Showing 39001 words to 40131 words out of 40131 words

Chapter 14 - A Tunanina Complete Book By Safiyya

Safiyya   

01 Jul 2026

132

gefen k'afafunta ta sunkuyar dakai tace "mamie barka da war haka, "barkanmu
yarinyar mamie dafatan bakya zazzabi ko? "Inayi amma da dare shimad'in ba sosaiba "to
sannu Allah yaraba lafiya, ta zare Ido tace "Allah mamie bani da komi ni kitambayi yaya Deen
kijima.

Barr ya ja gemunsa yace "baruwana nikam, nasan dai bakiga bak'onki ba watan jiya dana yau
Tayi mishi k'uri tana tunano yaushe tayi last period natama. Take ta tuno wata biyu kenan, ita
sam ta manta ma da wani mensuration period ma.
Ta soke kanta jikin mamie tace "Allah mamie sharri ya kemin nibanda komi "uhmm yarinyar
mamie miyasa kikeson boye mana abin farin cikinmu? Ta kwabe fuska kamar zatayi kuka "Allah
mamie ban saniba nima, murmushi mamie tayi tare da cewa "amma ke wata iriyan nurse ce
haka mara kula? "Uhmm nifa mamie... Dasauri barr yatareta "sweetie kada kice komi, nadai
kusa zama baba kawai, hararansa tayi sai kuma ta cukume mamie tana dariya, duk kansu
sukasa dariyan suma cike da farin ciki.

Koda Abba yadawo, Bahijja ta fesa mishi, yayi murna sosai yayi addu'an Allah raba lafiya.
Yayin da sophy tayi ta nok'e kai wai ita kunya.

Adaren taje gidan umma inda beasties nta take.
Sabida tazo gidan umma ciwon nak'uda ya kamata ko kafin a fidda mota faya ta fashe, sai
kawai aka kira nurse a kusa dasu takarbi haihuwan.
To shine akabarta tayi wankanta anan.

Sophy tunda ta rik'e baby sai kallonsa takeyi cike da sha'awa.
Inta kalli jamee sai ta kalli baby sai kuma ta kalli jameel wanda suka tarad agidan, zuwacan
sai tasa dariya.
Jamee ta dallah mata harara "to uwar sharri mikike tantancewa? Cike da dariya tace "ina duba
wa yafi wani son abin lokacin yin cikin, sabida naji ance in yaro yafi kama da d'aya acikin
iyayensa to wannan yafi kwazo yayin samuwarshi.

"La'ilaha illallahu!! Jamee taja salati tana kama haba, tace "Beastie yaushe kika zama mara
kunya haka? Su jameel suka kwashe da dariya har da sophy, ta kallo barr tace "kinganshi nan
shine ya lalatani "baruwan yaya Deen kedai dama can kunyar gulma ke gareki, ta kaimata duka
abaya tace "aike kika koyamin "dalla ni baruwana "tasaki dariya tana kallon barr tace "zumana
Ai ruwanta na jikinta ko? Ya kauda fuska cike dajin kunya yana jinjina rashin kunya lil sis data
koya yanzu.

Jamee da jameel suka soma yi mishi dariya, tana sabe da babyn aka fad'anta ta bi hanyar fita
zuwa parlour tana cewa "baby dai yayi kama da babansa, wannan yanuna Beastie bata da
k'wazo a tafiya zuwa birnin dad'in.

baki bud'e barr yabi bayanta da kallo, yayin da jameel ya kallo jamee yace "kindai ji k'awarki
tagano ke lazy ce a turaka, harara ta dalla mishi barr kuma ya tallabe mishi k'eya

"Allah lil sis tazama sai addu'a kam. "Aikuwa dai.

Dare yayi sosai sannan suka wuce gida.
Adaren ranar kam barr ya kashe bakin sophy murus da salon soyayyar sa.

Washe gari aka rad'a suna yaro yaci sunar Abban jameel suna kiransa da Baffa.

Sophy k'irjin biki akwati d'aya ta cikawa mai jego da kaya tare da na baby masu kyau da tsada.

Yawan barcin datake yasa jamee ganowa tana da ciki aiko tasata gaba da tsokana tahanata
barci a bed d'in dole ta tashi takoma d'akin umma tashige bedroom ta kure ac ta bage sai
kwasan barci takeyi domin daren jiya barr baibarta tasami barcin kirkiba.


Satinsu biyu sukayi haramar tafiya mai duguri tare da mamie bikin eshat yazo saura sati d'aya
yarage.

Barr ya wuce sai ana saura kwana d'aya zai halarta.

Biki ya k'ayatar sosai, amarya ta tare gidan mijinta lafiya yayin da sophy tacigaba da rainon
cikinta cikin kwaciyar hankali.





*Bayan shekara bakwai*
Sophy zaune a parlour tana koyawa wata kyaky kyawan yarinya lissafi, wanda zatakai
shekara shida sosai yarinyar take fahimma, wasu yara maza 'yan biyu suka shigo tare da barr
Deen wanda su kuma zasu kai shekaru hud'u.

Dasauri yarinyar ta je ta rungume barr tana cewa "oyoyo Abbiena ya d'agata sama yace "my
sweet insaf ya katatu dafatan kinyi assignment d'in da kyau "Alhamdulillah Abbie, mun gama
tare da ummie, "aha yayi kyau.
Fist born d'insu kenan Aisha ta kwarar mamie.

Ya juya yana kallon sophy Wanda hassan da hussain suka kwanta ajikinta suna yi mata surutu

Ya d'aga mata gira yace "yadai madam ba ko magana ko dai labour kikeyi domin naga kina cije
baki.
Murmushi tayi tace "to sannu doctor mai gani har hanji yamatso ya rik'e face d'inta yana son
had'a bakinsu ta kauda duska, da Ido tanuna mishi su insaf wad'anda suka zuba musu Ido ya
saketa yajasu zuwa d'akinsu sai da ya tabbatar sunyi barci ya topesu da addu'a yaja musu
k'ofa.
Sophy tana tsaye gaban mirro tana murza humra ya iso baiyi wata wataba ya d'aga ta cak zuwa
bed, cikin shagwaba take cewa "zumana kayumin hak'uri hakanan nafa tsufa, inbaso kake katso
kanomin labour ba

"mmn twins ki hak'uri taimakon ki zanyi fa, ta kai mishi dukan wasa ak'irji tabu'e baki zatayi
magana yayi gaggawan kullewa da nashi tuni wasan yasanja salo zuwa aikin lada, suka lula
garin maji dad'i.

*Tamattttt bi hamdullah*


*ALHAMMDULILLAH ALA KULLI HALIN*

Anan nakawo k'arshen labarin *ATUNANINA* labarin k'irk'irarrene ba'ayi don wani ko wataba.
Abinda yayi daidai ayi amfani dashi na a kasinsa kuwa ayi watsi dashi.

*ina rok'on Allah yayafemin kuren danayi ciki*


*YABO DA JINJINA AGAREKI YAZAMA DOLE*
*BEBEELO*
*domin da gudun mowanki labarin yasami kammaluwa,na gode sosai Allah yabar k'auna Amin*

*INA ALFAHARI DA KU K'AWAYENA NA KWARAI*
*My jamee(Aisar) My sis(Zainab vc)k'anwata (Mamie Waru) Aunty Khady(k'amshi) Yaya sadiya
(mmn Ihsan) Sweet Hameeda(Haermeebrah) Allah yak'ara dank'on zumunci Amin*

*BAN MANTA DA KUBA*
*'Dau kakin Al-umman gidan Sophy And VC novel, Safiyya na yi muku godiya tare da
yaba, Allah ya saka da alkhairi amin*


*All groups da labarin *ATUNANINA ya lek'a ina gaidaku tare da yimuku fatan gamawa lafiya
Allahumma Amin*

*sai kuma Allah mai komi mai kowa yasake had'amu a sabon littafina bayan sallah mai suna
Wat....* banfad'aba😃


*LOVE U ALL MASOYANA*😘😘














*Mrs j moon*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login