Showing 21001 words to 24000 words out of 36238 words
Chapter 8 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi
kowa cikin duniyar nan daga ni sai ke,kin ji ko?"
Ta ce to Uncle, ya ce yauwa Bebyna, bari na watsa ruwa, ta ce to. Suka yi sallama.
Ya yi shiru, ya kula A'isha tana matuƙar son shi, kunya ce kurum ke ɗawainiya da ita, shi yasa shima yake
jin nauyin yi mata wasu abubuwan, amma yanzu ya san ya ɗauko gangarar cimma burinshi.
Bayan ya yi wanka ya fito zuwa (Dinning table) bayan ya yi wa Uche waya kan cewa ya kawo mishi abinci,
ya dubi Uche ba kowa a gidan ne? Uche ya ce Madam ta fita, amma bai ga fitar amarya ba. Zuciyarshi ta
tafi ga tunanin yaushe rabon da ya samu kulawa daga Jummai? Ba zai iya tunawa ba, domin tun lokacin
da ya zo mata da labarin auranshi da A'isha, ta canza har yau bai gane kanta ba. A fili ya ce, "Allah ka
shirya wannan baiwa taka." Yana rufe baki tana shigowa,ta nufo shi "ka dawo ne? Wallahi nima na je gida
ne na duba Innarmu." Idanu kurum ya zuba mata.
Ta ja kujera ta zauna,ba ka yarda ba ko? Ta soma magana cikin karya murya, irin ta wanda ke cikin
damuwa ɗinnan, ta ce ni yanzun ai ko zan haɗiyi Alƙur'ani ka daina yarda da magana ta, duk abinda na
faɗa ƙarya ka ke ɗauka, tun da ka samu yara masu jini a jika, ni ko na tsufa."
Ya ajiye cokalin hannunshi.
"Jummai don Allah ki zauna ki yi tunani, irin yanda ki ke tafiyar da gidan nan matsayinki na uwargida ya
dace? Ni kaina yanda ki kayi watsi da duk lamurana,ki ka kama ƙawayan bariki masu kai mutum ga
halaka,yawo tamkar an yi miki ƙauri da kan kare. Da na miki magana sai ki kawo duk maganar da ta zo
bakinki ki caɓa min." Ya nuna tebur ɗin gabanshi "Look at, yanzu tafiya fa na dawo ku biyu cikin gida
amma sai kuku shi ne mai kawo min abinda zan ci, shima ɗin sai da na roƙa. A ce kamar ni bani da wata
ƙima cikin gidana?"
Ta ce, "To kai ne ai duk ka canza min, yanzu A'isha ce a gabanka." Ya ce,"Ita ce take ganin girmana, amma
fa duk wanda na kawo na ajiye ai so ne ya kawo haka ba wai ƙi ba. Ni dukkanku ina sonku,ki kula da wani
abu A'isha, yarinya ce kuma ba mazauniya ba ce,ku ko kullum muna tare da ku, amma duk da haka sai
ƙorafinku ya tsaya a kanta? Kun yi mata adalci kenan? Shiru Jummai ta yi, amma a zuciyarta faɗi take yi,
adalcin banza,za ku gane kuskuranku. A fili kuwa sai ta ce, to shikenan, kayi haƙuri yanzu me kake so inyi?
Cike da jin daɗi ya ce, ina so ne ki canza ki koma Jumman da na sani da, kici gaba da kula da ni tare da yin
riƙo da muƙaminki na uwargida sarautar mata, kada ki yarda ki yi watsi da shi, wata ta samu. A'isha ki
ɗauke ta ƙanwa, bata da raini zata girmamaki, ta kuma sunkuyar da kai tare da cewa , insha Allahu zan yi
yadda ka ce." Ya ce, "To na gode, sai batun yarannan su Suwaiba ya kamata su fito da miji ko ya ya ki ka
gani?".
Ta ce, "Haka ne,nima fama nake da su,samarin na su duk ƴan yara babu mai shirin yin aure yanzu,ka yi
musu magana da kanka,ni sun riga sun gama raina ni." Ya ce, "Shikenan, zan gan su." Sai suka ci gaba da
hira tana gaya mishi cewa kayan shafanta gami da turarukanta sun ƙare, ya ce, to za ya bata ta saya. Da
yake ranar ita ce dashi,ta kula da shi yanda ranshi ya gamsu cewa ta gane kurenta, ta yarda da dabarar da
zasu sake tunda magani ya ƙi sai a koma kissa, don haka ko gurin ƙwanciya ta yi mishi ba zata, sannan ta
sake ba shi haƙuri.
Hadiza tana ƙwance suna waya da Hajiya Lanti mahaifiyarta, tana kuka tana sanar da ita cewa, Saddiƙ ya
mata wulaƙanci saboda wannan A'ishar,tun suna can ƙasar da suka tafi ya dawo don kawai ya ɗauko ta
daga makaranta, sannan tunda ta dawo sai abinda ta ce.
Haka ya ɗauki ƙwanana ya kai mata, na yi magana ya fi ni fushi, yanzun da haka zancen da nake miki yau
ƙwananshi biyu,ya ɗauke ta sun tafi ko'ina ni,ni ban sani ba. Sai yanzun na ganshi suna zaune da waccan
tsohuwar Hajiya Jumman,ko tun yaushe ya dawo be neme ni ba? Oho."
Hajiya Lanti ta ce,da Allah ni rufe min bakinki, kin bani kunya, kishiya ki ke wa kuka, sai ka ce ba nonona
ki ka sha ba? To bari ki ji in zaki dage ki dage, kuɗi za ki ƙwaƙwalo in bazama kin tsaya yin zuciya,an ce
miki fada ko kishi ne silar kawo ki gidan nan? In baki sani ba, bari ki sani, na shiga na fita na kutso ki
Wannan gidanne don kawai ki wawuro min dukiyarshi,ke dai dage ki samu ciki kada ki tsaya kishin
banza." Hadiza ta ce, "Hajiya ni dai na fi son ki samo min taimakon da hankalinshi zai dawo kaina." Ta ce,
kuɗi za ki kawo Hadiza." Ta ce, "zan kawo." Hajiya Lanti ta ce,a to, Hadiza ta ce to dama gobe ni ce da
girki,in sauke kenan in daina fushin?.
Lanti ta ja dogon tsaki, "in ba iskanci ba dama ina ke ina fushi? Sauke ki kuma bashi haƙuri yaƙi ɗan
zanba ne Hadiza,kin ji ko?" Ta ce, "To Hajiya sai kin zo."
*** **** **** ***
Satin A'isha biyu, Uncle ɗin ta ya yi mata waya cewa, gashi nan zuwa. Ta ce Uncle sauran fa sati ɗaya mu
koma makaranta,ka bari mana sai ana sauran ƙwana uku". Ya ce, "Lallai ma Beby,waton ba kiyi missing
ɗina ba ko?" Ta ce, "Nayi mana Uncle." Ya ce, "To gaya min da me ki ke tunani?" Ta ce,Da abubuwa da
yawa nake tuno ka, ya ce gaya min ɗaya.
Ta yi shiru, ya ce ina jin ki mana." Ta ce, "Ka bari dai ai zan gaya maka in na dawo." Ya ce, "ke ɗin? Kin
kasa gaya min yanzun a waya sai a gabana ne za ki iya? To ni bari na faɗa miki ɗaya,kina ji na? Ta ce, Eh."
Ya ce, da lallausar fatarki, da kuma zazzaƙan leɓanci..." Da sauri ta kashe wayar tare da rufe fuska sai ka
ce a gabanta yake. Shi ko dariya yake mata, ta kunna wayar ta tura mishi saƙon cewa "Uncle kai fa babba
ne,ba ka jin kunya?" Ya duba saƙon, sai ya tura mata cewa,a cikin soyayyar ma'aurata Beby ba jin kunya
wani abu ma sai in kin dawo." A ranshi ya raya cewa, bari na kashe maganar, sai ya rubuta cewa Beby
shin za ki iya gaya min ya ya kike ji a duk lokacin da jikina ya haɗu da naki? Ya tura mata,aiko ya kashe
magana don tana karantawa ta kashe wayar gaba ɗaya. Ta ƙwanta tana tunanin shi, Uncle tamkar zuga
shi ake yi.
Umma da Abba sun yiwa A'isha nasiha a lokacin tahowarsu, Umma ta ce,"Ni dai A'isha ina ƙara yi miki
nuni ne da haƙuri, musamman kasancewar ku,ku uku gidan mijinku. Ki kama kanki da bakinki, kada ki
yarda ki haɗa kai da wata don kawai ki musguna ma wata,gara ace ke ake cuta ba ke kike Cutar ba.
Sannan ki riƙe mijinki."
Abba ya ɗora da cewa,"ki zamo mai yi masa biyayya ki zamar masa wadda zata kai shi gidan Aljanna,ba
wuta ba."
A'isha a cikin aurenki ki sa ma ranki cewa, bautar Ubangiji ki ke yi, kada ki kalli ƙyale-ƙyalen duniya da
abinda ke cikin ta. Ta ce,"To Abba insha Allahu zan yi yanda ku ka ce."
Jabiru Sarkin tuƙi ya ɗauki hanya da su,yayin da suke zaune a baya suna ƴar hira. Lokacin da suka iso gida
ta yi mamakin ganin Hadiza ta zo mata sannu da zuwa, cikin dakewa ta amsa,yau kam Hajiya Jummai
tana gida. A'isha taje ta gaisheta, itama cikin sakin fuska ta amsa. A ran A'isha ta ce, ina ma ace har
zuciyarsu, saboda gajiya A'isha ko tashi daga kan sallaya bata yi ba, bacci ya yi awon gaba da ita. A haka
Uncle ɗinta ya same ta,bai tashe ta ba cak ya ɗauke ta ya ɗorata kan gado.
Hijabin kurum ya zare mata daga ita sai ɗaurin ƙirji, da alama ma wanka ta yi kafin sallar,zama ya yi ya
zuba ma fuskarta idanu, komai na yarinyar yana son shi.
A hankali ya runƙufo ya sumbaci leɓunanta, sannan ya miƙe don yin shafa'i da wuturi, sannan ya zauna
gaban laptop kafin lokacin da zaya ƙwanta. Ya so ƙwarai ya sami hutu da ƴar Bebynshi, amma ta gaji sai
dai ya mannata a jikinshi suka ci gaba da bacci.
Washegari girkin Hadiza, da rana A'isha ta yi zoɓo don ya yi waya za ya aiko a ɗauka, Hadiza tana zaune a
babban falo taga Uche ya zo ya amshi ƙwando kamar ta yi magana ta dai share.
Da yamma da ya dawo bayan ya shiga gurin Jummai, ya fito ya shiga gurin Beby, duk da cewa duk inda ya
shiga lokacin shigowa gida ko lokacin fita ba ya zama, amma ya kan ɗan yi jum gurin A'isha saboda yana
shan ruwa ko zoɓo.
Bayan ya fito ne ya nufi ɗakinshi kamar yadda ya saba, sai mai girki ta bi shi. Wani sabon salo wai sai
Hadiza ta shigo wai ta zo (danning) inji darling don su ci abinci, kamar kar taje amma jin cewa Uncle ke
kira sai ta fito. Ba shi a gurin sai Hadizan kaɗai, sai ga Hajiya Jummai,jim kaɗan shima ya fito. Ya kallesu,
kowacce fuska a ɗaure in ban da A'isha wadda hankalinta ke kan T.V Hadiza ta ce, tana son ya haɗa su su
dinga cin abinci tare, sai shima ya ga da hakan zata yiwu,da zai so. Don haɗin kansu yake nema ba
rabuwar kansu ba. Ya yi musu sallama su suka amsa. A'isha ta ƙara da cewa sannu da fitowa." Ya
ce,"yauwa Beby." Ya dubi Hadiza "Na ji daɗin wannan zaman, Allah yasa ya ɗore" duk suka ce, "Amin."
Nan Hadiza aka buɗe abinci, maigidan aka soma zuba mawa, sannan ta tura ma saura plate kowa a
gabanta,wai ta zuba abinda ta ke so.
A'isha ba gwanar cin abinci ba ce,don haka kawai sai ta ɗan zuba romon farfesun kazar dake gurin tasa
cokali tana sha. Ya dubi plate ɗin beby wannan ne abincin? Gira ta ɗaga tare da yin murmushi, Hadiza ta
ce, shi yasa baki yin ƙiba ko? Kullum kamar a hure ki ki faɗi, tana magana tana dariya, A'isha ta fahimci
magana ta gaya mata da wasa,don haka ba tare da ta dube ta ba tace, "ai ƙiba ciwo ne,ke baki sani ba
ne." Hajiya Jummai dai tana ji ba ta ce ƙala ba, kuma abincin da tasa sai juya cokalin take yi tana
mamakin,yau ita ce zaune da kishiyoyi biyu? Abin tamkar cikin mafarki.
Shi ko sam bai ma fahimci suna jefa ma juna magana ba ne, musamman da yaga Hadiza tana fara'a ta yi
maganar. Sannan A'isha bata nuna wani fushi ba. Hadiza ta ji haushin kalmar A'isha, amma bata da ta
cewa, A'isha ba ta jima ba ta miƙe, Uncle ya ce, har kin ƙoshi? Ta ce, na ƙoshi Uncle." Ta dube su sai da
safenku, dukkansu sun amsa ne a maƙoshi,ko mene ne yasa dukkansu suke jin zafin ta? Ta tafi ya bita da
kallo, komai na Beby yana birge shi, musamman tafiyarta cikin natsuwa, tamkar mai tausayin ƙasa, wani
sa'in shi kanshi sai ya dinga ganin tamkar yanga take yi. Hadiza ce ta buga cokali akan plate ya yi ƙara,
sannan ya dawo daga tunanin da ya tafi, cikin ɓacin rai ta ce "ko yaushe in A'isha na guri kowa banza
ne?" Ya ce "haka ki ke gani?" Ta ce, "Eh mana." Ya ce, shikenan. Ranta ya sake ɓaci, ta ce "sai ka ce wata
ƴar gwal?" Bai kula ta ba, shima ya miƙe ya nufi ɗakinshi suma suka watse kowace zuciya na raɗaɗi.
Washegari ma A'isha ta wuce makaranta, ta bar su suka ci gaba da neme-nemensu.
Wannan karon A'isha sun buɗe wuta,don daga wannan hutun sai na fita.
Hadiza dai kowane wata ana jiran a ji ciki shiga, amma shiru. Zaman su da Hajiya Jummai zama ne na ba
ruwan wani da wani, sai dai ana gumawa juna ta ƙarƙashin ƙasa. Cikin haka wata ranar Lahadi maigidan
nasu ya tashi da matsuwa ta buƙata, Jummai ke dashi to amma jiyan tana fashin sallah,yau kam Hadiza
ce a daddafe ya kai magriba, inda so samu ne ma tunda rana ya biya buƙatarshi, ana idar da sallah ya
shiga gida,kai tsaye ɗakinshi ya shiga,ya ɗauki waya ya kira layin Hadiza,sai da ta ɓata lokaci sannan ta
shigo.
Ya nufe ya dafa ta, sannan ya cire ɗanƙwalin da ke kanta na shaddar da ke jikinta, doguwar riga.
Abubuwan da ya soma yi mata su ne suka fahimtar da ita abinda ya ke so. Nan take mulkinta ya tashi ta
ƙwace daga rungumar da ya yi mata.
"Ba ka sanin darajata sai in kana buƙata,to gaskiya nima yanzu lokacina ne, kuma ba zan yi abinda ka ke
so yanzun ba." Idanunshi da suka yi jajir, ya dube ta, "Don Allah Hadiza ki bani haƙƙina, wallahi na matsu
da yawa,ki min taimako.
#####
[12/14, 18:12] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³—í ½í³—Page 11*
Ta sake taɓa baki dama ina da rana?" Ya ce, kada fa ki manta,duk matar da ta gujewa kiran mijinta, tana
ƙwana ne cikin tsinuwar Allah da Mala'iku." Ta juya mishi ƙeya kai ka san wannan Ni ban san shi ba, ya ce
in ma kuɗi ki ke so zan baki Hadiza, ya zo ya rungume ta ta baya. Ya dace a ce ina da mace fiye da ɗaya,
amma ina cikin wannan bala'in?" Ta fisge mai Beby yau ina Bebyn taka? Ya ce, duk ba wannan ba ne,don
Allah fa na ce. Ta ce, wallahi ni fa ba yanzun ba,yau ma ƙwata-ƙwata bana jin yi, amma tunda ka matsu
goman dare ka zo sai mu yi ciniki a ɗakina kuma nima ni ke so yanda ka kewa Bebyn taka ita ƴar gwal
bata bin miji sai dai ya bi ta. Ta dube shi, goma na dare ina jiranka sai ka zo da kuɗi." Ta fice abinta, ya
bita da kallo yana haɗiye miyau,jin shi yake tamkar ya kama ta da ƙarfin tsiya.
Kan gadonshi ya zube rigingine mararshi har ta soma ciwo. Ya miƙe tsaye ina zan kai wannan matsalar
tawa? Gaskiya kafin goma na dare zan sha wahala. Ya raya a zuciyarshi,ya kalli agogo baƙwai ma yanzu ta
yi, ya janyo wayarshi.
Jabir ya kira bayan ya ɗaga ya ce,kana ina ne Jabiru? Ya amsa da cewa, ina nan gidanmu maigida,ya ce na
san zan takura maka, amma in zai yiwu ina son ganinka yanzun. Ya ce,ba komai maigida gani nan zuwa.
Kamar minti goma ya kira shi gani na iso maigida. Ya ce, yauwa Jabiru ina fitowa. Turare kurum ya ƙara
fesawa, sai kuɗi da ya ɗauka ya saka su cikin aljihunan nashi guda biyu,ya ɗibi wayoyinshi ya fita.
Tuni Jabir ya fito da mota, suka fita titi ya ɗan juyo ina zamu ne maigida? Ya ce,mu je makarantar su
Beby. Da sauri ya ce "lafiya dai ko?" Ya ce,a lafiya lau." Ya ciro waya ya soma neman shugaban
makarantar, bayan sun gaisa ya ce zan zo in tafi da yarinyar nan ne zuwa da safe. Mahaifiyarta ce ta zo
yau kuma sammako zasuyi, Allah yasa ba matsala? Shugaban makaranta ya ce, da matsala, sai dai tunda
kai ne zan iya yi maka alfarma, amma fa da safe a tabbatar da cewa ta dawo da wuri, saboda ta samu
shiga aji. Alhaji Saddiƙ ya ce, don wannan duk ba damuwa insha Allah zata dawo da wuri, ya ce to bari in
yi waya cikin makarantar.
Lokacin da suka shigo cikin makarantar, A'isha suna dawowa daga (Dinning) suna tafe suna yi wa juna
ba'a irin ta ƙawaye. Samira tana ƙwaiƙwayon tafiyar A'isha.
A'isha ta yi murmushi ko da haka ni ke tafiya da sai na fi awa ban kai ko nan da masallaci ba." Amina ta
ce,ba haka take yi ba,kunga yanda take yi nan. Sallamar da aka yi musu ne ta dakatar da su, mai sallamar
ta ce cikinku wacece A'isha Mustapha? A'isha ta dube ta, gani nan, ta ƙara da cewa lafiya? Lafiya lau,kina
da visitor. Ta dafa ƙirji,ni kuwa? Ta ce ba ke ce A'isha Mustapha ba?" Amina ta ce ki je ki gani mana. Cikin
fargaba ta ce,na bani ni A'isha,wa zai zo gurina da daren nan? Samira ta ce, Uncle ɗin fa? Cikin damuwa
A'isha ta ce, Uncle ya zo jiya fa. Suka ce muje mu raka ki, kasancewar kowane gurin gal yake da
haske,tamkar rana. Tun kafin su ƙarasa ta ce Uncle ne don ta hango motar sannan ga Jabiru a tsaye, ta ce
ina zaton ba lafiya ba,ban ga Uncle ɗin ba Samira,Suka ce to bari mu koma sai kin dawo ma ji ko mene
ne. Ta ce to.
Tana isa gurin cikin firgici ta ce,"Jabiru lafiya, ina Uncle ɗina?" Ga zatonta wani abu ne ya sami Uncle ɗin.
Jabir ya nuna mata mota, ya ce yana ciki, shiga." Ta kai hannu zata buɗe bayan motar,sai taga an buɗe
mata, daga ciki ta a shiga da sauri lokacin ne kuma wutar motar ta haska, ta kalleshi "Uncle lafiya?" Ya
jawo hannunta lafiya Beby, amma ba lau ba. Ta zaro idanu me ya faru? Abbana ne ko ummat? Ya ce, a'a
ni ne. Ta soma leƙa ƙafafuwanshi me ya faru da kai? Ganin yanda ta ruɗe kuma jawota jikinshi taimako
nazo nema gurinki, domin yanzun duk