Showing 54001 words to 57000 words out of 78696 words

Chapter 19 - A Zuriar Arab Compelet Book By Mhiz Innocence

bayan ya katse kiran

Komae mutuncin Stephen da yake gani anzo wajen daya kamata ya taaka wa diyarsa burki , ya
yana so ya lalla6a abarsa tana neman hanyar da zatayi fatali da hakan ?

Amma fah Stephen ? Idan yayi hakan kuwa ya kyauta ?

6angaren sanah kuwa dukda taji yana waya , bata kaawo komae a ranta ba dan kuwa fargabar
ma da take ciki kadae ta isheta .

Wae me yake faruwa a Nigeria tun bayan fitar souban daga gidan nan ?




"""""""""Abba da tunda ya fara magana yake kallansa yace

" Souban ka bude baki kayi mana bayani me kyau wanda zamu fahimta dan kuwa wannan
kwane kwanen ba gaaneshi mukeyi ba " Abba ya fada dukda cikin zuciyarsa a karye take na
ganin souban din wani iri haka

barrister souban saurayi me jini a jika amma yau duk se yake ganinsa wani iri kamar bashi ba

Souban ya gyara zama yana kallan wadanda ke xaune a dakin , kasancewar ranar juma'a ce
yasan duk wani dan gidan yana cikin dakin

A hankali ya fara zagaye da idanunsa ba tare da yasan hakan ba yana Kallan mutanen dake
zaune a dakin

Se dae me ? ya zaga idanunsa ko ina amma be hango ta b , Yayi mamakin yadda yaga babu
Sanah a dakin !

Tana makaranta ne ? Ya tambayi kansa

A'ah tabbas yasan tun kafin bikin aka tafi strike ,

Toh ko an aeke ta ne ? Ya sake tambayar kansa ! Dukda yasan hakan ba dabi'ar gidan nasu
bace

Wata amsa ce ta fito daga zuciyarsa wato " may be bata da lafiya ne " Wanda lokaci guda yayi
na'am da hakan dae dae lokacin da ya sake fahimtar Arman ma baya dakin

Cikin sakannin da basu wuce 2 ba amsar tazo masa cewa " Ya koma Cyprus tunda dama biki
ne kawae ya kawoshi.........

Kuyi manage da wannan pls yau qwuiwa nake ji wlh 😫


Mhiz Innocent ce..............��

*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻

�THE TALENT TROUPE WRITER'S�

Page 36

Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES �👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻

( Baby WhatsApp group link ) 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e


............Souban ya gyara zama sannan a hankali ya fara fadin

" Abba lokacin dana fita da safe zanje in taho da abokaena da sukazo daga abuja , da yake
safiya ce babu mutane sosae a titin , kawae wata mota tayi over taking dina sannan wadanda
suke ciki suka fito da sauri zuwa cikin mota ta

Cikin sakannin da basu wuce 5 ba black ya shaqawa souban wani abu dake jikin handkerchief
din dake hannun sa

Tun souban na qoqarin kaare kansa har yaji gaba daya jikinsa ya mutu , be sake sanin inda
yake ba se farkawa yayi ya ganshi a cikin wani bedroom a kwance

A hankali ya tashi yana dafe kansa dake saara masa kamar ze cire yana tuno abinda ya faru

Wajen mintuna 5 sannan wani ya shigo ya kalleshi bece komae ba ya fita , se can suka dawo su
2 shi da wani qaton mutum baqi sidiq dashi babu alamar annuri a fuskarsa ( black kenan ) riqe
da bindiga a hannunsa

Kallansu yake sosae yana so ya gane ko ya sansu ? Su waye su ? Me yake a dakin nan ? Shi
da ya kamata ace yanzu haka yana can yana shirye shiryen tafiya daurin auren sa

Cikin karyewar murya yace

" Bawan Allah me nake anan ? Meyasa kuka kawo ni nan ? Me nayi muku ? Ko da yake be
kamata in tambayi abinda na muku ba couz na san a cikin wadanda nayi case dasu ne ! So plss
Ku bari yau ranar farin ciki ce a gareni ranar daurin aure na , Ku bari bayan daurin auren se mu
dora daga inda aka tsaya , wannan ba lokacin wata maganar bane "
Dariya black ya sheqe da ita kana yace

" Toh mu kuma wannan lokacin ne kawae damu ! Kasan meyasa muka kawoka ka nan ?

Souban ya karkata kansa alamar yana ji

" So muke ka faasa auren matar da zaka aura yau din nan "

Dariya souban yayi kana yace

" Sorry wace mata kenan ?

" Sanah ! Black ya bashi amsa da sauri

" Impossible ! Wait a cikinku ma wae waye ne yake so in bar masa ita ?

Dayan dake kusa da black yace

" Ogammu ne , karka bari ya bayyana a wajen nan ba tare da ka amsa wannan buqatar ba "

" And so ? Souban ya fada yana kallansu su duka

" Kaaga barrister ! Rashin kunyar ka ta faara yawa fah , ka sani wani matsayin ka ba zeyi
amfani a wajen nan ba , kawae kayi biyayya shine abinda ze ceceka in kuma ba haka ba zakayi
nadama " black ya fada a kufule dae_dae lokacin da wancan ya fita daga dakin

Wajen minti 2 se gashi ya dawo riqe da wayar souban din a hannunsa dae_dae lokacin da Abba
yake kiransa lokacin da suna masallaci

Black ya kar6i wayar ya miqawa souban yace

" Kar6i ka daga wayar ka fada musu cewar ka faasa auren !

" Baze yiwuwa ba ! Souban ya fada

A fusace black yayi kansa da kan bindigar ya kwada masa a gefen kansa ya qara fadin

" Kar6i ka fada musu Cewar ka faasa auren nan "

Souban ya sake girgiza kae yana riqe da gefen kansa

Dayan da suke tare da black ya kaewa souban naushi a hanci and lokaci guda yana kae masa
a ciki

Haka suka hadu su duka suka dinga dukansa kamar wadanda aka aeko sannan black ya sake
cewa

" Zaka fada yanzu ko kuwa sena fasa qwaqwalwarka ?

Shiru souban yayi yana nazari , yasan idan be fada din ba zasu iya kashehi a banza , toh kuma
idan ya fada din yasan daga can 6angaren za'a fasa auren ne

Toh wannan ce kawae mafita in yaso idan ya koma seya fada musu abinda ya faru , yasan idan
hakan ta faru toh za'a daura musu auren su a nutse

Daga nan kuma seya binciko wadannan shashashan yayi maganinsu

hakan ce ta sanyashi fadin

" Ehh "

Black ya danna number abban kira 1 ya daga

Nan ne inda souban yake fadawa abba ya faasa auren , toh abinda yasa souban yace ya faasa
ne a bisa wasu dalilansa , yasan wannan kadae ya isa abinda zesa a jirashi aji menene dalilan
nasa ????

Daga nan basu sake azabtar dashi ba , yana dae zaune a cikin dakin , zasu kawo mishi abinci
da ruwa da sauran kayan buqata

Se kuma ranar da sukazo suka bude masa qofar ya fito daga gidan zuwa gida....

Shiru dakin ya dauka na wajen mintuna 10 babu wanda ya iya cewa komae , kowa da abinda
yake saqawa a ransa

Cikin matuqar tausayi gami da mamaki kowannensu ke kallan souban din sanda yake baada
wannan labarin

Abba dake zaune a qaramar kujerar parlourn yayi shiru hannayensa riqe da juna a ha6arsa

Be ta6a tunanin haka abin yake ba , be kawo ba haka zalika beyi zaton haka al'amarin ya
kasance ba , meyasa yayi gaggawa ? Ya tambayi kansa

Baffah yayi gyaran murya cike da dattako shima muryarsa a hankali da alama labarin ya tsuma
shi yace

" Souban !

Souban ya daga kae ya kalli baffah sannan ya maeda kan nasa qasa kafin baffah ya cigaba da
fadin

" Wato duk abinda kaga ya faru da dan adam toh dama can rubutacce ne a cikin littafin
qaddararsa , saboda haka ka riga da kaasan cewa daya daga cikin cikon imani hadda yadda da
qaddara ta alkhaeri ce ko akasinta "

Duk souban yasan wannan hakan yasa ya gyada kae , amma se yaji kamar ba zancen kenan
ba , dan yaji kamar maganar tayi ta kumayi alaqa da kuma baudewa da abinda ya faru dashi ,
amma seya cigaba da jin abinda baffahn yake cewa

" Saboda haka abinda zamu ce shine Allah ya kiyaye ya kuma tsare gaba "

Abinda souban yake da buqatar ji kenan , Dan haka yace

" Ameen " shi da ragowar da suke cikin dakin

Baffah ya cigaba da fadin

" Sannan muna me baka haquri souban , a bisa wadannan abubuwan da suka faru mun
daurawa Sanah aure da Arman !!!

Cikin wani irin yanayi dana kaasa tantancewa souban ya dago ya kalli baffah cikin ido abinda be
ta6a ba kenan , ya cigaba da kallan nasa ba tare da ya dauke ba , Dan kuwa so yake ya hango
wae wanene ma yake maganar ne ? Ko bayan tafiyar sa baffah ya haukace ne ? Ko kuwa
shaye shaye ya fara ?
A hankali ya maeda dubansa ga ragowar da suke dakin yana so yaji sun qaryata abinda baffahn
ya fada , sedae yaji shiru , babu wanda ya tanka , Me suke so su ce masa ne ?

Abba dae ya kaasa cewa komae Dan kuwa tausayin Dan nasa ya gama kashe masa jiki

Baba ne yayi qarfin halin fadin

" Qwarae kuwa souban ! Kayi haquri mun riga mun yanke hukunci cikin fushi ba tare da bincike
ba a lokacin muka daurawa Sanah aure da Arman "

" Ina ! Baze ta6a yiwuwa ba ! Abba ashe ku da nake tare daku ma kun kaasa fahimtar wane ni ,
toh su wane zasu fahimce ni ? Baffah meyasa kukamin haka ? Meyasa baku tsaya kun jira na
dawo kun tambayeni dalilina na fasa auren nan ba ? Meyasa zaku aurar da sanah zuwa ga
wani na ? Meyasa bakwa son gani na a cikin farin ciki ? Meyasa kuka za6i ku tozarta soyayyar
da muka gina ta shekara da shekaru ? Meyasa bakuyi tunani akan irin soyayyar da nakewa

sanah ba ? Meyasa bakuyi tantama akan magana ta ba ? Me....."

" Souban ! Abba ya fada cikin daga murya yana kallan souban da yake magana cikin rufewar
idanu

" Souban ashe baka da kunya ? Mu kake fadawa haka ?

Se a lokacin tunanin souban ya dawo , ya gane tukunna ma da wadanda yake tare " Iyayena ne
" ya tunasarwa kansa

" Ya Allah ! Ka farkar dani daga wannan mummunan mafarkin da nake dan zuciya ta rana dab
da tarwatsewa " ya fada a ransa .


*_Los Angeles_*

...........Kwanansu 2 a asibitin bayan yi mata aekin sannan aka sallamesu .

Ranar da suka dawo wajen maghrib ne dan haka kae tsaye daki suka wuce

Shine ya fara yin wanka , sannan ya fito ya shirya

Tana zaune akan gadon inda ya barta , sedae yanzu ta kishin gida ne

A hankali ya qarasa wajen yace

" Ki tashi kiyi wanka uhmm ?

Turo baki tayi tace

" Ni bansan tashi , na gaji "

Murmushi yayi yace

" Ae baki da damuwa ! Lem me help u " ya fada yana qoqarin daga ta

Da sauri tace

" A'ah ni fa ka bash shi "

Yace

" Nooo , pls kina buqatar taemako , ki barni na taemaka miki "

" Ni fa bana so " ta sake fada tana turo bakin dae

Ya bita da kallo yana lumshe ido

Tayi wanka ta fito cikin doguwar riga me dan baby hijab , tayi matuqar kyau kamar er tsana ya
bita da kallo sanda take qoqarin ficewa daga dakin

So samu ne yanzu haka ya janyo ta jikinsa ya rungume , toh so yake ya bita a hankali a hankali
harta saba dashi a matsayin mijinta ba yayanta ba shiyasa yake binta a sannu a sannu

Kae tsaye parlour ta fice ta zauna a kujera kana ta dauki remote control ta kamo MBC
Bollywood ta faara kalla

Seda ya zauna yadan danna wayarsa sannan ya fito parlourn bayan yayi sallah

Tana zaune akan kujera me 3sitter hankalin ta akan t.vn

Ya qarasa wajen t.vn kamar yadda ya tsammata kuwa film take kalla

Kae tsaye ya wuce kujerar da take kae ya zauna yana maeda hankalinsa kan t.vn

Bata kulashi ba dae ta cigaba da kallanta har wajen qarfe 10

A hankali taji wani bacci me dadi yana sakadarta , hakanne yasa ta fara lumshe dara_daran
idanunta

Ganin haka ya sanyashi matsowa kusa da ita , ita kuma ta samu damar Dora kanta a kafadarsa
tana sake lumshe idanun

Ganin haka ya sanyashi gyara mata kwanciyar zuwa kan cinyarsa

Ita kuwa ta gyara kwanciya hankali kwance abinta ta faara baccinta cikin kwanciyar hankali shi
kuma ya cigaba fa kallon , lokaci _ lokaci yana kallanta

Se da ya tabbatar baccin ya dauketa sosae sannan a hankali cikin nutsuwa ya daga ta cakk
zuwa kan gado , ya gyara mata kwanciyar ta , sannan ya ja mata blanket zuwa sama

Kae kallansa yayi zuwa cute face din ta dake qara kyau idan tana bacci gashi tayi wani fayau da
ita

Besan sanda ya saki wani qayataccen murmushi ba sannan a hankali ya kae bakinsa saman
goshin ta ya bata light kiss , sannan ya gangaro zuwa hancinta shima ya bata kiss , se yaji

kamar ana jansa zuwa bakinta , ya kae dubansa zuwa ga dan qaramin cute pink lips din ta ,
data turo shi gaba kadan kamar zatayi kuka , a hankali ya fara qoqarin bata kiss din dae_dae
lokacin da tayi juyi ta chanja 6angaren data kwanta

Seya janye jikinsa da sauri gudun karta tashi yana murmushi , yana tunanin duk lokacin daya
ta6a bakin nan yasan akwae rigima ranar .



.........Washe_gari qarfe 12:00 tana zaune a parlourn cikin rashin sanin abinyi tana jiran
dawowarsa kasancewar ya fita ne

Se taji ana knocking din door , da mamaki ta kalli qofar tana mamakin abinda ya saka shi
knocking din qofa yau , bayan yana da key a hannunsa

Mamakin nata ne ya katse sanda taji ana sake knocking din

A sukwane ta qarasa qofar , tunda tasan babu wanda zezo gidan nan idan bashi ba yasa kawae
ta bawa kanta amannar shi ne , dan haka ta bude qofar kafin ta kalle shi ta juya cikin parlourn

Se dae me ? A tsakiyar parlourn itama ta tsaya tana kalle kalle , sanye take cikin doguwar riga
baqa wadda take iya gwuiwarta , ta zubo da milk din gashin da bashi da yalwar tsayi , qafarta
sanye da wani hill shoe shima baqi

Se aka faara kallan kallo tsakanin su

Catherine na mamakin irin baewar kyau da Sanah take dashi , haka zalika ta kaasa gane a
wane yare ko qasa zata ajje sanah din ?

Cike da qarfin halin hali Catherine tace

" Me kikeyi a cikin gidan nan ? Ta fada cikin harshen turanci

Cikin mamaki sanah take kallan Catherine din jin wannan raenin hankali nata , toh taga alamar
tazo da raenin wayo , bari ta nuna mata wajen ta tarar , se kawae ta nemi waje tayi zamanta
tana janyo remote ta fara qoqarin kunna t.v

Catherine ta kufula ta qara fada cikin daga murya

" Hey u young lady ! Me ya kawoki gidan nan ? Ina Arman yake ?

Se a lokacin ta dago ta kalleta , ehh wato baby ya san da zuwanta kenan ? Shine ya saka ta
tazo har cikin gidan nan ? Yanzu rashin son da baby ke mata har yakae ya kawo mata wata

cikin gidan auren ta ?

Seta tashi a hankali sannan ta kalli Catherine tace

" In kin gama haushin naki , ga hanya can ki fita , shi kuma wanda kike nema din be kamata
kizo nan kina nemansa ba , kamata yayi kije inda kuka saba haduwa ba cikin gidan nan ba .

" Heyy ! Koma wace ke kar kiyi qoqarin shiga rayuwar Arman , otherwise I will kill u " ta fada
sounding seriously

Sannan ta dora da

" Zan tafi amma ki sani zan dawo , idan har baki rabu da lurv ba ! Ni Catherine se naga bayanki
" daga haka taja tsumman qafafuwanta ta fita daga dakin


Wasu qwalla sanah taji sun tarar mata a idanu wanda cikin sakannin da basu wuce 3 ba suka
fara tsere a kuncinta

Baby ? Anya kuwa ? Menene ya hadashi da mace ? Macen ma irin wannan ? Meyasa yake
qoqarin tozarta ta ? Meyasa yake so yaci mata mutunci ? Mace har cikin gidan auren ta ? Tazo
tana mata kashedi ? Tabbas baby ne ya bata fuska , in badan haka ba , ba zata zo ma har cikin
gidan ba
Se kuwa ta sake fashewa da kuka hadda sheshsheqa

Ita ba komae ne ya sakata kuka ba , se yadda mamama da daddy suka basu tarbiyya amma
gashi baby yayi fatali da wannan tarbiyyar , ashe in yazo wata qasar mace yake kawowa gidan
? Meyasa baby ya dauki wannan dabi'ar ? Ga qarin zubar mata da mutunci da yayi shine yiwa
budurwar tasa kwatancen inda yake zaune babu kunya ba tsoron Allah inda yake zaune ta
matarsa ta sunnah saboda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0