Showing 60001 words to 63000 words out of 78696 words
Chapter 21 - A Zuriar Arab Compelet Book By Mhiz Innocence
Har yanzu baka tafi ba ?
Sosa kae yayi kafin yace
" A'ah mamama daga can nake, zuwa nayi mu tafi "
Murmushi mamama tayi tana girgiza kae kafin tace tana kallansa yana sinne kae wae shi a
lallae dole kunya yakeji
" Toh ae zefi kyau ka tashi ka tafi, dan kuwa ma bacci take "
Dan shiru yayi kafin ya miqe yana fadin
" Bari naje na tashe ta !
" Iyeeeee ! Mamama ta fada tana riqe ha6a
" Toh kaje yau ka raba dare kana waya da budurwartaka, yau kam babu me takura maka "
Seya koma ya zauna
" Ae shikam shikenan ya shiga uku tunda har zancen nan yaje wajen mamama seta wajigashi
yasan kafin zata bashi matarshi " ( Ahh su mata manya í ½í¸¹ )
" Wlh mamama ba abinda take nufi bane, duk bata fahimci.....
" Allah ya tashemu lafiya " mamama ta katseshi da fadin hakan
Be qara cewa komae ba ya miqe a sukwane yana fadin
" Seda safe "
" Mu kwan lafiya " inji mamama
Seda ya fita sannan ta bishi da kallo tana murmushi .
Kwanakin da suka biyo baya sune na gyaran jiki da aka farawa sanah, wanda aka hadata da
amarya afrah ake musu tare, kafin kace meye wannan, tuni sanah ta fito tayi dass da ita ta qara
haske fatarta har wani qyalli takeyi, gashi tayi wani acan acan da ita kamar wadda aka sanya a
inji .
Ana saura kwana 1 daurin aure me lalle tazo tayi musu me shegen kyau, amarya da
muqarrabanta sun fito Cass dasu .
Ranar daurin aure da daddare za'ayi dinner, wadda daga nan za'a wuce kae amarya,
Dan haka qarfe 5 na ranar daurin auren masu Kwalliya suka fara aekinsu
Suna dakin da akewa amarya Kwalliya su 3n
Amrah akewa kwalliya dan se an gama mata za'a yiwa amarya
Ana gama mata kuwa aka yiwa amarya afrah ta fito a amaryar sak kuwa tayi matuqar kyau
Wayarta dake ajje tayi ringing
Amrah dake kusa da wayar tace
" Kae yah imam !
Afrah ta galla mata harara tana fadin
" Dillah can ni bani inji muryar mijina "
Sanah dase a lokacin da kalleta tace
" Ahh lallae afrah ! Ni wlh bansan sanda kika lalace haka ba "
Dae_dae lokacin data daga wayar ta amsawa sanah da
" Ranar da aka daura min aure mana "
" Lallae madam aure " sanah da amrah suka hada baki wajen fadin hakan.
Ita dae sanah tace ba zatae Kwalliya ba zataje a yadda take
Seda qyar ta yadda ayi mata light makeup bayan su afrahn sun saka baki, sannan suka fita
daga dakin dan zasu fara yin gaba ne kafin sanah din
Kwalliya er kadan ta mata mara hayaniya
Sanda akazo saka Jan baki win sakuwa yayi saboda taushin bakin, haka me kwalliyar ta haqura
ta saka mata lipgloss kawae
Se ta fito kamar wata er tsana, tayi kyau sosae abinta, sukayi sallama da me kwalliyar sannan
itama ta fito daga dakin dan tafiya wajen dinner
Dae_dae lokacin da take qoqarin wuce motar taji an janyeta ciki
Cikin matuqar razana ta bude baki zatayi qara
Se taji tattausan hannunsa wanda ya wadatu da qamshin turarensa dako a mafarki taji shi zata
gane wanene
" Shhhhh !!! Ni ne ! Ya fada cikin wani irin salo kuma a hankali cikin kunnenta
Seta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta fara kiciniyar qwacewa daga jikinsa
Shi kuwa ya sake riqeta yana shaqar qamshin dake tashi daga jikinta me matuqar sanyi
Tayi masa masifar kyau, ga fatarta data sake wani laushi kamar ta jariri
A hankali yace
" Ina kike shirin zuwa a haka ?
Ta turo baki tana kauda kanta gefe tace
" Dinner mana "
" Ohh dama haka ake ? Mata ta tafi unguwa ba tare da mijinta ya Sani ba ? Ya fada yana dage
mata girarsa 1
Se ta sake tura bakin kamar yarinya er goye
Bakin yabi da kallo yana nazartarsa kamar wani maye
A very cute lips, dan qarami dashi gashi daga gani zeyi taushi and se wani sheqi yake
" Ae ka sani "
Yaji ta fada, Se yaji kamar ana fuzgarsa ne ya sake maeda dubansa kan dan qaramin bakin
nata
Babu zato babu tsammani kawae ta tsinci bakinsa akan nata,
Cikin firgici gigicewa da tsoro gaba daya ga6o6in jikinta suka fara rawa, tayi azamar qoqarin
tureshi amma ina Arman fa yayi nisa..............
Mhiz Innocent ce.............��
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent í ½í¸»
THE TALENT TROUPE WRITER'S
Page 39_40
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES í ½í¸�í ½í±Œ Mhiz Innocent luv u owl í ¼í¼ší ½í¸»
( Baby WhatsApp group link ) í ½í±‡í ½í±‡
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
............Bata haqura ba dae ta cigaba da tureshi din, sedae kamar ma besan tana yi ba
Seda ya gaji dan kansa sannan ya saketa yana shafa kwantacciyar sumar kansa fuskarsa
dauke da wani qayataccen murmushi
Aekuwa kamar jira take seta saki kuka kamar wadda aka duka, ta fara yinsa hadda sheshsheqa
Da sauri ya riqo hannayenta yana fadin
" Am sorry, ki dena kukan kinji ?
Kamar bada ita yake ba dan kuwa cigaba tayi da kukanta tanayi tana qarawa
Wani iri yakeji a zuciyarsa wannan kukan da takeyi, hakan yasa a hankali ya janyota ya
rungume yana sake lallashinta
Qoqarin tureshi take amma dukda haka bata dena kukan ba
Seda tayi me isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya akae_akae still dae be saketa ba
Se can kuma cikin shaqaqqiyar murya tace
" Ni ka sakeni zan tafi "
" Ina ? Ya fada kamar besan Inda zataje ba
Shiru tayi kafin taga dae shirun ba abinda ze mata yasa tace
" Dinner mn "
Seya kwantar da murya yace
" Yanzu kina nufin a haka zaki tafi dinner ? Kinci wannan kwalliyar ga jikinki ko ina tashin
qamshi yake ? Fisabilillahi kinmun adalci kenan idan kika fita ? Ko wani qato ya kallemin ke ?
Seta juyar da kanta gefe ba tare da tace komae ba,shi kuma ya cigaba da fadin
" Toh kafin ma ayi haka, bari kiga ni in gyara zamana inyi ta kallanki ya fiye miki fitar da zakiyi "
Seta juyo ta kalleshi idanunta sunyi rau_rau alamar koda yaushe zata iya yin kuka
Be gama kallannata ba kuwa ta fara aekin nata na kuka
Ya yamutsa sumar kansa yana sauke ajiyar zuciya sannan cikin taushashshiyar murya yace
" Baby meyasa kike so ki dinga wahalar dani haka ? Meyasa ba zaki tausayamin ba ? Wannan
wahalar da kike bani ta isa haka, tun ina daurewa har na kaasa daurewa yanzun, plsss ki
tausayawa zuciyatah mana "
A hankali ta fara rage sautin kukan nata se taji tana buqatar sauraron abinda zece mata din
Ya cigaba da fadin cikin wani salo wanda bata Zata babyn nata bane
" Baby I luv u I luv u and I will always do "
Shirun dae tayi har yanzu kanta na qasa
Haka suka cigaba da zama cikin motar yana kallanta kamar wata T.V, ita kuma idan ta tuna
yadda ya hanata zuwa bikin nan da nan se qwalla ta taru a idanunta .
...Wajen qarfe 12pm yana kwance akan tanqameman gadon nasu, tun dazu yake kwance
amma ya kaasa baccin,baccin yaqi daukarsa se juyi yake daga wannan kusurwar se waccan
kusurwar
Tashi yayi ya zauna akan gadon ya kunna light din dakin yana dafe kansa, sannan ya dauki
gorar ruwan sanyin dake ajje akan side drawer yasha yana ajiyeta
Dole ne ma yasan abinda zeyi zuwa gobe, dole ya dauko matarsa yabar kwana haka nan
kamar wani tuzuru,da wannan shawarar ya sake kashe light din ya kwanta amma fah bacci
babu bayaninsa .
............Washe_gari qarfe 8 na safe a gidan na Arab tayi masa
Seda yakae motarsa bakin qofar part dinsu sannan ya ajjeta ya fito
Yana fitowa wayarsa nayin qara, kamar baze duba ba kuma seya tsaya ya dakkota daga
aljihunsa, Daddy ne
Hakan yasa ya daga cikin girmamawa yana karawa a kunnensa bakinsa dauke da sallama
Daddy ya amsa cike da kulawa yana dorawa da fadin
" Arman ! Ina son ganinka yau idan baka da uzuri "
Cikin tunanin abinda yasa daddyn keson ganinsa yace
" Tohm daddy, yanzu ma na shigo gidan bari na qaraso "
Da " Ohk " daddy ya amsa yana katse wayar
Shi kuma ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa 6angaren baffah da yasan indae ana biki acan duk
mazan gidan suke zama
Da sallama ya shiga parlourn baffahn
Daddy ne kawae a cikin dakin yana kallan tashar France 24
Ya amsa masa sallamar yana daukar remote ya saka t.vn a mute
Arman ta qarasa ya zauna a qasan carpet yana fadin
" Barka da safiya daddy "
" Barka dae Arman, ya aeki ?
" Alhamdulillah mun godewa Allah daddy "
" Toh madallah " daddy ya fada kafin yayi shiru sannan can kuma ya dora da fadin
" Arman ! Wato Dr Stephen yazo min da wata magana akan kaeda diyarsa cewar kuna soyayya
kuma yana nema mata aurenka, ya abin yake ?
Cikin sakanni fuskarsa ta koma a dinke tsaff kamar hadari haka zalika fushin kan fuskarsa be
hana bayyanuwa a cikin muryarsa ba
" Daddy ! Ya fada a kaurare sannan ya dora da fadin
" Ni ba sonta nake ba daddy, tace tana sona, ni kuma saboda alaqar dake tsakaninka da Dr
Stephen ya saka bance bana sonta ba, amma daddy na nuna mata duk wasu alamomi da zasu
saka ta gane bana sonta amma ta kaasa fahimta, but daddy bazan ta6a iya aurenta ba "
Shiru daddy yayi yana nazarin maganar arman din
" Qwarae arman yayi dae_dae daya kare wannan alaqar dake tsakanimsa da Dr Stephen amma
shima besan yadda za'ae su hada zuri'a da kafira ba, but In Sha Allah Allah ze kawo musu
mafita "
" Kayi qoqari Arman, ka tashi kaje Allah ze kawo mafita In Sha Allah "
A hankali ya sauke ajiyar zuciya danso yake kafin yabar wajen nan 6acin ransa ya ragu, ya
tashi yana fadin
" Allah ya yadda daddy, nagode "
" Amm baka ji ba " daddy ya fada
Seya koma ya zauna
Daddy yace
" Zaka shiga hospital ne yau ?
Seya sosa kansa yace a hankali
" A'ah daddy gskia babu tsarin haka yau a wajena "
" Ohk toh pls taemaka ka shiga hospital din ka duba idan akwae wata matsalar seka gyara, in
kuma babu shikenan kawae "
Da " Toh " ya amsa yana miqewa ya fice ya dauki motarsa ya wuce asibitin.
Shida ya shiga tun 9 saura bashi ya sami kansa ba se dab da magrib sannan yaje yayi sallah
kae tsaye ya sake wucewa gidan nasu.
.......A hankali yake takawa part din mamaman bayan ya sake ajjye motarsa a bakin wofar part
din yana addu'a a bakinsa ya qarasa shiga ciki
Babu kowa a cikin parlourn, seya fara wuwwulaga idanunsa koze hango 1 daga cikinsu
Dae_dae lokacin da take qoqarin sakkowa daga stairs sanye cikin doguwar riga me taushi da
hula wadda ta zameta rabin sumar kanta ta bayyana, seya sami kansa da qare mata kallo tun
daga qafarta har zuwa kanta, ya wani lumshe ido yana budewa still akanta
Dae_dae lokacin ta dago kanta sanda take dabb da qarasa sakkowa inda qwayar idanunsa
suka shige cikin na juna
A hankali ta qarasa sakkowa shi kuma ya gyara tsaewarsa yana kallanta
" Ina mamama ?
" Yanzu ta shiga part dinsu amrah " ta fada tana kauda kanta danta gujewa wannan mayataccen
kallan da yake mata
Wani qayataccen murmushin gefen baki ya saki sannan yace
" Ohk toh jeki dakko hijab dinki ki wuce mu tafi "
Dakatawa tayi daga niyyar tafiya da tayi ta tsaya tana kallansa
Ya dage mata girarsa yace
" Yeah ! Tunda sunqi bani matata in sunga na daukeki ae dole su shafawa kansu salama koh ?
Seta juya ba tare da tace komae ba ta fara qoqarin komawa saman
Cikin azama ya bita yana shan gabanta yace
" Allah kuwa kikace zaki min taurin kae zan tsaya ne in daukeki " ya fada yana fara tattare
hannun rigarsa
Seta zaro ido ganin da gaske yake ta fara qoqarin bin gefensa ta wuce
Gaba dayanta ya sure ta be tsaya ko ina ba se cikin motarsa dukda wutsil wutsil din da takeyi
tana
" Ni ka saukeni kar wasu su gammu "
" Toh menene ? Ae kinga ma se hakan yafi bada citta " ya fada a dae_dae lokacin da yake
ajjiyeta a kujerar me zaman banza
Sannan ya qaraso ya zauna a wajen driver ya tashi motar ya fice daga gidan gaba 1.
Kae tsaye suya spot ya tsaya ya siya gasassun kaji, sannan ya dawo ya tashi motar, ya sake
tsayawa a wani supermarket din ya siyi yoghurt da sauran kayan sha sannan kae tsaye ya
qarasa gidan nasu dake Nasarawa G.R.A
Shiya sauka ya bude gate din gidan sannan ya kutsa motar cikin madaedaeciyar harabar gidan
Ita dae tunda suka fara tafiya ba tace komae ba se cika kawae take tana batsewa ta cika tayi
fam qiris take jira ta fashe dan haka sam bata lura ma da abinda ya sissiyo din ba .
Seya qaraso 6angaren da take ya bude da murmushi kan fuskarsa yace
" Madam barka da zuwa gidanki " ya fada yana ware hannayensa na hannun dama
Dauke kae gefe tayi ba tace komae ba
Se ya sake murmushi yace
" Ohk an sake bani dama kenan in shigar dake ciki ? Well ! Hakan ma yayi " ya fada yana
qoqarin fara daukarta
Da sauri ta fito daga cikin motar, se a lokacinma ta tuna ko mayafiko hijab babu a jikinta .
Qaton parlour ne with well furnished ya hadu iya haduwa dan kuwa an zuba dukiya irin sosae
din nan, akwae kitchen a ciki se two bedroom duka dae a cikin parlorn,
Ya nuna mata 1 daga cikin bedroom din yace
" Ki shiga ciki kiyi wanka, bari nima naje nayi "
Ba tace komae ba ta wuce dakin shima da ya gaji da kyau kamar a qasar waje
Mintuna wajen 20 ta dauka tana wankan sannan ta fito daure da towel tana tunanin kayan da
zata saka tunda dae tasan ita ba tazo da komae ba
Tana bude wardrobe taga saetin dogayen riguna masu kyau kalar wadanda takeso
Kawae se taji murmushi ya su6uce mata ta dauki 1 daga cikim rigunan ta saka, sannan tayi
sallah ta nemi gefen gadon ta zauna kafin bacci ya dauketa .
Wajen qarfe 9 se gashi ya shigo hannunsa dauke da wani plate da jug da robar yoghurt, ya
qaraso ya ajjesu sannan ya kalleta
" Madam tashi muyi sallah koh ?
Kallansa tayi cikin rashin fahimta tace
" Ae nayi "
" Yes na sani, wannan ta daban ce "
Jiki ba qwari ta tashi ta gyara zaman mayafin ta sannan suka tada sallar bayan ya shimfida
musu dadduma .
Ita dae haka kawae taji jikinta yayi sanyi da al'amarin babyn, haka ya tilasta mata seda taci
kazar da yoghurt din kadan taci sannan ta miqe taja blanket ta shige ciki tana fatan bacci ya
dauketa a lokacin
Sedae addu'arta bata kar6u ba dan kuwa tana kwancen harya gama cin kazar ya tashi ya fita ya
dawo baccin be dauketa ba
A hankali taji ya hawo kan gadon sannan ya yaye bargon data rufa dashi ya janyo ta jikinsa
yana kishingida akan pillow
Bugun zuciyarta ne ya qaru amma ta dake tana sauke ajiyar zuciya
A hankali ya fara magana cikin taushi hannayensa akan sumar kanta me santsi
" Baby ! Kinsan kuwa tun sanda nake qaunarki ? Ina qaunarki ne tun kina qaramarki, da sonki
na tashi tun ina qarami, bansan sanda soyayyarki ta shigeni ba nidae kawae abinda nasani
shine na tashi ne naji ina qaunarki , na kasa fada miki ina qaunarki ne saboda karki gane basu
Mamama ne suka haefeki ba, dan kuwa bazan ta6a yafewa kaena ba indae ta dalilina kika
shiga wani hali, meyasa kike ganin 6acin raena duk sanda na ganki da wani ? Ko kikae zancen
wani ? Kishinki nake baby , ina jin zuciya ta tamkar zata faso qirji na a lokacin, baby ki
tausayawa wannan zuciyar me matuqar qaunarki dan kuwa ta azabtu shekaru da dama ya
kamata ace yanzun ta sami salama, baby ina sonki sosae pls kice kina so na kema " ya fada a
raunane
Bata iya cewa komae ba, sedae zancen nasa ya shige ta sosae ta yadda seda taji wata qwalla
ta zubo mata
Seya shagala da rarrashinta wanda daga nan zancen ya sauya.......
Daga haka na kamo hannun Ummulkhaer, dama Fateema bashir ke dauko rahoton ina
rubutawa ta tsaya zata qarasa daukowa, Maemuna ta janyo hannunta muka fice daga dakin
muna kullo musu qofar.. Daga