Showing 12001 words to 15000 words out of 36238 words

Chapter 5 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi

09 Jul 2025

1236

ita
kaɗai ba, sai ya haɗa duk ajin ya biya, shi yasa A'isha Musty ta yi suna cikin makarantar ga ƙoƙari.

Lokacin da Momi taje musu da batun A'isha ba ta ji daɗi, sai hankalinsu ya tashi. Uncle ya ce, sosai ne?
Me ya same ta? Momy ta ce da ɗan sauki Abbanta ya ce kice ta ɗan lallaɓo Abbanta ne. Koda Momy ta
shaida mata saƙon da sauri ta tashi zaune tana cewa, su biyu ne? Momy ta ce eh.

A'isha ta zura hijabi suka tafi, Abbanta yana zaune shi ko Uncle yana tsaye ya kasa zama. Ta shigo da
sallama suka amsa, Uncle ya nufo gurinta yana cewa, Beby me ke faruwa da ke ne? Bata ko kalle shi ba ta
nufi Abba,tana cewa, Abbana yaushe ka zo? Ya ce, jiya na zo, yanzun nan kuwa ina kan hanya ne dama na
zo ɗaurin auren friend ne,ta ke ta canza fuska, tare da canza magana,ta ce Yaya Umma fa? Ya ce,da tare
zamu zo sai kuma su Jafar ba su ji daɗin jikinsu ba.

A ranta ta ce,lallai Umma, wato da auren Uncle za ta zo? Ta ɗan taɓa baki sannan ta rusuna ta gaishe su,
suka amsa. Uncle ya sake tambayarta,me ya same ta? Ta ce,mura ce,kuma ta samu sauƙi. Wayarshi ta yi
ringing,ya ɗan fita don amsawa. Ai nan take zuciyar A'isha ta yanke mata hukuncin cewa amaryar tashi ce
ta kira shi,don haka sai ranta ya kuma ɓaci. Abbanta ya kula,don haka ya ce, "A'isha ki fa ƙwantar da
hankalinki,ki kuma zauna lafiya da maigidan ki, kada kiyi kishi irin na jahilan mata, kiyi kishi irin na mata
Annabinmu Muhammad (S.A.W) na san kina da labarin yanda suka yi nasu kishin kin ji ko? Ta ce, to Abba.
Uncle ya dawo ciki, Abba ya miƙe yana cewa, to ni zan yi harama fa. Ya fita Uncle ya dube ta.

"Beby na miki laifi ko?" Ta girgiza kai,ni ban ce ba, ya ce, amma kin nuna beby,kin kuwa san halin da ki ka
bar ni a ciki ina kiranki ki kayi banza da ni? Ta dube shi, sannan ta sunkuyar da kai cikin zuciyarta ta ce,
kaima ka san kuwa halin da ka sani? Amma a fili sai ta ce to yi haƙuri," tausayinta ya ji ya ce "kiyi haƙuri
kema Beby ban san cewa abin zai ɓata miki ranki ba da ko da aka matsanta min auren nan da ban amince
ba. Ta kalli fuskarshi nata ganin yana mata daɗin baki ne don ya lallashe ta, amma sai ta ce saboda ni
zaka ƙi koyi da Manzon Rahama? Idanunshi suna kallon nata ya girgiza kai, sannan ya ce, "Shikenan na
gode, amma babu fara'a? Ta yi ajiyar zuciya tare da lumshe idanu,sai nan ta girgiza kai tare da cewa, kada
ka damu zaka samu wani lokaci,ya fito tana biye da shi, sai yana tuhumar kanshi ko dai ya cutar da ita ne?
Ita kuma zuciyarta ba zata iya dariya ba,don haka bata jin cewa zata iya yin wata fara'a, ta leƙa Abbanta a
mazaunin kusa da direba, ta ce "ka gaida su Umma da su Jafar, insha Allahu wannan hutun zan zo." Ya
ce,to shikenan sai mun gan ki ta kalli gefen Uncle ta ɗaga mishi ƴan yatsunta guda uku, alamar bye-bye.
Ɗan murmushi kurum ya yi sannan ya furta da leɓunanshi a hankali,wai ƴar rigima. Abba yana kallonsu
amma ya yi tamkar bai san suna yi ba. Uncle ya ja mota suka tafi. Cike da takaici ta juya yanzun waton
Abba, saboda shima ba wani sonta yake yi ba, yafi son Uncle shi ne har da zuwa don za ayi mata kishiya?
Ya sani Umma ba zata zo ba koda lafiyar Jafar ƙalau tunda ciwon ƴa mace na ƴa mace ne.

A'isha ke nan.

Hajiya Jummai kuwa duk da ƙoƙarin da tayi don ta danne amma hakan ya faskara, duk wanda ya kalle ta
ya san tana da matsala,wai don ma ƙawayanta sun sakata a tsakiya suna tausarta, mamakin ta shi ne
dama aƙwai rana da zata zo har ta kasa maganin kishiya da kuɗin ta da komai? Ashe lokaci yana zuwa da
zata zauna da kishiyoyi biyu? Su ƙwana su tashi a gadon mijinta? Lallai duniya mai juyi,ta yi tsubbun ta yi
tsafin,ta ci nasarori shin me yake shirin faruwa da ita ne? Waɗannan tunane-tunanen su ne suke sakata
yin jingum,suke hanata bacci, kuma su ke barazanar saukar mata da ciwon zuciya, domin ba ta shirya ma
zuwan wannan rana ba,sai dai tana da burin ɗaukar kowane irin mataki bari dai taro ya watse. Manyan
mata kenan.

Bayan shagali, Amarya ta tare a gidan ta,ko'ince a ɗakinta, wanda ke nan cikin falon gidan Alhaji Saddiƙ,
da ɗakin na baƙi ne amma yanzun an gyara ma baƙi wani, amarya ta ci gayunta ga tanadi kala-kala da aka
yi don birge ango,ta ɓangaren jiki an sha nasha an cusa na cusawa,ban da na su kalolin asiran wanda
Hajiya Lanti duniya ta shirya mata,wato mahaifiyarta Hajiya Lanti lashe money. Tun tara angon yana gida
amma ko a ranshi ba ya da ra'ayin zuwa gurin amaryar tashi.

Flashing ɗin da ta gallaɓe shi da shi ne ya saka shi kiran wayarta,yana tambaya ko lafiya? Ta ce,taga bata
ganshi ba ne ya ce mata shi tuni yana gida, sannan ya kashe ita ko bayan feshe jikinta da tayi da turaruka
sai ta nufi ɗakin angon cikin wata shegiyar rigar bacci.

Hajiya Jummai tana leƙenta ta window har ta shige,nan ta zube kan gado tana son koda kuka kai ko
hawaye ne ya ɗan fito ta samu rahama, amma abin ya faskara. Ita ko amarya ta samu ango yana shafa'i
da wuturi, komawa ta yi ta ɗauko hijabi, bayan ya idan sannan ya ce ta zo suyi sallah irin ta ma'aurata.
ango da amarya ranar an darji amarci, duk da da farko ya yi fargaban kada ta mutu,don yana ɗaya daga
cikin abinda ya hana shi kusantar A'isha kenan, har yanzun.

Cikin satinshi da zai yi a ɗakin amaryar,ya sha shagali, har ma yaji tamkar kada ya bar ɗakin nata. Hadiza
ko gaban waye tana nuna rashin kunyarta matsawar maigidan yana kusa da ita. Shi ko namiji dama ɗan
son a ririta shi ne, don haka sai yake jin shi tamkar yanzun ne ya yi auren fari. Duk yanda Hajiya Jummai
ta ɗauki abin da sauƙi, sai ta samu ya wuce da tunaninta,don haka sai ta kuma bazama neman wata sa'ar.

A'isha ko tana makaranta daran amarcin su Uncle,haka ta ƙwana raya halin da suke ciki a zuciyarta, wani
satin da ya zagayo, Uncle ya zo gurinta, ta isa gurinshi fuskarta a tsare cikin girmamawa, kamar ko yaushe
ta gaishe shi, ya amsa yana mai kallonta, ganinta ya yi ta rame mishi, ya ce Beby don Allah ki cire komai

cikin zuciyarki,a gurina har ya ban ga ƴar da ta shiga raina ba tamkar ki ba,ta dube shi da son ta fahimci
gaskiyar maganar shi,sai taga ya yi mata ƙyau fuskarshi har wani ƙyallin goshi yake yi, daga ka ganshi kaga
sabon ango. Zuciyarta ta yi wani iri,lallai Uncle yana shanawa, shi ne yanzun zai mata daɗin baki.

Ta sunkuyar da kai,ya ce "ina don zanyi tafiya jibi ranar Monday,zan je Phoenix,saboda wani kasuwanci da
zamu bunƙasa a can, ina zaton zan kai sati biyu ko in wuce."

Ta ce, Allah ya taimaka,ya kuma ba da sa'a, akan abinda aka je nema, ya ce na gode da addu'ar ki,shiru na
ɗan lokaci Hadiza ta kira shi da ya ɗaga wayar sai ya ce, ya ya ne? Cikin shagwaɓa ta ke cewa,my love
kana ina ne? Ya ce, ina makarantar su Beby ne, menene? Kishi ta ji ya cika zuciyarta, ballantana in ya ce
Beby,komai Beby ita ta ma ƙosa taga wai ya ya wannan Beby take ne? A'isha dai tana jin shi,ya ce, "kin yi
shiru na ce menene? Ta ce, missing ɗin ka nayi dama, ya ce "ok ina zuwa kin ji? A'isha tamkar ta miƙe
domin ta gane da amarya yake hira,ta dai daure. Yana gama wayar ta miƙe ta ce,sai ka dawo kenan,
lokacin yin kitsonmu ya yi. Ya riƙo hannunta irin sallamar da zamu yi kenan? Ji tayi tamkar ta fisge
hannunta,ya ci gaba.

Beby zan tafi, ina kewarki,zan so ace tare muka tafi."

Cikin gatse ta ce,"To ba ga amarya ba." Sai bai fahimci gatse ta yi mishi ba, ya ce,"kin amince in tafi da
ita?" Haushi ya kama A'isha, ta ce yardata ka ke nema? Ni kuma a wa?" Ya ce,ni fa duk abinda zai maido
min da walwalarki shi nake son yi,a zuciyarta ta ce,ka ce dai kana son abinda zai baƙanta min rai,ya ce kin
ji ni me zan miki ki huce? Ta ce,wai to ni ce maka aka yi ina fushi? Ya ce, amma ai da ba haka ki ke ba,ta
ce to yanayin rayuwa ne yazo da haka, don haka mu duka sai mu ɗauki haƙuri da juna. Ya saki hannunta
tare da cewa shikenan,ni zan wuce Beby sai na kira waya" Ta rakashi kamar yanda ta saba, suka yi sallama
a gun mota.

A'isha ta koma ciki, zuciyarta da damuwa. Nata ganin Uncle ya samu wadda ta fita yanzun zaya daina
damuwa da ita, shi ko ya tafi ne cike da kewarta tare da son ganin ta dawo tamkar da.

Ran da Jummai zata fita daga girki, Alhajin ya sanar da ita cewa,yana son tafiya da Hadiza tafiyar nan da
zai yi. Nan Hajiya Jummai ta shafa ma idanunta toka, ta shiga masifar cewa, ita bata yarda ba, don ya ga
komai ya ce tana shiru shine zai zalince ta,to ita fa bata amince da wannan zancan ba.

Shiru ya yi yana kallonta,ga mamakinta sai taga ya miƙe tare da cewa, tafiya da Hadiza babu fashi, saboda
matanshi uku ba zai tafi shi kaɗai ba,ta ce to dole sai da Hadiza? Ya ce,to gaya min da wadda zan tafi,
A'isha tana makaranta,ke kuma ina ne ba mu je da ke ba? In bazaki manta ba,lokacin da aka ɗaura mana
aure dake ko sati ɗaya ba muyi garin nan ba muka bazama duniya, wata shidda muna yawon amarci.
Cikin waɗannan wa ya samu haka? A'isha ko airport ta taɓa zuwa ne?"

Hajiya Jummai ta fito tana cewa,na barka da Allah. Da kallo ya bita, ita wannan watau rashin mutuncin da
take yi wa wasu shi ne ya soma zuwa kaina,ya yi ƙwafa,ko a jikinshi ya ɗauki amaryarshi suka nufi
Phoenix.

Harkokinshi suna tafiya yanda yake so gefe kuma ga amarya.

Hadiza irin matan nan ne masu fi'ilin tsiya da ƙwarƙwasa,gata da son komai ace ita ce gaba, sannan tana
da son ƙyale-ƙyale. A da Hadiza baƙa ce, amma yanzun fara ce tas,sai dai in ka kalli ƙafar zaka gane farin
na mai ne. Tana da ƙiba kuma bata da tsawo,ga tumbi. Gaskiya sun yi soyayya ko ince suna soyewa. Tana
matuƙar son Alhaji Saddiƙ.


#######
[12/12, 13:22] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 7*



Ta fi son ace daga ita sai shi bata son ganin kowace mace kusa da shi, shi yasa take jin haushin wannan
shegiyar Beby ɗin da bakin shi ke yawan kira, don ta kula yanda yake yawan cewa Beby ko Jummai ba ya
kira haka,tana burin maye gurbin Beby ɗin nan.

Tun saura ƙwana huɗu a yiwa su A'isha hutu, makarantar kamar yadda ta saba ta samo tura ma dukkan
iyayan ɗaliban nasu text cewa rana kaza ne za'ayi hutu, lokacin da saƙon ya isa ga wayar Uncle ba layin
ba ne cikin wayarshi, tunda baya ƙasar ma. Kan wayar da layin ke ciki ma bada ita ya tafi ba, don haka bai
samu saƙon ba, ballantana ya ce aje a ɗauke ta, ƙa'idar makarantar ba sa ba da ɗalibai sai dai in iyayansu

ne ko waɗanda suka ɗauki nauyinsu. Sam Uncle bai san taƙamaiman ranar hutun ba, don haka koda
ranar hutun ta zo A'isha ba taga anzo ɗaukarta ba,a ƙarshe bayan kowa ya watse nan shugaban
makarantar suka shiga neman shi a cikin waya. A'isha ta ce, musu ya yi tafiya baya ma ƙasar gaba ki ɗaya.
Don haka sai suka ba da ta gidan wata Malama da ke nan cikin makarantar.

Wannan lamarin ya ƙara sa A'isha yarda da cewa yanzun Uncle ya daina yi da ita, ya daina sonta inda da
ne ba yanda za'ayi ya share ta, yanzun ya samu wata wadda ta fita, sanadin wannan yasa A'isha zama
miskila.

Gidan Malama Salamatu, gida ne mai tsari da tarbiyyar Islama, tana da yara ƴan biyu sa'annin A'isha,
suna son Aisha sai dai ta kasa sakewa da su,ba ta cika magana ba, sai dai sun kula tana da yawan ibada.
Malama Salamatu ma ta yaba da A'isha.

Ranar da ta cika ƙwana biyu ne ya ga saƙon ta cikin Internet ɗin shi, lokacin yana zaune yana duba
saƙonni. Hadiza kuma an dage ana ta danƙara uwar ƙwalliya, faɗin innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un ɗin da
ya yi shi ne ya saka ta juyowa ta dubeshi,nan ya ɗauko wayarshi ya shiga neman layin Hajiya Jummai.
Hajiya Jummai ta ɗauka lokacin ma tana gidan Kari, ya ce Jummai an ɗauko beby daga makaranta ne? Ta
taɓa baki sannan ta ce, wacece haka? Cikin sauri ya ce "A'isha fa" ta ce,sallahu ka bari cewa a ɗauko ta?
Sannan ta kashe wayarta, ta tsani wannan A'isha ballantana in yana faɗin Beby ɗin nan, ta ce ɗan rainin
wayo, Kari ta ce,hala mutumin naki ne?" Ta ce shi ne mana,kin ji shi ne? A firgice wai an ɗauko A'isha
daga makaranta? Karima ta ce, na kula duk da ya yi auran nan hankalinshi ya fi tafiya ga wannan A'ishan.

Jummai ta ce, shi yasa na tsane ta, har na fi jin kishinta akan Hadiza, duk da nasan Hadiza da uwarta Lanti
ba ƙyalle ba ne? Kari ta ce"ai dole ne kifi jin kishin A'isha, tunda wanda ake kishin domin sa ya fi sonta,(ta
ci gaba da cewa) ko me ya gani jikinta? Yarinya ba ƙugu ba sharaɓa babu nonon kirki. Koda yake kin san
ƴan ƙauyan nan fa suna da mugayan malamai, sai a mallake miki miji a kan Naira ɗari ko ɗari biyu."

Tsaki Jummai ta ja,ai ba'a ƙwana a gado kullum, kuma nima na san ba don sun min asirin da duk abin da
nayi kada ya ci ba wane su, shi yasa yanzun nake son in an gama aikin nan, ba makamin nan ya ce zai
karya asirin da suka yi mini ba? Yana karyawa zan ɓalle tsiya nima duk in ga bayansu,don duk sai na kashe
su,ni kishiya in ba a lahira na aikata ba ko mai nayi mata ban huce ƙwanciyar da tayi na gadon mijina ta
ɗanɗani kalar soyayyarshi ba,ta sha min zumar da ba kowane namiji ne ya iya ba da ita ba". Kari ta yi
dariya, tare da cewa, shegiya mutuniyata,in na tuna baya,ba ki da ƙyau, amma tunda naga Alhajinki ya
riƙe ki daga wasu mazan na san ba ki da sauƙi. Jummai ta ce,ai wallahi duk mazan da aka yi harka a can
da ba su san komai ba,ke dai bari kawai." Suka tafa tare da sakin dariya.

Shi ko Uncle tsaye ya miƙe rike da waya yana jan tsaki layin Jabir ya nema, bayan ya ɗauka ya ce Jabiru
don Allah maza-maza gobe da asubahi ka nufi makarantar su Beby,sun yi hutu ba'a ɗauko ta ba." Jabir ya
ce,ko aje yanzun ne? Uncle ya ce a'a bana son tafiyar dare,kai dai don Allah kayi sammako. Sannan ya
kashe wayar, ya dubi Hadiza wadda ta cika ta yi dam sakamakon yanda yake kiran Beby, ta ce to ita bata
san hanya ba ne? Da bazata koma gida ba? Ya dube ta cike da haushin abinda Jummai ta mishi, sannan ya
ja tsaki ya fita, takaici ya rufe ta,lallai zata ɗauki mataki a kan A'isha.
Daran dai Alhaji Saddiƙ sun yi ƙwanan doya da manja ne, shi da amarya.

Washegari Jabir yana idar da sallar Asubahi ya ɗauki hanyar makarantar su A'isha. Maigadin ya yi wa
bayani tare kuma da neman taimakonshi,kan cewa gurin wa zai je yanzu? Maigadin ya ce "Gaskiya gara
ka koma in dai ba sunanka aka saka ba kan cewa,kaine zaka ringa zuwa ɗaukar ta ba,don ba zasu ba ka
ba, lokacin da Jabiru ya kira maigidanshi ya shaida mishi yanda suka yi da maigadi,shiru ya yi lokacin yana
shirin zuwa mitin ne ya ce, "Jabiru ka koma gida nima zan taho yau insha Allahu,in na ɗaukota na dawo."
Furucin ya firgita Hadiza saboda ɗauko ta daga makaranta za su koma gida? Ta hura hanci gami da girgiza
kai, dole ma tasan me wannan yarinyar take taƙama dashi.

Ƙarfe taƙwas na dare suka sako ƙafa cikin gidan,ban da wayar shi da yake son ɗauka da ke cikin gidan,da
baza ya shiga gidan ba,ko ta kan Hadiza be bi ba ya barta da ƴan aiki suna ta ya ta ɗiban kaya,ya yi cikin
gidan,kai tsaye ɗakinshi ya nufa,ya ɗauko wayar da number ɗin (P.C) ɗin su A'isha ke ciki matsalar babu
caji. Batir ɗin ta,ta hannunshi ya cire ya saka sim ɗin ya fito ya leƙa gurin Jummai kamar yanda ya zata
bata nan sai su Suby ya nufi waje. Yana fita su Hadiza na shigowa, ya ce mata sai ya dawo bata amsa shi
ba dama bai jira amsar ta ba ya tafi abinshi.
Jabir ke jan motar har suka iso, ya kira (P.C) a waya in da ya tabbatar mishi cewa tana nan gidan wata
Malama nan cikin makarantar yanzun zai yiwa Malamar waya,ya ƙara da cewa ba ya gari ne da yazo,
amma su shiga Malamar zata fito, har ƙofar gidan Malama Salamatu wani malami ya kai su, sannan ya yi
musu sallama a gidan lokacin A'isha har sun ƙwanta batayi bacci ba amma ta yi shiru cikin tunanin Uncle
da abinda ya yi mata,sai taji ƙwanƙwasa ƙofa gami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0