Showing 18001 words to 21000 words out of 40131 words

Chapter 7 - A Tunanina Complete Book By Safiyya

Safiyya   

01 Jul 2026

133

d'aura aure gobe.
"Nan da lokaci k'ank'ani zan iso, don haka kada kiyi barci, kijirani, kuma kimin girki mai sauk'in
nuna kafin in iso, bai jira cewarta ba ya katse kiran yanajin wani nushad'i aransa, mai makon
k'uncin dake damunshi duk inyatuna da batun auren.

Eshat sarkin sa ido tanaganin tamik'e zata pita, ta duro itama tabiyota bayanta.

Su biyu a kitchen sai aiki sukeyi, suna hira kad'an kad'an.
Mamie tasamesu, agogo tafara kallo taga k'arfe d'aya saura na dare.

"mikukeyi har yanzu bakuyi barci ba?
Ad'an zabure suka juyo, domin basuji motsinta ba sai dai maganarta sukaji.

"Yaya Deen mukewa abinci, yace yana hanya.
Cike da kakabi mamie tace"Allah ya shiryaku, ace duk abincin dake gidannan arasa wanda
zaici inya iso saikin shiga kitchen da uban darennan baku tsoron almatsutsui.

Cike da dariya tace "wallahi mamie munfi k'arfin shaid'anu, "uhmm naji Allah dai yak'ara
tsaremu "Amin 'suka amsa.

Coffee ta had'awa Abba tafice tabarsu suna k'ok'arin kammala girkinsu.

2:00am ya iso, suna zaune apalour zaman jiransa.

Eshat charting takeyi da hubbynta yayi da Jamee ke free call da oga jameel, wacce bayan
sungama girki ta iso, ita kuwa sophy barci keson d'aukanta, ta kwanta abisa Cushing.

Ahaka yasamesu, alokaci daya ya d'imauce da ganin mai kama da lil sis d'inta, domin eshat duk
yadda sophy tayi nasa kaya tare da parking na sumarta shi tayi, 9t were ma irin nata tasa
banbancin colour ne kawai.

Ganin yakasa k'arasowa ciki, yasa sophy isa wurinshi tajawo hannunsa zuwa dinning area.

Yanayi mishi sannu dazuwa su Jamee suka k'ataso

Sosai yake duban eshat yana jiran k'arin bayani.
Itako sai murmushi take mishi domin bak'aramin kwar jini yayi mataba.

Tayi saving d'insa.
Ci abinci barrister nmu, sai inyi maka bayani.
Kai ya gyad'a tare dayin bismillah yasoma aikawa da tumbinsa hakkinsa.

Barr yasha mamaki dayaji k'anwar ustax ne, wai babansu d'aya.
Ak'asan zuciyarsa yace anya ba tsintarta suma sukayiba, kamar yadda muka sami lil sis ba?
Kai ina da ja akansu kam, amma bari muga zuwa wayewar gari.

Yayi musu sallama tare da godiyan girki yashige room d'insa, suma sama suka yaye agajiye
idanuwansu cike dajin barci.

Daf da subahi sophy ta farka agigice saka makon mufarkin da dayi wai ita da mamie tare da
barr suna ta kuka anrasa mai rarrashin wani cikinsu.

Tayi addu'an falfawa daga barci sannan ta shiga toilet ta d'auro arollah tasoma nafila har aka
kira assalatu, lokacin Jamee da eshat suka tashi.

Tana sallame sallar subahi ta bingire a bisa sallayar, barci mai dad'i ya kwasheta.

*Mrs j moon*
[4/21, 3:58 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*
*31 to 32*
*©Safiyya*

*Gaisuwace agareki my sis Zainab vc, ubangiji Allah yayi Rahama ga Boy Al-Amin Allah yasa
majik'an musulmai ne. Allah yabaku dangana da juriyan rashinsa Ya shafe zuciyarku shafan
musulunci, Alfarmar Manson Allah SAW Amin*í ½í±í ¼í¿»


Sophy tasha barci mai yawa sabida ji take kamar barcin dare takeyi, sakamakon dad'in dataji
yayin barcin.

Misalin k'arfe sha biyu da minti arba'in wato daya saura, ta tashi.

Koda tabude idanunta bakinta d'auke da addua.
eshat tayi arba da ita zaune agefenta taci uban kyalliya sai k'amshin humra takeyi mai
dad'in shak'a.

Saidai kallo d'aya tayi mata tagano yayi kuka domin idanunta sun tasa kad'an kuma sun rage
fari ba kamar jiyiba

Murmushi tasakar mata tare da tanbayar ta ina beasty?
Ta kauda kai, idanunta suna shirin zubo da ruwa.
Azabure sophy ta mik'e zaune, takamo hannun eshat tabud'e murya sosai tace "ina
beastyna nace!!?

Ahankaki eshat ta amsa "taje gidansu, domin anfiso a d'aurawa mutun aure yana cikin gidansu,
sabida da haka tana can, amma nasan tana daf da shigowa yanzu.
Ahankali tasaki ajiyar zuciya tare da sakin hannun eshat.

Tamik'e tashiga bayi tahad'a kayan k'amshin na wanka.

tashiga ruwan tasoma gabatar da wankanta tana lunshe idanu domin k'amshin yayi mata sosai.
Had'in k'amshin Aunty Khady k'amshi kenan Wanda ta kawo mata gudun mawa hhh lol.

Ta d'au lokaci mai tsawo sannan tafito.
Eshat ce jingine a allon bed ta runtse idanu hawaye na zurara mata tamkar an bud'e tap.

Asanyaye sophy ta zauna gefanta, tasa hannu tana share mata hawayen, ta bud'e idanu tasa
karwa sophy murmushi tana rik'e hannunta.
Sohy ta had'e fuska, tace "kinga sis banson haka, inzaki fad'amin mikefaru kifad'amin bawai

kiyi ta kuka ba tam.

Eshat ta jijjiga kai, kamar zatayi magana sai kuma ta rungumeta tsan tsan wanda saida sophy
ta saki d'an k'ara tana cewa "ke!! ni sakeni kada ki ballani kiyiwa swt ustax d'ina illah.

Eshat ta saketa, tana goge fuskanta, tanashirin magana barrister ya turo k'ofa.

Eshat ce ta amsa mishi sallama tana dariya k'asa k'asa kuma ahankali ta furta "sannu da zuwa
Angonmu.

Cikin murmushin farin ciki ya amsa "yawwa k'anwarmu.

Sophy ta saki baki tana kallobahi, tana kuma tunanin wa yaya Deen ya aura kuma yaushe?

Ta kai dubanta ga reshi.
Yaci uban kyalliya cikin wani tsadadden yadi milk da ratsin golden, anyi mushi d'inki 'yar ciki
da babbar riga sai hulansa da ya kafa, bak'a, sajennan da d'an jemunsa sunsha gyara sai kyalli
sukeyi.

Ganin ya tsurawa cinyoyinta Ido yasa ta tuna da ba kaya jikinta sai d'an k'aramin towel, wanda
iyakacinsa cinyarta.

Ta tura baki ta jawo bargo tana kici kicin rufa.
Barr ya fizge bargon yayi cilli dashi gefe alokaci d'aya ya rungumeta tsan tsan a k'irjinta, yasa
hannunsa yana shafa tsakiyan bayanta yana kuma sunsuna sumar kanta zuwa wuyanta, tana
ta kici kicin kwace kanta, ta jiyo eshat tana tafi raf! raf!! raf!!! Da kuma k'arfi, tana cewa
"soyayyada dad'i wallahi Allah yabarmin Ku cikin kariyansa asha Zuma a more.
Sophy ta zare idanu cikin rawar murya tasoma cewa "yaya Deen karufamin asiri ka sakeni,
kada wani yashigo yaganmu haka, kasan bai daceba abinda kakeyi, duk da muna shak'ik'an
juna amma hakan haramun ne.

Mai makon yasaketa saima k'ara rungumeta yayi da kyau, tanajin yadda zuciyarsa ke bugawa,
ita kam jikinta rawa yakeyi.

Ganin yak'i sakinta kawai sai tasakar mishi kuka mai sauti.

Da sauri yasaketa, ya cire hularsa tare da babbar rigansa, tana son tashi ta gudu amma ya
danne mata cinya da gwaiwan hannunsa.

Cikin kuka ta kalli eshat wacce ke zaune bisa stool tana doka murmuahi, tace "keko sis kina
kallo ana cimin mutunci kinkasa cewa komi saima murna kikeyi, baki ko kishin d'an uwanki,
akema wasa da jiki, taja hanci sannan taci gaba "to wallahi alhaki awuyanki tunda kina kallo

kike marawa shaid'anci baya.

Eshat ta saki dariya tanacewa "lallai twins sis manya, yanzu mijin naki kike cewa na shaid'anci''
uhmm to kuwa kiyi gaggawan tubawa Allah ko ki fad'a halaka yanzu yanzu kuwa.

Batasan sadda ta ture barr ba ta isa wurin eshat ta cukumota tana fad'an "kina haukane da zaki
ce yayana uwa d'aya uba d'aya kice mijina? Ehye!!!!

Barr ya jawota ya zaunar, cikin sanyin murya yasoma magana "lil sis kiyi hak'uri tare da
tawakkali, domin haka k'addaranmu take tun farkon samuwanmu, Allah ya rubuta a lauhun
mahfuz cewa sai munzamo mata da miji.
To gashi Allah cikin I...... Azabure ta mik'e batare da tagamajin magar ba.
Tayi hanyar fita, cikin sauri eshat ta tareta"jibi yadda zaki fitafa, tureta tayi tana jifanta da
wani mugun kallo.

Batabi takan kowaba acikin parlourn Wanda yakasance shak'e da mutane 'yan biki cikinsu har
da doctors tare da nurses mata 'yan asibitinsu, sunzo tayata murna.
Sister Ummu nadrah tare da Aisha (mmn Ramla)
Suna cikinsu hhhhh lol.

'Dakin mamie ta fad'a bako sallama.

Binsu tayi da kallo sanda tashiga, har ta dire kan mamie wacce take cikin farinci.

Ta fad'a jikin mamie tana cewa mamie kina ina kayi wannan kwamacalan.

Tasaketa ta tsura mata idanu bako k'ifrata, tace "mamiena fad'amin gaskiyan zancen, shin wai
and'auramin aure da yaya deen?
Jim mamie tayi sannan ta amsa "kiyi hak'uri yarinyar mamie haka Allah yanufa barrister
shine zai zamo abokin rayuwarki ma'ana mijinki.

Wani k'ara tasaki mai sauti tare da dafe kanta tace "no!!!! Bazai yuwuba, yayana najini shine
mijina! Kai haba awani duniya akeyin haka mamie? Ta zube bisa gwaiwoyinta tana kuka sosai.

Sai kuma ta d'ago tana kallon mutanen cikin d'akin.
Dada fanna ce yayar Abba sai hajiya Fatima k'anwar Abban ustax agefenta wata farar mace
ce, mai tsananin kama da eshat, ba tantama mum d'in tace.

Tamik'e tasoma ja dabaya, tana cewa "to afad'amin cikinmu waye d'an cintuwa?
Farar matanta ta amsa "kece baby Zarah.
Idanu waje tace "waye Zarah? Wannan karan dada fanna ta amsa "kece, Nana Safiyya
ayanxu amma ada fatimatul zara'u sunarki kafin k'addara ta gifta na bacewarki.

Zuwa lokacin Jan numfashi take dakyat, cikin sark'ewar murya tace"yanxu ni bani da uwa balle
uba? nid'in 'yan kwararoce dama? Mara asali!!? Wayyo kaicona!! Ya salamu kakawomin agaji!!
Tayi baya zata fad'i sakamakon jirin da ya kwasheta.

Barr dake tsaye abayanta yatareta, yana jijjigata amma ko motsi batayiba.

a gigice eshat tasaki kuka, yayin da su mamie sukayo kanta.

K'awayenta doctor sukayi k'ok'arin bata taimakon gaggawa, kuma cikin ikon Allah numfashin
yadawo bugawa normal.
Akayi mata allura, tasami barci.

Kowa yafice domin ba'ason hayaniya ya dameta, barr ne kawai akabari agunta cikin room d'in
mamie.

Ya k'ank'ame hannunta yana tunanin ko inta farka zata amshe shi amatsayin miji?


*shin wai ma miya farune da har aka gano ustax babansu d'aya da sophy?*

*kubiyoni zuwa ranar Monday*🙊








*Mrs j moon*
[4/24, 12:06 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*33 to 34*

*©Safiyya*

Hajiya Sadiya ce zaune tare da ustax saif acikin d'akinsa, Wanda aka ware masa cikin gidan
uncle d'insa Alhaji Adam kuma surukinka Abban su nafisat.

Wani magana suke tattaunawa mai mahimnanci, sosai suka d'auki lokaci mai tsawo suna nemo
mafita.

Hajiyan tamik'e tana dariya ta ware hannunta alamun dak'uwa tare dacewa "Allah my boy
bakada kunya, ya sosa sumar kansa ya amsa "Allah mum ina da kunya sosai kamar mace.

Murmushi tayi kawai batare da tace komi tasakai zata fice, ustax yace "yawwa mum ajiyemin
wannan emblem d'in, yana magana tare da jawo durowar gefen gadonsa, abin mamaki emblem
d'in yace d'auke inka ganni, yayi ta nemarsa baiganiba abinda ya haddasa shi fidda komi na
cikin durowar.
Wani photo ne yaja hankalin mum d'in wanda garin binciken da ustax keyi ya watsoshi tare da
'yan uwansa.

Photon take kallo cike da mamiki, taya akayi saifullah ya d'aukeshi batare da tasaniba.

"Yawwa mum gashi nagani, ashe acikin sip nasa shi. Jin tayi shiru yasashi kai dubansa bisa
abinda yad'auke mata hankali.

Matsowa yayi sosai domin ganin pic d'in daya had'au hankalinta haka
Dariya yasaki kad'an yana sosa k'yeyarsa, "mum kina kallon surukarki ce sadda take jaririya?
Baijira amsawar taba yaci gaba"wallahi inason photon sosai, watarana muna hira nabuk'aci
tabani album d'inta amma wanda take baby ingani, to shine na d'au wannan photon sabida
yayimin kyau sosai, ganin tayi nayi tayabashi shine take fad'amin yayantama yanason pic d'in
sosai domin shi har enlargement yasa akayi mishi yasa a room d'insa, to nima zanyi enlarge d'in
sa insa a parlourn mu.

K'uri tayi mishi da danu har yakai k'arshen zancensa.

Ta dubeshi cikin sark'ewar murya "biyoni tace dashi tare da fice da sauri, shima bayanta yabi
da sauri gabansa na fad'uwa.

Sunyi jigun jigun a babban parlour n gidan su sophy.
kowa zuciyarsa nakai kawo, domin sanda mum ta isa da pic d'in batayi musu
bayaniba sai dai cewa da tayi maza maza atashi atapi gidan surukan saif koda suka nemi k'arin
bayani tace in sunje ta tabbar da zarginta zasuji,
amma tabbas da akwai matsala.

Mamie, Abba tare da barrister sai Abban jamee d baffan mamie, sukayi sallama sukashigo tare
da samun wuri suka zauna jikinsu duk asanyaye.

Alhaji Adam ya kai dubansa kan hajia sadiyya yana mai cewa "ke muke saurare hajiya, taja
numfashi sannan ta fidda photo tare da d'agashi tana cewa"wannan photon nakeson sanin aina
aka sameshi?
Tak'ara dacewa don Allah don sonku da ma'aiki SAW kada kuboyemin komi, domin inaji ajikina
babyn cikin pic d'in 'yatace da aka nema akarasa ranar da ta kwana uku aduniya, tayi jim
sannan ta d'ora da"inko itace to babbas aure yaharanta tsakaninta da saifullah sabida ubansu
d'aya.

Parlourn ya d'au salati tare da sallallami.

Hajiya Fatima ta karbi pic d'in tana kallo aiko tace "wallahi fatimatul zara'u ce, ga d'ankunnen da
nasa mata tare da zobe kai Allah itace ma ba tantama.
"Allah mai iko ni fatie.

Palourn ya d'au shiru zuwa can mamie tayi k'arfin halin amsar picture tare da kallonsa, gabanta
ya k'ara sakin dam!!!

Kayan dasu tsinci sophy sanye dashi a jikinta shine ranar dasuka tad'a mata suna suka sanya
mata akayi mata picture domin tarihi.

Cikin sanyi mamie ta labarta musu gaskiyan lamari.

Allahu Akbar!!! Mutanen parlourn sukad'au kabbaran

Atake parlourn ya kaure da murna tare da jajantawa juna saikuma tarin godiya daketa yiwa su
mamie da sa albarka tare da addu'o'in gamawa lafiya.

Atake Abba yazartar da hukunci a d'aurawa sophy aure da barrister, kowa yayi na'am da hakan.

Amaimakon abari zuwa azahar a d'aura sai kawai baffan mamie yanemi da ad'aura yanxu tunda
mutane sun had'u.

Hakako akayi ana d'aurawa aka zarce da d'aura na Jamee da jameel sannan akayi na ustax da
nafee duk ak'ofar gidan su sohpy akayi.

Saibayan angama mutane sukejin labarin yadda lamari ya juya.

Koda nafee tasami labari tayi ta rawa da murna wai tayi bai bai da zama da tunkiya. ( kunjimin
'yar buhu wai kishiya ce take cewa tunkiya ooo)

Duk bidirin da akeyi sophy na kwance na Saharan barcinta mai cike fa mafarkai barkatai.

Bayan tashinta taji bak'on labari wanda yajefata cikin rud'ani


*kuyi hak'uri da wannan yarona baya da lafiya, ina baran add'o'in Ku please*í ½í±í ¼í¿»




*Mrs j moon*

[4/25, 12:01 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*35 to 36*
*©Safiyya*

Ahankali ta motsa, zuwa can tabud'e idanunta, d'akin yayi duhu kad'an alamun anrage hasken
fitillar d'akin kuma dare ma yasoma shiga lokacinsa.

'Dakin tabi da kallo, can ta hango barrister zaune hannunsa rik'e da AL-QUR'ANI k'asak'asa
takejin fitar muryansa, cikin k'ira'a mai dad'i.
Ta yi shiru tana saurarensa,zuwa can tamik'e tashi ga toilet.
K'aran rufe toilet d'in, ya ankarar da barr tashinta.

Bata jimaba tafito d'aure da towel, ta isa inda mamie ke jera dogayen rigunar sallarta, ta zura
wata 'yar madai daiciya tasa dogon hijab ta fuskanci alk'ibla.

Sallolin da ake binta ta gabatar sannan ta dora da sallar magrib.
Bata tashi wurinba saida ta sallaci isha'i tayi safa'i da wutri tayi addu'a mai tsayi sannan ta
shafa tare da mik'ewa.

Rigar ta cire ta maida inda ta d'auko.
Ta zaune bisa stool agaban mirror d'aure take da guntun towel d'in.
Cinyoyinta duk awaje.

Duk abinda takeyi Idanun barr nakanta, itama tasan yana kallonta amma ko kallon inda yake
batayiba, hasalima ita haushi keba.

Lotion wai k'amshi ta lakato tana murzawa zata Shafa, barr ya dako zuwa wurinta zuciyarsa
cike da fargaba.

K'irjinsa ya kwantar abayanta ya dank'e hannunta, yana kallonta ta cikin mirrorn.
Wani yerrr taji, ya sassana wuyan zuwa sumarta, tuni yaji wani abu ya tsarga mishi har tsakat
kansa,bugun zuciyarsa ta k'aru, ya k'amk'ameta sosai yana wani fidda numfashi.

Itama numfashi ta sauke da sauri, ta bude baki kamar batason yin magana tace "uhmm ya
Deen ka sakeni inyi shafa, ahankali ya saketa ya sa hannun cikin lotion d'in ya lakato tare da
murzawa, yasoma shafa mata abayanta, tanajinsa yaci gaba da shafa mata, awasu sassa
najikinta.
Idanunta ta lumshe tanajin wani abu nataba mata zuciya.
Ya gangaro zuwa k'irjinta, yana k'ok'arin kwance mata towel, da hanzari ta rik'e masa hannu,
cikin sark'ewar murya tace "kabarshi haka, nagode.

Yayi banza da ita yana cigaba da jan towel d'in ita kuma ta rik'e kam.

Yayi murnushi mai sauti, ya matso daf da kunnenta yace "lil sis bafa abinda zaki boyemin
ajikin ki, sabida komi na sani.
Idonta arufe ta amsa" Allah bakomi ba dai, dariya yasaki yana cewa "ina kallon abin kamar
yanxu nake yimiki wanka tare da Shafa, kuma in samiki kaya sannan in goyaki kiyi barci.

Shiru tayi mishi, ya gara mannewa ajikinta ya sassauta voice d'insa yana cigaba dacewa "lil sis
don Allah kisoni kamar yadda nake sonki, tsawon lokaci, tunkina zanin goyo nake sonki har
zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login