Showing 12001 words to 15000 words out of 30509 words

Chapter 5 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi

09 Jul 2025

1300

magana,jiya ma nake sanar da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon ki ba,

saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."

Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ƙila zai neme ta. A'isha ta yi ajiyar
zuciya,lallai ya kamata ta sanar da Umma, domin dai ba su san komai kan Uncle ba. Sai da
Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki abinda ke damuna,
amma sai kin yi min alƙawarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin fargaba Umma ta ce, "Sanar
dani,ba zan gaya mishi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe Uncle ɗan yankan kai ne? Ashe duk
kuɗin shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da cewa "Wane Uncle ɗin?" A'isha ta ce, "na
Katsina, kinsan ƙawata ƴar Katsina ce nan dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da
Uncle ɗin nata, Umma ta shiga damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya
kuwa A'isha zancan nan gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta
yi ƙarfin hali ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, domin dai
duniya yanzu babu gaskiya, kuɗi suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum
shi ko yana da nashi burin a kanka".

A'isha ta soma kuka tana faɗin, "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai taɓa yarda
ba saboda ya yarda da Uncle ni dai na haƙura zan auri Uncle ɗin tunda dai dama na san
ƙarshena mutuwa zan yi."

Abba da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin tun ɗazun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A ranshi ya
ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke ɓoye musu,ya zama dole ya shiga ya sanar da su gaskiyar
lamarin domin ya yarda Alhaji Saddiƙ ba zai mishi ƙarya ba,ba zai cuce shi ba,ba zai ci amanar
shi ba, kuma ba zai kasance ɗaya daga cikin masu shan jini ba.
Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ƙarfin halin cewa "kuna hira ne? Umma
cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da faɗin "lafiya dai ko?
Umma ta ce "da sauƙi dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da yake yi kenan?" Abba ya
ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddiƙ mana ta shiga jero mishi bayani yanda A'isha ta sanar da ita.
A'isha dake ƙwance jikin Ummanta tana kuka,ta ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so
ba, amma duk da haka zan aure shi.

Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da kansa ya yi
min bayanin zargin da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya Jummai duk Mata da ya
aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma ne? Duk sun rasu," A'isha ta zaro
ido, Abba ya ci gaba da cewa, "ina so ku sani cewa, dukkan mai rai mamaci ne, haka nan
matansa da suka riga mu gidan gaskiya,ku yarda wa'adinsu ne ya zo, batun yana yankan kai
babu gaskiya cikin zargin da mutanan unguwar suke mishi."

Umma cikin matsananciyar damuwa ta ce, "to yanzun Abbansu matan nasa suna mutuwa haka
za'a bashi A'ishan?.

Ya ce, "Haba Fatima,ya ya ki ke dawo da hannun agogo baya? Na gaya miki na sake gaya miki
aure babu fashi, mutum baya mutuwa face ƙwananshi ya ƙare. Ya fita yana cewa "ki zo."

Ɗakinta ya shiga, Umma ta biyo shi jikinta babu ƙwari. Ya dube ta yace, "Haba Fatima,me zai
sa kiyi min haka? Ke kin san son da nake ma A'isha,kin sani ba zan cutar da ita ba, aure bautar
ubangiji ne, zan yi murna a ce ta mutu tana ibada,don haka ki natsu kuma ki ƙwantar da
hankalin ki,ki bani goyon baya. Ki yaƙi shaiɗan mu tattaushe ta,nima wallahi ƙarfin hali nake
yi,in tana ganinmu cikin damuwa zata kasa ƙwantar da hankalinta kullum zata zama cikin
fargaba."

Umma ta ce, "Shikenan, zan yi yanda ka ce," ya ce "yauwa, addu'a kurum ita ce magani,ki
tsaya tsayin daka da addu'a,ba dare babu rana. Itama A'ishan ki tsaya kanta ta dage da yin
azkar safe da yamma. Cikin fargaba ta ce "To."

Sanda Umma ta shigo ɗakin A'isha, ta samu A'ishar tana zaune gabanta wayar ta ce tana ta ruri
tsabar tsoro ya hana A'ishar ɗaga wayar Umma ta kalli fuskar wayar Uncle ɗina haka taga an
rubuta nan take ta gane,ta cewa A'isha an sa shi mana? Ki natsu ki ƙwantar da hankalinki,ki
mishi magana cikin natsuwa,kada ki ɗaga mishi hankali,kin ji?" Ta ce "Ina jin tsoron shi ne
Umma" Umma ta ce "Daina tsoron shi, shi ba mugu bane sharri ne mutane suke masa, ɗauki
wayar." Ta kai hannu zata ɗauki wayar, ta katse a karo na biyu.

Ya sake kira a karo na uku, Umma ta ɗauki wayar ta miƙa mata, hannunta yana rawa ta amsa ta
danna green ta sa a kunne. Cikin muryar nan tashi mai natsuwa da hikima yace, "amincin Allah
ya tabbata a gareki Humaira Beby". A'isha ta dubi Umma,harara Umma ta zabgo mata, sannan
ta fita can gefen. Ya ce "kina jina ƴar Abba?" Ta daure, sannan ta ce, "Ina yini Uncle?" Ya ce,
"lafiya lau,kin dawo lafiya?" Ta ce, lafiya lau, ya ce "Masha Allah" a zuciyarta kuma faɗi take,
Allahumma kafihim bima shi'ita,tana maimaitawa tana sake faɗa,ya ɗan yi gyaran murya,ya ce
"A'isha ina labari?" Ta yi shiru,ya ƙara sanyaya murya,ya ce "A'isha kina ji na?" Ta ce, "Umh" ya
ce, "zan zo week end,tun Friday kin ji? Kamar ta ce A'a, sai kuma ta ce Umh, ya yi ƴar dariya
sannan ya ce "to Bebyna,me da me zan kawo miki?" Ta ce,babu komai.ya ce Shikenan, sai na
zo, tace, "To ka gaida Nafisa" cikin jin daɗi ya ce "ita kaɗai ban da Hajiyarmu?" Da sauri ta ce
"har da su." Ta ƙosa ƙwarai ya gama maganganunshi, kamar ko ya sani, ya ce "to bari na ƙyale
ki sai kin ganni ko?" Ta ce Uhum, ta riga shi kashewa,ana shi gefen bai damu ba zaton shi
kunya ce.

Daran juma'a,sam A'isha bata runtsa ba, tama rasa tunanin da zata yi, duk da lallashin da
Umma take mata, bayan sun karya, Umma ta matsa mata suka shiga kitchen don girka abin
tarbar baƙo.

Sun gama sha biyu da rabi nan Umma ta bar ta ta haɗa mishi zoɓo da sauran kayan sha. Ta
shigo falo ta ƙwanta kan kujera, Umma ta fito don zuwa kitchen ta ce har kin gama?" A'isha ta
ce,eh, Umma ta miƙa mata waya ga shi yana ta kira ni ina wanka." A'isha ta amsa Umma ta
koma ciki.
Wayar ta soma ringing. Ta tsurawa wayar ido, ita dai kullum ƙara tsoron shi ma take yi, amma

ba ta da yanda zata yi dole ta ɗaga wayar tare da addu'a a can ƙasan zuciyarta. Sannan ta ce,
"Salamu alaikum" ya ce "wa'alaikumus Salam, Beby ina ki ka shiga ne? Ina ta kiran wayarki?"
Ta soma magana cikin in'ina, "ina....am......wannan ne a kitchen ne," ya yi ƴar dariya, "ni kike
yiwa girki kenan?" Ta yi shiru, ya ce "ok,shiru yana nufin eh ne,to na gode. Yanzu haka na shigo
Jigawa, masauki kawai zamu je, sai na iso kenan" ta ce,to, Ya kashe wayar.

Ta tsaya tana kallon wayar,daddaɗar muryarshi har yanzun tana yi mata gizo, murya mai cike
da kamala kamar yarda fuskarshi take nunawa ta tuno suffarshi a fili ta ce lallai Uncle bashi da
makusa in ban da na mugun halinshi koda dai su Umma suna ƙaryatawa.

Ta fito wanka tayo alwalla tana idar da sallar azahar mai ta shafa sama-sama saboda zafin
garin ta zazzago farar hoda a hannunta,ta ɗan murza a fuskarta ko madubi ba ta duba ba,dama
ita bata ƙwalliya. Don haka ba ta ma duba madubi,kai ita fa ko kaya bata da zaɓi duk wanda
Abbanta ya sai mata sun yi,don tana saka kaya ne don suturta jiki ba wai don gayu ba, ta ɗaga
aƙwatinta ta ciro kayan da ke sama. Wata atamfa ce ta mutanan Ghana, fara ce ta saka taje ta
ɗauko abincinta,ta zauna tana ɗan cakula tana dai cin abincin ne amma hankalinta duk yana
kan Uncle ganinta ƙila ma tun yau zai gama da ita. Jafar da Munnir suka shigo,suna cewa
Umma ga Uncle ɗin mu ya zo yana waje yana waya. Umma ta ce, "tare da Abbanku su ke?"
Suka ce "a'a shi kaɗai ne, amma Yaya Abdulrahman yana gurinshi, ta ce "Abbanku yau ina ga
aiki ya mishi yawa ne,ko gida bai dawo ba, ina ganin daga Office ɗin ya wuce Masallacin
juma'a.

Jafar ya fita waje,jim kaɗan ya dawo. "Umma Yaya Abdulrahman,ya ce ki bada makullin ɗakin
baƙi" taje ta ɗauko, A'isha kam tana zaune kamar gunki tana jin su. Yaya Abdulrahman ya
shigo, "Umma Uncle yana ɗakin baƙi ya ce yabi ta Ofis ɗin Abba,sun tafi masallaci, shima yaje
ya yi sallah ya koma Ofis ɗin basu dawo ba shi ne ya zo nan gida". Umma ta ce, "bai kira
wayarshi ba?" Yana ta kira bai samu ba sai yanzun. Umma ta ce, "To ai shi kenan, tunda ma ya
sameshi. Ta leƙo falo "A'isha tashi ki je ki shirya mishi abinci,ki kai mishi." Jiki babu ƙwari ta
tashi ta fita.



____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*Ɗandano page 8*


*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son

PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT}:--1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala
ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```



*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin
shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*```


Babban tire ne ta shaƙe shi da kuloli masu ɗauke da kalolin abinci. Sai plate da cokali, da
sallama ta shiga,ƙasan zuciyarta kuma tana maimaita addu'ar Allahumma kafihim bima shi'ita.

Ya yi matuƙar ƙyau cikin shadda mai tsada kalar ja mai duhu,hular da takalman duk kalar jan
ne,ƙamshin daddaɗan turarenshi ya cika falon. Duk da tsoronshin da take ji bai hana zuciyarta
yaba ƙyanshi ba. Ta dire tire kan tebur ɗin, gabanshi ta jawo teburin sannan ta sunkuyar da
kanta ƙasa ta ce sannu da zuwa Uncle, ya ce "yauwa ƴar Bebyn Uncle,I hope kina lafiya?" Ta ce
"lafiya lau,ya ya su Nafisa da su Hajiya?" "Duk suna gaishe ki, cikin jin daɗi yake bata amsa,
domin yarinyar ta shiga ranshi har yana mamakin yanda wasu lokutan ya kan shagala da
tunaninta,ya kan ji kewar ƴar siririyar muryarta, da Beby face ɗin ta, abinda bai taɓa yi kenan a
kan mace ba, duk matan da ya aura baita jinsu kamar yanda yake jin A'isha ba,a ranshi. Ta cika
kofi da ruwan zoɓo mai sanyi ta miƙa mishi cike da ladabi, ta koma gefe ta zauna, ya ce "No,
come on hau kujera ki zauna,ta ce nan ya yi Uncle, ya ce to nima bari na sakko ƙasan, ta yi
sauri ta hau kan kujerar ta ɗan ɗofanu yana ƴar dariya shima ya gyara zaman shi.

Sannan ya soma shan zoɓon ta gefen idanunta ta ke kallonshi. A ranta ta ce "Oh,ga mutum har
mutum, amma cikin zuciyarshi gara kura da shi. Ya katse shirun da cewa "Beby in Allah ya
gwada mana ki ka koma gidana, ina son kina min wannan zoɓon kin ji?" Ta ɗaga kai alamar ta ji
ya ce "to abincin fa zo ki zuba min," ta ce to, tana buɗe kular farko yaga saƙwara fara ƙar-ƙar,
ya ce "ai shikenan Beby yau kuwa har in tafi ita zan ta ci.

Nan ta zuba mishi da miyar agushi, ga nama manya-manya,ya cika cikinsa dam,ko magana ba
ya iya yi, sai da ya gama sannan ya dube ta yana goge fuska da fari ƙar ɗin handkachief ya ce,
Beby kin ganni babu ba ka sai kunne ko? Ta sunkuyar da kai.

Ya ce,"Beby sai naga kamar kin rame min a ido hakane?" Ta ce na ɗan yi mura bayan haka
kuma ga makaranta," ya ce "kin manta ɗayar ga kuma maganar aure". Ta rufe fuska, ya yi ƴar
dariya sannan ya ce zan sa su kawo kaya da zarar na koma gida nan da sati biyu zuwa uku,kin

zama ƴar mutanen K.T? ko?" zancan ya daki zuciyarta, nan take ta raya ma ranta haka yana
nuna nan da sati huɗu zuwa biyar zata baƙunci kabarinta, tunda an ce matan nashi ba sa wuce
sati biyu zuwa uku suke mutuwa.

Ya katse ta. "Ko ya yi nisa a rage?" Da sauri ta girgiza kai,ya ce "a barshi haka?" Ta ɗaga kai
alamar Eh. Nan ya ciro mata tsarabar ta, abubuwan ci ne tare da turaruka har da wata ƴar Tedi
ta wasan yara. Ya miƙa mata ledojin ya ce "to duk da kin ce baki son tsaraba gashi nan ki basu
Jafar ke kuma ga naki" ya miƙa mata Tedi.
Baki ta saki tana kallonshi, shima ita yake kallo tamkar masu kallon soyayya, sannan cikin
sanyin murya ta ce "Uncle me zan yi da wannan?" Ya ce "wasa mana" ta ce, "am not a small
girl," ya ce haba? Ta sunkuyar da kai tace,da gaske,ya ce shikenan to ki ajiye min in kin haifa
mana Small boy sai ki na bashi yana wasa," ga mamakin shi sai ya ji tace "in kuma na mutu
fa?"

Da sauri ya dube ta,a ranshi ya soma zargin ko taji cewa matanshi suna mutuwa ne? Amma a
fili sai ya ce,"nima ina yawan tuna haka, sai dai duk sanda na tuna cewa zan iya mutuwa ko ke
ki mutu ban ga ɗan kaina ba, ina shiga wani mawuyacin hali, zuciyata tana sonki da yawa." Ta
sunkuyar da kanta ƙasa,ko dai mummunan zato ne a ke mishi? Ko dai zargi ne? Ƙwanan matan
nasa ne suke ta ƙarewa? Ya katse mata tunani da cewa, "ki na tsoron mutuwa ne? Ko kina
zaton in kin aureni zaki mutu ne?".

Cikin dabara ya sako mata tambayar,don yana son ji ko ta samu labarin matanshi suna mutuwa
ne? Nan take ta gane nufinshi,don haka sai ta ce "a'a bana tsoron mutuwa,sai dai kullum
tunanina yana kan ayar da ke sanar damu (kulli nafsin za'ikatul mauti), kaga dukkan Musulmi
yana da ƙyau ya dinga tunawa ranshi zata ɗanɗani mutuwa, sannan in ajali ya yi kira ko ince in
ajali ya zo ba za'a ƙara ma mutum ko second ba.

Alhaji Saddiƙ ya dube ta cike da farin ciki,ya ce haka ne Beby, lallai kina da kaifin basira. Haka
nan duk bawan da yake yawaita tunanin mutuwa zata iya riskarshi a kowane lokaci,za ki
sameshi yana mai matuƙar kiyaye dokokin Ubangijinshi, ina saka rai kema kina ciki? Ta
sunkuyar da kai tare da faɗin insha Allah ya ce, to ba zaki taɓe ba.
Sannan ya canza zancen da cewa,me kike shiryawa bikin? Ina nufin waɗanne shagulgula za
kiyi ke da ƙawayanki? Saboda in na tafi ba zan dawo ba, sai ɗaurin aure, shiyasa nake son in
sallame ki."

Ta dube shi,a ranta ta ce, inyi shagalin me? Bayan ni ƴan ƙwanaki ne suka rage min,a fili kuwa
sai ta ce, "ba zan yi komai ba." Ya ce, "Haba! Ko walima?" Ta girgiza kai tare da ƙoƙarin maida
ƙwallar da ke son zubo mata. Ta ɗan saka hannu ta ja hancinta kamar tana mura, sannan ta
ƙago murmushi ta ce "kasan Uncle bani da ƙawaye bayan haka ma ni ban cika son hayaniya
ba,so kaga gara na barshi ko?" Ta faɗa tare da duban shi,ya ce "shikenan Bebyna" ya saka
hannu cikin aljihun ya ciro rafar ƴan ɗari biyar guda biyu dubu ɗari kenan,"gashi gudunmawata,"

zatayi magana ya tare ta da cewa, "kul ki kakiyi magana, ke dai ce ne Allah ya cika mana
burinmu,a ranta ta ce Amin in ba shanye mini jinina ba ne. Ya ce zaki shiga gida ko? Da sauri ta
ce,eh tare da kallonshi ya yi ɗan murmushi sannan ya ce, "kin ƙosa ki tafi ko?" Ta sunkuyar da
kai tare da girgiza kan alamar a'a, ya ce "to ga kayanki nan ƙwashe. Ta miƙe tare da ƙwashe
kayan ta ce mun gode. Ya ce,ba ki ɗauki Tedi ɗin Small beby ɗin tamu ba,ta kalli Tedin sannan
ta ɗauka ya ce in Abbanki ya shigo sai ki ce ina jira, sannan ki bar wayarki a kunne kin ji? To
tace,ta fita.

A gadon Ummanta ta zube kayan tare da zama gefen gadon ta rafsa tagumi. Umma ta fito daga
(toilet) ta tsaya tana kallon kayan da iyayen kuɗin da ke zube a kan gadonta, ta ce "A'isha
waɗannan kayan fa?" Ta ce "Uncle ne ya ce in kawo ma su Jafar?" Ta ce, "wannan kuɗin fa?"
Me yasa ki ka amsar masa kuɗi?" Ta ce "Umma nayi-nayi ya bar su yaƙi wai cewa ya yi
gudunmawa ya bani don na ce mishi ni ba zan yi shagalin biki ba.

Umma ta ce duk da haka da dai baki amso ba, A'isha ta dubi Ummanta ta ce, "ki aje a gurinki ni
sai in dinga ganin tamkar yana biyan kuɗin jinina ne da zasu sha....." Ke! Tsawa Umma ta daka
mata, sannan ta ce "A'isha bana son jin irin waɗannan surutan daga bakinki kenan kema kin
yarda da mummunan zargin da al'umma suke ma mutumin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0