Showing 1 words to 3000 words out of 36238 words

Chapter 1 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi

09 Jul 2025

1234

____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO Book 2📗*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*page 1*



A hankali ta maida ƙofar ta rufe, sannan ta juyo da nufin ta ƙaraso cikin ɗakin. Idanu ta zare tare da dafa
ƙirji, sannan ta ce "innalillahi" lokaci guda ta juya baya ta runtse idanu,duk ta yi haka ne sakamakon ganin
Uncle ya fito daga wanka daga shi sai gajeren wando,yana goge jikinshi da tawul. Ta kama ƙofar zata
buÉ—e, ya ce "Beby" ta ce "Umm." Ta ce "bari....em....bari na dawo in ka gama ban san kana ciki ba ne,don
Allah ka yi haƙuri." Ya ce "Me ki kayi min? Ki zo kiyi aikinki,kin ji ko" ta juyo amma ƙasa take kallo tana
tafiya ta ci karo da gado, da sauri ta É—ago idanunta ta sauke su akan gadon, cikin mamaki ta tsaya kallon
gadon sam bai kai nata girma ba, kuma shinfiÉ—e yake da zanin gado an lailaye shi,ta É—ago kai ta kalli Uncle
tayi sauri ta kuma sunkuyar da kai don ganin har yanzun bai saka riga ba, kuma bai damu ba sai shafa
manshi yake yi. Cikin in ina ta ce "An....an ma riga an gyara ashe?" Ya dube ta,duk ta daburce. Ya É—auki
riga shirt fara mai gajeren hannu ya saka,ya tako zuwa gurinta.

Ya kamo hannunta ya zaunar da ita yana riƙe da yatsunta cikin nashi kanta yana kallon ƙasa har yanzu
bazata iya kallonshi ba saboda gajeren wandon bai rufe cinyoyinshi ba sannan duk cibiyoyinshi gashi ne,
ya É—an murza mata yatsun "Beby bai haramta ki ga tsiraici na ba,ko ni in ga naki ba" ta dube shi da sauri
ya ce "Yes saboda ni da ke halalin juna muke" Ta sauke kanta ƙasa amma zuciyarta tana son ya fayyace
mata komai don ita bata gane nufin shi ba,ya ce "yanzu dai Beby ni wanene a gurinki? Ma'ana menene
matsayi na?" Ta dube shi sannan ta kuma sunkuyar da kai,a hankali ta ce "Miji" ya ce "me ake nufi da
Miji? Ta yi shiru zuwa can ta ce "Wanda ya yi aure shi ne Miji" Uncle ya yi É—an murmushi don jin
shirmenta, ya ce to menene aure?" Ta ce "Aure?" Ya ce "Umh" ta ce kamar dai yanda ake yi mutane su
taru a É—aura shi kenan sai kuma a kai matar" ya ce "to daga nan fa?" Ta É—an dube shi sannan ta rufe
fuska, ya ce "Gaya min idan an kaita sai tayi me a gidan? Ta ce "zata rinka yin shara da wanke-wanke
tanayin girki,ta rinƙa kula da yara.

Ya shafa hannunshi yana cewa, "Good, ashe kin sani? Ta yaya akeyi ta samu yaran?" Ta ce "Iye!' Ya ce "Ya
ya za'ayi ta samu yaran?" Ta ce, "Ita ce zata haife su." Ya ce, "Haka nan zata haife su?" Ta ce "Eh,in cikinta
ya yi girma." Ya gyara zama don jin sun gangaro inda yake son ji, ya ce "To ya ya akeyi ciki ya fito mata?"
Ta ɗan yi jim,can ta ce, "Nima ban sani ba,ƙila wani abinci ake ci." Dariya ta kufce mishi, duk cikin matan
da ya aura babu wadda ba ta san kan zaman aure ba kamar A'isha, duk da cewa akwai sa'arta cikin su, ya
dube ta.
"Kina son ki san yadda ake a yi ciki?"

Kanta yana ƙasa ta ce, "Eh" ya yi ɗan murmushi ya ce, "In na tambaye ki abu ɗaya yanzun ba ki san shi
ba, idan baki san shi ba,zan haÉ—a su in miki bayani. Amma in kin san shi to zan bar ki har ki sani da
kanki,wato zai zama assignment,amma fa ba zaki tambayi kowa ba,kin yarda?" Ta ce"To ya ya za'ayi na
sani in ban tambayi kowa ba?" Ya ce "Zaki sani,yau da gobe." Ta ce "To yi tambayar in ji". Ya ce "Kin san
Haila? Da sauri ta saka kanta cikin cinyoyinta,don ya taɓo mata abinda ta fi jin kunya a rayuwarta,don in
tana Haila ko Ummanta tana jin kunyar ta sanar da ita, sai dai ta yi ta nuƙu-nuƙu har Umman ta gano da
kanta, ballantana Uncle wanda bata daÉ—e da saninshi ba,ba su yi sabon da zata yi mishi wannan maganar
ba. Cikin dariya ya ce, gaya min mana Beby,kin taɓa yi ne? Miƙewa ta yi har tana cin karo ta fita da gudu.

Ɗaki ta koma ta faɗa kan gado zuciyarta tana ta bugawa, ita dai tana matuƙar jin kunyar Uncle,shi bai
sani ba ne zai mata wannan tambayar?.

Shiko dariya ya dinga yi,lallai dole ya haƙura da A'isha yanzu don ba ya son takura mata. Ya fi son a yi
komai cikin sauƙi kuma cikin ilimi.

Jummai kuwa tana ɗaki cikin murna haka nan wani gefe sai ta ji ranta ya ɓaci, da tana da iko ko macen
ƙuda ba zata yarda ta saukar mata a kan miji ba, balle mutum, shi yasa ta sha alwashin ko zata tafi tsirara
ne sai ta halaka duk macen da ta ce zata zauna zaman aure da mijinta. Ta sani goben nan yarinyar nan ta
zama gawa,don haka ita ranta kar yake, insha Allahu. Ƙwana ta yi tana kai-kawo cikin ɗakinta,don ba zata
iya runtsawa ba.

A'isha tana zaune tana tasbihi , sai kurum taga an turo mata ƙofa da ƙarfi. Cikin tsananin firgita ta miƙe
tsaye, ganin Hajiya Jummai tuni ta soma karato addu'a cikin zuciyarta. Hajiya Jummai ta yi sororo ganin

A'isha tsaye. Ta ce, A'a, ihun wa nike ji? Sai na ji kamar kakari a nan É—akin." A'isha ta ce, "Kai,anya nan
ne?" Ta É—an yi tsaki tare da cewa, "Gaskiya ba nan ba ne." Hajiya Jummai ta shiga waige-waige, zuciyarta
tana mai tabbatar mata ihun A'isha ta ji, amma abin al'ajabi A'ishar ce gabanta tana mai tabbatar mata
cewa ba a ɗakin ba ne. A'isha ta ce "Allah ba nan bane Hajiya." Sannan ta ɗan rusuna ta ce, "ina ƙwana
Hajiya?" Tsaki mai ƙarfi taja sannan ta fita a fusace, tare da sakin ƙofar da ƙarfi. Aisha ta yi shiru,a ranta
tana son sanin me hakan ya ke nufi? Daga baya sai kurum ta taɓe bakinta gami da ɗaga kafaɗarta alamar
su dai suka sani,ta koma ta zauna tana nazarin hirarsu da Uncle ta jiya. Daga bisani ta miƙe ta nufi kitchen
ba don Uncle ba ne ya yi mata wannan tambayar game da Haila da zata ce É—an iska ne,Don dai ta san
halin Uncle shi ba ya iskanci. Uche ta samu yana aikinshi, suka gaisa sannan itama ta shiga haÉ—awa Uncle
abin karyawa. Uche yana É—an taya ta,É—akinta ta nufa da tiren, tana shiga ta same shi zaune bakin gado
cikin shirin fita. Ta dubi agogo,taƙwas saura ƙwata, ta ce Uncle har ka fito?" Ta dire tiren a gabanshi ta
shiga haɗa mishi tea. Ta miƙa mishi sannan ta soma zuba mishi dankali da kwai tana saka mishi bota jikin
bread,ya ce har fa na manta ina karyawa a gida,bari na sakko ƙasa Beby" ta miƙe ta ɗauko dardumar
sallah ta shimfiÉ—a mishi, ya zauna ya shiga karyawa, sannan ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa cike da jin
daÉ—i, sannan ya ce "Ya gajiyar gudu jiya daga tambaya Beby sai ki ka gudu ko?"

Cikin cinyarta ta saka kanta,ta ƙi ɗagowa me zai sa Uncle ya dinga irin wannan maganar? Ai wannan
kamar na ƴan iska ne. Ita fa ko a school ba ta wannan hirar da ƙawayanta,nata ganin bai dace ba.

Ya ce "shin wai Beby menene abin jin kunya? Ta ce "Uncle don Allah ni dai ka daina wannan zancan." Ya
ce "na daina Beby, shikenan?" Ta É—aga kai alamun "Eh" ya ce "To oya ci abincin ki." Ta ce, Uncle nifa sai
anjima zan karya, wannan duk naka ne" Ya ce,ya ya zanyi da wannan Beby? Ai babu tsari ga kowane
musulmi ya zauna ya yi mugun ci, Manzon Allah (S.A.W) yana kasa cikinsa kashi uku ne, É—aya abinci, É—aya
ruwa, da kuma ya shaƙi numfashi dashi,don haka kin ga tunda da shi muke koyi, sai mu ma mu ƙwatanta.
Zaka ci ka ƙoshi amma ta yanda ba zaka kasa tashi ba.
Aisha ta ce, "Haka ne." Sai kusan tara ya fito daga É—akin,yana son yarinyar ta shiga ranshi,ba ya gajiya da
zama da ita yana son shirmenta,wani sa'in ta yi magana tamkar babba, wani sa'in kuma ta yi masa aikin
ƙuruciya,waton shirme.

Kai tsaye É—akin Jummai ya nufa,don yi mata sallama kamar yanda ya saba,in ba ya É—akin ki zai zo ya yi
miki sallama da safe in zai fita. Tana zaune abin duniya duk ya taru ya yi mata yawa, yanzun haka jin ta
take yi tamkar ta yi hauka,don tsabar baƙin ciki. Ina ma kuka zai ƙwace mata ko zata samu sassauci.
Sallamar maigidan ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, tsayawa ya yi yana kallonta. Itama ta É—ago idanunta
jajir tana dubanshi, ya ajiye jakar hannunshi ya nufi gurinta ya tsugunna a gabanta cikin sassanyar
muryarshi, ya ce "Jummai" ya kamo hannunta, "wai shin Jummai me yake damunki ne cikin watannin nan

duk kin rame kin lalace,dube ki don Allah sai ka ce wata tsohuwa?" Kalmar da tafi tsana kenan a kira ta
da ita, wato tsohuwa. Hawayen da take ta so su zubo ko zata samu sauƙi suka ƙi zubowa, sai gasu yanzun
sun zubo masu zafi ma,ta ce dole ne ka ce min tsohuwa tunda yanzun ka samu yarinya ƙarama wadda
zata iya haihuwa,ba irina ba juya. Ya miƙe tsaye cike da jin haushi, "kinga matsalarki ko? Kin gani ko? Me
yasa ne ke har kullum ba ƙya fahimta? Nifa ina son sanin matsalarki ne ba wai ina kushe ki ba ne,in baki
son in san damuwarki Jummai ai sai in barki tunda ke ba ƙaramar yarinya ba ce. Ace kullum bawa ba zai
sakawa zuciyarshi salama ba,koda yaushe sai baƙin rai. In kina da matsala ne ba sai ki faɗa min ba? Ta ce
"Ni dai don Allah je ka kawai,ka bar ni inji da kaina." Ya ɗauki jakarshi tare da cewa, "Allah ya ƙyauta." Ya
fita.

Ihu ta saka ita kaÉ—ai,a ruÉ—e su Suwaiba suka shigo suna cewa, "Lafiya Anty Jummai?" Tana huci ta ce "ku
bar ni zanci uban yarinyar can" Sofy ta ce, "Me tayi miki ne Anty? Yanzu mu je muci ubanta? Ta ce a'a ku
bari ba yanzun ba,ni zan yi maganinta. (Waya ga sa kai a uku) Yinin ranar Jummai sun ƙule ita da
Aminiyarta, suna neman mafita. Ta rantse ta kuma rantsewa cewa maigidan yana kusantar yarinyar gashi
an ce zata mutu shiru bata mutu ba,ta dubi Kari,ko dai zan sa mata guba ne? Kari ta ce "a'a komawa
zamu yi gurinsu." Ta ce dibi asarar da na yi ta kuÉ—i, amma ace maganin bai ci ba? Kari ta ce,mu koma
musu kawai gobe ke in abin ma ya ƙi wallahi sai mu nufi Nijar,zan binciko miki wani malami ko ince Boka.

Sun bar zancan a kan zasu koma in basu ga dai-dai ba,su nufi jamhuriyar Nijar, Allah ka tsare mu,Amin.

A'isha ko sam bata ma san hidimar da suke yi ba. Ranar ƙuƙewa ta yi tana ta ƙoƙarin yiwa Uncle ɗinta
gurasa da miyar taushe. Ta haɗa zoɓonta mai daɗi, Uche ne ya taimaka mata ,Marka mai aiki taje ta
sanar da Hajiya Jummai ta same ta suna magana da Karima,don haka ta sanar da su Suby cewa, amarya
ta samu sake, tana can kitchen ta girka banza da wofi. Nan ko suka nufi kitchen É—in suka shiga buÉ—e mata
kuloli, suna cewa, me wannan ƙwamacalar wannan ƙazamiyar ƴar ƙauyen ta ke yi ne haka?" Aisha ko da
kallo ta bisu, Sofy ta ce, ashe ma abincinsu ne irin na ƴan ƙauye. Suby ta ce,ke gaja wa kikayi wa wannan
ƙwaɗon? Ita dai kallonsu take yi ranta yana zafi,ta ce ina ruwanku da kayana? Duk suka haɗa baki gurin
cewa,sai mu zubar dashi,dube ta Æ´ar matsiyata kawai, A'isha ta É—auki kulolin ta ta nufi É—akinta ta dawo ta
ƙwashe sauran kayan,su kam sai dariya suke yi mata,suna cewa in dai Alhaji ki kayi ma wannan ƙazantar
ba ci zai yi ba Æ´ar neman gindin zama,zaki gane kuranki. Tagumi ta zuba tana zubar da hawaye,tuni ta
kula waÉ—annan za su takura mata.

Yau tun huÉ—u Uncle ya dawo, domin tunda ya kira A'isha sau uku bata É—auka ba,ya soma tunanin ko dai
bata da lafiya ne? Ita ko sam bata ma san inda ta jefa wayar ba, kuma damuwar da take ciki bata tuna
mata cewa tana da waya ba, domin dawowarta a jiya ne ma ta É—auki wayar. Amma ba sa zuwa makaranta
da waya. Lokacin da ya shigo tana wanka,zama ya yi yaga fitowarta, da ɗaurin ƙirji ta rufa da tawul ta ɗan

yi yaƙe tare da kallon agogo tana faɗin, har ka dawo? Shi ko ita yake kallo yana son gano halin da take
ciki,jin bai yi magana ba ne yasa ta maida kallonta gareshi ya ce "Beby me yake damunki?" Ta zauna bakin
gado cikin irin murmushin takaicin nan,ta ce ba komai. Ya dawo kusa da ita wani guri yana miki ciwo ko?
Ta ce "a'a,me ka gani ne Uncle?" Ya ce, "Sau uku ina kiran wayarki ba ki É—aga ba, sannan yanzun na zo sai
na same ki ba yanda ki ke ba.

A'isha baki kai lokacin da zaki haɗiye damuwa ba,sanar dani matsalar ki?" Ta girgiza kai "Yi haƙuri
Uncle,ka bar zancan,maganar waya kuwa ni na ma manta ina da waya saboda ka san zaman makaranta
yasa na saba da rashin waya." Ya ce, "Ni fa Allah sai kin sanar da ni." Ta ce, "to ni ban san me zan ce maka
ba." Ya ce, wani guri ne yake miki ciwo? Ta girgiza kai tare da cewa, a'a.



#######
[12/9, 07:33] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 2*



Ya ce, To mene ne? Hawayen da take maƙalewa suka soma zubowa,ta ce su Suwaiban nan ne, ya ce
Suwaiba? Ta É—aga kai "Me suka yi miki?" Ta ce, Ni dai kawai ka ce musu ba ruwansu da ni in ina abuna,
tunda dai ni bana shiga cikin harkarsu, ya ce to kiyi haƙuri zan musu magana." Ta share hawayenta, ta
miƙe ta kawo mishi ruwa mai sanyi,yana sha taa ce, "Yau fa na maka abinci,baza ka ci na Uche ba, Allah
yasa zaka iya ci?" Ya ce, "Me yasa ki ka ce haka? Ta ce, saboda ban ƙware ba,ni kuma gani da son yin
girki." Ya ce,zan ci koma ya ya ne,ai Beby kina da ƙoƙari, na san nan gaba zan huta da cin abincin masu
aiki ko?" Ta yi dariya, ya ce, sannan kada ki ce na dawo da hannun agogo baya,shin me ya haÉ—a ku dasu
Safiya? Ta ɗan ɓata rai ganina kawai suka yi ina girki cikin kitchen sai suka hau buɗe min suna zagina wai
ƴar ƙauye ina haɗa ƙwamacala,na samu sake.

Suna ta yi min,ni kuwa na fita dan sun ce zasu zubar min." Ya ce, "Ke da wanene cikin kitchen É—in?" Ta
ce,ni da Uche ne,yana taya ni, ya ce to kiyi haƙuri.

Koda ya fita É—akin Hajiya Jummai ya nufa,tasha adonta tamkar ba ita ce cikin damuwa ba É—azun,
shawarar Karima ta ɗauka wadda ta shawarce ta da cewa ta yi ƙoƙarin ɓoye sirrinta cikin ranta ta daina
bari ana gane damuwarta. Ya dube ta "Jummai ina yaran nan ne?" Ta ce, "Sannu da zuwa,ka dawo?" Ya
ce, "Eh" ta ce, "Su Suwaiba?" Ya ce "Eh," ta É—auki waya ta kira Safiya ta ce,su zo É—akinta yanzun. Koda
suka shigo, ganin Uncle sai suka yi tsimi-tsimi ya ce kece ki ka tura su su je suyi wa A'isha rashin mutuncin
nasu? Ta dube su,me ku ka je kukayi mata? Suby ce ta soma cewa,nima dai ban sani ba, Allah Anty sharri
ne. Sofy ma ta ce, to mu yaushe ma muka ganta ni na ma san ta dawo ne? Bai yi magana ba ya ciro wayar
shi ya kira Uche, ya ce ya same shi a É—akin Hajiya Jummai. Nan a gabansu ya tambaye shi cewa ya gaya
mishi gaskiya me ya faru tsakanin A'isha da su Suwaiba. Ya É—an soma inda-inda, Alhaji ya ce, daina
kallonsu,ni ne na É—auke ka aiki kuma ni ke biyanka don haka bana son kana kallonsu,in zakayi magana."
Nan dai Uche ya sanar da su duk yanda aka yi, duk da yana tsoron masifar su. Nan ko Alhaji ya soma
faÉ—a,ya ce maza su fita hanyar matarshi, domin kan A'isha kowaccensu zata iya kama hanyar gidansu,a
cewarshi don A'isha ba ta da gidan da yafi wannan, tunda nan ne gidan aurenta.

Hajiya Jummai ma dai ta daure ta ce musu su fita harkarta,ta yi musu faÉ—a a gabanshi, amma yana fita ta
ce,lallai yarinyar nan har ta samu guri ta soma kai ƙara? Tabɗi,lallai zata san da wa take yi. Su Suwaiba ma
sun sha alwashin cewa sai sun ƙuntata mata.

Ita ko bata san suna yi ba ma,don bai ce mata ƙala ba. Koda ya shigo rashewa ya yi a tsakar ɗaki nan kan
sallayarta ta shiga jera mishi kayan gabanshi,ya buɗe babbar kular tare da cewa, tunda kin ƙi gaya min
sunan abincin da ki kayi min bara na duba da kaina, ganin gurasa luhu-luhu ya sa shi sakin baki, sannan
ya dube ta cike da mamaki, "Allah ke ce ki kayi wannan gurasar Beby? Ta ce,ba tayi ƙyau ba ko? Cikin
fargaba take magana,ya ce ina dai mamakin iyawarki. Ya É—auki É—aya ya yaga,ya saka cikin bakinshi yana
taunawa, ya ce Beby kin yi zaman Kano ne? Tana dariya ta ce, Uncle abinda ya yi Kano ai shi ya yi
Jigawa,ya ce haka ne,ba zan ci gurasar nan ni kaÉ—ai ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0