Showing 18001 words to 21000 words out of 101327 words

Chapter 7 - Afiyya Book Compelet Novels By Aishatu

Aishatu   

08 Jul 2026

166

kwalkwalwata is very sharp, kallonka kawai zanyi I can see through
you.
" To ayi karatu da kyau"

Na gyada Kai na juya na bi bayan su, makarantar da Dan tafiya daga Ausar haka mukaje a
kafa, kafin mu karasa ba karamar gajiya nayi ba. Ina zuwa mukaje office din principal ni da
Mino, ya dubeni yace

" Amma Malam Sa'idu baice min yarinyar karama bace sosae"

Mino ta dubeni ta kalla principal din Amma batace komai ba, Dan Bata San yadda sukai da
principal da kawu ba. Haka yasa ni a gaba ya kaini class, mutane da yawa a cikin class din,
banbancin dake tsakanin makarantar Dana Bari da wannan abin ba zai auni ba. Yace nayi
introducing kaina ma Yan class din na fada musu, sannan ya Samar min guri a gaba na zauna,
ya Kira wata Sauda yace ta Zama kawata. Na zauna a seat din Ina rarraba idanu a ajin. Yan
kusa dani sunata kallona yawanci mamakin kankanta ta suke. Ban Jima ba first period ya shiga,
wani malami ya shigo, duka muka tashi Dan gaishe shi ya amsa yace mu zauna, duka muka
zauna ya rubuta physics a board, anan na fara wondering kenan ss1 aka kawo ni, ni js3 Zan
Shiga fa!



Shatttzzzx
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Na Kara runtse idanuna Ina kokarin dadira wukar a wuyana,
many thoughts running through my mind, idan na kashe kaina kowa zai huta, tunda suna ganina
tamkar liability ce gare su to gwara kawai na kashe kaina zaifi sauki. Ina dirzawa naji wani irin
azabar zafi saboda wukar ko yanka albasa seka dirza balle kashe Kai, na yarda wukar na saki
kuka tareda durkusawa a gurin, se Kuma wani tunanin yazo min, idan na kashe kaina Allah a
wuta zai saka ni, Ina kallo Mama da Abbu zasu tafi aljanna, I can't be able to reunite with them,
ko Kuma Kawu Sa'idu da Ummaan su Mino da ta cuce ni suje aljanna ni da aka cuta saboda na
kashe kaina na tafi wuta! Da sauri na Mike Ina girgiza Ina fadin that's not possible I've to live, na
dauki wukar na fito tsakar gida, akwai wata tsohuwar rijiya a gidan na jefa wukar ciki, danma
kada na cigaba da ganinta suicidal thoughts din Yana zuwa min. Na koma daki na kalla kayana
se Kuma na fara tunanin ko dai na gudu ne? Na Shiga duniya kilan na samu wani Mai imanin ya
dauke ni! What idan na fada mugun hannu da yafi su Kawu Sa'idu? Na ayyana hakan. Zuciyata
se taci galaba a kaina, na bude trolley karama na dauki necessary na saka hijab, I've made my

mind I'm leaving this house. Na fito Ina zuwa zaure mukai kicibis da Yaya, ya tsaya Yana
kallona Nima Ina kallon shi, hawaye na sauka Kan kuncina, ya kalleni tun daga kasa har sama,
mamaki sosae a fuskar shi, ya bude baki zaiyi magana nayi saurin ketare shi Zan wuce Dan ya
Gama Bata min budget, hannuna ya kamo hakan yasa na tsaya Ina kicinayar kwacewa,
" Ina Zaki je Afiyya? Me ya faru dake? Me akai Miki?"

Duka a tare ya jero tambayoyin, na kwace hannuna daga tsatsauran rikon da yayi min, Amma
kafin na Kara daga kafata na bar gurin tuni ya rike hijabi na, jawo ni yayi har cikin gidan, inata
turjewa Amma seda ya maida ni, na tsugunna a kofar dakin Ina jin shima haushin shi nakeji,
kaina kamar zai fado saboda kukan da nakeyi, ga jikina dake ciwo.
" Kina ganin idan kin gudu shikenan kin Gama Shan wahala? How will you even think of this?
Wa Kika sani Ina Zaki je?"

" Ka rabu Dani na tafi, na gaji da wannan rayuwar gwara naje ko Ina ne tunda kowa baya
Sona!"

" Wayace Miki ba a sonki? Muna son ki mana, ni Rooks and your Nanny, you've to stay for us
kinji?"

Ya Jima Yana lallashina seda yaga na hakura sannan ya barni yaje ya siyo min abinci a wani
eatery ya kawo min naci sannan na shiga daki na kwanta wani bacci me nauyin gaske ya dauke
ni.



ISTANBUL, TURKEY


Daddy ya cire glasses din idanun shi, tamkar cire glass din zai Kara Masa karfin jin sakon da
yake amsa ta waya ne, Amma sede maganar da ake Masa tayi Masa nauyi a cikin Kan shi ya
kamata yama bada hankalin shi gaba daya akan maganar.


" So yanzun Kai a Ina kaji wannan labarin da kake fada min?"

Daga dayan bangaren yace

" Ranka ya Dade bazan iya fada maka ba Amma yarinyar tana cikin matsala, Alhaji Abubakar
Bai cancanci jinin shi yasha wahala ba, shiyasa na Kira na fada maka!".

" Wannan hakane na Kuma gode sosae!"


Wayar ya kifar ya Mike daga Kan kujera ya Isa jikin suit holder dake gefen shelf dinsa, ya
dauka ya zura sannan ya rike kugun shi ya fada tunanin Abbuna, haduwar su ta karshe a ringim
ne da sallah yaje gidan shi yake ce Masa

" Abubakar me yasa baka kokarin hada Afiyya da Yan uwan mahaifiyar ta"

Ya gyara Zama yace

"Mariya ta kawo karata kenan?"

Abbu yayi dariya yace

" Halima ta rasu, ta bar yarinya a kaida tunda princess karama ce to ya kamata su zasu dinga
nemanta, Yallabai Babu Wanda ya taba zuwa gidana da sunan sunzo sun ganta, to yazan
musu? Ita Mariya ai tana zuwa hutu Ringim, ko yaranku Bata taba turowa ba su ganta, me
yasa Bata taba cewa na kawo Mata Afiyya ba. Se yanzun zasui accusing Dina Wai na rabasu
da yarsu? Yallabai bazan dinga tura ta gurin su ba suna ganin kamar liability ce, Zan rike yata
duk ranar Dana mutu Allah will take care of her"


Daddy ya hargitsa kanshi Yana tuna wannan maganar, tabbas Abbu yayi gaskiya laifi Kam nasu
ne bana shi ba, ya tuna yayi ma Ummiey magana tace ita ba yadda zatai, shi ya kamata ya
dinga neman su Basu su neme ni ba. Runtse idanun shi yayi Yana tuno sakon da aka fada
Masa yanzun a waya cewar kwata kwata bana cikin jin dadi, idan ya ganni bazai gane cewa ni
ce ba. Cikin sauri ya tattara kayan da zai wuce dasu gida ya fito daga office din. Chauffeur din
shi na ganin shi ya karaso da sauri ya karba suitcase din hannun shi, ya bude Masa backseat
bayan ya shiga ya rufe, cikin turanci da accent din can yace

" Sir where are we heading to?"

"Drive me home!"

Daga haka ya karkata akalar motar zuwa hanyar gida, lokaci lokaci Daddy Yana picking calls
mostly office related calls ne. A yard din gidan yayi packing sannan ya fito ya bude mishi ya fito
da wayoyin shi a hannu Yana kashe su Dan kaidar shi kenan, Yana dawowa zai kashe wayar,
baya son stress. A parlor ya samu yaran dukka suna zaune, su hudu, babban shi ne sarki na
biyu me sunan shehun borno, na uku Harith se autar su Nadia. Gaba daya Babu Wanda yayi
aure, sarki ne ma ake zancen nashi da shehu, Amma Harith ba wani shekaru ne dashi ba balle
Nadia shekara biyu ta bani. Suna ganin shi Suka Mike kowa da murna kamar kullum Suka tare
shi, shehu ya karba suitcase din shi daga hannun chauffeur daya rako shi, bading din su yayi

sannan ya juya,

" Ina Umminku?"

" I'm here Darling! Welcome home"

Ta fada tayi kyau cikin gown da akai Mata ado da stones, fuskar ta tamkar an Ciro tata an saka
min, dama ance min Kama take da Mamana, Dan wasu Basu ma gane su saboda Kama, Nima
na yadda da hakan Dan akwai hoton su na biki a parlon mu da Kuma na ranar sunan shehu
Dana suna na. Fuskarta dauke da murmushi tace
" Ya aikin you look tired and worried"

Ya nufi hanyar dakin shi ta mara Masa baya yace

" Ganin ki ya warware gajiyar, lemme have a quick shower"

Ta gyada Kai tace ita Kuma zata dakko Masa Kaya kfin ya fito. Bayan sun Gama dinner sunyi
Hira da yaran Suka koma daki sukai Shirin bacci, ta zauna gefen gado hannunta dauke da
water bottle Tasha wasu pills sannan ta dube shi bayan ta Mata masauki akan bedside drawer
ta dube shi ya lumshe idanu ya daura hannun shi akan goshin sa, tasan mijin ta tasan idan yayi
hakan Yana cikin damuwa ne, hannunta ta daura akan hannun da ya daura akan goshin tace

" Darling how can I help you!"

Ya bude idanun shi ya tashi zaune ya dubeta, she looks disturbed also yace

" Mariya kin taba tunanin makomar yaran mu Bayan mun rasu kuwa?"

Da rashin fahimta tace

" Me ya kawo wannan maganar darling?"

" Kawai ki bani amsa"

Tayi shiru na Dan lokaci kafin tace

" Yanzun Babu zumunnci, ba kowa zai rike maka danka ba idan Babu ranka, gata da zaka ma
danka shi ne tarbiyya da ilimin addini da zamani"

Ya gyada Kai yace

" Akwai wayanda sun so suyi hakan Amma Allah Bai Basu dama ba. Kin taba tunanin Ina Afiyya

take?"

" Wacece Afiyya?"

Ya girgiza Kai wani haushi Yana Kara Kama shi yace

" Afiyya Yar Halima da Abubakar"

Tace

" Ooh ai Maryam ta tafi da ita NY ba?"


" You failed me Ummin Yara, Baki masan inda Yar Yar uwarki take ba, why? Kin manta tsakanin
ki da Halima ne? Afiyya Kun yadda ita Babu me nementa, wallahi Baku kyauta ba"

Tayi shiru ta kasa cewa komai itama once in a while hakan Yana damunta, takan tuno yarinyar
Amma ta rasa meye yake hanata nemanta.




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send
evidence to 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Na Gama Shirin makaranta, na kalli Nanny dake juya kayana
zuwa daidai nace

"Zan tafi makaranta, Amma ba yau Zaki tafi ba ko?"

Tace min

" Eh ba yau ba, kije ki karba abinci ki wuce"

Nace

" To Nanny se na dawo!"

Haka na dauki jakata na fito tsakar gida, wainar gero aka Miko min naci, nasha ruwa sannan
muka tafi cikin ayari. Nanny ta fito da kayan ta fara wanke min, Ummaan su na zaune tana tabe
baki dama tun can bawai su nayi da Nanny bane Dan hakan itama Bayan gaisawa da sukai
Bata Kara bi ta kanta ba. Tayi nisa a wankin Kawu Sa'idu ya shigo, Dan tun asuba yake fita,
yawancin se kowa ya tafi makaranta yake shigowa ya karya sannan ya Kara fita Kuma se dare.
Ni kaina bansan wanne irin aiki yake ba, zai fita dai ya dawo, su kule a daki su dinga zance da

baka San me sukeyi ba. Ta wanke hannun ta ta zauna kamar yadda ya zauna Yana fadin

" Fanta jiya an fada min kinzo, ban shigo gida da wuri ba"

Ta danyi dariya tace

" Har yanzun anan ana fitar dare kenan?"

Yayi dariya shima saboda Mamana tana da Rai takan ce Masa Wai me yakeyi a waje ya Dade
har cikin dare? Se yace mata shi baya son sa idanu.

" Nazo Naga yata, har an saka ta a makaranta, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci!"

Yayi murmushi jin Dadi yace

" Fanta dama Ina Neman ki, naso har karshen sati naje maiduguri na sameki"

Nanny ta gyara Zama tace

" Akan me fa?"

" Akan dukiyar Afiyya ne, bakya ganin ni ya kamata ace nake rike da dukiyar ta tunda ni ke rike
da ita?, Amma yaronnan Babawo sede kawai duk wata ya turo min kudi na kula da ita..."

Nanny mamaki ya karu Akan nada, dama tunda yace zai rikeni tasan tabbas dukiyar da Abbu
ya barmin yake yiwa, to Amma batai Yi tunanin zai iya fallasa abinda yake ji ba.

" Wai kana nufin shi Karamin Alhaji Bai baka komai ba?"

" Inafa ya bani Fanta? Maryam ce zata Bari ya bani. Tabi ta kankane komai, ni nake wahala da
yarinya Basu ba"

Nanny ta sauke ajiyar zuciya but ya kamata tasan me yake faruwa, hakan yasa tace

" Basu kyauta ba, ai tunda Kai ke rike da ita ya kamata komai nata ace a hannun ka yake, ya
kamata ace komai Kai kake kula dashi"

Yayi tsaki irin na bacin Rai dinnan yace

" Lokacin da akai rabon gado, akwai kadarori wajen uku da yace kada a taba ta Afiyya ce ta
makaranta, da wani gida da Kuma wata gona se gidan Mai a Kano, Babawo ko takaddu gurin
Bai zo dashi ba, ganin sun tubure ba zasu bani komai ba yasa nace musu kawai sede duk wata
su dinga aikon da kudin ciyar watta, shi ne nake tsira da wani abun fa!"

To bansan me Nanny ta yiwa kawu ba da har yayi trusting dinta yake bude Mata cikin shi bayan
Kuma daga Ummaan su matar shi Babu Wanda ya taba fadawa abinnan, Nanny ranta ya
mugun baci, ta rasa ya zata kwantata son zuciyar Kawu Sa'idu, ya takura se ya rike ni, hatta
kudin abincin da ba wani abincin arziki ake bani ba se an biya shi, wannan wanne irin rashin
zumunci ne, Bayan tasan lokacin da nawa uban nada Rai yayan shi da komai nasu shi ke
dawainiya dasu.

" Fanta so nake ki lallaba su ko gidan man ne a bani, nasan dukka kowa na ganin girman ki, ke
kika go kowa sanin abinda yake akwai, gidan Mai ya dawo hannuna, na Miki alkawarin Zan
dinga fitar Miki wani Abu a ciki"

Nanny tace

" Wannan ba matsala bane, Dana koma zanyi magana da karamin Alhaji"

Ya Mata godiya se tace Masa

" Me yasa Afiyya baka maida ta can makarantar ta Abuja ba? Bayan suna baka kudin
makarantar ta"

Yayi dariya yace

" Makaranta ai makaranta ce Fanta, ko Ina aka kaika zakai karatu, kinji tsadar makarantar ne ai
wannan almubazzaranci ne"

Hawaye Suka taru a idanun ta tayi saurin shanyewa ta koma aikin ta, shima ya Shiga ciki Yana
jin burin shi Yana daf da cika.


Kamar yadda teacher na zaure yayi ma su Junaidu alkawarin da zarar ya cika sharudda
ukunnan to kuwan zai ga aiki da cikawa, Yana gamawa ya fice zuwa inda yake koyar aiki, yayi
aikin shi se ya tafi majalissar su ya zauna, ya samu dukka suna gurin Dan kaida ce duk
yammaci se sun hadu a wañnan gurin. Suna ta Hira suna dariya Malam da Jarma na zuke
zuken abinda suka Saba, shi Junaidu ya rage sosae saboda dama influence din su ne, Amma
huzaifa Bai ma taba zuka ba shikam Malam he's always the lead. Bayan an gama maghrib
kowa ya Kama gaban shi. Fatima ce da girki tun karfe hudu ta kammalla haka take badai kaga
tayi Daren girki ba. Ruwa ta tafasa ta shiga wanka, tana watsa ruwan taji wani kaikayi a duk
inda ruwan ya sauka, ta dubi jikinta gurin yayi jawur tamkar ta kone, a gigice ta dubi ruwan tasa
hannunta Amma shima hannun tana fito dashi se kaikayi yayi jawur, zani ta daura ta fito a guje
tana kwalawa Hajja Huwaila Kira, kafin Hajja ta fito tuni Hasiya ta fito ta same ta tsakar gida
tana faman sose sosen jiki, Hasiya tace

" Fatima ya akai?"

Ta kasa magana se nuna Mata take da hannu, tana Susa, lokacin Hajja ta fito itada Amarya
suka samu Fatima tana Neman cire zanin jikin ta, ga yaran duk sun zagaye ta wasu a ciki na
kuka, hannunta Hajja ta kama Suka shiga daki, Suka fara duba jikinta, duk inda ta Sosa yayi
burdi yayi Kuma kwaf kwaf kamar konuwa. Hajja ta Yi shiru Dan ita ta rasa abinda zata ce tunda
take Bata taba ganin abin ba, ta dauka hijabi tace da Hasiya

" Ke ki zauna da Yara, ni Kuma da Amarya zamuje general, ki aika a fada ma Malam"

Da hakan Suka Taya Fatima ta shirya,suka samu Keke napep Suka tafi general, kowa idan aka
bude gurin gani suke allergy be hakan yasa focus din maaikatan asibitin, sede ana
administering drugs din kamar bama shiga suke ba, in fact tunda jikin ba bukatar su yake ba
kokarin reacting musu take. Anan Malam yazo ya same su, hankalin shi ya tashi ganin
maaikatan sun ce sede su turasu AKTH suga dermatologist kawai, Malam ya karba takardar, ga
Fatima ciwon se Kara Hawa take, se ihu take tana Kiran sunan Allah tana su taimaka Mata
kaikayi zai kasheta.



A wannan Daren da Junaidu ya dawo ya samu gidan tamkar gidan makokin, yaran na tsakar
gida sunyi jugum, Wanda sukai kuka zuwa lokacin sun hakura, Bai bi ta Kan kowa ba ya shige
dakin abin shi ya zauna Yana ayyana ya kamata ace zuwa yanzun aikin shi yaci Akan Fatima,
tunda kuwa Jarma yace Masa tamkar yankan wuka haka aikin malamin yake, Yana cikin zaune
Sega zainab ta leko, tunda sukai abin kudinnan yarinyar ke shishigge Masa tana son ganin ta
wanke laifin ta. Yana zaune ta shigo ya dago ya kalleta yace

" Meye?!"

Ta zauna tace

" Mama ce Bata da lafiya!"

Ya gyara Zama yace

" Me ya sameta?"

Ta zauna tana kuka ta fada mishi komai, maimaikon taga ya canja yanayin fuskar shi zuwa
tausayi, se taga Yana murmushi, yace

" Abin yazo kenan! Kije zata ji sauki"

Zainab

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login