Showing 30001 words to 33000 words out of 36238 words

Chapter 11 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi

09 Jul 2025

1243


haka sai ta ce to bari Uncle ɗin yazo ya kira Likitan don ya ce duk abinda ta ce zata ci sai yazo tukunna.


#######
[12/16, 08:36] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 14*



Hajiya Lanti ta ce,ke rabu da su, waɗannan likitocin masu tsirfar tsiya,ba ni plate nan ki gani in bata.
Nafisa ta ce,ki dai yi haƙuri mu bi dokarsu kada ta ci ta kuma yin aman su ce sun faɗa mun ƙi ji. Hadiza ta
ce, haka ne kuma a bari ɗin. Tana magana tana taɓa Hajiyar alamun ta bari.

Uncle ɗin ne ya yi sallama ya shigo da sauri Hajiya Lanti ta ja baya tana faɗin sannu da shigowa Alhaji, ya
amsa da cewa yauwa sannu da zuwa. Suka gaisa har tana durƙusawa. Ta ce,ya ya me jiki? To Allah ya
inganta mana yasa a sauka lafiya, ya ce Amin nagode. Hadiza ma cike da fara'a ta gaishe shi, tare da yi

mishi murna. Ta ƙara da cewa, insha Allahu ƴan biyu zata haifa,sai a bata ɗaya. Ya ce, Allah ya bi bakinki
Hadiza. Hajiya Lanti tana dariya tana cewa,kai waɗannan yara.

Ita dai A'isha tana ƙwance tana jin su. Ya matso kusa da gadon ya duƙa ya ce "Sannu Beby" a hankali ta
ce,zan ci naman da su Hadiza suka kawo,da hanzari ya ce Nafisa zuba mata,me su Hadiza suka zo dashi?
Wai zata ci. Nafisa ta ce, sai in Likitan ya zo,ɗazun ya ce kada ta kuma cin wani abu sai in yazo. Hajiya
Lanti ta ce,ni dai na ce da kun bata,ba lallai ne tayi aman ba. Nafisa ta ce bari dai in kira Likitan.

Uncle ɗin ya tashi, bari in kirashi ta ce zauna kawai Bros,bari na kirashi,ta fita. Ko da ta samu Likitan cikin
Office ɗin shi, suka gaisa ta ce mishi,ta zo ne don Allah ya yi ma yayansu magana ba kowa ba ne zai kawo
abinci ta ringa ci, saboda yanda ya daɗe babu haihuwa, wasu za su yi baƙin ciki,da samun cikin
musamman kishiyoyinta,don haka ya zo yanzun ma an kawo wani nama wai zata ci, kuma ita bata yarda
da naman ba,don haka tana son ya hana ta ci. Da hanzari Likitan ya miƙe tare da cewa, Madam nima nayi
wannan tunanin,ba zan so wata matsala ta faru ba,na gode da wannan taimakon da ki kai min."
Likitan ya shigo suka gaisa da Uncle ɗin,ta hanyar riƙe hannu. Ya ce,ka ce inzo? Uncle ya ce eh, wani
nama ne aka kawo shine take son ci. Likitan ya ce, "Yallaɓai ba zata ci komai ba yanzun ba sai zuwa da
safe, saboda wannan ruwan da muke ƙara mata yana tare da abinci,ba ma buƙatar ta ci komai yanzui."

Fuskar su Hajiya Lanti Nafisa ta kalla, sai ko taga sun kalli juna da ɓacin rai. Likitan ya fita tare da cewa,in
ka fito ina Ofis,ya ce to Doctor nagode."

Hajiya Lanti ta ce, to ni zan tafi ke zaki jira mijinki ne? Ta ce , to. Tana dubanshi ya ce to jira sai muje ɗin.
Hajiya Lanti ta ce to bani cooler in tafi da ita mu ma ci can ko? Hadiza ta ce to ko Nafisa tana so? Nafisa ta
ce a'a nagode." Ta ɗauki kular,wai bari ta rakata ta hau mota. Nafisa ta ce , to.

Suna fita shima ya nufi gurin Likita, Nafisa ta koma kusa da A'isha ta ce,ke wace irin wawiya ce zaki ce za
ki ci? So kike ɗan cikin muna murna kisa ayi watsi dashi? Baki san su Lanti ba ko? Kar su kuma kawo wani
abu ki ce za kici kin ji ko? Ta ce,to. Shima Uncle ɗin naki yasan komai don dai su maza ba su cika ɗaukan
irin waɗannan abubuwan da mahimmanci ba ne, likita ya ce baya son kowa ya kawo abu ace ki ci, ya yi
taka tsantsan, duk abinda tace tana so ta ci to ya kasance shi ne zai sa waɗanda zuciyarshi ta yarda da su
su dafa mata. Uncle ya ce shikenan. Likitan ya ce ko gidan mahaifiyarka kawai ya fi dacewa a dinga kawo
mata duk me zata ci,ya ce ƙwarai kuwa na gode insha Allah zan kiyaye.

Hadiza kuwa suna tattaunawa da mahaifiyarta kan cewa, duk wannan Nafisar ce ta ɓata musu shiri,
Hajiya Lanti ta ce,ni ba wannan ne matsalata ba, damuwa ta kuɗin da na kashe gurin amso wannan
maganin. Kai ina ma wannan cikin jikinki yake,kinga tun cikin asibitin nan sai mun ƙwashi kuɗi. Hadiza ta
ce,ke dai bari, Hajiya yanzun ya ya zamu yi da wannan abin? Lanti ta ce wa? Ai tunda ranta na so sai ta ci
shi, gobe zan ɗinɗima tunda yau ne aka ce kada ta ci saboda ana mata ƙarin ruwa, gobe da sassafe in zaki
taho ki biyo ki amsa. Ki zo mata dashi,sai ki ce wani ne ki kayi. Ta ce, to shi yasa ai na ce su bari na tafi da
shi tunda ba zasu ci, tunda ba nice nazo dashi ba,na su zaton ke ce ki ka dafa. Haka ne inji Hadiza, zan
biyo, suka yi sallama,ta dawo Hajiya Lanti kuma ta hau mota.


**** *****. ****

Goma dai-dai Uncle ya kula Nafisa tana hamma, A'isha tuni ta yi bacci,don haka ya miƙe ya je bakin
A'isha ya tsugunna ya sumbaci kumatunta, sannan ya zo gurin Nafisa ya ce "Sister tashi ki je ki ƙwanta
kema sai da safe." Hadiza ma tayi musu sai da safe, sannan suka fita.

A cikin mota take ce mishi "Darling amma ran A'isha ya biya da naman nan ko in yo mata wani gobe
tunda tana so? Gashi ance mace mai ciki in ta buƙaci abu a bata in dai da shi kada ta haifi ɗanta da tabo."
Ya yi ɗan murmushi, "inji hadisin hausawa ko?" Hadiza ta ce, "Allah gaske ne." Ya ce,to ki kawo mata,
amma fa ba lallai ba ne ta ci tunda Likitan bai ce da safe zata ci wani abu,kai ko dai ki barshi kawai ma."
Hadiza ta ce, a'a zan mata ko bata ci ba na san mutanan gurin za su ci, ya ce shikenan.

Ranar ƙwana Uncle ya yi yana sallah, ya kasa bacci. Washegari tunda Asubahi ya kira Abbanta. Bayan sun
gaisa, Abba ya tambaya ko lafiya? Uncle ya ce, A'isha ce bata jin daɗi ba, tana asibiti. Abba ya ce, "assha
gado aka bata kenan?" Uncle ya ce wallahi, amma da sauƙi ba sai kun zo ba. Sannan ka taya ni addu'ar
Allah ya sauke ta lafiya. Abba ya ce,ashe? Lallai nayi murna Friend, Allah ya bamu masu albarka. Uncle ya
ce Amin. Daga nan ya nufi asibitin don yaga yanda suka ƙwana. Zaune ya same ta tana sallah, gaskiya yaji
daɗi sosai,ya zauna har ta idar ta juyo ta dube shi, ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby ya ya jiki? Ta
sunkuyar da kai ta ce,da sauƙi. Ya ce ina Nafisa? Ta ce ta shiga wanka. Ya ce,to daƙyau,kema kin yi ne? Ta
ce eh, nayi shi ne na ji ɗan ƙarfi. Ya ce su Abba suna gaishe ki,ta ce gaya musu ka yi bani da lafiya? Ya ce
eh mana, har ma nace musu kina da ciki." Ta saka kanta a gwiwarta tare da faɗin haba dai don Allah. Ya
ce to mene ne? Ta ce,ni ina jin kunya yanzun su Hajiyarmu sun ji? Ya yi murmushi.

"Sun ji mana,tun lokacin da Likitan ya sanar damu."

Ta ce, "Shi kenan ba zan kuma zuwa gidan ba" ya ce "Don me?" Ta dube shi, yanzun kowa ya san abinda
na yi na samu cikin kuma? Ya yi dariya, sannan ya ce, a'a ba wanda zai sani,ke da ki ke makaranta, wasu
za su ce a ruwa ki ka sha." Ta ɗan yi murmushi don ganin ya maida ita doluwa,ta ce "Ai na san ba'a sha a
ruwa." Yasa dariya.

Nafisa ta shigo tana cewa "Bros ka zo kenan?" Ya ce, "wallahi ya ya kuka kwana?" Ina ta tunanin dare?
Nafisa ta ce bacci sosai mu ka yi kaga gashi har ta yi wanka,ta yi sallah. Ya ce aiko naga da sauƙi yanzun
me zaku ci inje gidan Hajiyarmu in sa ayo muku? Nafisa ta ce,Mama two me zamu ci? Ta ɓata rai Anty
Nafisa bana so, Uncle ka ce ta bari fa, cikin murmushi ya ce , Sister bama so gaskiya, ya dubi A'isha ƙyale
ta Beby gaya min me zaki ci? Ta ce,da zan samu waina ko irin ɗan waken nan? Ya ce zaki samu ya miƙe,
har ya fita. Ya dawo zaki ci farfesun irin na jiyan a zo miki da shi? Ta ce a'a, ya ce shi kenan.
Hadiza ta zo lokacin suna karyawa. Hadiza ta aje mata kular a gaba gashi kin ji ƴar'uwa na yi miki wani ne.
A'isha ta ce na gode, yanzun kam na ƙoshi amma anjima zan ci. Ta miƙa ma Nafisa ta ce Anty Nafisa gashi
ki sa can gefe kada ku ci min fa. Nafisa ta ce, to A'isha Hadiza kam daɗi ne ya rufe ta.

Hajiya Jummai kam an bazama nema,an nemo kuma an samo,ana kan aiwatar wa. Satin A'isha ɗaya a
asibiti, ta samu sauƙin aman. Sai dai kasala tare da tsirfa iri-iri har yau abinci in ba daga gidan Hajiyarmu
ba ne bata ci. Hajiyarmu kuwa ko yaushe mai aikin ta tana kicin tana dafa duk abinda A'isha ta buƙata,
sannan addu'o'i ko yaushe tana nan tana tofa mata su cikin ruwa tana sha. In za'a kawo abinci sai an
kawo, shi kam Uncle shi ne mai jinya, duk wadda yake ɗakinta zai je ya bata haƙƙinta in ya kintsa jikinshi
zai dawo gurin A'isha.
Ya lura da ita, musamman saboda dare Hajiya Jummai ce ta so ta nuna rashin amincewarta ya ce haba
Jummai,in kin lura A'isha tana buƙatar kula,ba fa wai ta samu sauƙi ba ne, dole sai da mai kula in kuma
da wanda ya dace ya kula da ita,to ni ne. Ta dai ƙyale shi ne kawai.

Kullum sai Ummanta da Abbanta sun kira ta sun tambayi jikin umma ta kan bata shawarwari masu kyau
game da rainon ciki. A daddafe cikin ya yi wata biyu, suka yi waya da Samira inda Samira take cewa
wannan satin ne za'a koma makaranta, ta ce, ina sane ni da nasha ciwo kamar ba zan tashi ba tun daga
wannan dai ciwon? Samira ta ce ayya amma me yasa ba a samun wayarki? Ta ce,ke dai bari,ni da

tunanina manta da batun wata waya, sai dai mun haɗu a makaranta. Samira ta ce to shikenan, Allah ya
sawwaƙe, A'isha ta ce Amin.

Koda Uncle ya dawo ta ce mishi an koma makaranta, sai ya ce mata wace makaranta? Beby gaskiya ba
zaki koma makaranta da ciki ba." Ta dube shi cikin rashin walwala ta ce, Uncle kana nufin ba zan zana
(S.S.C.E) ba? Ya ce haba Beby,ke sai ma ance miki,kina ganin yanzun ban bari ki yi nisa da ni? Ta ce,
gaskiya ba zan so haka ba, wata uku fa kawai ya rage min in gama duka,don Allah Uncle ka daina wannan
maganar." Ya ɗaure fuska wata shekarar kin zana, ganin yanda ya ɗaure fuska, abin da bai taɓa mata
ba,sai ta yi shiru ta kifa kanta kan filo, shi kuma ya fita abinshi. Kuka ta ringa yi wiwi,na ta ganin Uncle bai
mata adalci ba, ita a nata son ran ta koma makaranta tunda ba wanda ya san tana da ciki, har ta gama.

Da daddare ko da ya shigo ta bashi ruwa, sai dai ba ta cikin walwala,ya amsa yana sha yana kallon
fuskarta, wadda ta kumbura ta yi dam. Ya aje kofin da sauri,me ya samu fuskarki Beby? Ta sunkuyar da
kai babu komai, ya ce ban yarda ba kin yi kuka ko? Ta ɗago ta ce mishi, a'a sai hawayen da take maƙalewa
suka zubo ya kama hannunta suka zauna, yanzu saboda na ce ba ki komawa makaranta ba shi ne ki ke
kuka? Beby na fiki son karatun ki domin alƙawari na ɗauka cewa zan tsaya har sai kin ji da kanki cewa kin
gaji da karatu, amma yanzu koda ba ciki duka-duka yaushe aka sallamo ki daga asibiti? Ba ki gama
murmurewa ba" Ta ce, Uncle ko a makaranta fa zan kula da kaina." Ya yi shiru yana kallonta,sam baya so
ko kaɗan ya ga yarinyar cikin damuwa, ya ce to daina kuka za ki koma, amma sai kin ƙara murmurewa,
sannan in naga kina cin abinci. Ta ce, to Uncle zan dinga ci. Nan fa A'isha ta dinga ƙarfafa jikinta don
kawai ta samu ta koma makaranta, sai dai duk da haka cikin nata mai saka laulayi ne da tsirfar zan ci kaza
ba zan ci kaza ba,ga saurin fishi. Wata rana tunda safe ta ce da Uncle idan zai dawo ya zo mata da
agwaluma, ya ce ni kam ina zan ga wata agwaluma? Ba na zaton cewa duk Katsina za'a samu agwaluma,
amma zan sa a duba. Yinin ranar neman agwaluma gurin mutum huɗu ya baza,neman agwaluma. Ita
kuma tana ta yi mishi waya a ƙarshe washegari a Kano aka siyo cikin baƙar leda ya tashi Jabiru ya dawo
gida lokacin ƙarfe uku na rana ya same ta tana shan ƙanƙara ta fiya wota, ya ce Beby me yasa kike shan
ƙanƙara? Kada in sake gani ta ce, to da ya aje mata ledar agwaluma komawa ya yi gefe yana kallonta, da
gudu ta tashi ta ɗauko ruwa a firij ta wanke ta soma sha hannu baka hannu ƙwarya. Tausayinta ya cika
shi, ya ce Beby bana son wannan gudun da ki ke yi,kin ga cikin ki bai yi ƙwari ba,ta ce na daina.

Washegari kuma ta ce zogala, gidansu Hajiyarmu ya yi waya aka kawo mata shi da yawa,ta yini ci. Irin
waɗannan abubuwan suke sa Uncle tunanin yanda zata zauna a makaranta,ba za'a bari a zo kullum
ba,week end ɗin da yake zuwa sun gaya mishi don shi ne, sannan ita abin tattalin shi ce,a yanzun saboda
mutane da yawa suna bashi shawara kan cewa ya kula da ita sosai, saboda maƙiya ko ɓarayi masu yin
garkuwa da mutum don su amshi kuɗi irin waɗannan abubuwan suna sa shi tunanin barin ta ta koma,
amma ya san makarantar su akwai tsaro, sannan albarkacin addu'ar da yake yi ko yaushe Allah zai kare
mishi ɗan shi.

######
[12/17, 11:31] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 15*



Cikin wannan halin wata rana A'isha tana ƙwance da daddare, Uncle yana ɗakinshi,yau Hadiza ce da
girki,tasan komai dare zai dawo ɗakinta,don haka ba ta murɗa key ba. Shiru-shiru har ɗaya ta wuce, ita
ko bacci na cin ta, don haka ta rufe ƙofarta,ta ƙwanta tana karanta addu'ar bacci ta gama bata gama ba
oho bacci ya yi awon gaba da ita. Can cikin baccinta sai wata ƙatuwar mage ta nufo ta, nan suka soma
gabza dambe ta nayi tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta,mage ƙoƙari take ta cafko mata cibiya,
Allah bai bata Sa'a ba, suka yi wa juna kaca-kaca duk ta yayyaƙushe A'isha, itama ta ji ma magen ciwo. A
tsorace ta farka da addu'a, sai me,magen ta gani a kan durowar gefen gadon ta murtukekiya. Ta yi wani
tashi ta nufo ta,da matsanancin tsoro ta ƙwala ihu tare da kai ma magen nan duka da filo,ta miƙe tana
waige-waige saboda bata san in da magen ta shige ba,ta nufi ƙofa da gudu tana salati, tana buɗe ƙofa
Uncle yana fitowa, shima da gudu saboda duk wanda ke gidan ba zai ce bai ji ihunta ba.

Hanyar fita ta nufa ya yi sauri ya riƙo ta, ta sake ƙwala wani ihun tana ƙoƙarin fizgewa. Abinda ya bashi
mamaki, wani mugun ƙarfi ya ji ta yi. Ta ƙwace zata fita, ya kuma damƙo ta da ƙyar,ya kai ta ƙasa ya
danne ƙafafunta da hannuwanta. Nan ya shiga tofa mata addu'o'i, sai ta yi laƙwas. Ya ɗauke ta zuwa
ɗakin yana shiga ta soma ihu da sauri ya fito da ita kan kujera ya ƙwantar da ita yana tofa mata addu'o'i.

Hajiya Jummai tana leƙensu ta window, haka Hadiza daga falonshi ta leƙen su. Hajiya Jummai ta fito da
sauri tana cewa, "Lafiya Alhaji?" Ya ce, wallahi nima ihunta na ji. Ta zo ta tsugunna tana cewa, A'isha me
ya faru ne? Ina, A'isha sai wani gunjin kuka take yi. Addu'a dai yake ta tofa mata, Hadiza ma ta fito suka
zauna cirko-cirko. Jummai tana ɗan mutsu-mutsunta da baki tana tofa mata amma a zukatan su farin ciki
suke yi, kowacce tana zaton nata asirin ne ya ci, kafin safe ta yi wani sharaf ta daina gunjin kuma bata ko
motsi.

Tun cikin daren ya kira Alhajinmu ya sanar mishi, ya ce mishi ko su wuce asibiti? Alhajinmu ya ce, a'a ya
bari sai zuwa da safe. Suna idar da sallar Asubahi sai ga Alhajinmu,ba za ya iya tuna zuwanshi na ƙarshe
gidan ba sai ko yau.

Lokacin da ya iso su Uncle ɗin suma fitowar su kenan daga Masallacin. Duk ya yi zuru-zuru yana sanye da
farar jallabiya. Alhajinmu ya zuba ma A'isha idanu, inda take ƙwance kaman ruwa. Ya dubi ɗan nashi ya
ce, Abubakar wai ya ya abin ya faru ne? Uncle ya ce , nima ban sani ba, ihunta kawai na ji na fito, da na
kamata ma zan maida ita cikin ɗakinta sai ta fara ihu.

Hajiya Jummai ta ce,ko mafarki ta yi ne,ni ƴasu?. Uncle ya ce in kaga yanda muka dinga cin dambe da
ƙyar na kai ta ƙasa, na soma karanta mata addu'o'i. Alhajinmu ya nufi hanyar fita, Uncle ya bishi.

Bayan sun fito suka tsaya a harabar gidan, ya dube shi.

"A gaskiya Abubakar al'amarin yarinyar nan ba na zaton na asibiti ne, Malamai zamu samu. Uncle ya ce ,
to yanzu ya ya za'ayi?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0