,ina jin ka,ya ce oh gaya min, ta ce ni ina sallah ne, ya ce good,me kike roƙo? Da
sauri ta bashi amsa da cewa cikawa da imani da rahamar kabari, tare da samun Aljanna
maɗaukakiya." Ya ce "Umhum? Yana son jin ƙarin bayani, ta ce "Shikenan nake roƙo," ya ce
"batun aure fa baƙya yi mana addu'a? Shiru ta yi jikin shi ya yi sanyi ya ce A'isha in tambaye ki
wani abu? Ta ce eh, ya ce zaki sanar dani gaskiyar maganar? Ta ce,in har na sani ba, ya ce "kin
ji wasu maganganu ne a kaina?" Ta ce kamar me? Ya yi ɗan jim sannan ya ce koma na me? Ko
kirkina ko akasin haka?.
Ta rasa me zata ce ya ce ina jinki nasan duk mai irin sunanki in dai ta ci sunan bata ƙarya.
Sanar da ni. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Uncle duka biyun na ji da kirkin da kuma akasin
hakan. Ya ƙwanta rigingine jikinshi ya yi matuƙar sanyi sannan ya ce "Beby tsorona ki ke yi ko?
Kin tsane ni ko? Kina zargina kema ko? Na sani na dai na burge ki ko? Muryarshi ta soma
rawa, shi kenan ba zan matsa miki ba Beby zan barki kema kina tsoron haka bana son ki mutu
domin kin shiga raina sosai" ya kashe wayar ya jefar da ita a kan gado sannan ya ɗauko filo ya
rufa akan fuskar shi tare da matsewa yana jin wani pain a cikin ranshi.
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account numberí ½í±‡í ¼í¿»*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala
ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin
shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 10*
A ɓangaren A'isha kuwa duk