Showing 18001 words to 21000 words out of 36238 words
Chapter 7 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi
ta tuna jiya duk ya kalle mata jiki, musamman ƙirjinta da take jin
kunyar ko a riga taga mutum na kallon mata su, shi kam farin ciki ya farka da shi tamkar ya biya
buƙatarshi da ita. Tana gama abinda zatayi ta ce tana son zuwa gidan su Anty Nafisa, ya saka Jabiru ya zo
ya kaita mana? Sai cewa ya yi ni zan kai ki Bebyna, tana wanka ta dinga kallon guraren da Uncle ya yi ta
mata wasanni da su, ta yi murmushi in tana tuna yanda taga Uncle ya fita cikin hayyacinshi sai taji wani
alfahari, ashe itama mace ce.
Riga da siket ne a jikinta na pink ɗin atamfa ƴar Holand,ta ɗora baƙar after dress mai shara-shara, ta saka
baƙin takalmi, fuskarta tasha fenti. Ta kalli madubi cikin zuciyarta ta ce, wasa-wasa fa nima nayi. Ina da
ɗan kyauna dai dai gwargwado. Ta saka turare mai sauƙin ƙamshi, saboda ta san tare da Uncle zasu fita,
kuma gidan Nafisa zata je da ba za ta saka turare ba, saboda bin umarnin da Manzonmu ya yi mana kan
cewar bai halatta ba ga mace ta saka turare in zata fita. A wata ruwayar ma an ce in har ta saka to in ta
dawo tayi wankan janaba.
A'isha ta fito tana kulle ɗakinta a ƙasa kuwa kusa da ita,jakarta ce baƙa da kuma ledarta mai ɗauke da
kayan da zata kai ɗinki, Uncle ya fito ya yi ƙyau cikin suit baƙaƙe tamkar matashin saurayi,daga ɗakin
Hajiya Jummai ya fito ya kalleta da murmushi,ta sunkuyar da kai shi Uncle ba ya irin kunya ne? Ta raya a
zuciyarta,ya shiga gurin Hadiza ya ce mata,ya tafi. Tana ƙwance kan gadonta ko kallonshi batayi ba, ita
dole tana fushi an ci amanarta, shi kam bai saurari amsarta ba,ya fita abinshi.
A'isha ta duƙa ta ɗauki jakarta, ya iso shi kuma ya ɗauki ledar tayi saurin dubanshi gami da zaro idanu,ya
ce muje,ta ce to kawo ledar. Ya ce zan riƙe miki ne ta girgiza kai,don Allah kawo na riƙe Uncle ba
girmanka ba ne. Ya matso kusa da ita saitin kunnanta ya raɗa mata inji wa ya ce ba girmana ba ne? Ko ke
kanki ba sai in ɗau abina ba,ta ce haba dai? Ya ce to bari ki gani,ya kai hannu ta ja baya tare da cewa,ana
fa kallonka,ya ce na san su Suwaiba a gurin sai naƙi wasa da Bebyna? Ta ce to muje, suka jera yana riƙe
da ledar, suna fitowa nan ma'aikatan tun daga kan mai ba fulawa ruwa zuwa direbobin sun zo don su
amshi ledar amma duk ya hana su, sai dai jakarshi ta Ofis ce ya ba Jabiru.
A'isha ko hakan ya yi matuƙar bata mamaki, shi da kan shi ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan shi kuma
ya koma can gefen inda Jabiru ya buɗe mishi,yana zama cikin hannunshi ya saka nata. Yanayin susar da
yake mata a hannu ya sa tajin kasala, har ma bata san lokacin da idanunta suke lumshewa ba,sai da suka
hau titi sannan ya ce, "Jabir mu fara zuwa gidan Nafisa mu sauke Beby,ya ce to maigida. Hannu yasa ya
kwanto da ita kafaɗarshi,a hankali ya raɗa mata cewa, jikinki yana da laushi Beby, ina son ƙamshinki, ɗan
murmushi ta yi tun jiya yake faɗin wannan kalmar.
Wayarshi ce ta shiga ruri,ya ciro ta daga aljihun suit ɗinshi, ya kalli fuskar wayar ya shafa kumatunta tare
da cewa, Abbanki. Da sauri ta ɗago daga kafaɗarshi tare da cewa, don Allah? Bai bata amsa ba sai dai
taga ya ɗaga wayar yana cewa, "Assalamu alaikum, Friend an tashi lafiya? Bayan sun gaisa ne yake shaida
mishi cewa dama batun bikine zai sanar da su na yarinyar ƙanwar Umma da za'ayi ranar juma'a mai zuwa
ɗin nan,in sun samu zuwa to,in ma basu zo ba ba matsala.
########
[12/13, 17:32] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³—í ½í³— Pages 9*
Aisha duk tana jin su, bata san sanda ta dafa bayan Uncle ɗin ba,tana faɗin "Ɗan bani don Allah Uncle ba
ni Abban." Tana magana tana girgiza shi, cikin yanayin irin na shagwaɓaɓɓu, ya ce to gama Beby ɗin,da
zumuɗi ta amsa,ta ce Abbana ina ƙwana? Bayan sun gaisa ta ce, bikin Naja ko na Sauda? Ya ce na Naja ne
za'ayi ranar juma'a,cike da zumuɗi ta ce zan zo insha Allahu, Abba ya ce a'a in mijinki ya ce a'a ba komai
dama dai don ku sani ne,ta ce dama zan zo hutu,ya ce to sai kunzo bawa maigidan naki,ta ce to ka gaida
min su Umma." Ta miƙa ma Uncle,suka koma kuma kan batun kasuwancinsu, daga bisani kuma suka yi
sallama kan cewa sai sun zo. Suna isowa gidan Nafisa, suka shiga harabar gidan suka sauke ta,ta ce
"Uncle ba zaka shiga ba?" Ya ce, nayi latti, idan na dawo ɗaukanki zan shiga, ta ce to. Ya miƙo mata ledar,
tare da cewa,sai na dawo,ta ce to ka dawo lafiya,ta nufi hanyar da take zaton nan ne ƙofar falon. Shi kam
zamanshi ya gyara tare da yin ajiyar zuciya,sakin fuskar Beby a yau ya samu ƙwanciyar hankali.
Ta ƙwankasa ƙofar ana ukun ne Nafisa ta iso,ta leƙo sannan ta buɗe cike da zumuɗi,tana cewa Bebyn
bros ce? A'isha ta shiga tana cewa,amare, Nafisa ta amshi ledar tana cewa, kawo in taimake ki. A'isha ta
ringa juyi cikin ƙaton falon mai shegen tsari tana cewa, wow Anty Nafisa falonki ya tsaru,gaskiya
maigidanki ya iya zaɓen guri.
Nafisa ta ce, maigidana ko maigidanki? Ai da gidan da abin da ke ciki har shirya gidan duk Uncle ɗinki ne.
A'isha ta sake kallon falon "kai gaskiya Uncle ya San tasta, mutumin nan ya haɗu da yawa fa, shiyasa
kome ya zaɓa zaka ganshi ya haɗu. Nafisa ta zuba mata idanu tana dariya cikin mamaki ta ce, A'isha
yaushe ki kayi baki haka? Wasa mijinki ki ke yi, ta ce Allah Anty Nafisa kinsan gaskiya na faɗa, domin
Uncle ko kaya ya saka sai kiga tamkar don shi aka ƙera su. Nafisa ta riƙe haɓa tana cewa, lallai A'isha kin
shigo gari yarinyar,ta ja hannunta,to zo mu shiga cikin ɗaki. A ɗakin ma haka A'isha ta yi ta santin gadon
da sauran kayan tare kuma da koɗa Uncle ɗin nata,ta zube kan gado tana kallon Nafisa tana cewa "Anty
Nafisa ga shi kema kin yi ƙyau, Nafisa ta zauna tare da dafa A'isha wai yaushe ki ka zama haka ne? A'isha
tana dariya ta ce,me nayi wai? Sannan suka gaisa ta ce, ina Bros? Aisha ta ce, tare muke, ya yi latti ne
shiyasa ya wuce, amma in ya dawo za ya shigo. Ya ya maigidanki?" Nafisa ta ce, yanzun za ki ganshi yau
yana gidan uwargida ne.
A'isha ta taɓa baki gami da cewa, don ma ku biyu ne, da ace kamar mu ne daga can gidan sai ya wuce
wani gidan,don ma Allah yasa gida ɗaya muke. To yanzun kuma ke kaɗai kike kuma Anty Nafisa? Ta ce
"eh mana, sai dai ƴan aiki na" Nafisa ta dafa A'isha tare da cewa,sai kurum ki kaji auren Uncle ɗinki?
A'isha ta gyara zama tare da cewa,hum ai na ji mamakin auren Uncle,in kin ji takaicin da nayi sai da na kai
zuciyata nesa, sannan fa na iya zana jarabawa.
Nafisa ta miƙe,bari inje in kawo miki abinci, A'isha ta riƙe ta,ban daɗe da karyawa ba,bari sai anjima. Nan
fa zan yini sai naci abinda nake so " Nafisa ta zauna tana cewa, "ai dukkanmu babu wanda ya so auren
bros,ke shi kanshi ma fa ba wai yana son auren ba ne, don dai babu yanda zai yi ne."
A'isha ta ce,ni barni. Yana sonta har fita ya yi da ita waje."
Nafisa ta ce,"Amma dai kin san yafi son ki ko gaban waye yana faɗa." A'isha ta ce, "Gaskiya ni ban
gaskata ba." Nafisa ta ce, "saboda me?" Aisha ta ce don yana musu abinda ba ya min." Nafisa ta gyara
zama "me kenan? A'isha ta taɓa baki, duk garin nan Anty Nafisa ke kaɗai ce nake gaya miki matsalolina,ni
ko ba wai na matsu ba ne,kuma ba jaraba ba ce,hasali ma matsayina na budurwa kuma yarinya na san
bai dace in yi wannan zancan ba. Amma zan gaya miki ne ba wai don ki faɗa ma Uncle ba,sai don ki yarda
cewa Uncle yafi son matanshi fiye da ni,kin san cewa Uncle bai taɓa taɓa ni ba?."
Nafisa ta zaro idanu,"kai haba?" A'isha ta ce wallahi, amma amaryarshi har da fita ƙasar waje da ita."
Nafisa ta ce,wai har yanzun? A'isha ta ce, Allah kuwa,ba wasa nake ba, da yana cewa ban isa ba, yanzun
fa? A'isha ta ce God forbid,ai sai ya zata na matsu ne, Nafisa ta ce amma ai addini bai hana ba, kuma in
da baki damu ba yanzun ai kin kai ki damu ɗin, tunda ba dutse bace ke, A'isha ta ce koda zamu tabbata a
haka ba zan taɓa ce mishi ƙala ba, tayi ƴar dariya tare da cewa kuma shikenan sai ince Uncle me yasa
baka ƙwana da ni? Suka yi dariya tare, A'isha ta ce Allah ko ke ce Anty Nafisa na san ba zaki ce ba. Nafisa
ta ce bazan ce ba, amma zancan zan maka fuska. A'isha ta ce, "Ni fa ban damu ba,ni da ina makaranta
ma,in ya saba min naje makaranta na damu fa? Haka dai suke ta hira har suka zo kan batun su Hadiza nan
Nafisa ta shiga ba A'isha labarin wacece Hadiza,ta ce daga Hadiza har Jummai sun auri Bros ne, saboda
kuɗi,kuma dukkansu babu wadda bata buga duniya ba. Kuma shi Bros da Hajiyarmu sun ƙi yarda cewa
Jummai tana da hannu a cikin mutuwar kishiyoyinta, A'isha ta ce nima haka kawai sai inji zuciyata tana
zarginta musamman da wannan ƙawar tata Hajiya Kari.
Nafisa ta ce, kamar kin sani ke dage da yin addu'a, amma batunki da Bros zamu ga yanda zamu yi yanzun
dai ki barshi ya gama amarcin da Hadiza, yanda in ya juya kanki zai san kuna da banbanci. Haka ta yini
suna hira suka shiga kitchen.
Biyu dai-dai mijinta, Alhaji Bello ya shigo. Nan A'isha ta saki baki tana kallon yanda Nafisa ta ruga da gudu
ta rungume mijinta,ta ma manta da wata A'isha a gidan, sai da ya tafi sannan Nafisa ta samu natsuwa.
A'isha ta ce tabɗi,Anty Nafisa kina sha'aninki, ina ma zan iya na dinga yiwa Uncle ɗina haka? Ta ce kin ko
san da kin ƙara haskawa cikin zuciyarshi. Hadiza zata iya shi yasa ki kaga tana ɗan jan hankalinshi. A'isha
ta yi ɗan tagumi ta tsurawa mirrow ido tana tunanin shin zata iya? Ta dubi Nafisa ta yi ɗan tsaki ina jin
nauyin Uncle shi ne matsalar amma ina son in burge shi. Nafisa ta ringa yi mata dariya.
Biyar dai-dai Uncle ya kira Nafisa,wai ga shi a ƙofar falonta, suka fito suka buɗe mishi ya shiga. Nafisa ta
yi kicin, A'isha kuwa kamar yanda ta saba, ruwa ta kawo mishi ya amsa yana kallon fuskarta, sannan ya ce
A'isha Allah ya shayar da ke ruwan Alkausara, yanda ki ke gusar min da ƙishina, shiyasa ko bana ƙasar nan
duk lokacin da naji ƙishi,sai kin zo raina kuma sai na miki addu'a. Daɗi ta ji sosai sannan ta ce, "Allah yasa
in sha tare da kai Uncle." Ya ce, "Amin Bebyna."
Nafisa ta iso da abinci,ya ce wa zai ci? Tayi turus kai mana Bros ya ce ni kam sai kuma nan da tara na
dare. Na riga na ci na rana. Yanzun Beby ta fito mu wuce gida. Bayan sun fito, Nafisa ta ce to telan fa bai
san measurement ɗin ki ba, A'isha ta ce,zan aika da kayana sai ya yi min girman su, masu ƙyau inji Uncle.
Nafisa ta ce kada kaji komai Bros, bayan sun shiga mota ta miƙo ma A'isha tsarabar da ta bata, tare da ki
fa yi amfani da shi yanda na miki bayani, A'isha ta ce to na gode,sai mun yi waya.
Bayan Jabir ya ɗauki hanya ne sannan Uncle ke cewa, tsarabar me ki ka samo Beby? Ya kai hannu gurin
ledar, kawo in gani. Ta yi saurin ɓoye ledar ba fa wani abu ba ne,ya yi ɗan murmushi tare da cewa, "Mata
ba ku rabuwa da tarkace."
Tun fitar su A'isha, Suwaiba da safiya suka shiga gurin Jummai,suna bata labarin abinda A'isha da
maigidan sukayi har ma da ƙarin gishiri,wai ya rataya jakarta. Jummai ta ce jaka fa ku ka ce? Suka ce jaka
mana, kuma ta ratayawa ko kunya da girmanshi da komai,tsaki ta ja ni ku daina gaya min tunda ku baku
da fus cikin gidan,ba ƙwa taimakaman da komai. Safiya ta ce in mun yunƙura zamu daki banza sai ki ce
a'a," ta ce Allah wadaran halinku tunda ba ku da wata dabara sai ta duka,ku fitar min daga ɗaki, ance
muku yanzu ana ya yin duka ne? Sai dai na ƙarƙashin ƙasa. Suwaiba ta ce to ba sai ki nuna mana yanda
zamuyi ba? Ta ce,ai yanzun duk zamanku tare da ni ba ku ɗauki wani darasi ba? Allah wadaran zamanku
tare dani, ta miƙe ta nufi toilet tana masifa,shegu kun iya yawon bin ƙana nan yara suna rarake ku, amma
baku iya sanin yanda za ku zauna da mutane ba, yanda za ku ƙuntata ma yarinya, ya gagare ku.
Ranar dai haka ta yini cikin ƙuncin zuciya, gefen Hadiza yau kam a cike da A'isha ta yini ga takaicin
jiya,nata ganin ya danne mata haƙƙinta, sannan yau ba girkin A'isha ba, amma ya fita da ita don itama
tana kallonsu ta window ɗinta, nata ganin ya fi son Aisha. Ƙaramar yarinya tana juya shi son ranta,don
haka koda lokacin ƙwanciya ya yi,ya yi sallama da sauran matan nashi ya shige ɗakinshi ba tare da ya
shiga gurin Hadiza ba,don ta san ita ce dashi,ƙin zuwa ta yi, dole tana fushi, shima bai neme ta ba, kuma
ko washegari bai leƙa inda take ba,hakan ya ƙona zuciyarta.
Ranar Alhamis suka sauka Jigawa,niƙi-niƙi da tsaraba,ga kuma gudunmawa. Aisha ta tattala dubu biyar
ɗinta zata bada, sai kuma ta ji Umma da Abba suna mata godiya,wai Uncle ɗin ta ya bada dubu hamsin,
talatin nata, ishirin na shi. Tun ranar A'isha suka wuce Gumel, ita da Umma,su Abba sai gobe in sun zo
ɗaurin aure. Inna Rabi ta ji daɗi sosai da wannan gudunmawa,nan A'isha ta zama tauraruwa gidan bikin
kowa sai birge shi ta ke yi.
Washegari ana gama ɗaurin aure Uncle ya yi mata waya cewa ta leƙo suyi sallama shi zai wuce, lokacin
suna cikin gidan maƙota, tare da su Naja da ƙawayanta. Nan ta fito ta same shi cikin mota,ta shiga ta
zauna ya rufe. Sannan ya ce Beby ƙwana nawa za kiyi? Ta ce, duk sanda ka ce Uncle zan shirya in jira ka.
Ya ce, to zamu yi waya? Ta ɗaga kai alamar eh,ya sa tafukan hannunshi biyu ya ɗago fuskarta. Kallo ɗaya
ta mishi ta lumshe idanunta,tana jin nauyinshi. Cak numfashinta ya tsaya lokacin da taji saukar
leɓunanshi kan nata leɓunan ƙamshin turaranshi ne ya doki hancinta.
A hankali ta buɗe idanunta,na shi idanun a lumshe ƙyakƙawar fuskarshi irin ta fulanin Katsina KT cike da
annuri. Ba zato shima ya buɗe nashi idanun zata rufe nata, da idanu ya yi mata alamar kada ta rufe. Suka
zuba ma juna ido, Kasa jurewa ya yi ya jawo ta zuwa jikinshi, sannan ta yi ajiyar zuciya tare da runtse
idanunta sakamakon jinta cikin wani yanayi, muryarshi a sarƙe ya ce Beby yaushe zan zo in tafi da ke
zanyi kewarki da yawa. Ta ja numfashi muryarta ƙasa-ƙasa ta ce,nace duk randa ka zo. Ya ɗagota tare da
cewa shi kenan sai nazo kanta yana ƙasa don kunya ta ce, to . Ya ɗauki kuɗi daga gaban motar ya ce
gashi,ta dube shi ka fa bani kuɗi jiya, ya ce ki ƙara Bebyna, sai mun yi waya? Ta ce,eh ya kuma kama tafin
hannunta ya sumbaci tsakiya,tsigar jikinta ta yi yar,ta kalleshi, sannan ta fita daga motar. Ta koma ciki
bayan ta ɗaga mishi hannu alamun bye-bye.
Kano ya ƙwana,sannan washegari ya nufo K.T lokacin da ya shigo gidan tsit, wannan lamarin yana taɓa
zuciyarshi, kullum ya shigo gida tamkar ya shigo maƙabarta. Ya buɗe ɗakinshi ya shige kan kujera ya
zube, sannan ya jingina da bayan kujerar,kai wannan abu yana damun ƙwanyar shi, duk gidan abokanshi
in sun shiga,ya kan ji hayaniya sa'an nan ƴaƴan su kan shigo suna oyoyo, saɓanin gidanshi kullum shiru
mata biyu a ciki amma ko T.V da wuya, ya shigo ya taras an kunna kowace tana ɗaki tana ƙwance, ya ja
tsaki shi yasa in A'isha tana makaranta ko son tuno gida ba ya yi,ita kaɗai ce wadda in ya kalleta ya ke jin
annuri.
Ta tare shi da ruwa mai sanyi ko zoɓon nan nata mai daɗi, ya kai hannu kan leɓunanshi yana son tuno
yanda ya ji lokacin da leɓunanshi suka mannu da nata,ya sauke ajiyar zuciya, sannan yasa hannu cikin
aljihu ya ciro wayarshi. Layin A'isha ya nemo lokacin tana shafa mai,ta fito wanka, tana cikin ɗakin inna
Rabi, cikin uwar ɗakanta, da sauri ta ɗaga wayar.
Ta ce, "Assalamu alaikum! Uncle ina ta neman layinka network ya ƙi shiga, ya yi ɗan murmushi gani na
sauka gida yanzun nan, ta ce ina ka ƙwana? Ya ce Kano mana,ta ce ka sauka lafiya?" Lafiya lau Bebyna,ki
kula min da kanki. Tayi murmushi,nima haka. Ya ce ke ma me?" Ta ce, yanda ka ce,ya yi ƴar dariya, zanyi
yanda ki ka ce,kafin ki dawo ki cigaba da kula dani...
#######
[12/14, 07:15] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³—í ½í³— Page 10*
Ta ce na manta kana da wasu masu kula da kai ɗin har su biyu, ya ce "ai Beby yanda kowa ke kula dani
daban, sannan in muna tare da ke ki ringa ji a zuciyarki ba