Showing 24001 words to 27000 words out of 101327 words

Chapter 9 - Afiyya Book Compelet Novels By Aishatu

Aishatu   

08 Jul 2026

169

Ni zanyi magana kiyi min tsaki? Meye nufin ki"

Itama cikin daga murya tace

" Ya bazan maka tsaki ba, duk kokarin da nake ganin mun cimma burin mu Amma Kai baka
gani?! Meye zaka dinga tsorata Bayan munyi da Kai aure zaa Mata da Wanda yafi kowa munin
Hali a duniya, yadda ba zata taba fahimtar potentials dinta ba! Ka barta tayi ta karatu bazai taba
Mata amfani ba, Bayan haka aure a shekara goma Sha biyar zaayi mata, Kai dai Yi kokari kaga
ka samu yadda zakai ka juya zuciyar da tunanin Yan uwan ka!"

Kawu ya sauke ajiyar zuciya, ya kalleta with adoration yace

" Kina da kwakwalwa! Kinsan wannan satin dukka zasu zo saboda kamawar December, anan
Zan samu na Gama kullin da ya kamata nayi!"





Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send
evidence of payment through 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 18


Babu jimawa Dan ko sati baayi ba na fara exams dita, ana gamawa na daina zuwa, haka
Ummaan su tace mu daina zuwa gwara mu zauna a more mu a gida. A wañnan lokacin Babu
wani aiki na gida da ban iya ba,gaba daya na canja from the butter Afiyya to a house help,
wanki ma da nake ganin wahalar shi shima na iya sosae Dan har nata take bani nayi Mata,
ayyukan dake sani wahala duk na daina jin wahalar su tunda na riga na sawa Raina sun Zama
dole, Dole se nayi Dan hakan Babu amfanin na dinga Bata Rai na a banza. Rayuwa sosae take
canjawa Kuma indai Kai mutum ne dole ka karbi wannan canjin da yazo maka.

Ranar da zaayi hutu ranar zamuje karbar result din mu Kuma a wañnan ranar Rooks tace min
zasu taho daga NY, Dan hakan fuskata kawai zaka kalla kasan Ina cikin madaukakin farin ciki.

Na Gama shiryawa na fito tana zaune kofar daki kamar yadda ya Zama kullum nan take zaune,
tana bin gidan da kallo, ta kalleni tayi tsaki Wanda yasa na juyo fuskata dauke da murmushi,
tace

" Daina kallo na se kace mayya, da wasu kumatun ki a gurin masu lotsawa"

Maimaikon naji haushi se na Kara sakin murmushi Wanda ya bayyanar da hakorana, ta mike
zata kawo min duka nayi saurin gocewa tayi tsaki ni Kuma nayi saurin ficewa Ina dariya, Yaya
na samu tsaye shi da Mino a kofar gida, idonta yayi ja da alamu kuka tayi, shi Kuma fuskar shi
na nuna lallashi, ganin su a wañnan yanayin se naji Babu dadi ban Kuma tsaya ba kamar yadda
nayi niyya, se Yaya yace min

" Ba magana?"

Na juyo Naga Mino na Mana wani kallo se na dauke kaina nace

" I saw you guys talking shiyasa!"

Ya harareni yace

" Ke na zauna jira, Ina son muyi magana kafin ki tafi, shi ne kin fito zakiyi tafiyar ki?'

Na tsaya tareda daidaita tsayuwa ta nace

" Yaya! To gani ai"

Ya matso gefena, we were so close da har Ina iya jiyo kamshin turaren shi me sanyi, kodan
saboda idan naji kamshin Ina jin sanyi cikin Raina ne shiyasa nake jin sanyi ne dashi. Ya fara
tambayata ko naci abinci? Saboda yasan ba lallai an bani ba, nayi murmushi Ina kallon shi nace

" I ate, ka barni naje sauri nakeyi"

For that mean time mun manta Mino na tsaye, ita Kuma se kallon mu take bakin ta a bude,
tasan we're close Amma batayi tunanin closeness din mu yakai haka ba. Nayi gaba shima ya
biyo bayana, haka muka jera Muna tafiya Yana ta min hira se Naga within shortest of time har
mun karasa makaranta, lokacin an baje se kalilan dake zuwa karbar result din su, Ina karasawa
class teacher din mu yace

" Amina Baki zo da wuri ba"

Na langwabar da kaina nace

" Sir kayi hakuri"

Ya gyada Kai na gaishe shi sannan Suka gaisa da Yaya, ya Mika masa result yace

" Tayi kokari sosae na gaske kuwa, idan akwai abinda yafi na daya tabbas Amina zata dauka,
she sure is an asset!"

Nayi murmushi Ina jin dadin praises dinsa, Yaya ya Masa godiya sannan muka juyo, ya dubeni
da idanun shi da Suka washe tas daga Jan da sukai dazun, sunyi haske har wani maiko maiko
suke, he looks so happy Wanda yasa naji kamar banida wata damuwa se kallon fuskar shi da
murmushi yaki daukewa akai!
" I'm proud of you!"

" Thank you"

Se Kuma mukai shiru kawai muna tafiya a hankali, iska na kadawa kadan kadan duk zafin garin
Ringim Babu Sabida sanyi ya fara shigowa se bishiyo Yi dake kadawa! A Haka muka karasa
gida zuciyar mu tamkar an Mana bushara saboda kallon mu kawai zakayi kasan farin ciki na
dawainiya damu. Tun daga nesa naga mutum ya juya baya, gabana ya yanke ya Fadi I can
swear tamkar statue din Abbuna ne a tsaye, hatta tsayuwar jikin da komai tamkar na Abbuna,
Yaya ya dubeni yace

" Kinga Uncle Babawo! Let's go to him"


Na dauke kaina na cigaba da tafiya ta a hankali tamkar kwai ya fashe min a ciki, Bai lura da
yanayin da nake ciki ba ya karasa gurin da Uncle Babawo ke tsaye ya rike hannun sa, Ina
hango tsantsar farin cikin da yake ciki na ganin kawun shi. Yana juyowa muka hada idanu dashi
ya saki hannun Yaya ya nufo ni fuskar shi dauke da farin ciki, he looks so much like my Dad, se
naji fushin da nike dashi bazan iya cigabawa ba, na nufe shi da gudu Amma Kuma se na kasa
rungume shi na rike hannayensa and I found myself crying, yayi shiru yana bubbuga bayana
Yana fadin

" Ya Isa! Shiyasa tuntuni naki zuwa saboda banason na ganki kina kuka, ya Isa I'm sorry kinji?"

Na gyada Kai na, na fara share hawayena se Kuma na fara dariya Ina gaishe shi, ya dinga
kallona daga fuskata da ta canza sosae zuwa kayan dake jikina, ya dubi Yaya yace

" Daga Ina kuke Haka?"

Nayi sauri nace

" Naje karbar result Dina ne, dama bansan wa Zan nunawa ba, class teacher din yace nayi

kokari sosae"

Ya gyada kan shi ya karba result din Yaya ya shige gida, he went through everything sannan ya
shafa kaina yace

" I'm proud of you my Baby. So bani labarin Ringim"

Nayi shiru bansan me zance Masa ba, zance Masa abincin da zanci ma wahala yake min, ko
Kuma Zan fada Masa tamkar Yar aiki haka nake a gidan riko na. Na girgiza Kai nace

" Nasan yanzun kazo, idan ka huta I'll gist you"

Ya gyada Kai na Mike na Masa sallama na bar shi da result din a hannu Yana kallona har na
shiga gida, Ina shiga na samu ana gyaran kayan Miya, nasan saboda Baki yau zaayi Miya


" Gidan uban wa Kika tsaya? Baki San kinada aiki a gida ba ko?"

Naji muryar ta daga gefena, bance Mata komai ba nasan zuwa lokacin ta Saba da wannan halin
nawa tunda akan shirun da nake Mata bazan iya irga sau nawa tana kaimin hannu jikina ba,
Amma anjima idan ta Kara min irin haka ko kallon ta bazan Yi ba Amma Kuma Zan Yi abinda
tace. Kamar lokacin se na shiga daki na cire uniform Dina nazo na daura shinkafa, kafin ta dahu
an kawo markade, nayi Miya Ina jin kamshin na duka na, se naji yunwar da nake ta dannewa ta
taso min, naji Yunwa nake ji Amma se na daure na koma daki har lokacin da zaa bani nawa.
Mino na zaune Itada Siyama suna hirar bikin da dudduba Kaya, na kwanta Siyama tace min

" Afiyya ke baayi Miki ankon ba? Ki fadawa Uncle Babawo tunda yazo"

Nayi murmushi kawai bance Mata komai ba, to me zance atamfa falle biyu an kasa min bayan
da dukiyata aie cin abinci. Bayan sallar laasar Ina cikin tuka tuwo naji sallama a bakin kofa, cikin
sauri na Mike Dan Babu tantama muryar Rooks ce, tana ganina ta taho da gudu tana sakin ihu

" Afeey darling!"

Na rungume ta a jikina Ina fadin

" Rooks darling welcome"

Ta sakeni tana Kare min kallo na samo Mata kujera ta zauna gefena ni Kuma Ina tuka tuwo, ta
kalleni tareda matsar da kujerar ta tace

" Baki jin zafi? Bazan iya Zama anan ba"

Ta tashi ta koma can nesa Dani, nayi murmushi Ina tuna da can lokacin da nake da gata ko
suya ake a kitchen bana shiga Wai kada ya fallatso min, gani a gaban murhu Ina tuka tuwo.

" Ya hanya? Ina Mummy?"

Tayi murmushi tace min

" Mummy da zamu taho tare se tayi bakuwa, matar yayar Abbah ce tazo wannan ta Istanbul din"

Bansan ta ba Amma Ina jin ta a bakin Rooks, na gyada Kai muka fara Hira har na Gama kwasar
tuwon, ta rkeni idanun ta sun kada tace

" You do all this everyday?"

Na langwabar da Kai nace

" Yeah! And I'm fine our little secret darling"

Na fada Ina Mata wink, ta biyo ni daki hannuna cikin nata, anan taga su Mino Suka Mata
magana ta gaida su sannan tace min

" Me yasa komai se kice it should be secret, you are suffering fa"

Nayi dariya na dauki hijab na fito Dan tun safe Kawu Sa'idu yace idan Mummy tazo na tafi gidan
ta. Na fito Ummaan su ta fito ta dubeni, wani skirt da riga ne a jikina ya dage saboda jikina ya
fara karbar hormonal changes, atamfar tare Uncle Babawo yayi Mana da Rooks wani zuwa da
yayi, Ash ce Kuma kunsan atamfa Ash nada saurin kodai so duk ta kode,
" Ki wuce ki canja Kaya, ki saka na wannan akwatin naki"

Na juya nace Mata

" Ai duk kin daukar wa hafsa, saura kadan Zan saka da biki"

Ta daka min tsawa Rooks tayi gasping saboda tsorata da tayi ta kalleni taga ki gezau banyi ba ,
na koma na dakko wata atamfar blue na saka na fito muka tafi.

" Afeey Dan Allah haka kike rayuwa? Kingan yadda Kika koma kuwa? Nidai gaskiya Zan Fadi
gaskiya"

Na girgiza Mata kaina nace

" Zan daina yadda dake, idan na fada me Zan canja Rooks? Bazai canza komai ba sede bacon

rai, Nanny tace min watarana komai zai wuce and I also believe in that!"

Hakan Dana fada se yasa tayi shiru kawai muka cigaba da tafiya har muka zo gida, a parlor
mukaa samu wasu Yan samari suna zaune, tunda muka shiga hankalin su ya koma kaina,
Rooks ta karasa tana fadin

" Yaya nd Yaya shehu sannun ku da zuwa!"

Suka amsa Mata, ta dubeni sannan ta dube su tace

" My cousin Afiyya"

Na gaishe su Suka amsa da murmushi a fuskar su, dayan ya gyara Zama Yana kallona da
niyyar yimin magana se ya fitowar mummy da bakuwar ta ya katse mu

" Abin kunya ai naku be da Baku San inda yarinya take ba, dangin uwa da aka sansu da jin Kai
Amma ku kuka Yi fatali da yarinya marainiyar kwaya daya, abin kunya akanki ya Kare Mariya"

Mummy ta fada tana huci

" Nidai na fada Maryam, Kun kasa rike yarinya kwaya daya Kun barta tana watangaririya a
Ringim, kunci amanar zumunci.."

"Ku me kuka ci! Ke kin Isa ma kiyi zancen zumunci, kinada Baki? Ai Baki da bakin fadar
wannan"

Duka muka Yi shiru muna kallon su, ni ba maganar su nakeji ba se kallon matar da ke ta kumfar
Baki nake, so nake na tuna fuskarta, why does she look so much like me? Babban Wanda shi
ne Sarki ya karasa gefen mahaifiyar shi ya rike hannunta Yana fadin

" Ummiey ku Bari Mana Dan Allah, mu tafi"

Ta kwace hannunta tana fadin

" Zaki San ni Kika fadawa magana Maryam"

Mummy tayi tsaki tace

" Kije da borin kunyar ki dai!"

Ni ban taba ganin manya na fada ba, se Naga scene din banbarakwai, ta juya tana huci ko lura
batayi Dani da nake tsaye ba, tana fita shehu ya bi bayanta, na zauna Ina gaida Mummy wadda
lafiya kawai tace min tana kuka, Rooks ta dawo gefena ta zauna idanunta sunyi ja itama, waya

ta dauka ta fara fadin

" Babawo kazo ka sameni Ina gida, ku taho da Tijjani yanzunnan. Afiyya ta gama Zama gidan
Sa'idu tunda shi Maci amana ne!"





Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria. Send
evidence of payment through 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 20



Kamar yadda yayi min alkawarin cewar zai zo da yamma hakan ce ta faru,sede shi kafin yazo
Yaya ya riga shi zuwa. Muna daki ni da Rooks ni Ina kwance Ina kallon frozen cikin system ita
Kuma tana ta ciye ciye. Me aikin su ta kwankwaso sannan ta shigo tace Mana a parlor Yaya
yazo. Nayi saurin mikewa Wanda yasa Rooks kallona tace
" Meye abin sauri kamar Zaki Fadi?"

Nayi murmushi nace

" Ba Dadi jira"

Ta tabe baki ta cigaba da tauna popcorn din da take ci, na zauna Ina yarda hijab din hannuna
nace

" Rooks naaa! Muje Mana"

Ta kalleni tana murmushi tareda fadin

" Ban taba ganin kina gaggawa akan Abu ba"

Ban ce d ita komai ba na zura hijab dina na nufi kofar fita a bedroom din, tayi saurin mikewa ta
biyo bayana, a parlor muka same shi an jera Masa drinks kamar wani bako, Mummy dama ta
fita tun dazun ta Shiga fada, kamar yaji footsteps Dina ya juyo ya zuba min idanun shi , na Dan
kalleshi briefly Ina murmushi sede idanun nashi bazan iya kalla na tsawon lokaci ba, Zama nayi
har lokacin I felt his eyes akaina nace

" Yaya tun jiya baka zo ba?"

Ya danyi murmushi yace

" Haba dama kina nemana ne?"

Na tura bakina Wanda yasa shi dauke Kai ya maida Kan Rooks dake faman tambayar Ina yaje
tunda tazo Bata ganshi ba. Nan muka hadu munata Hira wadda mostly ma shida Rooks dinne,
se shi ne yake sako ni a ciki. Mun fi minti talatin se ga sallamar Yaya shehu, na daga idanuna
Ina kallon shi, he looks so much like baban su Rooks, kana kallon shi ba se an fada ba kasan
he's a royalty, tafiyar shi ma kawai cikeda Isa yake yinta, a fuska zakaga tamkar Yana da girman
Kai Amma idan ka zauna dashi zakaga ko kadan he's simple as what you can't imagine,
kyakyawa ne musamman idanun shi Dan ni dai su suka fi burgeni dashi, se Kuma leben shi.
Kullum idan Yana magana lips dinsa kawai nake kallo yadda yake motsa su a hankali. Yana da
tsawo kana kallon shi zakasan Yana zuwa gym yadda abs dinsa ke fitowa musamman idan
kayan jikin shi sun Kama shi, he's a man to kowanne gaba. Muna hada idanu ya sakar min
murmushi, na mayar masa har ya zauna ya bawa Yaya hannu suka gaisa, Rooks tace

" Ya shehu wannan sunan shi Yaya, gidan su Afiyya yake Kuma cousin dinmu ne"

Ya Shehu ya saki fuska ya Kara Mika Masa hannu a Karo na biyu suka gaisa, Rooks ta dubi
Yaya tace

" Yaya Shehu, Afeeys' cousin and also my cousin!"

Yaya ya tsira Masa idanu kamar zai ce wani Abu kawai se ya Mike, Ina ganin hakan Nima na
tashi Ina fadin

" Yaya tafiya zakai?"

Ya gyada min Kai yace

" Ai Naga kunyi bako, Zan dawo anjima"

Banji dadi ba Sabida ganin shi ma ko bazan Yi magana ba nutsuwa yake saukar min, Haka Ina
kallo ya tafi na dawo na zauna Ina duban Ya Shehu da yake kallona admiringly yace

" Afeey Babu magana! Ko na tafi I'm not welcome?"

Na girgiza Kai na zauna na gaida shi, ya Bata fuska yace

" Seda ma na roka"

Na danyi shiru Ina kyabe fuskata kamar zanyi kuka, yayi dariya wadda tasa na shagala Ina
kallon shi yace

" I got you exactly where I wanted to! Wasa nake come on bani labari"

Nima se nayi dariya na gyara zamana nace Masa ni banida labari, se yace min zai bani Mai
dadi, Rooks dake gefe tace

" A'a ya kamar Kun manta Dani ne?"

Ya kalleta Yana harar ta da Wasa yace

" Shut up my Friend! Tashi anan"

Haka ta Mike Ina Mata dariya tace Masa ita tafi son Sarki tasan da shi ne bazai taba korar ta ba
not ever, yace yaji taje, abinda na lura dashi they're close gaskiya sun Kuma Saba sosae.
Tunda ta tafi se mukai shiru se shi yace

" Ok tell me, me yasa Baki taba Neman Ummiey ba"

Se na kalleshi sannan na dauke kaina daga kanshi nace

" Ta Yaya Zan nema ta bayan ban santa ba!"

" Hakane Kuma! I hope kin yafe musu?"

Nayi dariya nace

" Basuyi min komai ba fa! Stop making it sounds somehow"

Ya gyada Kai. Kwanaki suka cigaba da tafiya kullum Yaya Shehu se yazo Haka Yaya sede Basu
Kara haduwa ba, idan Yaya yazo se yayi ta complain shi baya son yawan cousins gaskiya,
ranar har na Dan ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login