Showing 15001 words to 18000 words out of 36238 words

Chapter 6 - Mummunan Zato Book 2 Halima Abdullahi Mashi

09 Jul 2025

1235

da sallama,ta amsa, sannan ta tashi ta buɗe Malama
ta ce an zo ɗaukar ki A'isha kunna wuta. A'isha ta kunna wuta tare da cewa da wannan daren Momy?
Haka ta ji ƴan biyu suna kiranta don haka ɗan zamanta a gidan itama take mata duk abinda taga yaran
suna yi. Ta ce eh, fito da jakarki,ta koma ta kinkimo jakar Momy ta amsa tare da cewa ɗauko ɗayar, A'isha
ta ce gashi su Hassana suna bacci ba mu yi sallama ba,ta ce ba komai zan sanar da su,in hutu ya ƙare ki ka
dawo ina fata zaki zo? Ta ce insha Allah, har mota ta rakata. Sun gaisa da Uncle ya yi mata godiya sosai

sannan ya yi mata alkhairi kamar yanda ya saba babu ƙirgawa. Aisha dai ta shige bayan mota ta yi shiru
sam bata son komawa gidan rayuwar ƙwana uku a gidan Malama Salamatu ta yi mata daɗi.

Jabir na jan mota suna zaune a baya ƙala dai bata ce mishi ba tunda ya shigo motar suka ɗau hanya kasa
jurewa ya yi ya lalibo hannunta ya saƙala yatsunshi cikin nata,bata hanashi ba sai dai bata kalleshi ba
yanayin salon da yake yi gurin murza hannun nata kansa ta ji wani irin yanayi. Saitin kunnanta ya rusuna,
ya raɗa mata cewa ki yi haƙuri Beby, nayi laifi,ba tare da ta dube shi ba ta ce name? Ya ce na manta na
tafi na barki,ta girgiza kai tare da ɗaga kafaɗu,ai ba komai, rashin sakin fuskarta shi ne ya hanashi yi mata
hira shiru har suka shiga harabar gidan sai dai hannunshi yana cikin nata. Jabir yana tsayawa ya fito ya
buɗewa maigida ƙofa, Uncle ya ce kai mata kayan ciki Jabiru. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ya jawo hannunta
tsaya mana Beby ta koma ta zauna. Ya fuskance ta sosai, Beby kiyi haƙuri,ta ce me kayi min ne Uncle wai
shin? Ya zuba mata idanu. Kina nufin ban miki komai ba? Ta girgiza kai tare da cewa, a'a. Ya ce,to in haka
ne meye ki ka canza min,ki ka dake min ba kamar da ba? Na shiga wani hali Beby,hakan yana soya raina
fa. Sai a nan ta dubeshi zuciyarta na gaya mata cewa da gaske ne zancan da yake miki da bai manta da ke
har na tsawon kwana uku ba, duk da an mishi text amma a fili sai ta ce, kayi haƙuri to yanayin rayuwa ne
ka san ya kan canza wata rana ƙila zan daina ya sake yin ƙasa da murya tare da cewa,haba Beby,wata
rana fa ki ka ce? Ta ɗaga kai ya ce kenan ni da farin ciki sai wata rana kenan? Ta ce, Uncle ai kai ba zaka
zama cikin baƙin ciki ba saboda kana da amarya in ba kaga fara'a ta ba ai zaka ga tata. Ga mamakin ta sai
taji ya ce, haka ne, amma sai dai ni nafi son ganin taki ɗin,ta yi shiru,ya ce kin ji me nace? Ta dube shi duk
da a duhu ne amma tana iya ganin annurin angonci a fuskarshi, kuma gashi ya tabbatar mata cewa yana
ganin fara'ar amarya. Ƙila da amaryar ce zata ɗaure fuskar da sai yafi haka ruɗewa, ya ɗan matsa
hannunta da ke cikin nashi,ta yi firgigit ta kalli gurin da yake, ya ce na sani kina tunanin abinda na yi miki
ne ko? Ya ci gaba da sam ban za ci yin auran nan nawa zai ɓata ranki ba, da ban yi ba, ba tasan sanda ta
ce Uhum ba, saboda ta san labari Uncle ya ke,wai kace baka san ran mace zai ɓaci ba,za ka yi mata fa
kishiya ne, amma ka ce baka san yin hakan zai ɓata ranta ba, wannan ma hira ne,shi kam da ya fuskanci
ba zata lallasu ba, sai ya ce shikenan mu shiga ciki.

Addu'a ce a bakinta, har ta buɗe ɗakinta, ta shiga. Da wanke toilet ta soma sannan ta kakkaɓe gadonta,ta
kulle ƙofarta ta ƙwanta, cikin bacci ta ke jin ƙwanƙwasa ƙofa,ta kalli agogo sha biyu,a ranta ta ce to
wanene? Maida kai ta yi ta ci gaba da baccinta, don bata zaci Uncle ba ne, tunda ba ya ƙwana ɗakinta ko
ma ya ƙwanan baya kula ta.

Washegari da aiki ta tashi, ta yi sallar Asubahi,ci gaba ta yi da aikace-aikacenta, ta share ko'ina ta goge ta
kunna turarukan wuta ko'ina ya ɗauki ƙamshi,ta faɗa toilet ta yo wanka ta fito tana yin filla-filla da
kayanta. Nan ta dinga ɗago kayan da Uncle ya yi mata, lokacin yana ji da ita, ta cire su gefe. Sannan ta
ciro zannuwa da lesuka tun na cikin aƙwatinta,ta zube su duk zata ba da a ɗin ke mata su ne. Yanzu tana
son English wears gashi ba ta sa su ba, duk sun mata kaɗan. Sai wani (3)ne da t-shirt ɗin shi ta saka,ta
cire saura ta zuba su cikin wata leda da niyyar zata ba Mima ƴar gidan Anty Sadiya, wanda zata ɗinka ɗin

ma Anty Nafisa zata yi ma waya ta bada a ɗinko mata, tunda ba ta san inda zata kai ɗinkin ba, duk
zamanta a gidan ba tayi wani ɗinki ba, sai dai Uncle ya siyo mata (r) kawai, zama da su Samira ya sa ta iya
zama gaban madubi, duk da basa yi a makaranta, amma suna labarin mahimmancin yin ƙwalliya a gurin
mace,su kan ce mata mace doki ce sai da gayu,su kan yi labarin cewa in sun yi aure zasu ringa yin
ƙwalliya ga mazan nasu. Amina kan ce ai in auranta ya kusa ƙananan kaya zata shiga kasuwa ta jibgo,
A'isha tana gaban madubi tana tuna hirarsu,nan ko ta zage ta zabga ƙwalliya ta saka sarƙa (passion) har
da ta ƙafa da ƴankunne zobuna da warwaro da ta kalli kanta a madubi sai da ta furta ni ce kuwa? Ta gyara
gashinta,tana cikin saka wayarta a caji taji ƙwanƙwasa ƙofa,ta zo bakin ƙofar ta ce, "Wane ne?" Muryar
Uncle taji ya ce,ni ne Beby buɗe min,ta buɗe fuskarta ya soma kallo a ranshi ya ce jiya i yau waton babu
fara'a kenan.

Ta kauce ya shiga sannan ta kulle ƙofar cike da mamaki ya bita da kallo ta burge shi fiye da
tunaninta,sumar kanta da ke ƙwance a dokin wuyanta ta tsuma shi, kamar yanda ta saba ta tsugunna ta
gaishe shi duk da ba fara'a ya ji daɗi ya amsa tare da cewa lafiya lau Beby,kai amma fa kin yi ƙyau, shiru
ta yi tana zaune nan inda ta gaishe shin, tana wasa da zoben dake ƙaramin yatsanta,ya dubi ɗakin a
zuciyarshi ya ce yarinyar tana da tsafta sosai, ya ce Beby ina so in Zauna da ku in kin gama yanzun cikin
falona, ta ce, to ina zuwa.
Duk sun hallara a falon A'isha kurum suke jira. Hadiza takaici Hajiya Jummai takaici gashi su kansu sun ƙi
kallon juna tsakanin Jumman da Hadiza sai ƴan harare-harare. Aisha kamar ta saka hijabi sai kuma ta
fasa,ta ɗauki hula baƙa kalar wandon tasa, gashinta kuma ya bazu a bayanta,silifas baƙi ta saka sannan ta
ɗauki wayarta ta nufi falon.

Hadiza da ta ƙosa taga A'isha sai da numfashinta ya kusa ɗaukewa lokacin da A'ishar ta shigo da sallama,
Uncle ne kurum ya amsa. A'isha ta ƙara tsare gida, ganin amaryar ta su duk suna zaune ne kan kujera mai
zaman mutum uku sun sa shi a tsakiya.



########
[12/13, 07:51] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 8*

Aisha me ladabi sai kurum ta zauna kasa a gabanshi ta kalli hajiya Jummai ta ce,Hajiya ina kwana? Itama
ta cije ta ce,lafiya lau Aisha kin dawo kalau? Ba tare da ta dubu Hadiza ba,ta ce ina kwana? Yi tayi tamkar
ba ta ji ta ba,sai da Uncle ya ce ana gaishe ki,cikin yatsina ta amsa,shi ko sai kallon Aisha yake yi,ta dube
shi ta ce Uncle gani.

Hadiza ta kuma cika da mamaki ta maimaita kalmar tace Uncle? Lallai wannan yar bariki ce,dubi yanda
tayi wata shiga tana ta yatsina sai kace yar wani da wata ga wani ladabin kinibibi za a wani zauna
gabanshi,maigidan ya yi gyaran murya ya ce,dalilin tara ku a nan shi ne,ina so in kara tunatar daku cewa
yanzun kun zama ku uku don haka sai ku yi ta hakuri da juna,musamman ke Jummai,tunda ke ce
babba,ku ma dole ne kuyi mata biyayya ban da raini,sannan ga masu aiki nan ni nake biya,don haka na
kowane in ma basu isa ba a nemo wasu,haka nan duk mai wata bukata sai ya tambaye ni ,game da kwana
kuma sai kuyi shawara dai dai ko bibbiyu?."

Hajiya Jummai ta ce,bibbiyun za'ayi, Hadiza ta dube ta gami da tabe baki ta ce,bibbiyu? Gaskiya ba zan
iya kwana hudu ban gan shi ba,Hajiya Jummai ta dube ta,ko Aisha mamaki ya cika ta,wannan tana nufin
tafi kowa son shi kenan? Jummai kuwa cewa tayi sannunki da karfin hali,kina nufin kin fini son shi ne?
Hadiza ta ce kina shakka kenan? Wani murmushi Jummai ta yi irin wanda ya ke nufin baki san da wadda
ki ke magana ba. Sannan ta ce kin tafka kuskure,amma za ki ga aya.

Aisha ko wayarta ta ciro ta shiga yin game,jin suna ta musu ne ya dakatar dasu da cewa,kai ku min
shiru,an ji naki ra'ayin kema anji naki,Beby ke me ki ka ce? Hankalinta ya tafi ba taji ba,ya sake cewa,
"Beby." Ta dubeshi "Na'am,Uncle me ka ce?" Haushi ya cika su Hadiza,ya ce ke me kika ce game da
kwana? Ta girgiza kai uncle bani da zabi,ya sanyaya murya saboda me? A ranta ta ce ko na zaba me
kwana da kai zai kare ni dashi? Amma a fili sai ta ce ,ba komai ni kaga ba zama nake ba,ya ce a a wannan
ba dalili ba ne,ta kara sanyaya murya,Uncle Allah na yafe musu,su yi yanda suke yi,ta mike ta tafi. Ya bi ta
da kallo sannan ya ce,ba zai yiwu ba. Hadiza ta ce,me zai hanashi yiwuwa darling ba itace ta ce ba.
Jummai ta ce kawai ka bar ta tunda ita ce ta yafe ya ce to in ita ta yafe ni ban yafe ba,baku ganin cewa
yarinya ce sai mu taru mu cutar da ita? Ya mike ina zuwa, Hadiza ta ce yanzun binta za kayi? Ko
sauraronsu baiyi ba,ya tafi.

Hadiza ta miƙe ranta ɓace tana cewa,tabɗi, wallahi ba zan zauna ba ƙaramar yarinya tana juya mu son
ranta,ɗazun ya taramu fiye da minti goma muna jiranta yanzun kuma ta tafi ya bita, bayan da ta zo ɗin sai
da ta gama yiwa mutane kallon banza," Haka ta wuce tana mita.

Jummai kuwa kasa magana ta yi ita mamakin ta wai ita ce haka, ita ce kuwa? Ita ce Jumman da tasha
alwashin kai duk mai ƙararran ƙwanan da ta aurar mata miji lahira? Yau ita ce da kishiyoyi biyu? Ba dan
bata da kuɗin da zata biya ayi mata aikin ba,ba don babu malamai ba sai don me? Tana son jin amsar
wannan tambayar.

Aisha kuwa tana shiga ɗakinta kan kujera ta faɗa ta ɗauki ƙafarta ɗaya ta ɗora kan gado, tana karkaɗawa,
wani irin zugi take ji a cikin ranta. Wai duk yanda take jin Uncle,a ranta waɗannan matan sun fita? In ma
Jummai ta furta za ta iya yi mata uzurin daɗewar su tare, amma Hadiza fa da tazo jiya-jiya,ba ta yarda ta
fita son Uncle ba,to abinda tafi son sani yanzun ta ji duk suna son Uncle to shi Uncle ɗin wa yafi so?.

Muryarshi ce ta katse ta, inda ya ce, "Beby ban yarda da hukuncin ki ba,ko kina tunanin ba zan miki
komai ba, dole ne kema yanzun ki ringa kwana dani. Ya zauna bakin gado ya ɗora hannunshi kan ƙafarta
wadda ke kan gadon ta ce "mai yasa ya dace ɗin? Ya ce Beby me yasa kikeson dafa ni cikin ruwan sanyi
ne? Ya murza yatsun ƙafarta. Beby kina ji na?" Ta ce "Uncle, Allah ba haka ba ne,kaga ni zan je gida ne ma
ko ba zaka kai ni ba?" Ta zuba mishi idanu, ya yi ɗan murmushi ba zan kai ki ba, sai in kin yarda da batun
cewa za ki dinga gyara shinfiɗata, duk bayan kwana biyu ko huɗu. Ta ce, to naji na yarda duk ƙwanakin da
ka yanke ya yi min. Ya sunkuya ya sumbaci ƙafar dai-dai tafin ƙafarta, wani abu ta ji zir har cikin kanta, har
sai da ta yi girgiza tare da yin ajiyar zuciya. Lokaci ɗaya kuma ta sa tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce
"Beby ina son abubuwa a tare da ke, cikin su har da wannan kunyar ta ki." Ya miƙe yau fa kece da gyara
shimfiɗa, don jiya kin ƙi ki buɗe min ƙofa, kuma gobe zan koma in ƙarasa harkokina a can Phoenix,ko
zamu je?" Ta ce, a'a ka dai koma da amarya kawai,ya ce Beby kenan ƴar daru, ta ce yanzun har wani daru
gareni? Ya ce ai ke darunki daban ne,babu faɗa babu hayaniya cikin ruwan sanyi ne. Ya fita yana cewa,
haka ne ko?" Ta ce haka ka ce.

Tana kishingiɗe tana kallon (Zee Aflam) fim ɗin soyayya suke yi,in tana kallon finafinan soyayya sai ta
rinƙa jin yana taɓa zuciyarta, ta sani tana son Uncle ta girma ne cikin son shi,ba wani namiji dake birge ta
in bashi ba. Amma shi tana shakkar son da yake mata,ta san dai so ƙwaya ɗaya ne tak, kuma nata shi take
yi ma wa,to shi fa wa yake mawa cikinsu? Matarshi da suka yi auren saurayi da budurwa, kuma zamanin
ƙuruciya? Ko ita da ya aura tana yarinya ya kuma kasa haɗa shimfiɗa da ita? Ko amaryarshi da ya ke
shanawa da ita? Saboda son ta fa wata ƙasar zai je sai da ya tafi da ita, ita ko ko nan da can bata taɓa
zuwa ba, daga gida sai makaranta, sai ko garin su in taje hutu. Unguwar ta kuwa ba ya wuce gidan
Hajiyarmu,Anty Sadiya ko Anty Fatima. Gidan Nafisa ma ba taje ba, tunda tana makaranta aka yi bikin
yanzu dai take son zuwa kafin ta tafi hutu Jigawa. Jin da tayi an dafa mata cinya shi ne ya dawo da ita
daga tunanin da take yi, da sauri ta dubi ko wane ne don ta ɗan razana, ganin Uncle ta yi cikin kayan
bacci ya zauna kusa da ita, gabanta ne ya sake faɗuwa, amma da ta tuna cewa tana al'ada sai kurum ta
ƙwantar da hankalinta, ta ce sannu da shigowa Uncle,ta miƙe ta kawo mishi zoɓo cikin zumuɗi ya amsa
tare da cewa, Beby ƴar albarka, har kin min zoɓon? Ya cika kofi ya soma sha idanu lumshe sai da ya sha
yafi rabi sannan ya dube ta, nayi missing ɗin zoɓonki sosai Beby, ta ce, to yanzun zaka sha har ka gaji.

Ya kalli wuyanta kullum yana sha'awar shafa wuyan nata,leɓunanshi suna ƙwadayin sumbatar wuyan ya
ce, Beby yau dai za ki yi gyaran shimfiɗa ko? Ta kasa kallonshi, amma ta ce to, ya miƙe da jug ɗin zoɓon a
hannunshi ina jiran ki,ta ce to.

Tana son kallon fim ɗin nan amma haka ta haƙura ta miƙe ta ƙara fesa ɗan turare ta nufi ɗakinshi. Tana
kama ƙofar, Hadiza na fitowa daga ɗakinta. Ta yi saurin zuwa gurin ƙofar tana ke! Ke!! Tsaya ina za ki
shiga? Aisha ta dube ta sannan ta shige, itama Hadizan ta shigo,ban gane ba, tunda ka yarda cewa ƙwana
ɗai-ɗai ne to ai yau ni ce da ƙwana." Ya dube ta wa ya ce miki ta ƙwana nan jiya? Hadiza ta ce, to an hana
ta ne? A'isha ta yi sororo tana kallonsu,bata da lokacin hayaniya, don haka sai ta nufi bedroom ɗin shi da
niyyar ta yi abinda ya kawo ta,ta fita watan gyaran shimfiɗa.
Aiko sai Hadiza ta yi caraf ta cafke mata hannu cikin ɗaga murya take cewa, Malama kada ki shigar min
ɗakin miji,don yau nawa ne,ran A'isha ya ɓaci, ta tsani ayi mata ihu,don haka sai ta fisge hannunta ta juya
tana jin lokacin da Uncle ya ce wa Hadiza dama haka halinki ya ke? Beby zo nan." Ya miƙe yana kiranta,ai
wannan tuni ta kai ɗakinta, ta zauna kan gado ta riƙe kai ta tsani ayi mata ihu a kai. Ita ba ta iya masifa
ba,bata saba ba, amma duk ba wannan ya fi bata takaici ba irin yadda Hadiza take nuna mata kan Uncle
ba zata barta taji da kishin dake cin zuciyarta ba.
Shi kuma Uncle saboda yafi son Hadizan ya kasa hanata. Ya tura ƙofar ya shigo, ya tsaya a gabanta ya
maida hannuwanshi baya,ya ce "Beby tashi kizo mu je." Ranta ya kuma ɓaci,tamkar ta dubeshi ta ce ba
zan je ba. Amma kimar shi ta wuce haka,koda ba zataje ɗin ba ba zata iya yi mishi rashin kunya ba,don
haka sai ta girgiza kai "kayi haƙuri Uncle, ba zani kuma shiga ɗakinka ba, cikin sanyin murya ta ke
magana.

Ya jawo kujerar madubi zuwa gabanta, ya zauna,ya kira sunanta cikin tattausar murya, ya ce A'isha sai
yaushe zamu yi zaman aure? Da farko na barki ne saboda kasancewar ki ƙaramar yarinya, yanzu kuma kin
girma ya kamata mu canza,shiru tayi mishi, ya ce kin ji ni? Ta sunkuyar da kai,ni dai kurum kai min
alfarmar cire ni cikin masu zuwa ɗakinka." Ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna, amma Beby ni kin
amince in dinga zuwa naki ɗakin ko?kai kurum ta ɗaga mishi ya ce shikenan zan ƙwana nan kenan ko?" Ta
ce "In kana ra'ayi."

Duk da cewa bai so ba lokacin da ya ce tazo su yi sallah don yiwa Allah godiyar zuwan wannan rana sai ta
sanar da shi cewa tana fashin sallah, amma ya ji daɗin yanda suka yi bacci tana lafe a jikinshi. Sannan ya
yi wasanni da ita,ita kanta irin yanda yake mata ɗin yasa ta jin daɗin cewa itama mace ce.

Sai dai washegari ta kasa kallonshi,in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0