Showing 18001 words to 21000 words out of 30509 words
Chapter 7 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi
sai ta ji babu daɗi har ma ta yi da ta sanin amsa shi, sai ma duk ta
ji tausayin shi ya kamata,ta ji kamar yana kuka. Abbanta zai ji daɗi in yaji labarin nan kuwa? Ƙila
ma ya ce ba zai yafe mata ba. Da sauri ta tashi ta duba agogo,sha ɗaya saura, ta ɗauki ɗari
biyu ta fita, da sanɗanta ta fice bakin titi ta siyo kati ta dawo ta shige. Sai da ta kulle ƙofarta ta
hau katifarta ta loda katin, gabanta yana ɗar-ɗar ta soma kiran layin shi kasancewar wannan ne
karo na farko da ta taɓa kiran shi.
Dai-dai lokacin shi kuma yana ta neman layin Abba don ya shaida masa ya haƙura da auran,
amma wai layin is switch off,sai ga call ɗin A'isha Beby kamar yanda ya rubuta a cikin wayar
tashi. Ya tsura ma sunan ido, kada dai idanunshi ne suke mishi gizo? Ya dai ɗauka ba tare da
yin magana ba,ta ce "Uncle" ya ce "Na'am" ta ce "nifa ban zarginka,don Allah kada kayi fushi
dani ko da na samu labarin tun a school ne na san dai an confuse amma ba dai na yarda
bane,don Allah in nayi laifi kayi min afuwa." Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "ba ki da laifi Beby,
domin nima sai da nace a'a Abbanki ya ce babu damuwa, amma bari kiji wani abu,kin ga ke
yarinya ce ko? Amma zan rantse miki da wallahi-wallahi ban taɓa shan jini ba, duk wani laifi
game da sicret cold zargi ne,ban san shi ba, batun mutuwar matana ƙarar ƙwana ce kurum,kin
yarda da haka? Jikinta a sanyaye ta ce na yarda,ya ce "to Beby ki ƙwantar da hankalinki, addu'a
za ki dage da yi Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi kin ji ko?" Ta ce "to,kaima ka
daina fushin? Ta ci gaba kada fa ka sanar da Abbana," ya yi ƴar dariya bana fushi da ke, kuma
insha Allah ba zan taɓa yi ba, itama ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "to sai da safe,ka kwanta.
Ya ji daɗin kalmarta, sannan ya ce "to zan yi yanda ki ka ce,kema ki ƙwanta tare da mafarki mai
daɗi na twins ma su kama da face ɗin ki,ta kashe wayar da sauri.
Hajiya Jummai ta kalli kayan, sannan ta kalle shi.
"Me ka ke nufi da waɗannan kayan?" Ya dube ta "Na ki ne mana" ta taɓe baki, "Ni fa gaskiya
duk zannuwan nan ba suyi min ba,babu kala ta, maimakon ka bani kuɗin na saya da kaina?
Kuma ina son canza kayan ɗakina, sannan ga su Suby." Ya ce, "Jummai, gaskiya ni dai ba zan
bada kuɗin wasu kaya ba,kin san nawa na siya waɗannan kayan? Game da gyaran ɗaki dai
zan baki dubu ɗari,su Suwaiba kuwa dubu hamsin zan bada kada a kuma damuna,cefanen gida
kuwa mun gama magana da Uche,ya rubuta komai." Ta sake fusata, domin ta kula ma
ƙwangilar da take so ta yi bazata samu ba kenan, komai ƙit da ƙit? Ta dube shi "don kurum
zakayi aure, sai ka dinga komai faɗa-, faɗa? Ga wani maƙo da ka koya,da Uche ne yake faɗin
abinda ake so?" Ya ce,"to ke ko yaushe baki gida kin ma fi ƙarfin ki ce min zaki guri kaza,koda a
waya ne sai dai na dawo baƙya nan, lokaci ya ƙure min dole na sauke abubuwan dake gabana,
Uche kuwa shi ne yake girkin nan,don haka shi ne yasan abinda za'a nema.
Ta ce, "Kana lokaci ya ƙure,ba saura sati uku bane bikin? Ta ce, "batun lefe fa? Sai ka kawo a
haɗa" ya ce ai lefe ya daɗe a gidan su amarya." Ta miƙe cike da masifa.
"Lallai Alhaji Saddiƙ aurenka na wannan karon ya banbanta da na baya, wannan karon aƙwai
ƴar zargi." Ta soma kuka, "maƙiyana sun samu galaba,wato lefen ma ban isa ko gani inyi ba, na
gode." Ta fita tana cewa gara daka nuna min babu ruwana abinda babu ruwan mutum ai daɗin ji
ne da shi. Ya bita da kallo,wato ita bata san ma ta mishi laifi ba,bare ta bashi haƙuri ko ta mishi
bayani shi ne ta zo tana tuhumar shi,ya samu labarin ta saida motar da ya siya ma su Safiya da
Suwaiba, domin wanda ya gyara motar ne yake sanar dashi lokacin da ya je ɗaukar tashi motar.
Da be ga ta su Suwaibar ba yace sun zo sun ɗauka ne? Sai yaron mai gyaran motar ya ce, a'a
wani ne yazo ya ɗauka, kuma ya gaya mishi cewa Babanshi ne ya sayi motar. Alhaji Saddiƙ shi
dai alwashi ya sha ba zai ƙara sai wa yaran koda mashin ba.
Hajiya Jummai ta kalli Hajiya Kari.
"To kin ji yanda muka ƙwashe da Alhaji,babu abinda ya fi bani haushi wai har an kai lefe bani da
labari saboda rainin hankali, ke kayan faɗar kishiya ma shi ya siyo min, saboda haka ina son
mu koma gurin Boka, gashi bakon ya ce in biki ya rage ƙwana goma in koma,to gashi yau
sauran ƙwana taƙwas. Tunda jiya tara ya ce min ne ko nawa ne ma oho."
Hajiya Kari ta ce, "To gobe sai mu je,in ce dai kin binne abin da ya baki?" Ta ce "ina fa ni ban fa
san taƙamaiman lokacin ba sai jiya,na san zai kama zigar waɗannan ƴan iskan ƙannan nashi
ne" Hajiya Kari ta ce "Bari mu gama da amaryar, har su ba za'a barsu haka ba, sai mu shiga
tsakaninsu." Hajiya Jummai ta ce, "Da ko kin taimaka min,ba ma dai irin tsinanniyar Nafisan
nan, gashi yafi ji da ita duk cikin su."
Ta binne surkullen da aka bata,ta kuma yayyafa na yayyafawa kamar yadda aka umarce ta.
Sannan ta nutsu don tana son samun kuɗi a hannunshi, duk da wannan karon ya tsuke mata
bakin aljihunshi, ta samu dai-dai gwargwado.
Lokaci na ta zuwa gida kam ya sha fenti da gyara, yanda ya ba ta kuɗin canjin kayan ɗaki, haka
ya ba su Fatima da Sadiya da Nafisa kuɗi su siyo na ɗakin A'isha, sannan shima nashi gefen
sai da ya canza komai. Nan fa ta tada balli kan cewa shin wannan amaryar ta fi sauran ne yake
ta faman kashe kuɗi har da sa mata kayan ɗaki? To ba zai yiwu ba,ya ce Jummai ki daina tada
jijiyar wuyanki akan abinda ba za ki hana ba,yarinyar nan ko ba ni ne zan aureta ba kusan dole
ne in mata kayan ɗaki, ballantana gidana za'a sa,kina cewa ba zata yiwu ba,za ki hana ne?
Kema fa na baki haƙƙinki."
Su Hajiya Karima ne suka tausasheta da cewa yarinyar da ba mazauniya ba ki ke damun
kanki? Gawa ce fa.
Ita ko A'isha, amarya duk ta gama sukurkucewa,iyayanta ma suna daurewa ne kurum,tuni
ƴan'uwa da abokan arziki sun cika gida don yin biki.
Ranar ɗaurin aure ta kasance asabar,don haka ƴan ango sun iso juma'a domin ana gama
ɗaurin aure za'a ɗauki hanya da amarya. Alhaji Saddiƙ ya kasa zuwa ɗaurin auren,waya ya yi
wa Friend ɗin shi kan cewa ba zai samu zuwa ba,don ba ya jin daɗi. Lafiyar shi lau sai dai yana
ganin kamar za'ayi ta nuna shi,ko kuma Friend ya shaidama ƴan'uwanshi halin da ake ciki,ko su
iyayan in sun ganshi su dinga mishi kallon wanda zai yi musu sanadin ƴarsu da dai sauran
tunani kala-kala.
Daren juma'a aka sanya amarya a lalle,ba ta saka kowace ƙawa ba, sai dai ƴaƴan ƴan'uwa
sa'anninta. Da dare suna ƙwance a kan katifa zuciyar A'isha cike da tunanin gobe zata rabu da
Ummanta da Abbanta,ƙila ma rabuwar kenan. Hawaye ne suke bin gefen kumatunta, wayarta
tana ta ruri. Naja ta ce Amarya wayar ki na neman agaji, A'isha tasa hannunta ta lalubo
wayar,muryarta a dusashe ta ɗaga wayar tare da cewa "Assalamu alaikum, Nafisa ce?" Ta ce
"amaryar mu,na so in zo ban samu zuwa ba, sai dai in kin zo gobe mun haɗu, " ta ce "to ina yini
ya ya su Hajiya? Nafisa ta ce, kowa lafiya, gama Hajiya nan,sai dai nasan ba zata ɗaga wayar
ki ba saboda Brother ɗinmu ɗan fari ne,tana mishi kara.
A'isha ta ce,to ki gaida ta,ta ce to ga Uncle ɗin naki dama yazo ne nace ya kira min ke gobe. Ta
ɗan yi ƙasa da murya kada ki manta da addu'o'i daren yau, saboda Allah ya yi mana jagora a
cikin ɗaurin auren da za'ayi a gobe. Shiru kawai A'isha ta yi mata, sai kawai ta ji Muryar Uncle
yana cewa, Beby kina jina? Ta ce eh, zuciyarta kuwa sake karyewa ta yi hawaye ya shiga sintiri
a kumatunta, ya ce na kasa zuwa ne Beby sai ina ganin tamkar ban yi wa mahaifin ki adalci ba,
ina jin nauyinsu, kukan da take maƙalewa ya kufce mata, ranshi ya daɗa tsinkewa, ya ce "A'isha
kiyi haƙuri daina kukan zan yi miki magana ne," ta share hawayen ta sannan ta yi ƙoƙarin tsaida
kukan ta ce, ina jin ka, ya ce ina son ki tashi daga wannan kukan ne kiyi alwala, nafila za kiyi
tare da addu'o'i kin ji ko? Alkhairin da ke tare da auren,ki tsaida zuciyarki,ki daina wasi-wasi,ki
saka a cikin ranki cewa duk yanda Ubangiji ya yi dake dai-dai ne,kin amince?" Ta ce "Uncle
dama ni bani da wani zaɓi sai wanda Allah ya yi min, sannan zan yi duk yanda kace." Ya ce
yauwa Beby sai da safe.
Tsam,ta miƙe,Naja ta bita da kallo,ta shige (toilet) ta ɗauro alwala.
Naja ta dube ta, Angon yayi lallashi kenan mu ko munyi mun gaji kin ƙi kiyi shiru? Ɗan
murmushi ta yi sannan ta ce,Naja kenan ba zaki gane ba ne, sannan ta tada sallah. Sai ya
kasance wannan dare duk wanda yasan halin da ake ciki tsakanin Katsina da Jigawa idanunshi
biyu ya kwana, kuma tsaye gaban Ubangiji, ana ta kai kuka. Zuwa wayewar gari kowa ya tattara
komai ya miƙa wa Allah, sai sauraro duk sun nutsu da cewa duk abinda Allah ya yi daidai ne.
A'isha kam sai ta wayi gari zuciyarta sake duk ƙuncin da take ji ya washe, sai dai ɗan abinda ba
za'a rasa ba. Hakan ya yiwa Umma daɗi har ta isko Abba cikin ɗakinshi,tana shaida mishi
cewa...
____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 11*
*ƘARSHEN FREE PAGES*
*Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki akan farashin
masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata
zaku turo kudin ku ta wannan account numberí ½í±‡í ¼í¿»*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala
ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin
shirya sai kiyi magana*
Shaida mishi cewa yau kam A'isha ta saki ranta,suna cikin zantawa sai ko ga A'isha ta yi
sallama domin gaida Abbanta, bayan ta gaisheni ne ya ce "yauwa ƙawar Ummanta dama ina
son in kira ki domin inyi miki nasiha duk da cewa tun da bikin nan ya matso muna tayi miki,na
farko dai nasihar da zan miki ita ce, zaman aure ya banbanta da zamanki na gida,don nan
iyakaci kici abinci ki ƙwanta da dai sauransu. Yanzun kam da zaran an ɗaura aure Akwai wasu
haƙƙoƙi guda goma da suka hau kanki na mijinki.
Na farko shine ki yi masa biyayya duk abinda ya ce kiyi,ki yi masa, matsawar bai saɓawa addini
ba, kamar yanda ki ka sani babu biyayya ga abokin halitta don saɓawa mahalicci.
Kima zama mai tsafta kamar yanda ki ka ga Ummanki tana yi, tsafta bata jiki kurum ba har da
muhallinki.
In kuma ya kira ki zuwa shinfiɗarshi kada ki bijire.
Ta dubi Abba da sauri kamar tana neman ƙarin bayani, domin A'isha yarinya ce sannan ba wai
suna zama da ƙawayanta suna hirar samari ko ta aure ba ne,haka nan bata da wata ƙawa
wadda ta yi aure ballantana ma taji labarin zaman auran, kazalika ita ba ma'abociyar
karance-karance ba ce, ita ana ta zaton in an mata aure zata na girki tana kai ma mijin ruwan
wanka tasa mishi na buta kamar yanda ta gani Ummanta tana yi, sai ko gyaran ɗakin Abbanta
da Umman bata bari wani ya yi sai ita.
Abba ya katse mata tunani da cewa, ma'ana in ya neme ki kada ki guje shi, Umma ta ce,nima
na miki duk nasihar da ta dace,na sani ke dama mai biyayya ce,ki girmama ƴan'uwansa,ki ɗauki
mahaifiyarsa tamkar taki, haka mahaifinshi, matarsa ki yi mata biyayya."
Hawaye suna zuba daga idanunta, ta ce insha Allah zan yi Abba da Umma, suka sa mata
albarka tare da yafe mata,ta miƙe ta fita suka bita da kallo cikin tausayin ta yayin da ita kuma ta
wuce cikin tsananin damuwa.
Ƴan ɗaurin aure sun hallara in da aka ɗaura aure. Maroƙiya ta shigo tana rangaɗa guɗa, A'isha
dai-dai lokacin tana wanka wanda Umma Rabi ta matsa mata ta yi umma Rabi ƙawar Ummanta
ce,tun suna dutse tana fitowa ta ji gidan ya kaure da guɗa, duk sai taji wata fargaba a cikin
zuciyarta. Inna Uwani Ƙanwar Umma, ita ta ciro mata wani leshi baƙi mai ado, ruwan lemon zaki
tasa ka,sun bata siket da bes da kuma pant duk baƙaƙe.
Aunty Hasiya mata ƙanin Abba ta ce ni ban ga ma rigar nono ba cikin kayan? Umma ta ce ba a
saka ba, Umma Rabi ta ce to me za'a sakama ƙirjin ba komai, ita dai A'isha tana jin su,
Ummanta ta ce kin ji saka kayanki ki tafi nan duk iyayan banza ne suka taru. Ta gama shirinta ta
fita, bayan an ɗan natsa da gama ɗaurin aure sai kuma aka shiga shirin tafiya Katsina,kai
amarya. Duk wanda ya cancanta ya yi wa amarya nasiha ya yi mata,dangin Uwa da na Uba.
Idanu ta zuba ma Ummanta a zuciyarta tana raya cewa, ta yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe.
Haka nan aka fita da ita tana ta rusa kuka.
Abbanta da sauran mutane suna waje gurin mota suna ta ce waɗanda zasu je Katsinan,don
kowa yana son zuwa, kuma tafiya ta gari ba kusa ba,don haka suka ce dole ne wasu su haƙura
ba kowa da kowane zasu je ba, an fito da ita tana cin kuka ganin Abbanta sai kuma ta ƙwace ta
nufi gurinshi.
Ya riƙe mata hannu yana cewa haba menene haka kuma? Ganin yanda take rusa kuka har ma
wasu daga cikin dangi suma sun soma taya ta, sai Abban ya kama hannunta ya ce,zo muje,
ɗakinshi suka je ya zaunar da ita ya shiga lallashinta da cewa menene na damuwa bayan ta yi
musu biyayya sannan ya san Friend ɗin shi zai kula da ita, zatayi karatun ta duka biyun, kuma
suma da an ƙwana biyu za su zo shi da Ummanta. Ya miƙe ya ɗauko alƙur'ani izifi sittin da fiƙihu
da Tauhidi ya ce ki riƙe wannan kin ji A'isha?" Ta share hawayenta tasa hannu biyu ta amsa tare
da cewa , to Abba da gaske za kuzo? Ya ce in Allah ya so, tashi muje ga mutane can sun shiga
mota ke dama ake jira. Allah ya yi miki albarka zan kira ki in kun isa,ta ce to. Abba da kanshi ya
kai ta har mota inda ta zauna tsakiyar Inna Uwani da kuma Aunty Rabi matar ƙanin Abba. Suka
nufi Katsina bayan ta yiwa gidan su kallon ƙarshe, tare da duban Abbanta da Yaya
Abdulrahman Munnir da kuma Jafar.
Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki akan farashin
masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan kuna bukata
zaku turo kudin ku ta wannan account numberí ½í±‡í ¼í¿»*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu matsala
ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin
shirya sai kiyi magana*
[12/4, 20:23] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³— Page 12*
Can katsina kuwa, gidan Alhaji Saddiƙ yana cike da danginshi, na gefen Hajiya Jummai da
kuma ƙawayanta. Amma shaƙiƙan ƴan'uwanshi irin su Fatima, gidansu Hajiyarmu suke yin bikin
su. Kuma a nan suka yi girkin saukar amarya domin suna isowa direbobin zasu kira su a waya
kamar yanda suka shedawa direbobin.
Gefen Hajiya Jummai kuwa tana ɗaki tsakiyar aminanta suna ta tofin Ala tsine ga Alhaji Saddiƙ
ɗin da ƴan'uwanshi da kuma amarya da danginta. Tuni suka sa ma amaryar suni mai ƙararran
ƙwana.
Yamma ta yi sanda motar amarya ta iso, tunda suka shigo Katsina direbobin suka yi waya suka
sanar da su Hajiyarmu. Nan take su Fatima Anty Sadiya su Nafisa da sauran dangi suka ciko
mota da kuloli ɗauke da nau'ikan abinci kalolin abin sha, suka nufo gidan Brother ɗinsu. Suna
shigowa kallo ya koma kan su nan dai aka je aka tsegun tama Hajiya Jummai ita da ƙawayenta
suka fito falon suka shiga yada habaici, domin tsarin gidan ƙaton mahaukacin falo ne mai ɗauke
da ɗakuna huɗu, falon ya shiryu da kalolin kujeru na alfarma gefe-gefe.
Kusan seti uku ban da (dinning), ɗakin Hajiya Jummai sai na su Suby sai ko na A'isha, yanzun
ɗayan na baƙi ne, sai hanyar da zaka bi don zuwa gefen shi yanda ya shirya kujerun falon yana
nufin kamar kowace mace da nata, domin kalar kujerunki kalar labulanki