Showing 1 words to 3000 words out of 101327 words
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: AFIYYA
One (Free page)
✍️ Ayshatuuu
RINGIM, JIGAWA STATE.
Taken mu a kullum shi ne " Jinin dabo ringimgim da ka garin karamci" mun amsa wannan taken
Dan mu mutane ne masu karamci da dattako, masu riko da alada, garin me ruwa, me kifi
Wanda suka San kansu a wajen noma. Bari na barku hakan kada kuce na Koda garin mu da
yawa, believe me idan kuka je ringim zaku San ba karya nake ba.
Sunana Amina Abubakar Salihu, Amma anyi min lakani da AFIYYA kasancewar na ci sunan
kakata data haifi babana ne. Kakana Alhaji Salihu shi ne wazirin sarkin ringim kunga kenan na
hada jini da sarauta. Na kanyi tunanin Anya infertility wato rashin haihuwa baya running cikin
zuriar mu? Ko Dan ba hakan ya kamata nace ba , zance tabbas infertility na yawo cikin familyn
mu. Dukda haihuwar ana yinta sede batada yawa, da anyi daya shikenan, se ta tsaya. Hajiya
Amina ita ce kakata, asalinta mutuniyar Ganjin gebi ce. Ita kadai ce matar daya aura Bai Kara
Kuma wani auren ba. Yaranta su biyar ne. Mahaifina Abubakar shi ne babba se Wanda ke bi
Masa kawu Sa'idu, se Yar tsakiyar su Mummy Maryam, me bi Mata se kawu Ahmad ana ce
Masa Tijjani autansu Uncle Salihu amma Babawo ake Kiran shi, my very own savior.
Kamar yadda muka sani lokacin da westerners Suka kawo karatun boko an fara dauka ne daga
gidajen masarautu Dan a bada misali ga sauran alumma su biyo baya. To mu dinma hakan ce
ta kasance lokacin da yaran sarki zasu tafi se aka hada da Babana da Kuma Kawu Sa'idu aka
kaisu. Hajiya Bata so saboda tana ganin kamar wani Abu ne ake son koyawa Yara Dan a dauke
hankalin su akan turbar musulinci. Da kyar aka samu akai convincing dinta ta amince Suka tafi
makaranta, sede kawu Sa'idu fur yaki idan an kaishi se ya gudo ya tafi gidan Gwoggon su dake
kyarama, duk kuwa da tsakanin Ringim da kyarama akwai tazara Amma hakan zai gudu. Idan
mahaifina ya dawo yayiwa Hajiya complain tayi fada Amma a banza tunda ita Baso take ba
Amma tana ganin Dole tayiwa waziri biyayya, Kuma ba zata so yayanta Suki Masa biyayya ba.
A haka aka Gama karatun Babu abinda kawu ya tsint, da waziri ya fahimci hakan se kawai ya
kaishi kasuwa yace gwara ya nemi abinyi kada ya ja Masa magana a gari. Nanma Babu wani
abinda yake illa yaje yayi shawagi ya tafi yawon shi, sede a wañnan shekarar baya ga waccan
budurwar baya ga gidan wane, Kuma kowa saboda darajar waziri yake kyale shi.
Daddy a kings college dake Lagos anan yayi secondary School din shi, Yana gamawa aka
bashi offer Amma se yaki karba akan shi fa se yaje ya Karo karatu. Hajiya Babu yadda batayi
dashi ba Akan yayi aure Amma yaki. Haka ta kaishi Kara wajen fulanin sarki se ta nuna Mata
itama fama take da nata dan maslaha kawai su kyalesu suyi masu addua.
Mahaifiyata sunanta Halima, ban taba ganin ta ba, asalin ta Yar shehun borno ce, akai alliance
Akan zaa hada auren yayarta da Baba Mustapha Dan sarki Wanda yake saan Abbuna ne Kuma
tare suke karatun acan UK. Yayar ta ita Kuma Mariya, da zasu zo aka saka mamana ta Mata
rakiya, bayan an gama komai se sarki yace ai tunda Halima tazo se a hadata da da Abbuna
tunda Suma Yan uwa ne. Haka akai aka daura aure mazan na can wata duniya, kowanne se
gani yayi an aika Masa da matar shi. Abbu yace min Bai taba ganin mace kyakyawa kamar
mahaifiya ta ba, me hakuri da juriya irinta ba. Ya fada min zamansu Zama ne sukai Akan
fahimtar juna da soyayya.
Shekara na zagayowa Ummin Istanbul kamar yadda muke ce Mata ta haihu Amma mamana
shiru ko Bari babu, wannan haihuwar daidai Gama karatun su Suka dawo Nigeria, precisely
Ringim, sosae aka tarbesu aka nuna jin dadi musamman haihuwar Ummiey ta dada musu.
Anan suka cigaba da rayuwa, Abbuna ya samu aiki a Lagos ga damuwar da mamana ta saka a
ranta na rashin haihuwa se aikin yazo Masa da Dadi yasan zata Dan ji Dadi idan tayi nisa
dukda bawai takura Mata ake ba, Hajiya me tsananin Kara ce Kuma ta fada min Bata taba
suruka ta gari ta kirki me Kara da kawaici who owns a golden heart irin mahaifiyata ba. Baba
Mustapha da Ummiey se Suka bar kasar gaba daya, a hakan rayuwa ta cigaba da tafiya.
Bangaren Kawu Sa'idu yayi aure matar shi Zinatu, a yawon shi ya samo ta Yar Kano ce Muna
kiranta Ummaah, a yanzun bazan ce muku komai akanta ba Amma nan gaba kadan zaku gane
irin rawar data taka wajen lalata rayuwata, idan Babu Ummaah cikin labarin AFIYYA to labarin
bashi da amfani. Kawu ba karatu yayi ba , shi ba Sanaa yake ba sede standing order da
Abbuna yayi Masa duk wata akwai amounts din da yake bashi, dukkan yayan shi Abbuna yake
daukar nauyin karatun su. Shi ne kadai Wanda ya haihu da yawa, Ina tunanin kamar ma ya riga
Abbuna yin aure. Danshi na farko sunan sarkin Ringim gareshi shi ne aka Kiran shi Baba, na
biyu shi ne Yaya, sunan waziri gare shi, bazan taba manta Yaya a rayuwa ta ba, mutum me
alkhairi Wanda yaci sunan me sunan shi. Ta uku sunan Hajiya ne da ita ana kiranta Mino, se
Siyama se Hafsa. Banda saa a gidan na girmi Hafsa Siyama ta girmeni. Haka yaran shi suke.
Mummy Maryam tana auren daya daga cikin yayan sarkin Ringim tana zaune a NY yarinyar ta
daya Rukayya muna kiranta Rooks. Kawu Tijjani yana Kano da matar shi Anty Salma, yarsu
daya Basma se Uncle Babawo shi ne a UK precisely a Lancashire yake. Shi Bai ma tana
haihuwa ba.
Abbuna seda sukai shekara ashirin Basu haihu ba, Abbuna yayi kudi,ga ilimi gashi successful
business man Amma Babu haihuwa har ya gaji da zuwa asibiti suka fawwalawa Allah. Se at the
last minute da suka fitar da Rai sannan kamar Wasa mama ta fara laulayi suna zuwa asibiti akai
confirming ciki gareta. Bayan kwana biyu Suka tafi Germany rainon ciki. Kowa yaji labarin cikin
se yayi farin ciki Banda Wanda suke adduar Allah yasa kada ta haihu idan Abbuna ya mutu
gado nasu ne. Saura sati daya a haifeni waziri ya fara rashin lafiya kamar zai mutu. Dole Abbu
ya tafi Nigeria Dan sadawa dashi, Ashe rashin lafiyar ba ta tashi bace kwanan shi daya da zuwa
ya rasu. Wanann sakon da ya samu Mama se ya sata ta fara labor, dama tasan cs zaa Mata
tunda ta Dade Bata haihu ba. Take aka shiga da ita ot baa fito ba seda sabuwar halitta wato ni!
Seda mukai sati daya sannan Abbuna ya dawo jikinta yayi sauki muka dawo Nigeria, a wannan
dawowar gaba daya Babu wani dadi, Mama taso waziri ya ganni ya rike no kamar yadda yake
Mata nasiha kullum cewar watarana zata hahihu zata dauki danta a hannunta. Se gashi lokaci
yayi Amma baya da Rai. Abbu ya saka min Amina, Mummy Maryam ta saka min AFIYYA
lokacin tanada tsohon cikin Rooks. Mama Bayan zaman makokin ya lafa ta tafi borno seda ta
zubar da wanka sannan ta dawo. Rasuwar waziri ta girgiza mutane sosae nan akazo tunanin
Wanda zaa bawa sarauta kowa ya nuna Abbuna yake so Amma se wasu suka nuna ai baya
Zama balle a bashi, why not Kawu Sa'idu. Shi dinma so yake a bashi Kuma ace Yana cikin
council members na emirate ai yayi gaba kawai. Hakan Bai kasance ba aka bawa Abby shi
Kuma se ya wakilta kanin waziri kamar yadda Hajiya ta fada Masa. Wannan abin ya Kara Bata
ran Ummaah da kawu Sa'idu.
Satin Mama biyu da dawowa muka koma Lagos muka fara sabuwar rayuwa, idan ka kallesu ka
kalleni zaka Yi tunanin ni din jikar su ce ba Yar su ba, Dan sunyi girma ace ni din Yar su ce. Na
samu gata na samu tarbiya na Kuma samu jin Dadi sede Bai daure ba, Allah ya yanke min
hakan ya jefo min wata hanyar da zanbi Dan ya gwada imanina. Shekarata daya Mama tayi
rashin lafiya kwananta biyu a asibiti Allah ya Mata rasuwa.
AFIYYA is not free! Pay through 3091721807, Aisha Hassan kwalam, First bank of Nigeria
(FBN). Send evidence of payment through 09063467258.
Ayshatuuu
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: AFIYYA
Two (Free)
✍️Ayshatuuu
Junaidu sunan shi, mahaifin shi Malam Ibrahim Wanda yake haifaffe Kuma zaunannen Kazaure
ta jigawa. Mahaifin shi babban malami me Wanda yasan alqur'ani da litattafai. Ko Ina zakaji anyi
kwatance da tsoron Allah irin nashi. Sede bawai a malimtar ya tsaya ba shi din manomi ne haka
Kuma Dan kasuwa ne Wanda yayi karatu sosae a ilimin zamani, shiyasa malumtar ma take
tafiya yadda ya kamata. Allah Yana da hanyoyi da dama na jarabtar bayin shi, duk imaninka
baka wuce kaddara,
Matan auren shi hudu, Babbar wadda ita ce uwargida Yar Roni ce Hajja Huwaila, ita ta Haifa
Junaidu Wanda a yayanta shi ne na uku. Gaba daya yaranta biyar. Me bi Mata ita ce Hasiya
wadda Yar nan cikin garin kazauren ce, se ta uku Yar Daura sunanta Fatima, amaryar shi Kuma
Yar wani abokin shi ce ya bashi ya aura me suna Sadiya. Gaba daya yaranshi sun tasar ma
goma Sha biyar. Yadda aka San gidan malamai gida ne Wanda zaman lafiya da kwanciyar
hankali ya yawaita,nan dinma hakane sede idan Mata suka taru Dole akwai abubuwa na kishi
da Dan rashin jituwa. A alaadar gidan tun kafin ka Gama primary zakai izu talatin, kana zuwa
js3 kayi sauka seka tafi boarding ka cigaba do littatafia. Karatu ana idar da asuba zaa fara,
Bayan sallar Isha a daura, Dole kowa se yaje ko ya hadu da fushin malam.
Wasu iyayen sun iya banbance yadda yaran su suke tun daga yanayin kukan su suna jarirai da
Kuma yadda suke muamula da Yara sa'o'insu idan sun fara girma. Junaidu yaro ne me kuka
Yana yaro, kukanshi ya baci, Kuma duk abinda Hajja take ya fara kukan nan se ta katse shi,
Yana da zuciya Dan ko an daura shi a po yace ya Gama baa zo da wuri ba to idan akazo tsarki
zai ce bazai tashi ba. Cikin dare idan ya tashi Shan ruwa kafin a dakko a bashi yayi fushi bazai
karba ba. Wannan halayen nashi yasa ake cewa Hajja tafi son shi saboda gudun zuciyar shi
yasa dukkan attention dinta take Kansa, shima Baban wato malam daya fahimci hakan se
kullum kafin ya fita se yayi rubutu ya kawo a bashi. A hakan ya fara girma har Yana fitowa waje
yayi Wasa da Yara saanin shi dukda ba sosae yake hakan ba Amma duk ranar da ya fita wasan
to se ya daki yayan mutane, a gidan su ma idan kannenshi da yayun shi suna Wasa Yana zuwa
kowa zai kwashe kayan wasan shi idan ba hakan ba ta kansu zai bi ko Kuma ya dinga wurgi
dasu. Kowa tsoron shi yake he's a villain and also a rogue!
Primary aka Kai su Amma baya zuwa se ranar da ya ga dama, shi ne shugaban bad gang na
cikin makarantar kullum rana idan har suna cikin makarantar to tabbas zasu daki wani ko su
sumar da wani. Kullum ana filing complain office din headmaster, har ya gaji ya fadawa Malam
halin da ake ciki. Malam ya dawo gida ya aika a Kira Masa Junaidu, ya shigo a nutse saboda
haka yake, idan ka kalleshi zakaga zallar nutsuwa a tattare dashi Amma idan ka kalleshi ko ka
zauna dashi zaka San Allah ya Masa hallittar nutsuwa shi Kuma ya bijire. Ya tsaya a tsaye Yana
cewa Malam gashi yazo,yayan shi Suleiman ya kalle shi ya kalla Malam sannan yace Masa ya
nemi guri ya zauna, ko kallon shi baiyi ba balle yasa ran zai zauna hakan ya batawa Suleiman
Rai, Yana tashi ya dauke shi da Mari, Amma ko gezau Junaidu baiyi ba se huci kawai da yake
Wanda ke nuna ranshi yayi mugun baci, seda malam ya Masa magana sannan ya tsugunna
shima yadda tsugunna din kawai se yasa kunyi dariyar takaici.
" An kawo min Kara cewar baka zuwa makaranta, idan Kuma kaje kana dukan yayan mutane..."
" Inji wanne Dan shegiyar?"
Ya fada Yana Kara Bata Rai tareda mikewa tsaye, Suleiman ya Mike yakai Masa naushi a take
bakin shi ya fara jini, yasa hannun shi ya lakuto Yana ganin jinin yayi Kan Suleiman ya cakumi
wuyan shi ya fara naushin shi, Malam ya Mike da kyar ya raba su, yana sakin Suleiman ya zube
a kasa saboda yadda ya karbi naushi a jikin shi, tabbas jikin shi ya fada Masa. Malam ya dafe
Kan shi ya kwallawa kanin shi sarki Kira, Babu shiri sukai asibiti da Suleiman. Baa Kara tada
maganar ba Amma Malam ya dage da kaiwa Allah kukan shi.
Tun daga wanann abun gaba me karfi ta shiga tsakanin Suleiman da Junaidu, Kar kuyi tunanin
me sauki basa magana Koda zasu bangaji juna, wannan ya dagawa Hajja Huwaila hankali ya
bar Mata abun Fadi wajen kishiyoyi. Lokacin da ya kusa Gama primary se ya fara Shan taba,
bakin shi ya fara nunawa, ya daina zuwa karatun da suke na Bayan sallar asuba, ya daina zuwa
gaida kowa a gidan, abincin gidan Banda na dare to baya ci. Can wajen kanti akwai wani
garejin gyaran mota nan yake zuwa da yamma anan yake samun kudi anan Kuma ya fara Shan
taba, da Abu yayi gaba we aka fara bashi Wiwi Yana zuka, baka taba shi da robb da yake
shafawa a leben shi da Kuma namijin goro Dan kada kaji warinta. A hankali Malam ya fara
gajiyawa da halayen Junaidu se ya fara fita daga alamuran shi. Tun ranar da ya daki Suleiman
a ranar Malam ya fara tsoron Junaidu Amma dukda haka yana Masa fada Hajja Huwaila na ma
na kokari sosae Akan shi shiyasa ya daina zuwa gidan. Akwai lokuta da iyaye suke samun
matsala, itace tun Yana karami ake tankwara shi idan ya bushe zai karye, lokacin da Junaidu ke
fatali da kayan wasan Yan uwan shi ya kamata a tsawatar Masa Amma idan yazo ya nayi se
Hasiya ta dinga tafi tana cewa ga gwarzo yazo, yanzun zai baza yaran da basa son yin karatu
se Wasa kawia Suka sani, ko sun Kai kararshi Huwaila ce kawai zata lallashe su Amma sauran
matan se suce ai maganin fitsararru yakeyi. Wannan shi ne abinda ya bashi lasisin yin duk
abinda yakeyi, a unguwa ko ya daki Dan wani saboda Malam se kauda Kai, a makaranta baya
zuwa Amma form teacher batai reporting ba saboda tana ganin irinsu Junaidu rashin zuwansu
yafi zuwan su alkhairi. Kowa ya taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar shi, tarbiyyar Bata iyaye
kawai bace, ni na yadda cewar tarbiyyar duniya ita ce tarbiyyar, duniya makaranta ce kowa se
ta bashi ilimin da yake bukata.
AFIYYA is not free, pay 300 into 3091721807, first Bank of Nigeria. A'isha Hassan kwalam.
Send evidence thru 09063467258
Ayshatuuu.
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: AFIYYA
Three (Free)
✍️Ayshatuuu
Mutuwar Mama ta girgiza mutane da dama saboda rashin lafiyar da tayi ma ba kowa bane ya
San batada lafiya, it was very brief Amma da yake karar kwana ce se gashi ta rasu ta barmu ni
da Abbuna. He was completely shattered beyond imagination, har ya koma ga Allah Babu ranar
da baya cewa " da Halima nada Rai, Allah sarki Halima" maganar shi kenan, kullum Rana se ya
bani labarin ta sede idan baya gari ko bana nan. A luth ta kwanta aka Gama duk wani cike cike
da ya kamata sannan yayi booking flight within few hours suka dakko gawar zuwa Kano, kafin
mu karaso an turo Mana motoci daga Ringim Emirate council Wanda zasu tafi da gawar zuwa
inda dubban mutane ke jira a sallace ta. Abbuna yana rike Dani a kafadar shi tunda muka taho
nayi bacci bayan Nanny ta bani oat nasha. Muna zuwa danginta da suke nigeria duka sun biyo
flight zuwa Kano sun karasa Ringim, ita mamanta Bata gidan Kuma ita daya ta Haifa, asalin ta
Yar Ethiopia ce, so Bayan sun rabu da shehun borno ta koma kasarta, acan Bata wani Jima ba
ta rasu, so nidin jini da yawa ke bin veins dina. Ina baccin Nanny ta shiga Dani ta goya ni a
wañnan yammacin aka kaita makabarta aka binne ta. Abbu was devastated, kallon shi kadai zai
baka tausayi kowa yabin halayen kirkinta yake. Mutane da yawa kallon Abbu Dani ke saka su
kuka na tausayin mu. Tunda na farka a baccin aka bani abinci naci se na kankame Nanny dama
ni me kowa ce saboda ban Saba ganin mutane a gidan mu ba. Idan Naga mutane Kuma to se
na nanike mamata ko Abbuna, idan Babu daya se na nanike Nanny. Kwana uku mutane suka
baje yawancin zaman makokin Ina jikin Abbuna a kofar gida Dan naki Zama ciki, kowa se yaji
tausayi na. A Rana ta bakwai Bayan an gama adduaa aka raba gado, a cikin dangin Mama
Babu Wanda yace zai tafi Dani shima Kuma Abbu Bai yiwa kowa tayi ba, sun tafi suna ta jin
rashin dadin rasuwar Yar uwarsu. Duk yadda rayuwa zatayi Dole mutum ya cigaba da rayuwa,
duk wani bakin ciki da zaka dandana akwai ranar da zai wuce kaji kamar baayi ba. Bayan gidan
ya watse Hajiya tayiwa Abbu nasiha sosae Amma se yace Mata shifa tayi hakuri aure daya ne
Kuma yayi Amma