Showing 6001 words to 9000 words out of 36238 words
Chapter 3 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi
Saddiƙ ya iso gida yamma ta yi kis,don ma basu tsattsaya a hanya ba,
rashin samun Jummai a gidan ya yi mugun ɓata mishi rai,shi dai wannan ɗabi'a me yaƙi da addini,da
matan zamanin suka ɗauka tana ɓata mishi rai, ace mace ba zata nemi iznin miji ba,in zata fita saboda
rashin sanin hukuncin musulunci,ko a waya ba zata kira ta nemi izini ba,ya samu su Suwaiba sun cika
gidan da kiɗa tare da ƙawayansu,sun sha wanduna suna ta rawa ga ƙwalaban totolyn emzolyn nan zube
a ƙasa, ranshi ya ƙara ɓaci ya shiga ya tarwatsa su tare da yi musu tatas. Ya ce, ina Jumman da ta ɗaure
muku gindi? Cikin maye Sofy ta ce,ta yi tafiya tun jiya, al'ajabi ya cika shi,ya nufi ɗakinshi ranshi yana
matuƙar zafi. Ya zauna bakin gado ya soma kiran layin ta, ga mamakin shi tama ƙi tafiya,a ƙarshe ma sai
aka ce a kashe layin yake.
Wasa-wasa har wayewar garin ba ta babu labarin ta, kazalika ci gaba da neman layinta ko zai samu,shiru
kai daga baya sai ya soma tunanin ko dai ta ɗan fita unguwa ne, ta samu matsala ko mota ta kaɗe ta
haka? Yin wannan tunanin ya saka shi kiran danginsu, har da nata wato makusantanta,yana sanar dasu
rashin ganinta tun jiya. Ya san ba nisa tayi ba,don ba ta fita da mota ba, kuma bata saba tafiyar ƙwana ba
ma in dai ba ƙasar ta bari ba, komai dangatakar ku da ita ba zata taɓa zuwa ta ƙwana don zumunci
ba,nata ganin ƙasƙanci ne ta ƙwana gidan da suka fi su kuɗi, amma gata can ai ta ƙwana a bukka,nan fa
hankula suka tashi.aka shiga neman asibitoci,ranar basu iso ba sai daf da magriba,kai tsaye gida kowacce
ta nufa, lokacin da ta iso gidan yana cike da dangi shi kuma yana daga harabar gidan in da wani ɗan
sandan ciki yake neman ƙarin bayani daga bakinshi.
Sai kurum gata ta shigo, ganin maigidan yasa ta ji faɗuwar gaba,don sam ba tayi zaton zai riga ta dawowa
ba, amma da yake tana zaton yau ya dawo,tun da haka suka yi dashi, sai ta isa gurinshi tana cewa "Sannu
da zuwa Alhaji, har ka iso? Na ɗan fita ne" bai iya ce mata komai ba, sai dai ya dubi wannan (C.I.D) ɗin ya
ce shi kenan ma gata nan ta dawo.
Suka yi sallama ya tafi, shi ko ƙin shiga ma gidan ya yi,yana tsaye cike da mamakin baƙin halayen da
Jummai ta zo mishi da su yanzun yi,abin har ya kai ta da yin ƙwanaki. To ina taje? Ya na nan har aka kira
sallah, ya shige masallaci, ita ko tana shiga cikin gidan ta same shi cike da dangi ana ta jaje. Turus ta ja ta
tsaya, tana son sanin wanene ya mutu? Shin ko dai A'isha ce har ta mutu kafin ma ta dawo? Ta yi amfani
da maganin? Kai in ko haka ne lallai zata sake komawa ta mishi sabon biya,don ya cancanta,haba shiyasa
taga Alhaji a waje babu fara'a,ya ma kasa amsa ta,ta dubi jama'a sannan ta ce, "Haɗarin mota ne?" Nan
kuma sai taji sun ɗauki salati, suna tambayarta a ina abin ya faru? Sai kuma ta yi sororo tare da cewa,wai
dama me ya tara su haka? Nan suka shaida mata labarin ɓatanta,nan fa ta hau masifar cewa inji uban
wa? Ita da taje biki? Shi ne za'a ce wani ta ɓata? Wata Yarsu ta ce, to mu dai maigidan ki ne ya yi waya
tun jiya kuma sai nemanki ake yi cigiya gidajen radiyo da na talabijin. Ta ja tsaki, "To ni biki naje, shima
bayanan ne kuma na kira shi a waya ban samu ba." Nan dai kowa ya tashi yana Allah to ya kiyaye gaba,
gaskiya ta ji haushi don duk tasa ma ranta cewa A'isha ce ta mutu.
Sai bayan da kowa ya tafi sannan ta kira su Suwaiba,tana tambayarsu yaushe ne Alhaji ya dawo? Suka
shaida mata tun jiya, kuma ya tambaye su sun ce ta yi tafiya. Cikin ɗar-ɗar ta zauna,shi kam bai ma shigo
gidan ba da ya yi isha'i gidansu Hajiyarmu ya nufa, don ya sanar da su dawowar Jumman,nan har yake
yiwa Hajiyarmu complain ɗin halayen da Jummai ta shigo da su, ya ce ada bai san ta da duk waɗannan
halayen ba, sai yanzun.
Hajiyarmu kuwa haƙuri ta bashi tare da cewa, zatayi mata magana. Sai sha ɗaya saura sannan ya nufo
gida,tana ta gadin zuwan shi,don haka tana kallon shigowarshi, sanda ta shiga ɗakinshi yana watsa
ruwa,ta zauna. Yana fitowa da ya ganta fuska ya ɗaure tamkar bai taɓa dariya ba,ta rasa ta ina zata soma
mishi magana,can dai ta daure ta ce, "Alhaji ka min haƙuri,na san ban ƙyauta ba, amma wallahi na kira
wayarka taƙi shiga,dama wata ƙawata ce dake Kaduna ta ke aurar da ƴarta," ya ce "to yanzun sai ki koma
Kadunan," ta zaro idanu, Haba don Allah,ka yi haƙuri Alhaji, nayi laifi, ya eh da haka ni ne dama sarkin
haƙuri shiyasa sai ki min abu ki ce inyi haƙuri to na gaji ba zan ɗauki yawon gantali ba, don haka sai ki
koma".
Tayi saurin zubewa gwiwa biyu a ƙasa,don Allah ka rufa min asiri, insha Allahu ba zan ƙara ba,don Allah.
Ya ce ,don Allah ni tashi ki bar min ɗaki,shashasha wadda ba ta san darajar kanta ba,bare na aurenta,ke
kenan yi nan yi nan,gara ma kin canza hali,don wallahi ba zan ɗauki wannan rainin wayon ba. Ta fita dai
tana mai jin zafin abinda ya yi mata, amma cikin ranta tana cewa,ƙwanan nan zaka zama zauna nan in
Allah ya yarda,duk wannan cin mutuncin da ya yi mata sai ta rama.
Shi ko ƙwanciyarshi ya yi tare da yi mata addu'ar Allah ya shirye ta, ita ko A'isha tana can gurin Ummanta,
suna shan hira, tana ba Umma labarin yanda Uncle ya ke kashe mata kuɗi,ko da Ummanta ta ce, to suna
zaman lafiya da abokiyar zaman tata? Cewa ta yi suna yi har ma take bata labarin zannuwan da ta ba da a
kai mata, Umman ta fahimci ƴarta bata zuwa gurin mijinta a cikin hirar tasu, inda take cewa, ita sau ɗaya
ta taɓa zuwa ɗakin Uncle ya ce ta gyara mishi shimfiɗa, sai kuma taga shimfiɗar a gyare.
Umma ta ce,ai yanzun ke don rashin hankali ba zaki shiga ɗakin mijinki ba duk ranar girkin ki ki gyara safe
da yamma?" A'isha ta yi shiru, Umma sai faɗa take mata, ta ce "Lallai yarinya in ko haka za kiyi,za kuwa ki
zama koma baya gurin mijinki,ai wannan gyaran ɗakin shi ne zai sa yaji dake fiye da yanda ki ke labari
yanzun, duk irin biyayyar da zaki mishi na banza ne in har ba zaki gyara mishi shimfiɗa ba."
######
[12/10, 19:21] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³—í ½í³— Page 4*
Aisha ta ce , to Umma shi ne fa ya ce wai ba zan iya ba,wai sai nan gaba. Shiru Umma ta yi don ta san
A'isha yarinya ce, amma har da ma shirmenta,in ban da haka yara ma ƙanana waɗanda ba su kai ta ba
sun san aure bare kuma ita? Sam ta kula A'ishar ma bata gane me take nufi da gyaran shimfiɗa ba.
Aisha ta ce, to in na koma ai zan ringa yin gyaran.
Kafin ranar dawowarta, Umma ta zaunar da ita ta koya mata shan kayan marmari masu saka ni'ima a jikin
mace,duk da yanda Umma ta nuna mata cewa su kankana,shan rake,aya,ayi kununta da dabino shan
romon kaza da sauransu,suna saka mace tayi ni'ima. A'isha ba ta gane wacce irin ni'ima Umma ke nufi
ba,ga nata zaton jikinta zai yi fresh ko ƙiba zatayi ko ko fari, Umma take nufin zata ƙara? Oho. Ita dai tana
can ta soma amfani da su, sai wasu tsumi da dai sauran abubuwan sha na mata, waɗanda basu da illa.
Itama nata gefen Hajiya Jummai ta gama aiwatar da komai nata,wato guzurin Nijar, don haka jiran
sakamako kawai take yi.
Ana saura sati ɗaya hutun A'isha ya ƙare, Uncle ya yi mata waya cewa yana nan bisa hanya,don haka ta
soma shiri da ya zo zasu juya. Tamkar kada ta tafi ta ji, sai dai wata damuwa tun jiya ta soma jin wata
faɗuwar gaba har ta sanar da Umma. Umma ta ce, tayi ta addu'a itama zata taya ta.
Sun tsaya a Kano sun yi siyayya, Uncle dai sai tuni yake mata da Amrif Cory, dariya ta ringa mishi, shi kam
ya ce na yaba da ƙamshinsa gami da ɗanɗanonsa, duk tsarabar da A'isha ta zo da ita gurin Jummai ta kai
ta ce gashi nan ta raba ta ba kowa.
Hajiya Jummai ta ce, a'a bani da wanda zan ba tsaraba,ki dai aikawa da su Hajiyarmu,ni kuma bari in ɗan
samu riɗin.
A'isha ta ce, to da kanta ta ce don Allah Uncle ya kaita ta ba su Hajiyarmu tsarabar su. Sun yi godiya mai
tarin yawa, a nanne ma take jin zancan auren Nafisa, lokacin da Uncle suke magana da Hajiyarmu, ashe
wani abokin Uncle zata aura, mai suna Alhaji Bello,yana da mata ɗaya da ƴaƴa uku,fatan A'isha Allah yasa
lokacin bikin suna hutu, har ma tayi wa Uncle ƙorafin hakan, Uncle ya ce kada ta damu,in tana da rabon
za'ayi tana nan to za'ayi cikin hutun. Lahadi tana zagayo wa Uncle ya haɗa komai na makarantar A'isha ya
maida ita. Sun maida hankali kan karatunsu yanda ya kamata.
Jummai kuwa, kullum cikin zuba idanu take yi taga ta ina aikinta zai fara? Amma shiru. Nan fa hankalinta
ya sake tashi, ta shiga surutu ita wane laifi ta yi? Duk abinda ta yi ba ya ci,da yake an ce duk abinda ka ke
yi shi kake zaton kowa yana yi,don haka sai ta bar abin kan cewa suna tufka mata asirine, shi yasa. Yin
wannan hasashen yasa ta garzaya gidan Aminiyarta don neman wata mafitar.
Aisha ta zamar mata annoba, bala'i. Aminiyarta ta ce,sake neman wani gurin zamu yi da zai yiwu ni dai da
mun dangana da Indiya, can ne ƙarshen tsafi ba ki gani ko cikin fina-finansu? Jummai ta ce,don Allah
kuma gaske ne yana yi?" Karima ta ce ,"Zauna nan,ai in zaki miƙe,miƙe sahibata wani aikin sai Indiya,ko
Chaina, kafin ma mu dawo tun muna can za'a ɗauki ran banza mu huta."
Jummai ta ce,ba zuwan ba,ba kuma kuɗin nake ji ba,don sai na iya sa duk wani abu nawa a kasuwa in
amshi kuɗin,matsalata mutumin gidana, kin san cewa har zuwa yau ba mu koma normal da shi ba? Tun
zuwanmu Nijar ɗin nan har yau,na kasa gane kanshi. Sai ya yi ta dakemin yana shan ƙamshi.
Karima ta ce, "ke Aminiyata nemi kuɗi in ma bai barki ba ni sai in je miki. Menene amfanin Amintakar? In
ana zuwa lantsandan gaban lahira inji ƴan magana to zani,in samo miki mafita game da kishiya. Ai ki
daina damuwa,mu za'a gaya wa Boka? Jummai ta yi ajiyar zuciya, daɗi ya rufe ta,a duniya bata da tamkar
Karima, ta ce, "Aminiyata Allah ya ja mana ƙwana,ni na san bani da masoyiyar da ta kai ki duk duniya."
Ji toshewar basira.
In sun samu hutu.
A'isha duk ranar girkinta,ta kan shiga ɗakin Uncle ɗin ta gyara mishi gado har ma da sauran gurare,
sannan ta saka mishi turaren wuta mai ƙamshi, amma bata kwana tunaninta ma bai kawo mata ta ƙwana
ɗin ba, har ƙwanakinta na hutu suka cika ya yi mata komai ta koma.
A'isha ta maida hankali kan karatunta, bata wasa sai dai zama da su Samira ya yi matuƙar wayar mata da
kai. Su kan zauna suyi hirar samarinsu kamar yanda ƴan mata kan yi. Amina kam kullum bakinta yana ba
su labarin Kabir,Samira ma bata da zance sai na Adam.
Kowacce in tana labarta yanda take ji game da abin ƙaunar nata, A'isha kam baki take saki ta yi ta
kallonsu. Samira ta ce, A'isha wai ke kullum tamkar ba ki waye ba, haka ki ke jin kike wai baki da saurayi
ne? A'isha ta girgiza kai tare da cewa,ni bani da wani saurayi.
Amina ta ce,ni wallahi ban da ina da Adam ɗina ko da sai na ce don Allah ki haɗa ni da Uncle ɗinki mana?
Samira ta ce,ai gayen ya yi ne, A'isha ta yi ɗan murmushi, sannan ta ce,shi Uncle ba fa yaro bane. Samira
ta ce ji wannan ai ba yarinta ake kallo ba a maza,ƙwalitis ake dubawa, shi Uncle ɗin ki yana da duk
ƙwalitis ɗin da ake so ga namiji."
Aisha ta ce,ni ban san wani ƙwalitis ba fa da kuke magana" Dariya suka shiga yi mata, A'isha ta ce,kun ji
lokacin sallah ya kusa, ya kamata mu soma shirin shiga Masallaci."
Duk lokacin da suke ire-iren wannan hirar, A'isha kan tambayi kanta, menene wannan ɗin da su Samira
suka damu kan su dashi? Ita dai ta san burgewa kamar Uncle in ya yi ƙwalliya,yana matuƙar birgeta,
bayan wannan ba ta san komai ba.
Ƙwanci tashi su A'isha an shiga (SS3) duk da batayi wata ƙiba ba, amma ta ƙara tsawo.
Ƙirjinta kuma ya bunƙasa har yana ɗan rinjayarta, shi ne ma sanadin yin ɗan rusunawarta wanda wasu
ƴan makarantar nasu suka fassara shi da yanga, zuwa yanzun ta san mene ne aure,me ake yi in anyi shi?
Sai dai ita mai tsananin tsoro ce.
Shi kuwa Uncle har yanzun ba ya tunanin taɓa ta, domin yanzun ya gama yarda cewa ƙwanciyar da yake
yi ne da ƴaƴan jama'a suke mutuwa, duk da yana tsakanin buƙatar hakan, saboda yanzun Hajiya
Jummai,damuwarta ma tai yawa,don ta ce an sa mata hannu na asirin da tayi bayi ci,tana nan dai tana
fafutukar haɗa kuɗin zuwa Indiya ko Chaina.
Aisha wadda yanzun shekarun ta sha baƙwai kenan ta samu shekara biyu gidan Uncle ɗinta.
Ganin haka ya sanya jama'a suke ta kai-kawo kan cewa Alhaji Saddiƙ dai yanzun mata sun daina mutuwa
a gidanshi, sai dai haihuwa shiru,don haka mutanen da a baya suke zaginshi sai kuma suka shiga kawo
mishi tallar ƴaƴansu.
Nuna musu yake yi ba shi da ra'ayin sake aure,don haka su yi haƙuri.
Yau bayan tashinsa daga Office,gidan Hajiyarmu ya nufa, ya samu Alhaji Sunusi wan mahaifinshi,amma
ƴaƴa maza suke. Alhajinmu yana jin maganar Alhaji Sanusi sosai, domin yanzu ku san shi kaɗai ne ya rage
mishi a maza, cikin dangi. Alhaji Saddiƙ ya zauna suka gaisa,ya juya ya gaida Hajiyarmu, Alhaji Sunusi ya
ce wannan zuwan naka ne fa Abubakar, Uncle ya dube shi tare da gyara zama sannan ya ce, to ina jin ka
Baba. Alhaji Sunusi ya yi gyaran murya sannan ya ce, maganar Hadiza ce ta kawo ni, Uncle ya dube shi
wace Hadiza fa? Alhaji Sunusi ya ce,ai ba ka ma san ta ba? To Hadiza ta gidana, tun lokutan baya na sani
kaima ka sani tsayawa ta yi tsayin daka kan cewa kai take so, amma a lokacin kowa yaƙi saboda kai ba a
son ra'ayinka ba,to sakamakon haka har izuwa yanzun taƙi kowa ta ce ita dai sai kai, gashi an tashi bikin
ƙannanta su Hussaina shi ne muka yanke shawarar aura maka ita kawai.
Uncle ya dubi gefen da Hajiyarmu take zaune,tana ta nazarin littafin ƙawa'idi, ya sani tana jin su sai dai ba
zata taɓa magana ba. Sannan duk ƙwaƙwarka ba zaka iya gane me ke fuskarta ba, ma'ana zancan ya yi
mata daɗi ko ko akasin hakan, sannan ya dawo da dubansa ga Alhaji Sunusi wanda ya san yanzun nan
zasu hau sama su faɗo in dai ya bashi amsar da ke bakinsa, ya ce Alhaji ai ko lokutan baya na san anƙi in
auri Hadiza ne saboda matsalar da ke tare dani, ta mutuwar matana, yanzun kuma an yarda ne saboda
an ga nayi aure matar bata mutu ba,don haka ni dai a bawa Hadiza haƙuri, ta nemi mijinta kawai."
Alhaji Sunusi ya ce, inji wa ya ce maka don wannan matsalar ne? Mu dai burinmu mu ga ƴaƴanka."
Alhaji Saddiƙ ya ce, "Gaskiya ba ni da ra'ayin mace fiye da biyu, kuyi haƙuri."
Ran Alhaji Sunusi ya soma ɓaci, don haka cikin fusata ya ce, "Abubakar ba wai na zo neman izininka ba
ne, umarni na zo baka domin ko mahaifinka ne na bashi umarni baya tsallakewa,in ma mahaifiyarka ce
zata zuga ka to ku sani daga kai har ita aure babu fashi."
Uncle ya ce, "Allah ya huci zuciyarka,ba ruwan Hajiyarmu cikin wannan zancan, Hajiya da ke jin su ta rufe
littafin hannunta, sannan ta dubi wan mijin nata ta ce, Yaya Allah yasa alkhairi, kuma yasa muna da rai
za'ayi." Jin haka yasa gaban Alhaji Saddiƙ ya faɗi, ya sani zancan ya tabbata tunda Hajiyarmu ta amince,
Alhaji Sunusi ya miƙe yana cewa, "Duk yanda muka yi zaku ji gurin Alhajin gidan nan." Ya tafi.
Shiru Alhaji Saddiƙ ya yi,yana kallon ƙasa,shi da yake tunanin lokaci ya kusa da zai daidaita tsakanin shi
da A'isha,don yin zaman aure cikakke, sannan sai kuma a kawo mishi batun wani auran? Shi fa ya sani ya
so ya auri Hadiza a lokacin yana cikin tsananin son haihuwa, amma yanzun sam babu Hadiza a ranshi, duk
da ko can da ɗin ma ba itace ta ƙi shi ba, dangin mahaifinshi ne suka ƙi, musamman Hajiya Lanti da Alhaji
Sunusi mahaifanta yanzun kuwa ya sani ganin daɗewar A'isha a gidanshi ne yasa su amincewa.
Hajiyarmu ta katse shi da cewa,ka ci gaba da addu'a,zamu taya ka. Ka zama mai biyayya sannan ka shiga
shirin bikin,to kurum ita ce kalmar da ta fito bakinshi, ya miƙe tare da cewa,ni zan ƙarasa gida. Duk ƴan
ƙwanakin yana cikin damuwa.
A'isha tana school, Hajiya Jummai kuwa damuwarta ta sha ƙarfin tashi,don haka ita bata ma kula da me
yake ciki ba, ganin haka yasa yau ya shiga har